Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 51

Sponsored Links

{51}

Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..

~~~Gaba ɗaya hankalinta da tunaninta na ga kyakkyawar halittar da ta gani shiyasa driving ɗin a sannu take yi har ta ƙarasa airport, samun Jalil tayi yana ta faman mita domin jirginsu yajima da sauka sannan yajima rabonsa da ƙasar shiyasa yake jin kamar yayi tsuntsuwa ya tafi kawai ba tare da ya jira shalelen ba wacce itace ke binsa ma’ana daga shi sai ita,

“you are very stupid….. For how long zanyita jiranki” yace da ita lokacin da ta karasa inda yake zaune yana jiran ta,

“am very sorry yaya Jalil….”

“Hmmmmm finally…” ya faɗa yana sabar jakarshi,

Sun hau hanya sun fara tafiya ya dube ta yace “shalele wai har yanzu babu wani labari a kasa?”

“wanne iri kenan?”

“aurenki mana, yanzu ai kowa aurenki yake jira, ni i thought kafin na dawo daga Malay ma zan zo in samu anyi aurenki….”

“oh yaya Jalil kudai baku da magana sai ta aurena wai haka kuka gaji dani ban saniba?”

“ba gajiya muka yi dake ba kawai muna sone muga kema mun Mika ki ga wanda ya dace…..”

“to har yanzu dai, kuma ni ko saurayin ma bani da shi”

“Haba, karya kike, kyakkyawar budurwa kamar ki”

Dariya suka yi gaba daya suka cigaba da tattauna maganar har suka isa gida nan ta wuce bedroom ta barsu anata marhaban lale da zuwan sa, Malika ta kira awaya tace tazo da sauri akwai labari, mintuna 30 sai ga Malika ta karaso nan suka wuce daki suka ƙule Jalil yana tsokanarsu yana cewa ashe har yanzu suna nan da wannan munafurcin nasu na zaman cikin ɗakin,

“Malika you know what? Am in love…..”

“wow…… Bani insha” Malika ta fada cikin mamaki dan ita dai a duk zamanta da Suhaila bata taba jin ta yaba da wani ba bare har tace tana sonshi,

“Ɗazu zanje dauko yaya Jalil a Airport na ga wani kyakkyawan guy….”

“umm humm sai akayi yaya?”

“sai nayi ta binshi har zuwa office din su, ban san komai a kansa ba amma dai na bama wani assignment akan ya nemo min dukkan abinda ya shafe shi”

Ajiyar zuciya Malika ta sauke kafin tace “shalele anya kuwa kina ganin babu damuwa? Idan kuma yana da aure fa??”

“dan Allah bari wanne irin yana da aure, kin ganshi kuwa very handsome? I don’t think yana da aure gaskiya….”

“Idan kuma yana da shi fa?”

Zubama Malika ido tayi na tsawon lokaci kafin tace “bazan iya jurewa ba, koda yana da aure to ya zame masa wajibi ya rabu da ita sannan ni ya aureni dan kema kanki kin san ina da zafin kishi kuma ba zan taba iya hada mijina da wata ba”

“amma anya shalele tunaninki yana baki daidai kuwa? Anya ba zamu yaudari kanmu ba idan har muka tsaya akan wannan matsayar? Ta yaya zamu yaudari zaukatanmu da cewa idan har yana da aure zai rabu da matarsa dan kawai saboda ke? Sake tunani dai….”

“Malika ni ina ganin ma kawai mu bar wannan maganar mu jira feedback daga wurin wannan guy din dan bama na son maganar yana da aure, what i believe is he’s single…. Not married”

“ok Allah yasa haka….”

Wayarta ta dauka ta kira Gabriel daya daga cikin securities din wurin aikin su samz wanda ta bawa aikin binciko mata komai da ya shafi samz, har tayi ta katse bai dauka ba haka yasa ta rabu dashi bata ƙara kiransa ba sai da daddare nan suka yi magana ya dan sanar da ita wadansu abubuwan da ya sani game dashi sauran kuma yace sai ya bincika sa’annan zai nemeta,

Tun a ranar ya soma gudanar mata da bincike cikin sirri yayin da ita kuma taci gaba da yi masa ɓarin kudi kamar babu gobe ataƙaice dai shine ya binciko komai tun daga kan phone no har zuwa inda samz ke zaune amma bai sanar da ita cewa yana da aure ba har sai bayan da soyayyar tayi nisa da girman da ba zata iya jurewa ba acikin zuciyarta, ranar da Gabriel ya sanar da ita cewa gobe ne birthday din samz kamar yadda ya binciko date of birth dinshi wani tsadadden boutique suka tafi ita da Malika wanda ke nan garin Abuja na manyan yara suka je suka ragargaji kudi suka iyo siyayyar gift ta aika masa duk da ta tuttura masa massages sau shurin masaki amma babu reply hakan bai sa ta hakura ko taji gwiwarta tayi sanyi ba asalima wani ƙaimi ya ƙara mata. Haka ta cigaba da bibiyarsa batare da ya sani ba wani lokacin haka kawai zata fita sassafe taje tayi parking daidai office dinsu dan kawai ta ganshi, tana ganinsa zata juya ta koma gida, ranar da suka je tare da Malika ta ganshi shiru Malika tayi na tsawon lokaci har sai da Suhaila ta yi mata magana wurin sau uku sannan ta ajiye wani gwauron numfashi tace,

“shalele guy dinnan kamar yana da aure…”

“me yasa kika ce haka?”

“ki yarda dani yana da aure, ki duba kiga yanayin nutsuwarsa, he’s very calm and gentle…….”

“wai dan Allah Malika meyasa kike son sai kin daga min hankali? Bari na kira Gabriel”

Wayarta ta ɗauka ta kira Gabriel yana dauka ta fara fada kamar yana ganinta “Gabriel i don’t want to hear stories, tunda jimawa na ce maka ka binciko min if samz is married or not but up to now ka gagara…”

“sorry ma, zan binciko in the next 2 days i promise you”

“ina jiranka…”

Cikin kwanaki biyu ya binciko mata kuma ya sanar da ita cewa samz fa yana da aure hatta sunan matar da address din gidan da komai sai da ya sanar da ita nan hankalinta ya tashi ta rasa inda zata saka kanta daga karshe suka yanke shawarar su zo har gida su shaƙa min kuɗi ko wai zan bar musu mijina sai dai fa duk da kaca kacan da nayi musu hakan bai sa sun sauka daga doron turbar da suke kai ba.
***
Shirin tafiya Lagos muke yi sakamakon wani aiki da aka tura samz wanda zai je ya yi wata ɗaya, da dafarko tsokanata yayi yace min “baby zanje Lagos zanyi 1 month zaki zauna anan ko Kano zaki koma sai na dawo kema sai ki dawo?” kwance nake a jikinsa amma sai da na tashi saboda firgici na ɓata rai sannan na turo baki,

“ni kai zan bi bazan iya zama ni ɗaya ba….”

“no baby, ba zan tafi dake ba….”

“saboda me?” na bukata ina zaro ido,

“saboda rowa kike yimin yanzu…. Idan munje ma rowa zaki tayi min”

Idanuwana na rufe da tafukan hannuna ina murmushi,

“wai kai baka gajiya ne?”

“uhmmm” ya bani amsa yana bude fuskata,

“to kayi hakuri na daina…”

“baby ke raguwa ce…. Kina cewa you want to get pregnant, da haka zaki samu?”

Kallonsa nayi fuskata har tayi narai narai saboda ya fama min inda yake yimin kaikayi,

“yawwa ranar ina yi maka magana but you didn’t take it serious……. Nace ko za muje hospital muga Dr?”

“for what?”

“kaga har yanzu ban kara samun ciki ba”

Hannayena ya kama duka biyun ya rike bayan ya matso jikina sosai,

“baby…. Sau nawa zan fada miki ki kwantar da hankalinki akan maganar cikin nan, karki tayar da hankalinki ai ba muyi jimawar da zamu shiga damuwa akan bamu samu ciki ba……”

“boo ba zaka gane ba, kaga yanzu kowa zai dawo da hankali kaina tunda wancan cikin ya lalace kuma yanzu an dan kwana biyu”

“karki damu baby, komai lokaci ne kuma Allah ke yi, zaki samu ciki a lokacin da Allah ya so kuma a lokacin da hakan shine alkhairi agaremu”

Murmushi nayi na rungumeshi araina ina jin sanyi da nutsuwa suna shigata.

A cikin satin muka shirya muka tafi birnin iko Ikon Allah, duk da aiki yaje yi amma hakan bai sa mun kasa fita yawon shakatawa da bude ido ba, har tausayi yake bani saboda yadda baya samun hutu yadda ya kamata kullum sassafe yake fita bazai dawo ba sai magriba kuma yana dawowa zamu fita, nidai wuni nake a ɗakin da muka sauka cikin wani katafaren hotel hadadde kuma ƙayatacce amma bana leka ko ƙofa idan ya fita har sai ya dawo haka kuma tunda muka zo ruwa ake yi kamar da bakin ƙwarya kullum sai anyi ga uban sanyi duk da asauran wurare yanayin rani ne wato dry season,

Wuni nake Ina kallo da chaten dan bani da wani abun yi ni ba aikin gida ba ba girki ba har gajiya nake da bacci shiyasa muke fita da daddare kuma wannan dalilin ne ina jin yasa na fara hada ƙiba daga zuwanmu, ko ƙawalli da ta ganni lokacin 2 weeks da zuwanmu cemin tayi,

“ƙawalli anya kuwa ba ciki gareki ba naga kumatunki sun hau…..”

Kumatun nawa na shafa kafin nace “ƙawalli ciki kuma? Babu wani ciki”

“to Allah ya kawo ƴan biyu amma nidai ban yarda ba”

Duk yadda na fada mata kin yarda tayi sai hakura nayi na barta amma ni na san ba ciki bane dan yanzu haka ma period nake tun shekaran jiya na fara shima sai nasa yan guntun ƙunƙunin yake tun jiya saboda ina period ina jinsa shiyasa lokacin da ina da ciki yake ta shan bidirinsa babu abinda yake kawo masa cikas,

Batun Felicia da shalele kuwa duk ciki babu wacce ta hakura ko tayi sanyi, yanda suka sako samz a gaba tamkar zasu ci babu abin yana mutukar yimin zafi amma bana nuna masa duk da yasan nima a bangaren kishi babu dama ne,

Yau bayan ya dawo daga aiki saloon ya rakani, ganin ana huda kunne da hanci awurin yace wai idan zan amince zai so a huda min kunne a kara min guda uku akan ɗayan da nake dashi dan yaga awurin wata jiya awurin aikin su kuma yayi masa kyau but yana tausayi na kar a huhhuda min jiki ni kuwa tunda ya riga ya fada naji sai nayi zan samu nutsuwa tunda har ya fada da bakinsa yana so to gara inyi masa ya gani awurina akan ya gani a wajen wata yayi sha’awa, daurewa nayi aka huda min harda hanci aka saka min barima kuma ba yabon kai ba duk sunyi masifar yimin kyau, muna komawa ya gama waya da mommy ya ajiye wayar kusa dani ya shiga bathroom kawai naga text ya shigo kuma ta ɗan saman da yake bata gama tafiya sleep ba da haske sai kawai naga anturo ‘I received your alert, tnx alot darling Allah ya kara arziki” wannan shine kadai abinda na iya gani kenan naji raina ya baci zuciyata ta harzuka…..

 

*_Ummi Shatu_*

Back to top button