Cuta ta Dau Cuta Hausa NovelHausa Novels

Cuta ta Dau Cuta 23

Sponsored Links

*_Typing_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_ _

 

_Shafi na ashirin da uku_

___________

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA…_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE_

___________

…….Tsaff ta basu labarin komai da ya faru tun daga randa suka bar gida har ɗaura aurensu zuwa samuwar cikinta da yayta zubewa dama daina samuwarsa duka. Shigowar al’amarin Kainaat da ya zame mata wata fitila data haska mata hanya a yanzu. Turke Dafeeq da tai da dukan da yay mata zuwa tsintar kanta da tai a titi bayin ALLAHn da suka kawota gida suka taimaketa. Komai bata ɓoye musu ba. Duk dauriyar Baba sai da yaji hawaye sun cika masa ido. Sai dai kiran sallar asubahi da aka fara ya sakasu kasa cewa komai dole duk suka miƙe domin ɗaura alwala kamar yanda Baban ya basu umarni. Kasa haƙuri Mama tai dan tana tsoron shiga ɗaki Khadijah ta sake tunanin jefa kanta a rijiya. Anan baranda ta shimfiɗa sallaya domin yin tata sallar yayinda su kuma suke cikin ɗakinsu. Baba da Kamal kuma sun fice massalaci……

__________★

Maman Dafeeq data rangaɗa sallama a waya batare da jiran Dafeeq ya amsa ba ta cigaba da maganarta a ƙugule Kainaat na saurarenta. “Duk inda kake kazo gida a gobe, dan wannan shegiyar yarinyar daka jajibar mana a cikin zuri’armu ta dawo gida tace ƙarya kake baku rabu da juna ba. Hasalima raunikan data dawo dasu a jikinta na duka kaine kamata su ka kuma zubar mata da ciki. To nadai taƙaice maka zance yanzu haka nasa an kulle ubanta saboda yasa yan uwanta biyoni da makamai wai su kashe ni. Dan haka kazo maza muna nemanka ni da Babanka dan wannan sharrin datai maka sai an zauna kotu. Wlhy bazamu yarda ba. Kama taho da matarka ƴar arziƙi irin albarka dan tai maka shedar itace matarka a yanzu ba shegiyar ba. Ato kaji sai kai azamar tahowa”.
Ɗiff ta yanke wayar tsabar bala’i da ke cinta bama ta gama tantance dawa take wayar ba. Harga ALLAH Kainaat ta razana da mamakin wai Khadijah na gidansu Kano. To ta yayama akai ta iya tafiya a wannan yanayin? Wama ya bata kuɗin motar tafiyar to?. Koda yake ita miye nata ma. Ai wannan wata damace itama gareta da zata jijjiga rayuwar Dafeeq. Murmushi mai ƙayatarwa ta saki, tare da saka wata number ta rubuta text message. Tana turawa ta goge shi akan wayar tana sakin wani lalataccen murmushi. Kafin a fili ta furta, “Yaro mu zuba mu gani. Ni da kai ɗan halak ka fasa, dan CUTA CE TA ƊAU CUTA…” daga haka ta fita a ɗakin, wayar ta maida a inda ya barta ta haura sama itama…..

___________★

Kamar yanda jami’an tsaro suka buƙata an maida baba police station. Sai dai yanzu ba’a kullesa ba an dai yi shirin miƙasu kotu ne. An gama komai suna shirin barin station ɗin ne sai ga wani maƙwafcinsu da baƙi a mota. D.p.o ya bada umarnin a shigo da su. Shi dai baba koda suka shigo kallon rashin sani yake musu, sai da Khadijah da kanta ke ƙasa tana hawaye ta ɗago ne cikin zabura ta ce, “Baba Hakimi! Baba Harɗo! Aunty Mariya”.
Murmushi duk suke mata, yayinda aunty Mariya ta buɗe hannu alamar tazo gareta. Babu musu Khadijah taje ta shige jikinta tana kuka mai ban tausayi. Sun jima a haka sannan suka kai zaune bisa umarnin d.p.o, daga haka aka fara gaggaisawa. Iyayen Dafeeq dai nata harare-harare tunda suma basu san su Baba Hakimi ba a zahiri sai dai a labari wajen Dafeeq. Shi kuma bawai ya taɓa zama bane wajen sanar musu komai akan alkairin su Baba Hakimi garesu. Bayan an lafa da gaishe-gaishe Baba Hakimi ya sanar musu shi wanene da dalilin zuwansa nan ɗin…
“A jiya da dare wani yaro ya samemu da zance akan Khadijah da mijinta. Al’amarin ya bamu mamaki dan bamu san mike faruwa ba duk da kuwa suna a ƙarƙashin kulawarmu ne. Da farko zan fara da bama iyayensu haƙuri akan kasa maidosu gida tun a lokacin da suka zo garemu kam mu ɗaura musu aure. Munyi hakanne saboda gudun kada mu dawo dasu su sake wani takun guduwa tunda sun ƙudiri aniyar hakan dan dan yau ka haifesa ne baka haifi halinsa ba, shiyyasa na ɗaura musu auren na kuma katangesu a kusa da ni duk da nakan basu shawarar ko zasu koma ɗin amma suce ba yanzu ba. Na barsu ne har zuwa lokacin da zasu ji babu wannan zaƙin soyayyar dake ɗibarsu ta ƙuruciya. Zasu fi sanin muhimmanci da martabar kuskuren da suka tafka fiye da su dawo a sanda suke jin zaƙin soyayyar. Tabbas gaskiya ne Khadijah matar Dafeeq ce kuma ni shaidane da mutuncinta taje gareshi kamar yanda iyalina suka sanar dani, hakan ya ƙara ma bani ƙwarin gwiwar rungumarsu dan na fahimci wautar ƙuruciya da son zuciya irin ta yaranmu na yanzu ya fisgosu aikata abinda suka aikatan. Amma alhmdllh tunda ma aure sukai tunanin suyi bawai wata masha’a ba kamar yanda wasu yaran kanyi domin neman mafita…….”
Tsaff ya kwashe komai ya sanar musu tamkar yanda Khadijah ta faɗa a gaban su baba, ta kuma sake maimaitawa a gaban su D.p.o yanzu babu jimawa. Tunda Baba Hakimi ya fara magana babu abinda Baba ke saki sai ajiyar zuciyar sake samun nutsuwa. Yayinda iyayen Dafeeq suka birkice da borin wai ƙarya ne duk shiri ne. Dan haka a take sukai kiran Dafeeq a waya suka sanar masa…

________★

Lokacin da kiran ya shigo masa yana gida kwance a falo, dan gama sa’insarsa da Kainaat kenan ta dinga masa dariya da faɗin ya gama da matsalar gabansa sannan yazo su ɗaura daga inda suka tsaya tai shigewarta. Shine ya kwanta a wajen yana tunani da nazarin son gano inda maganarta ta dosa. Kamar bazai ɗauki kiran ba sai kuma ya ɗaga. Jin abinda mahaifinsa ke faɗa kaɗan ya rage ya wantsalo ƙasa da ga kujerar. Baima san ya lailayo wata bagidajiyar ashariya ba da faɗin, “Baba Hakimi tare da Khadijah a Kano?”.
Kafin Baban nashi ya bashi amsa d.p.o ya amshe wayar. Cikin bada umarni yace yazo Kano suna buƙatar ganinsa daga nan zuwa gobe. Zai kuma riƙe iyayensa a station ɗin har sai yazo. Bai jira cewarsa ba ya yanke kiran. Matuƙar tashin hankali Dafeeq ya shiga kuwa. Duk ya wani gigice da ruɗewa kamar wanda ya zare. Kuma shi a karan kanshi bama zai iya fadin abinda ya sakashi ruɗewar ba ma dan bai taɓa hasashe ko tsammanin Khadijah zata iya sanarma su Baba Hakimi abinda ke faruwa ba balle komawa gida a wannan halin, sakamakon imani da yay da ɗunbin soyayyar da take masa…..

__________★

“Kamar yanda nai alkawarin sanar muku wacece ni? Sunana shine Alimah kamar yanda kuka sani. Sai dai ni ba mutum bace kamar yanda kuke tunani…”
Babu wanda baiyi zaburar firgita ba a ɗakin, itako cikin rashin damuwa ta cigaba da faɗin, “Kamar yanda kuke rayuwa a gidajenku haka muma wasu a cikinmu nan ɗin ne wajen rayuwarmu. Dan haka na kasance ɗaya daga cikin masu rayuwa a gidan su Anoosh. Na shigo rayuwar ɗanku ne dan rama cuta da cuta. Saboda na fahimci bazai daina abinda yake ba cikin sauƙi. Na tsara shiga rayuwar ƙanwarsa Rabi’ah ne domin cimmasa ta inda bai zato ko tsammani ba. Dan haka ni da shi *_CUTA CE TA ƊAU CUTA_*. Abinda nai masa a baya kuma ba komai bane face sharar fage. Dan sai na sabauta rayuwarsa fiye da yanda ya ruguza ta ƴaƴan jama’a. Sai na bar babban gargaɗi wa ƴan baya masu irin halinsa a kansa ta yanda idan suka tinashi zasu shiga hankulansu yayin aikata makamancin abinda ya aikata. Dan haka JJ muje zuwa mataki na biyu dan yanzu ne wasan zai fara na gaskiya tsakanina da kai”.
Wani irin gigitaccen ihun tashin hankali JJ ya buga, jikinsa na wata irin jijjiga da magiyar dan ALLAH tayi haƙuri, ya tuba ya tuba ta taimakesa tayi haƙuri. Ina ko saurarensa batai ba tama ɓace ɓat a ɗakin. Daga iyayensa har ƴan uwan nasa suma a rude suke ta yanda bama fahimtar ihunsa da magiya suke ba. Dan tuni wasu ma sun bar ɗakin a guje. A ƙanƙanin lokaci labarin JJ ya fara zagaye anguwa da ga bakin waɗanda suka jiyo komai a gidansu. Dan danan ko’ina ya ɗauki zance, har aka samu mai ƙarfin halin zuwa anguwar su Anoosh ya fesa labarin da ya zarce cikin anguwa ya fara zagaye gari har kunnen ƴan jarida sai ga zance a gidajen rediyo. Yayinda wasu ma suka fara zuwa gida wai jin ta bakin JJ.
Hakan kuwa bamai yiwuwa bane, dan ganin JJ ya zama abu mafi wahala, wanda ma sukai ƙarfin halin iya juriyar ganin nasa da sun shiga ɗakin suke dawowa hankali a tashe sakamakon abinda idonsu ke gane musu. Dan batare da cin wuta ko ƙuna na gaba ɗaya fatar JJ tai wani irin saluɓewa kamar wanda ya ƙone a cikin man gyaɗa ko wata gagarumar wuta. Babu abinda yake a kwana da yini sai kuka da ihun magiyar a taimakesa jikinsa na ci da wuta. Sai dai abin mamaki a zahiri babu abinda ake gani sai jajur da jikin nasa yayi kawai. Tausayin rai duk da ana ALLAH wadai da abinda JJ ya aikata malamai suka haɗu ana masa addu’a da fatan Alimah ta bayyana kanta. Amma ƙiri-ƙiri babu Alimah babu dalilinta. Sai nau’o’in azabar da take ganama JJ kawai ke bayyana kansu. Dan bayan ƙuna sai ga JJ kuma na kukan son yin fitsari amma yaƙi fita. Ranar ma sunga tashin hankali akan wannan matsalar dan sai da dai takai an ɗaukesa zuwa asibiti. Shi kansa bai taɓa tunanin fitsari zai iya zama azaba ga mutum ba sai a ranar. Iya ƙoƙari likitoci sunyi dan ganin JJ yayi fitsari amma abu ya gagara, sai da takai har suma yake sannan aka samu ɗan kaɗan ya zuba, sai kuma zubar kaɗan ɗin ta sake zame masa wata sabuwar azabar data nema zama fin ta farko garesa har yana gigicewa kamar wanda ciwon hauka ke neman kamawa.
Mutane ƙalilan ne ke tausayin JJ, amma mafi yawa sai ALLAH ya ƙara da ALLAH wadai sukeyi. Lokacin da hotunansa da labarinsa suka fara zagaye social media batare da an san wanda ya ɗora su ba sai wasu a cikin ƴammatansa daya lalatama rayuwa da irin yaudarar da yay ma Anoosh suka shiga binsa da mugayen addu’a suma. Harda masu zuwa dubashi har gida ko asibiti. Abin kamar wata almara labarin JJ ya zama latest a yanzu musamman a media da gidajen rediyo..
Bata canja ba kuma akan abokansa suma nasu ya fara fitowa duk da dai bai kai ta’addacin na JJ ba da ya haɗa harda kisan kai….

__________★

Kamar yanda d.p.o yay alƙawarin riƙe iyayen Dafeeq haka kuwa akayi, dan saurayin Zuhrah da ke tsaye akan case ɗin ya nuna suma bazasu yarda ba har sai Dafeeq yazo ya bayyana gaskiya wa mutane sannan domin wanke Khadijah. Hankali tashe Dafeeq ya iso Kano tare da Kainaat daya taso gaba. Da farko batai niyyar zuwa ba, sai dai bisa ga tunanin shukama Dafeeq tsiya a Kanon ta yanda zai saketa ya kuma bata takardunta kan dole yasa ta yarda ta biyoshi. Kusan ƙarfe sha biyun dare suka iso Kano, dole yay haƙuri suka wuce gidansu dan su kwana. Sai dai Kainaat nata yamutse-yamutsen fuska wai tana ƙyanƙyamin gidan tsabar iskanci. Ba itace a gabansa ba dan haka ya watsar da ita. Washe gari daga sallar asuba a police station yay masa, sai dai kuma bai samu ganin iyayen nashi ba ance sai d.p.o yazo ƙarfe goma.
Hankali tashe ya juya gidan su Khadijah, inda ya tadda su Baba Hakimi da suka kwana anan. Sai dai ƙiri-ƙiri Baba Hakimi ya nuna shi bazai sauraresa ba sai sunje gaban d.p.o. dan gaskiya labarin abinda Dafeeq ɗin yazo ya aikata na ɓata Khadijah anan Kano ya matuƙar girgizashi da mamakin yaron. Yaso ganin Khadijah amma sai hakan ya gagara gareshi nan ma, sai ma wani abin mamakin daya sake cin karo da shi, wato ganin Kainaat ta fito a gidan ita da wata yarinyar makwaftansu da alama itace tai mata rakkiya. Wani shegen murmushi take masa cike da salon iskanci da nuna halin ko ina kula da mamakin da take karanta a saman fuskarsa……..✍️

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA…_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE_

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

Back to top button