Ikraam 64
64……
Mami bata wani sha wahalan shawo kan Na lado ba da yake ya ga kudi, bae ma tsaya binciken ko wa xata hada Ikram da ba yace an basu Ikram, shi dae Abba bae ce komai ba sae kallon yayan nasa yake da mmki ganin ya riga da yyi ma Amininsa alkawarin xae ba dan sa Ikram sae gashi lkci daya ya fasa, cike da farin ciki Mami ta koma gidansu Ikram tayi ma Ammi bayanin duk ynda suka yi da Na lado, ita dae Ammi bata ce komai ba sae tunanin irin halin wan mijin nata take, ynxu ko da ba Mami bne indae ya ga kudi hka xae yi ma yar su, karfe biyar da kusan rabi Mami ta bar gidansu Ikram bayan tace da Ammi gobe dad din Aliyu xae xo a daura auren, bata ma fada ma Ammi da wa xa ayi auren ba Ammi ta rako ta har bakin mota tayi mata gdya ta koma cikin gida ta dauki Hijab dinta ta kama hanyar gidan yayarta yakumbo don can ta kai Ikram da ta isheta da kuka daxu. Mami na komawa gida ta tar da Khaleel xaune balcony yana danna laptop ya mike da sauri ganinta, ta sakar masa murmushi tace “kana nn har ynxu ashe” yace “eh mami ban fita ba,” ya karasa ya amshi handbag dinta ta mika masa yace “daga office kike Mami” Mami tace “A’a daga suleja nake gidansu Ikram” bae ce komai ba ya juya da sauri yyi cikin gida ta bi sa a baya, wayarta ta ciro a jaka ta kira Mujaheed tace “Jaheed ka xo ynxu don Allah, akwae abubuwa da yawa da bamu yi mgna a kai ba” yace “to Mami gani nn xuwa” tace “ok” snn ta katse kiran, mikewa tayi tace “bari in je inyi wanka son” ya gyada mata kai ta haura sama. Washegari saturday dad ya je suleja da Jaheed da frndx dinsa aka daura auren Ikram da son din nasa a kan sadaki dubu hamsin, Ikram bata san wainar da ake toyawa ba tana gidan yakumbo hankalinta kwance don ixuwa lkcn dae ta daina kukan bnxan da take don ssae yakumbo ke riritata komai take so shi take mata, bata da hira da ta wuce ta Aliyu tun yakumbo na jin ddin hirar har ya gundureta, ta daina tanka ta kuma, ba laifi an dan yi taro gidan Ammi su mmn Altine da sauran makwabta da yan uwa, yakumbo bata je ba sbda tana tsare da Ikram kar ta kara gaba tunda ba hankali ya isheta ba, karfe biyar saura aka fara shirye shiryen wucewa da Amarya Abuja, tana bacci yakumbo ta tada ta taje tayi wanka, ba musu ta je yin wankan don duk ranar bata yi wanka ba tun wnda tayi jiya da daddare, ko da ta fito daga wanka taga su mmn Altine da kawayen Ammi xaxxaune a dakin yakumbo, gaishesu ta shiga yi maimakon su amsa sae taga suna sakin guda, sake baki tayi tana kallonsu, Yakumbo na dariya tace su fita su bar masu dakin ba musu suka fita tsakar gida suna dariya, Ikram ta turo baki tace “me suka xo yi nn yakumbo” yakumbo ta jawo ta ta shiga goge mata jiki tana cewa “gaisheni suka xo yi Ikram” da kanta ta shafa mata mai tana kallon kirjinta, Ikram ta fashe da dariya kmr tababbiya tana kare kirjinta tace “ke yakumbo nono na kike kallo” yakumbo tayi dariya tace “ashe yar tawa ta girma ta fara nono ban sani ba” Ikram ta galla mata harara tace “to shine xaki dinga kallon min, ae Mami tace in dinga sa Hijabi shi yasa nake sawa” vest yakumbo ta bata ta sa snn ta dauko wani tsadaddan less da Alkyabba da Mami ta kawo mata daxu da safe ta sa mata, ssae tayi kyau, da mmki Ikram tace “yakumbo wae ina xani kike sa min sabon kaya” yakumbo na daura mata Alkyabbar a ka tace “gidan Mijinki xaki Ikram” Ikram tace “mijina? Waye mijina, aure aka min?” ganin yakumbo bata ce komai ba yasa ta fasa ihu, yakumbo ta rungumota tace “kai ya hka Ikram” kuka ssae take kmr tasan meye aure, tace “yakumbo ni idan ba yayana bane baxan yi auren ba wllh” da kyar aka fita da ita daga gidan, sbda kukan da take yakumbo tace a tafi da ita Abujan kawae ba sae an kai ta gida ba, uwarta ta riga da ta sa mata albarka hka ma ubanta, kawar Mami daya da na momy daya ne cikin dankareriyar motar da aka kawo na daukar amarya, sae su mmn Altine da makwabciyar yakumbo don yakumbo kin xuwa tayi, ana kiran sllhn Maghrib suka iso makeken gidan sbda traffic da suka samu a hanya, har daki aka kai ta har lkcn bata fasa kukan da take ba tana cewa ita bata son auren, nasiha ssae su mmn Altine suka mata suka bar gidan bayan sllhn isha’i, frndx din Mami da Momy suka kara mata nasu a kai snn suka tafi suka bar ta ita kadae goma saura minti goma bayan sun yi assure dinta cewa ae Aliyu ne mijin nata kuma yana xuwa, sae a snn ta daina kukan da take sae bin dakin take da kallo tana jiran ganin ta ina Aliyu xae shigo dakin don kofofi uku ta gani, goma dae dae taji mota ya shigo gidan, ta kasa mikewa daga inda take sae kalle kalle take kmr munafuka, tana ji aka kulle kofa downstairs, ya shiga haurowa sama a hankali, duk da karancin shekarun Ikram hka kawae gabanta ke faduwa tana kallon bakin kofar da take jin motsi, tana kallo aka murda kofar dakin a hnkali ya shigo dakin kansa a kasa, sae kallonsa take duk da ba ganin fuskarsa tayi ba gabanta na faduwa don dim wuta ne a dakin, dagowa yyi a hnkali yana kallon kan gadon, ido hudu suka yi da shi, ta xaro ido ta mike da sauri tana kallonsa tace “yaya Khaleel”
[