Cuta ta Dau Cuta Hausa NovelHausa Novels

Cuta ta Dau Cuta 32

Sponsored Links

*_Typing_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_ _

 

_Shafi na talatin da biyu_

____________

*_ZAFAFAN DAI_*

*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*❤‍❤‍❤‍

*_KASANCE D’AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*

_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_

*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*

*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*

*TSUTSAR NAMA Billynabdul*

*GUDUN K’ADDARA Huguma*

*AMEENATU Mamuhghee*

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR… ZAFAFA BIYAR NAKU NE_

___________

…….Alhamdullah ƴan rakkiyar amarya da wasu a dangin ango duk sun wuce. Sai gidan yayi tsitt kasancewar babu mai yaro a wanda suka rage. Kuka sosai Khadijah tasha a sashenta daya rage babu kowa sai ita kaɗai. Mamy dai ta tura mata masu aiki sun gyara ko’ina tsaf. An kuma kai mata abincin rana. Sai da akai sallar la’asar kuma sai ga Noor da baƙi ƙawayen Mamy. ALLAH yasota babu jimawa tai wanka. Dan ɗan barcin da tayi bayan ta gama kukanta yasata jin nauyin jiki, shine ta watsa ruwa lokacin data shiga yin alwalar la’asar. Cikin girmamawa take gaida ƙawayen surukar tata. Wayayyun mata ƴan boko da naira ta gama nuna kanta a jikinsu. Duk da acikin su akwai wanda sukaso Abaan ya auri ƴaƴansu hakan bai hanasu yaba ƙyawun Khadijah da nutsuwarta ba. Sun kuma tabbatar da Abaan ɗin ya samu dai-dai shi a yanzu ba irin Kainaat ba mai buɗaɗɗen ido sa’ar shekarunsa. Haka dai suka fito suna sambarka da ambaton masha ALLAH. Koda Noor ta musu rakkiya nan wajen Khadijah ta dawo ta ɗan tayata zama, dan ɗazun dama tazo ta samu tana barci. Hakan yayma Khadijah daɗi sosai, dan ta rage kewa, sannan Noor ɗin ta taimaka mata sun gyaro sashen Abaan kamar yanda ta bata shawarar suyi. Sai gab da magrib ta koma nasu sashen, tabar Khadijah da kewa da zullumi. Dan ji take kamar tai tsintsuwa ta koma Kano, sai dai kuma tasan bakin alƙalami ya riga kuma ya bushe…..

_________★

Ƙarfe biyar da kusan rabi motarsa ta shigo gidan. Kamar kullum yana tare da Awwal. A yanda ya fito motar a kasalance zai sa ka fahimci a gajiye yake. Dan hatta ƴar saman suit ɗinsa riƙe take a hannunsa ya ɗan sagalata a kafaɗarshi. Kai tsaye sashen Mamy ya nufa, ya bar Awwal na tattare masa tarkacensa kamar yanda ya saba.
Sassanyan muryarsa ta fargar da su Mamy dake hira zuwa garesa. Duk da tunkan ya shigo dama ƙamshinsa ya musu sallama. Cike da girmamawa ya gaida gwaggonninsa biyu da suka rage basu wuce ba. Sai wasu mata biyu da suma suka gaishesa cikin girmamawar. Sai Noor da itama ta gaishesa, sannan shima ya maida hankali ga Mamy dake binsa da kallon tausayi, dan gani taima kamar ya ɗan rame mata yau ɗin. Amsa masa tai da kulawa, tare da ɗorawa da faɗin, “Baffah kaci abinci kuwa yau ɗin nan?”.
Murmushi yay mata mai sanyi, sai kuma a hankali ya ce, “Mamy naci snacks da drink….”
“Baffah na drinks da snack aiba abinci bane. Shiyyasa naga ka rame min a ido wlhy. Kaga maza jeka wajen matarka an kai muku abinci dan ALLAH ka zauna kaci, sannan itama ka tabbatar taci kaga baƙuwace ita”.
Murmushin ya sake yi nan ma yana miƙewa, sallama ya musu ya fice dan shima dai yasan yana matuƙar buƙatar hutawar kam…

Tsaye take gaban mirror tana fesa turare dan kammala gyara jikinta kenan kamar yanda su Aunty Firdausi suka gargaɗeta da yi. Ratsa kunneta da sassanyar muryarsa tai yasata ɗan daburcewa, cikin sauri ta ɗauki ɗan kwalinta da bata kai ga ɗaurawa ba ta shiga ƙoƙarin warwarewa tana amsa sallamar tasa. A hankali ya janye idanunsa da ga kan gashinta dai-dai tana ɗora ɗan kwalin da faɗin, “Sannu da zuwa ina yini”.
Rigarsa dake saman kafaɗa ya sauke a ɗan kasalance ya amsa da, “Ya baƙunta? Badai kiyi kuka da zasu tafi ba dai ko?”.
Kasa bashi amsa tayi, sai ma idanunta da suka ciko da ƙwallan, amma tai dauriyar riƙesu. Freight ɗin dake ɗakin ƙarami ta nufa, ruwa ta ɗakko da kofi ta nufesa. Yanda ta zuba ruwan a nutse da ɗan rissinawa yayin miƙa masa ya sashi sakin siririyar ajiyar zuciya. Jin kaifin idanunsa a kanta ga shi ya haɗa hannunta da kofin ruwan ya riƙe yaƙi ya saki ya saka tsigar jikinta fara tashi yaam. Ji tai ta kasa daurewa ta ɗago a hankali itama, kai tsaye cikin idanun nasa natan suka shige, ji tai ta ƙara rikicewa ma, dan mijin nata akwai kwarjini da cika idon mai kallonsa.
Ganin yanda tayi ɗin ya sashi sakin murmushi, magana ta gaskiya yana matuƙar son mace mai kunya da sanyin hali irin na Khadijah, dan haka komai nata ke birgesa kai tsaye. Yanda baida hayaniya haka yake son mace mara hayaniya da rashin kauɗi. Kofin ya kai bakinsa batare daya sakar mata hannunta ba, sai da ya shanye duka batare da ya saki hannun nata ba dai ya jawota zuwa jikinsa a hankali ya zagayeta da ɗayan hannunsa, cikin kunneta ya raɗata mata “Haka ake tarbar miji dama Baddo?”.
Ji Khadijah tai inama ƙasa ta buɗe kawai ta shige dan kunyarsa. Yanda yake tafi da ita nasata mance ta taɓa aure, dan kunyarsa take irin sosai ɗin nan, kodan ya girmi Dafeeq a shekaru ne, ko kuwa yanayin kamewarsa da cikar kamalane ke sata jin hakan ita bata sani ba. Sun yi kusan minti biyu a haka kafin ya saketa, sai kuma a ɗan kasalance ya ce, “Bara nayi wanka na zo nai sayen bakin amarya dan naga dai take-taken ki kenan”.
Da sauri ta juya masa baya tana ɗan murmushi. A ranta tana jin mutumin nan nadabanne a cikin daban. Komansa na tabbatar mata lallai a duniya akwai maza akwai kuma mazaje. Jin yana ƙoƙarin fita muryarta acan ƙasan maƙoshi ta ce, “Mamy ta aiko da abinci a kawo maka?”.
Sai da ya kalla ƙyaƙyƙyawan agogon hannunsa da ɗan lumshe idanunsa da buɗewa a lokaci ɗaya shima murya can ƙasa ya bata amsa da, “Zan dawo anan naci after isha”.
Kanta kawai ta jinjina masa batare data iya kallonsa ba. Sai da taji ya fita ta ɗan sauke ajiyar zuciya tare da ɗagowa, idanu ta ɗan tsurama inda ya tsaya ɗin sai kuma ta saki murmushi, ita kanta tana mamakin yanda take tsintar kanta a wani shauƙi da kunya mai tsanani a duk sanda suka kasance tare. Ga wata kasala dake saukar mata da jin nutsuwa. Bayi ta shiga tai alwalar magrib duk da da ɗan sauran mintuna, amfani tai da sauran lokacin da ya rage tai zaman karatun Alqur’ani har sai da lokaci ya cika ta tashi ta gabatar da magrib, koda aka idar karatun ta cigaba dayi har isha’i. Ta jima tana addu’oi sannan ta tashi, gaban mirror ta koma tai ɗauri mai ƙyau tare da sake gyara kwalliyarta simple data sake fidda mata ƙyawunta. Ta sake saka turare sannan ta ɗauka mayafi ta yafa kamar mai shirin fita. Tayi ƙyau sosai, sai kwalliyar tata ta sake tabbatar da ita a amarya. Falo ta fito ta saka turaren wuta a kusan burner uku data gani, duk da kuwa falon yana ƙamshinsa abinsa. Kitchen ta shiga ta haɗa abincin dan tunda aka kawo anan aka ajiyesa. Ta kawo kulolin ta koma ɗakko sauran ta samu ya shigo. Sai dai waya yake yi, yana zaune a kujera sanye cikin milk jallabiya datai masa ƙyau sosai kamar wani balaraben Saudiyya. Ga ƙamshin turarensa mai daɗi ya cika falon. Yanda yake wayar cikin yaren filatanci haɗe da turanci dolene ya birgeka. Duk kai kawon da take tsakanin kitchen zuwa dining idonsa na kanta, ta masa ƙyau sosai, haka kawai sai wayar da sukai da Doctor Giɗaɗo ɗazun ta faɗo masa a rai, wai Kainaat nada ciki. Da sauri ya ture tunanin gefe cikin halin ko’in kula, dan shi ko kaɗan baiji wani abu na kishi akan hakan ba, shi yama manta da wata Kainaat can a babin rayuwarsa, yama yi zaton ta koma ga iyayenta tuni ashe wai tana Adamawa harma ta sake wani auren, gaskiya bai taɓa sake tabbatar da Kainaat kidahuma bace sai yanzu, yayi nadamar auren yarinyar nan a rayuwarsa, amma ba komai ai yayine domin Mamynsa, gashi kuma yaci ribar biyayyar da yay mata a farko tunda gashi a karo na biyu ta sake haɗashi aure da choice ɗinsa, hakan kaɗai garesa Alhmdllh. Isowar Khadijah wajen ya sashi yin sallama da wanda yake wayar tare da ture batun Kainaat gefe, cikin ɗan risinawa kanta a ƙasa ganin ya kammala wayar ta furta, “Hamma ga abincin (yanda taji Noor na kiransa). Wani kalar ɗan waro idanu yay waje, sai kuma kamar a ɗan shagwaɓe ya ce, “Hamma kuma baddo! Wannan ai salon hanani rawar gaban hantsi ne”. Cikin rashin fahimta da jin yanda yay maganar a wani can ƙasan maƙoshi ta ɗan ɗago ta kallesa. Manyan danunsa ya lumshe mata tare da wani kalar ɓata fuska a daƙile ya ce, “Eh mana, miya haɗa ango a daren farkonsa da wani Hamma can. Inama laifin irin su kankanar zuciyata, madarar raina, gobar ruhina haka sai na san ango nake.”
Dariya sosai Khadijah keyi, dan harga ALLAH ya bata matuƙar dariya, irin waɗan nan sunaye haka. Ganin yanda take dariya har fararen jerarrun haƙoranta na bayyana ya sa ya saki murmushi shima. Haka yake son ganinta cikin farin ciki, dan yasan ya tsamota cikin danginta tana cike da damuwar kewarsu dannewa kawai take. Miƙewa yay har sannan fuskarsa da murmushi ya nufi dining ɗin, hakan yasa itama haɗiye sauran dariyar tabi bayansa. Ita da kanta ta zuba masa abincin, sai dai kaɗan ta saka kamar yanda ya buƙata. Ganin ta zauna bata da niyyar zuba nata ya sashi kallonta da fararen idanunsa masu maruƙar rikita mata lissafi. Ƙasa tai da kanta tana wasa da yatsunta. Komai baice da ita ba ya ɗauke idanun, sai kuma ya ɗauki spoon ya saka a plante ɗin nasa a bincin. “Bismilla muci”. Ya faɗa babu alamar wasa a tattare da shi. Ji tai gaba ɗaya ta kasa musa masa. Dan girmansa da kwarjinin sa a idonta bana wasa bane. Kasa sakewa taci abinci tayi, sai juya spoon take a ciki da tsakura kaɗan-kaɗan. Shiko bai mata magana ba yana cigaba da ci a nutse rabin hankalinsa akan tvn dake dining ɗin yana kallon news. Ya ɗan ci sosai ya ajiye cokalin sai kuma ya zari tissue ya goge bakinsa yana kallonta. Tana jin yanda idanunsa ke yawo a jikinta amma sam ta kasa ɗagowa, har sai da ya fara ƙara mata abincin sannan ta ɗago da sauri. Kansa kawai ya ɗan ɗaga mata alamar taci yana miƙewa yabar dining ɗin, can falo ya koma ya sake zama a inda ya tashi yana buɗe laptop daya ajiye ya shiga aikin gabansa da duk bai wuce bincike akan noma ba dai. Dan in dai ka gansa da laptop aikin kenan kawai.
Tashinsa a wajen ya ɗan taimaka mata taci abincin, bayan ta kammala ta tattare wajen ta kai kitchen, sauran abincin take ta tunanin yanda zatai da shi, dan bata son barinsa ya lalace babu daɗi. Gashi ita ba waya ba balle ta kira Noor tace a zo a ɗauka. Ta manto wayarta a Kano, tun ɗazun take son magana da su ma hakan ya gagara. Rashin mafita ya sata fitowa, kanta a ƙasa ta nufo inda yake. Sai da ta ɗan saci kallonsa, ganin hankalinsa gaba ɗaya a screen ɗin laptop ɗin yake ta sauke ajiyar zuciya can ƙasa. A hankali ta ce, “Hamm….” sai kuma tai shiru ta kasa ƙarasawa. Murmushi ya ɗan saki batare daya kalleta ba, idanunsa akan screen ɗin laptop ɗin ya ce, “Uhumm ina jin ki! Batun Hamma kuma zan canja shi ai da kaina dan ni dai ba Hammanki bane”.
Duk da zancen nasa ya sata jin kunya haka ta daure ta sanar masa batun abincin. Karan farko ya ɗago ya ɗan kalleta ya sake maida kansa, ji yay ta birgesa, dan ta sabbatar masa ita ba almabazzar mace bace ba. Gefensa ya nuna mata ya ce, “Bismilla zauna bara na kira Noor sai ta aiko a ɗauke”. Kanta ta jin jina masa itama kawai, dan har ya riga yakai wayar kunnesa. Dai-dai tana ƙoƙarin zama a ƙasa ya ajiye wayar yana kallonta, kansa ya girgiza mata da faɗin, “No akoda yaushe nafi buƙatar jin iyalina a jikina in har ina gida. Karki sake kwantanta cewa zaki zauna ƙasa dan ina kujera. Dan haka bissmilla”. Ya nuna mata kusa da shi, inda ta tabbatar idan ta zauna dolene a jikin nasa zata kasance kamar yanda ya ambata………✍️

Ina kuke manyan mata da hajiyoyi munsamar muku sauqi Ina masu shaawar futa Egypt karatu ko yawan bude ido to gadama tasamu kaidai kawai kaiwa wannnan number magana 01017018846

Ba nan ummu khalifa ta tsaya ba tana kawo original Egyptian abaya da shoes da duk abinda mutum keso tana kawowa zuwa gida Nigeria

Ummu khalifa 01017018846

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

Back to top button