Hausa NovelsRainon Soja Hausa Novel

Rainon Soja 18

Sponsored Links

*️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*

 

Page 18
______________________
*Don Allah kar ki karanta ki fitar mun , haka duk wacce ta karanta bata biyani haƙƙina ta sayi littafin ba kar ta karanta mun idan ta karanta ban yafe ba…ga masu buƙatar payment regular group ₦500…Vip group ₦1000… Special payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank shaidar biya ta wannan number 08081202932 ko katin MTN ta Wannan number na sama ƴan Niger katin Artel 500f.*

Night update️________________________

A zuciyar sa ne yake faɗin “ Yarinya ta girma ace har yanzu wai indomie bata iya girkawa ba to mene ma ta iya ne ? Ƙila ko tea ka sata haɗawa sai tayi maka shirme don ba zaiyi teste ba . Tahowar Ma’eesha da ya gani ne yasa shi ɗan gyara zaman shi yana ƙara tanadar mata azaban da zaiyi mata na biyu don na farko ya sata ta ci abun da ta girka yanzu kuma wani sabon wahalar zai bata . Uncle I’m done ta furta tana washe baki don ita kan ta Tasan tayi ƙoƙari . Kallon left side ɗin shi yayi don baya son tazali da Plate ɗin indomien . Uncle…” ta kuma kiran sunan sa cikin sanyi da sarewa don ta fara tunanin ko bai masa bane ? Sai kuma ta kara duban girkin taga ko waye sai yace yayi irin shi dai mami ke yi mata . To mugun ta yake ji Miki Ma’eesha kinji rabu dashi Allah yafi shi tana magana a zuciya a sarari kuwa shagwaɓe fuska tayi Idanunta na narai narai ƙwallah na ciko su.

Muryar sa ne ya katse ta yana cewa “ aje anan ki zauna kusa dashi kema”. Yayi maganan yana shan kunu tare da kicinkicin da rai . Sam ta kasa Fahimtar ta zauna kusa dashi . Uncle kusa da waye zan zauna ?. Dirar da Lulun idanun sa yayi a kan ta kana yace “ Kusa da Abin da kika girka mana ko Ni sa’an wasan ki ne da zaki zauna kusa dani ”. Ganin yanda yayi mata maganan yasa ta saurin yin ƙasa tana zubewa kusa da ƙafafun sa tare da sauke plate ɗin itama . Uncle me yasa kake mun faɗa ? Mami fa tace kana Sona!

Rintse idanun sa yayi yana dafe saman Goshin sa tare da cewa “ Hohoho kai Wai ke bakin ki bai shiru ne , shi baya taɓa hutawa ne? Kaman wani irin so ma kike nufi? Ya ƙare maganan yana kallon kyaƙyƙyawar fuskar ta da ta tsaya shiru tana kallon shi . Uncle dama soyayya kala kala ne? Ai na ɗauka guda daya ne , amma yanzu faɗa mun dukan su sai na ji na faɗi irin wanda nake maka . Sakin baki yayi yana buɗe shi Hushiryar sa suna bayyana na mamakin surutun nata da yake gani baya da Wani amfani….Ma’eesha zaki mun shiru ko sai na miƙe?.

Saurin Girgiza kai tayi tare da cewa “ A’a na tuna Uncle Haidar , ba zan sake ba , ka zauna kaji kar ka miƙe. Dariya ne ya kusa kama shi wannan yasa shi ƙasa da kan sa yana kallon plate ɗin indomien. Saurin lumshe idanun sa yayi yana furta “ Ma’eesha waya yi Miki girkin nan?” . Yana bin yanda ta yi indomien a ido ba sai kaci ba kasan wannan dadin sa da dandanon sa na daban ne. Kamin yaji mene zata ce tuni ya kai hannun sa yana ɗaukar indomien duk da shi ba abincinsa bane , amma wannan yanda yaji carot da mai ga ƙwai data sanya daga sama. Abun sai wanda ya ɗanɗana. Jiki a sanyaya ta furta “ Kayi haƙuri Uncle Aliyu Wallahi haka Mami take yi shiyasa nayi maka irin shi .

Murmushi taga yayi yana fara cin taliar tare da lumshe idanun sa yana motsa laɓɓan sa tare da kiran sunan ta ” Ma’eesha please taho ki ɗauko mun ruwa a fridge….saurin miƙewa tayi tana ɗauko masa ruwan tare da ɗan risinawa tana aje masa ruwan . Zauna ki matsa mun ƙafa na!

Kwana biyu zazzaɓi nake yi ne shiyasa zaku ga update din namu too Short ✍. Mmnteddy

Back to top button