Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 3

Sponsored Links

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of expert & perfect writers)_

*GARIN DAƊI…..!*

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

*Wattpad:ummishatu*

 

*3*

 

~~~Ban bari naji ƙarashen abin da yake faɗi ba na runtse idanuwa na ina jin wani yanayi yana lulluɓeni wanda shi ba farin ciki ba haka kuma ba baƙin ciki ba, jin kamar bana tare dashi ya sanyashi katse kiran ya sake kirana cikin ɗoki da shauƙi, ɗagawa nayi jikina a mutuƙar sanyaye,

“Ranki ya daɗe ya na jiki shiru? Ko dai duk farin cikinne ya hanaki magana?”

“uhmmm” na faɗa cikin murmushin da bai kai zuci ba, murmushin shima naji yayi kafin yace,

“to shikenan zan bar ki ki cigaba da murnar ki zuwa gobe zamu haɗu”

Sallama muka yi ya katse wayar murna fal ransa amma ni dai banji wata murna ko saɓaninta ba, kashe wayar tawa nayi gaba ɗaya nayi addu’a na shafa, inata saƙe saƙe acikin raina da haka har bacci ya ɗaukeni. Yau ma kamar jiya ƙawalli ce ta haɗawa yaya faisal kayan karyawa ni babu abin da nayi in banda wanka na shirya cikin blue ɗin doguwar riga nayi rolling muka wuce sashen su yaya Abdulhakim bayan mun karya, yaya faisal na zaune yana karyawa sai faman fara’a yake tayi kamar gonar auduga gaba ɗaya bakinsa yaƙi rufuwa, gaishe shi muka yi daga nan na kama bakina nayi shiru sai shida ƙawalli ne kawai keta hirarsu cikin barkwanci daga bisani ta tashi ta fita ya rage daga ni sai shi, kallona yayi cikin murmushi yace,

“kinji yadda muka yi da abba ko? Insha Allah gobe ina komawa zan sanarwa da gida yanda muka yi dashi….”

“wai gaggawar me kake yi ne har haka?”

Wani murmushin ya sake yi kafin ya bani amsa da,

“babu maganar gaggawa acikin wannan lamari widat…. Insha Allah ma acikin month ɗinnan zan gama haɗa lefenki sannan zan samu gidan da zamu zauna a Abuja”

Murmushi nayi tare da faɗin, “wa yaga ganɗoki”

“naji, dama abin da nake nema ne kuma ya samu to me zan jira? Any delay is dangerous”

Dariya na ɗan yi bance komai ba, yau dai babu laifi na ɗan saki jiki dashi mun ɗan taɓa hira har azahar, da rana abincin da aka dafa a gida na kai masa shinkafa da miya da salad zuwa yamma muka fita tare dashi da ƙawalli tayi mana rakiya zuwa unguwar jan bulo gidan anty salaha, a can muka tarar da bishra wacce ta sake dan bata ma da ranar komawa gida da alama,

“wai ke sai yaushe zaki dawo gida ne?” na faɗa ina kallonta domin harga Allah bana jin daɗin gidan sosai da bata nan,

“babu ruwan ki, tun da ke baki zoba to ki ƙale ita da ta zo, kuma nan ɗin a jeji take da zaki wani ce yaushe zata koma gida” anty salaha ta faɗa cikin faɗa tana hararata,

“Allah ya baki haƙuri” na faɗa ina ɗan ɓata rai,

“haƙuri kaya ne, ai wallahi zaki yi auren kema kuma nima zan rama duk wannan rashin ziyarar da kike yi min”

“a’a anty tuba muke kar ayi mana haka” yaya faisal ya faɗa yana dariya, har magrib muka kai a gidan anty salaha daga bisani muka yi musu sallama muka tafi nan ya ajiyewa bishra kuɗi wanda ban san ko naira dubu nawa bane. Bayan da muka koma gida wata hirar muka ɗora daga ni sai shi a farfajiyar gidanmu sashen su yaya Abdurrahman lokacin ƙawallita ta tafi, har 10 muna tare kuma sai lokacinne muka yi sallama na wuce cikin gida shi kuma suka cigaba da zama da yaya abdulhakim wanda shigowarshi kenan cikin gidan,

Washe gari daurewa nayi ban koma bacci ba tun bayan sallar asubah saboda ina son in taya ƙawalli aiki yau, ƙarfe 6 naji shigowarta, bata zaci idona biyu ba tasa wayarta a charge domin har lokacin da akwai wutar nepa, tana shirin fita daga cikin ɗakin nayi magana,

“barka da zuwa, ina kwana?”

Fasa fitar tayi ta dawo baya tana dariya “yau sammako aka yi kenan? Kiyi baccinki wallahi”

Ƙoƙarin tashi zaune nayi ina gyara baƙar hular baccin dake kaina,

“muje in tayaki dan Allah”

Ba dan taso ba muka fita tare muka fara aikin, dankali da ƙwai muka haɗa masa da ƴar sos wacce ta ƙawatu sai tashin ƙamshi take, kafin 8 mun kammala komai, baccina na sake komawa a karo na biyu wadda bani na tashi ba sai 10:30 kuma wannan ɗinma mama ce ta tadani wai intashi in je muyi sallama da yaya faisal zai tafi domin yafi so ya tafi da wuri, wanka nayi a gurguje na fito, ina cikin shiryawa ina tambayar kaina wai ƙawalli itama tun da ta tafi bata dawo ba? Riga da wando na Pakistan na saka na yafa mayafi na fita, cikin shirinsa tsaf na tafiya na sameshi, ga breakfast ɗin da muka haɗa masa nan ya gama ci sai santi yake yi min, mun ɗan taɓa hira kaɗan muka fito na rakoshi domin tafiya, muna tsaye gaban motarsa ƙawalli ta shigo,

“ah me zan gani? Ba dai har ya fito ba?”

“ehh na fito Maryam, ai dama da ace baki zo ba da sai na nemoki kafin na tafi”

Ina jin su bance komai ba sai murmushi da nake yi, gaisawa suka yi kafin ya buɗe motarsa ya shiga,sabbin kuɗi ya miƙo min wai gashi mai yawan nawa ɗayan kuma na maryam, godiya muka yi ya ja motarsa ya tafi muka wuce cikin gida. Kuɗin da yabamu na bawa ƙawalli nata 5k nikuma 10k sannan na haɗa mata da biyu daga cikin turarukan da ya kawo min sannan na ɗiba mata chocolate ɗin, bayan tafiyarta wuni nayi ina bacci har yamma bayan na tashi ne na kira yaya faisal nan yace min ya isa gida, ayau na buɗe wayar da ya bani na fara amfani da ita har 11 na dare na kai ina transferring kayana dake cikin tsohuwar wayata saida na gama tura komai sannan na kwanta bacci domin gobe da aiki.

Kamar yadda yaya faisal ya faɗa yana komawa gida ya sanarwa da magabatansa maganarmu tare da damar da abba ya bashi na yaturo a tsaida maganar aure, satinshi biyu da zuwa yace min suma ƴan gidan su zasu zo nan shiri ya tashi agidanmu cikin weekend suka zo, mazane guda shida, mahaifinshi da yan uwansa guda biyu sai ƴan uwan mamanshi da aminin babanshi guda ɗaya, faɗin irin girmamawa da karramawar da aka yi musu ɓata bakine, haka suma sun yi bajinta sosai sun kawo Kuɗin aure na naira dubu hamsin da goro da alawa kaya guda wanda ya kasance na saka rana kuma sun bar ranar a matsayin nan da watanni shida masu zuwa. Yaya faisal ganɗoki tuni ya fara shiri nikam babu abin da nake shiryawa tun da gani nake bikin ma da saura.

Kamar koda yaushe yau na taso daga aiki ina cikin napep zai maidani gida, sanye nake da doguwar riga baƙa na saka baƙar hula a kaina na ɗora baƙin mayafi a kai, hankalina gaba ɗaya na kan wayata inda nake duba wani posting da A&U kitchen tools suka yi inda suke tallata wata blender mai kai huɗu wadda har dambun nama tana yi haka kuma tana yin sakwara, birki naji mai napep ya taka da ƙarfi sannan ya ɗauke napep ɗin mun yi gefe guda tamkar zamu hantsila, cike da masifa da ɓacin rai naga ya fita, sai lokacin hankalina ya kai kan wani matashin saurayi dake tsaye sanye cikin ƙananan kaya, fuskarshi sanye da baƙin gilashi wanda ya rufe idanuwansa rikif bana jin abin da suke cewa, dawowa mai napep ɗin yayi yana cigaba da masifa,

“haba mutane sai kace dabbobi, salon ka buge su kuma su goga maka masifa su zame maka jidali…”

“bawan Allah kayi hakuri makaho ne fa, baya gani”

Gaba ɗayanmu juyawa muka yi muna kallon wanda yayi maganar, wani ɗan dattijo ne jikinsa sanye da kaya irin na ƴan ƙungiyar direbobi, bai jira cewar mai napep ɗinba yaƙara gaba ya koma wurin wannan saurayin ya kama hannunsa wanda inada yaƙinin cewa napep ko mota zai tare masa, ƙura masa ido nayi ina kallonsa kyakkyawa ne masha Allah kuma idan ba sani kayiba ba zaka taɓa dangantashi da makanta ba, jin mai napep ya fincikemu da ƙarfi ya sani gaggawar dakatar dashi wanda ni kaina ban san dalili ba, cikin hanzari na fita na nufi inda suke tsaye dattijon nan na Ƙoƙarin tare masa abin hawa, rasa abin da zance musu nayi daga ƙarshe nayi sallama dattijon nan ya amsa tare da kallona bayan ya maido da hankalinsa gaba ɗaya kaina dan jin abin da yake tafe dani,

“am baba dama zuwa nayi in bashi haƙuri akan abin da ya faru, wallahi mai napep ɗin bai san cewa baya gani bane, ya zaci ko da gangan yayi mana haka amma dan Allah yayi haƙuri…. Bawan Allah dan Allah kayi haƙuri”

“babu komai yarinya irin hakan ta jima tana faruwa, duk wanda yaganshi sai ya zaci yana da idanu shiyasa abu ƙanƙani sai mutane suyita kyararsa suna ganin kamar da ganganci yake shan gabansu idan suna tuƙi, makarantar makafi yake zuwa kuma kusan kullum nan yake zuwa ni nake tare masa abin hawan da zai mayar dashi gida”

Sake duban saurayin nayi da kyau sai naji duk tausayinsa ya ɗarsu a raina sannan kuma ya mamaye zuciyata gaba ɗaya,

“baba to mu tafi dashi sai mu saukeshi tun da naga bai samu abin hawa ba”

“a’a kuje kawai, ba drop kika ɗauka ba?”

“babu komai baba sai mu ajiyeshi koma ina zai je”

“gyaɗi gyaɗi ƴan dusa zai je”

“OK nima court road zanje, mu tafi babu matsala”

“Hashim zo ku tafi, Allah ya kiyaye hanya”

Kama hannunsa yayi yasakashi cikin napep ɗin yana yi mana Allah ya kiyaye hanya sai gobe idan yazo, shi dai har muka fara tafiya bai yi magana ba sai kai da yake ɗaga masa alamun to, ni kuwa tamkar na samu wani mirror domin kafeshi nayi da idanuwa ina kallonsa, farine sol dogo haka kuma bashida jiki yana dai sahun sirara, in banda makantar dake tare dashi sam bashida wata makusa,

“hajiya ina zamu kai shi?” naji muryar mai napep yana tambayata,

“gyaɗi gyaɗi ƴan dusa, idan muka saukeshi sai ka kai ni”

“to shikenan Allah ya saukemu lafiya”

Cigaba da kallonsa nayi acikin raina ina tunanin ko yaya wannan bawan Allah yake ji, gashi saurayi matashi wanda a yayi shekaru da yawa ace shekararsa 32,sai dai gashi nan tsaf tsaf dashi babu ƙazanta ko rashin gyara atare dashi, har mukaje gyaɗi gyaɗi ƴan dusa bai yi ko tari ba saida mai napep ya tambayeshi a ina zai saukeshi sannan yayi magana,

“kusa da sabuwar transformer…..”

Muna zuwa wurin kuwa yace ya isa ga gidan nan, Allah mai iko shi ne abin da naketa nanatawa acikin raina, aljihun wandonsa ya fara lalubawa zai ciro kuɗi, ɗari biyar guda ɗaya da dubu ɗaya itama guda ɗaya sai ɗari biyu, ɗari biyun naga ya ɗauka yana cewa mai napep,

“ga ɗari biyu ka ɗauki kuɗinka”

“barshi zan bashi Kuɗin” na faɗa ina kallonsa,

Sai lokacin ya ɗan jiyo ya kalli gefen da nake sannan naji yace “nagode Allah ya saka da alkhairi”

Daga haka ya juya ya nufi gidan su wanda yake dab da inda muka tsaya, ni dai har ya shige cikin gidan ban daina kallonsa ba har saida na daina hango shi…………….. ✍

 

 

*_Ummi Shatu_*

Back to top button