Auren Gado Hausa NovelHausa Novels

Auren Gado 45-46

Sponsored Links

…………” Ina jiran kayan. Tafada tana kashe wayar ta, tareda runtse idanun ta tana tunanin dama zata iya yimai hira tareda kwantar mai da hankali da tayi, domin yana bukatar abokin shawara, ba ruwan shi da kowa yayan shi ne abokin shawarar shi, gashi baya duniya, Abubuwa na faruwa Wanda yake hadiyesu batareda complain ba, she like his style na tsayayyen namiji jajircecce yafi Ahmed karfin zuciya, a haka bacci mai dadi harda mafarkin shi ya dauketa,
Gefen khaleel kuwa, bai iya tsinana komai ba ya koma gida, part din ta ya shiga yayi wanka ya canja zuwa kanan kaya kafin ya janyo troly ma dai daiciya ya fara zabar mata kaya, duk manyan kaya ne sai hijabai, kafin ya dauka yaje ya saka a motar shi, ya shiga gidan Momy, tana zaune tana waya Yanayin sallama ta kashe tareda sakin fara’a, “Ibrahim kadawo? Nakira manager yace kana office. “Eh am just coming back. “Fita zaka yi? “Eh zankai wa Naziya kayan ta indawo ne. Yafada kai tsaye, ” Ina zaka kai kaya? Ka sake ta ne? ” why zan saketa Momy likita ya bata bed rest so na kaita gidan ya Yar ta ta huta. Wani irin kallon takaici tayi mai ” khaleel karya dokata kake son kayi? ” ko kusa Momy bazanyi Abinda kika yi Allah ya isa akai ba. ” then what is your plan khaleel karka yi wasa dani fa ranka zai baci fiyeda tunanin ka. “Am sorry momy I wouldn’t insha Allah. Ya juya, ta rasa yazatayi da annoying boy din nan nata, duk Abubuwa sun cakude mata.

Key yabawa driver tareda yimai kwatancen gidan Aunty Raliya, domin yanada uzuri idan yaje bazai dawo cikin lokaci ba zata dauke mai hankali, wata motar ya dauka yayi sabon titi gidan Kawu, Wanda yasan by that time yadawo daga aiki, saida ya shiga har cikin gidan kamar y’an da suka saba ya gaida matan gidan kafin ya isa falon kawun,
“Khaleel kaine? Ya gaida shi ya zauna akasan dadduma, kafin yace, ” kawu nazo ne akan tafiyar da nafada maka, zantafi cikin satin nan insha Allahu. “Masha Allah toh ai badamuwa tunfa harkar cigaba ce kuma hakan nada kyau saikayi kokarin dawo da duk wasu dukiyoyin ka nan gida zaifi, saboda halin kasashen can, Allah ya taimaka yasa Albarka.”Amen Amen. “Toh da matan zaka tafi ko kai kadai? D’an shiru yayi kadan kafin yace ” da Naziya zantafi kawai saboda Momy…. Ya kora mai Abinda ke faruwa, “kai malam balkisu bata girma da rigima kullum, toh Allah ya baka ikon daukar duk wata jarabawa.
Daga nan ya dawo gida, Wanda ya samu driver ya dawo, dafe kai yayi tareda ciro wayar shi ya fara kiran ta.

Lokacin da taga sakon kayan ta shak’a sosai, wato ya samu Abinda yake so shikenan ta tashi aiki, har baya marmarin ganin ta tunda ya aiko da kayan, shiru tayi fuskarta a turbune har Aunty Raliya ta gano ta tace ” toh su naziya ansan dadin miji, shine ake fushi don baizo ba, ko dai inkirashi infada mai yazo ya dauke ki? “Kai Aunty niba haka bane. ” don Allah can sakarya karki fito ki nunawa mijinki soyayya, Allah yabaki miji karshen ado ki tsaya wani jan aji wata ta siye zuciyar shi kinsan dai bake kadai bace, don haka ungo wannan,. Ta mika mata cup mai hade da Zuma mai hadin magani, “shanye kibani cup yanzu banda sanya kitashi ki tsuma kanki mace ba gyara hoto ce don batada banbanci da naman da ba magi.

Kunya taji ta shanye ba musu ta mika mata cup din, she is ready ta gyara domin khaleel zata iya komai saboda shi, yanzu haka damuwar ta ko yaje wurin salifa ne, shiyasa takejin kishi sosai, khaleel ba irin mazan da mace zataso ta raba da wata bane. Jin karar wayar ta yasa ta sauke Ajiyar zuciya ta dauka. “Am sorry baby kinga kayan? ” nagani. Tace, “bazaki tanbaya me ya hanani zuwa ba?
” no need ai nasan kanada wani nauyin da zaka sauke. Fuskar ta a hade tafada tana nufar cikin dakin Aunty Raliya don kartaji me take fada.
“Nauyi??? Oh haka ne yanzu na tuna da inada wani nauyin, kinga d’an gata ko, bari inje in samu second wow Ibrahim you are very lucky Amare biyu in two nights. Kit ta datse kiran tareda kashe wayar baki daya. Dariya yayi cikeda nishadi ya nufi part din ta, kamshin ta kamar tana nan tuni yaji kasala. ” my weakness my pain relief, you are not here to heal my wounds. Ya zube a sofa ya runtse idanun shi yana hango each and every moment dinsu da ita, tuni yaji ya rasa natsuwa, ” oh god I can stay away for too long baby.

Gefen Naziya kuwa, ai kirjinta kamar zai fashe saboda kishi harda kwallar ta, saida Aunty Raliya ta kirata ta fito suci Abinci,
A wunin a cikin damuwa tayi shi har dare,
Ta kunna waya tana jira ko zai kirata shiru, harta kwanta tana kallon wayar, Wanda Aunty Raliya tuni tayi turaka, tabarta ita kadai a dakin sai d’an karamin yaron ta,
Khaleel tunda ya dawo mosques ya kulle part din ya koma cikin gidan, anan momy ta hada mai Abinci yaci ta zauna tana tayashi hira, yana faman tura bayanan shi ta internet, shigowa tayi cikin lingerie baka Y’ar guntuwa, saboda rashin tarbiya ta ratso harabar gidan kai bako hula kafarta sai takalmi mai gashi na bedroom.
Kirjinta a rukuun su bako bra tana tafe tana warware duwai wai Wanda kana gani kasan saida aka hada da taimakon bature, kamshin perfumes din ta ne marasa dadi yasa ya yi saurin dago kanshi ya ganta, lokacin yaji wani irin Amai da tashin zuciya, Wanda duk sanadin kwabe kwaben da akayi ne don jan hankalin shi da tsafin malamai, hanky din da ke gefen shi ya dauka ya rufe hanci tareda mikewa yace momy” am going inside.
Yayi gaba Abinshi, da system dinshi, ” OK good night my son. Tafada cikeda fara’a, itako Jakar juyawa tayi gaban momy. ” momy see nayi? Daga kasa har sama ta kalle ta, fauziya ma tafita fasali, “amma da kinsa bra zaifi salifa, kuma kin biyo tsakar gidan nan a haka gamasu gadi tundaga part din ki? ” oh what is there nida gidan mijina wazai samin ido, please zanbishi ciki don Allah kije ki kwanta da wuri bamason takura kar sai muna tsaka da hutawa muji motsin ki, good night. Ta juya tana kada mata duwawu kamar wata sa’ar ta. “Kan uba Amma salifa kina neman Abun da zanci uwarki keda uwar taki me daure miki gindi….. Saurin juyowa tayi a zafafe, ” what? Kamar zata kifeta da Mari tace “mai maita inji balkisu, uwata kika zaga? Fada inji wallahi yau har hakorin makkan ki sai ya futo. Kirji Momy ta dafe tareda zaro idanun ta duka waje tace ” salifa ni kike fadawa haka? Ni kike zagi? ” fin uwata kika yi da bazan zageki ba ke wacece, now excuse me kafin kisa infara tsiya ya anan nayi mugun hadi. Tayi ciki.
Bakin momy sake ta zube a kujera ” na shiga uku ni balkisu, Salifa haka zamuyi dake tun baki samu gindin zama ba?
Jeki Y’ar banza ai Wanda zaki tarar dai dai yake da iya shegen ki, yarinya inason kafaki inason in lallaba shi ya kulaki kifara da haka, toh kije ki karata na tsame hannu na, kuma ko gobe idan naso zan Aura mai wadda tafi uwarki kudi shegiya tanbadaddiya.
Dakyar taja kafarta tayi cikin daki tana tsinewa Salifa.

Yana shiga saida yayi bathroom ya yi brush domin kwanciya ya canja zuwa short bako singlet ya fito, inda yayi turus domin ganin tayi dai dai ta ware kafafun ta yana hango har kanfanta, “kut, ke uban me kikeyi anan? Yafada yana yamutsa fuskar shi domin Allah ya gani minti talatin shida ita sai ya Amaye y’an hanjin shi, wani irin juyi tayi tana mika domin emergency tasha yafara aiki kuma overdose, “dake nake sakko min a gado kafin ranki ya baci uban waye ya kiraki nan?
Ganin bazai zo ba ya tsaya unnecessary talks, ta taso tana layi hade da lankwasa, ” tana zuwa ta fada jikin shi, ” saika kirani ne? Kaifa mijina ne nazo ne ka rayamin wannan daren, so nake kasani ihu kamar yadda kasa wannan Karamar yarinyar, don’t worry kaima sai nasaka ihu, Allah ya horemin dadi. Saida yagama jin zancen ta ya jefar da ita gefe, “fyade zakiyi min kenan? Ok go ahead. Shine kawai ya iya fada, ya matsa zai kwanta a kujera, domin he just hate that bed, ta batamai gadon shi mai cikeda tarihi, tashi tayi ta kuma matso shi kamar zatasa kuka, ” haba khaleel macece nifa mai lafiya niba irin fauziya bace I can’t take it I need you please give me my right, tana kokarin rungume shi . “if you touch me once again…….. Yafada yana nuna ta cikeda gargadi mai tsauri,
“Mutuwa zanyi idan baka bani Abinda nakeso ba yanzu am honey wallahi please help me, meye wai a ciki mace kamar ni inzo Ina sallama maka jikina me daraja da tsada kana guduna, yanzu gani na kawai a haka ya isa ace ka yayyaga kayana kafara bani wuta Amma ka tsaya jan aji, don’t worry ba Wanda zaisan daga zuwa na ka kusance ni ,I know All this long sai jiya ita ka nemeta, ni am matured bazaka sha wahala ba zantaima ka mak…… Tureta yayi nesa dashi ya mike a zafafe, ” no need to prove your character to me I know you in and out, and listing, all my life bantaba zina ba don haka bazanyi rayuwa da mace irinki in gurbata zuri’ata ba, and yes don’t even dream again akan ni Ibrahim khaleel zan hada jikina da naki, ke nifa bawan Naziya ne kishi nake tayata banaso wata tana rabar matani yanzu ma dole inyi wankan tsarki, second, only her can move the man in me, ganin ki nakeyi kamar wannan wayar, Ke kin isa ki mayi mafarkin bin hanyarda my diamond tabi, she is a diamond, Unique my first lady and last, third, kina tunanin akwai Matar da zatasani ihu idan ba Naziya ba a duk fadin duniyar nan? Ita kadai ce mace a idanu na you are not woman enough for khaleel, now if you can excuse me I have something to do, get out. Ya nuna mata hanyar waje, wasu irin hawaye ne masu mugun zafi da takaici ke zubo mata, cikin zafin rai da kuma wai wayewa tayi wani irin kai hannun ta gaban shi tace “Wayyo khaleel wannan ai tafi karfin ta dole tayi ihu, ni ce size dinka nice mace dai dai da fitinar ka nice zan iya gamsar dakai insaka…… Kallon hannun ta yayi ya daga hannu ya wanketa da wasu irin hot hot slapped har uku, tuni ta sakeshi ta zube tareda sa ihu, hannu yasa badon yasoba yajata kamar leda ya watsa wajen dakin ya datse kofar shi.
Saida ta bugu da bango, Kara tasa mai karfi, har momy ta jiyo, kuma tasan ba kukan dadi bane wannan, tafito da gudu. Lokacin shi ya datse dakin shi yayi bathroom domin dole ya wanke jikinshi in and out.

“Ke me yafaru kuma? Momy tafada tana shirin dafata, ta buge hannun ta tana kuka tana rashin kunyar, ” karki tabani tunda bakida wutsiyar da zaki bani, wallahi Wannan yarinyar ta wanke ta bashi ya shanye baya ganin wata mace sai ita ace yaga mace kamar ni gabanshi kamar lagwani…… Barin wurin momy tayi domin bazata iya jin wannan rashin kunyar ba, ita da akwai Alkunya a tareda ita har yanzu. Ta shige tana tofin Allah tsine, da ace batayi mata rashin kunya ba da ta taimake ta Amma yanzu haka shawari take wadda zata ture mata gwamna tin shegiyar yarinya,

Saida yayi wanka kusan na minti talatin kafin ya fito, ya fesa room fresheners Kala Kala saboda karnin ta ya fita mai a dakin,
Saida ya kimtsa ya hau kujera yaja wayar shi, “Am missing you my diamond, ya kirata, Wanda har lokacin takasa bacci zuciyar ta na wurin shi, jitake kamar tazama kuda taje wurin shi, tayi wani irin sabo dashi da yanzu ko Kwana ba’ayi ba tafara ji ajikinta, lallai tana yimai zazzafan so, tana ganin kiranshi ta wasu hawaye masu zafi suka zubo mata, “bazan dauka ba sai yanzu zaka tuna ka Ajiye ni anan. Tafada cikeda wata irin shagwaba da batasan dalilin taba, saida ya kuma Kira ta kusa tsinkewa, tayi picking domin zuciyar ta batada karfin da zata iya rejecting dinshi, tana sakawa a kunne tafara kana nan kuka, Wanda tuni ta sagar mai da gabobin jiki da kuma zuciyar shi, “oh my god baby what is that? “bansani ba ai hoto kazo ka Ajiye dole ka manta dani anan.
Wani irin sanyi yaji har cikin tsokar jikinshi yayi wata Y’ar dariya mai Kara kadan, har taji sautin ta cikin kunnen ta, “kinfi karfin hoto my love you are my life my strength my diamond my pain relief. Ajiyar zuciya ta sauke, batasan lokacin da murmushi ya subuci daga fuskar taba, kalaman shi tuni sun sanyaya mata zuciya, “me kakeyi tundazu? ” gaskiya ko karya zanfada miki? “Gaskiya. ” hhhh Ina tareda Salifa she just left. Tuni ta maida fara’ar tayi tsit, ” hello my wife, are you there? Yafada cikeda tsokana, ” talk now ki tanbayeni what happened, “matsalar kuce ni zankwanta. Tafada a d’an hasale. ” hhhh yes matsala ce babba kuwa,Amma rashinki a tare dani shine babban matsala, I can’t sleep baby, do you know what, magana dake kawai yasa hankali na yatashi, baby I need you more wallahi.
Wani irin tashi taji tsigar jikinta nayi saboda y’an da yake kashe mata murya yana hura mata iska cikin kunnen ta cikin wayar,
“Kina sit bath din kuwa? How is the place, yafara healing? Shiru tayi domin bazata iya bashi Amsa ba, ” oh god kinga anbani cream da zamu shafa wurin ya warke da wuri na manta, zan shigo da safe inshafa miki kafin inje office, hope zaki bari inga ciwon namu?
“Um um. Tafada ” why? Toh ni zan baki nawa kigani kinjimun nima har ko Ina nawa na ciwo, tare zamuyi jinyar ai, nima an bani bed rest bazan kuma aiki ba sai mun warke, “kunya hirar ke bata don haka tayi Saurin canja zancen, “Ina so inje gida gobe. Saurin hadiye maganar yayi ” wane gidan? ” gidan malam nayi kewar Inna. ” Hmm kodai bakyason magana dani shiyasa kikeso kituna min akwai saurayin ki a gidan da kikeson gani right? Zaro ido tayi saurayi? Ni banda saurayi ai d’an uwana ne fa muntaso tare. “Ya isa gaskiya banaso kina zuwa gidan idan yana nan. “Toh ai bakomai tsakanin mu kuma ba anan yakeba yanzu haka ma yana lagos ya koma. “Kut are you communicating with him? Yafada cikeda kishi, don har cikin zuciyar shi baison sadiq din nan,
Jin yanda yake magana tasan kishi ke damun shi don haka tace ” nafasa zuwa shikenan? “Hmmm better. Kinga lokaci ya tafi ki kwanta kiyi bacci gobe early morning zanzo gidan, good night. Ya datse kiran batareda yaso ba kawai yanaso ta huta ne, ya kalli jikin shi dake wani irin dripping, ” hey relax zamu hadu gobe. Yafada yana murmushi, mikewa yayi ya shiga bathroom yayi alwala domin shifa yasani bashi ba bacci, haka itama ta Kwana a dadduma batareda ta runtsa ba tana Adduar Allah ya Kara mai kaunar ta ya kuma kade musu fitina a tsakanin su Allah ya karkato mata da hankalin Momy ta gano ita bamai cutar da su bace, saida tayi sallar Asuba ta kwanta, Wanda bata tashi ba sai da Aunty ta tasheta.A hankali ta sakko tace” Aunty Ina Kwana. ” lafiya kalau ki yi wanka khaleel na falo. Idanun ta a waje tace “karfe nawa yanzu?
“Don Allah wuce ki shirya yana tareda Baban yara. Cikin sauri tayi wanka ta shirya cikin wani lafiyayyen dinkin Atamfa ten pcs sket da dinkin ma ya zauna a jikinta sosai, Aunty ta bata lafiyayyar humra ta shafa ciki da waje ta gyara sumar ta ta zubota baya tareda murza dauri akai na yayi janbaki tasa ja a karon farko kuma taga tayi matukar yin kyau, har zata zura hijabin ta tafasa ta zura slifas dinta mai kyau da ya Kara haska fararen kafafun ta, kamar
Ka sace ta ka gudu, tafiya takeyi cikin natsuwa har ta iso bakin kofar falon, cikin natsuwa tayi sallama, mijin Aunty Raliya ya amsa tareda sakin fuskar shi, “kaga uwargida na sai yau nake ido biyu dake, lallai Matar manya. Cikin jin kunya ta gaida shi kanta akasa, Wanda khaleel tun shigowar ta ya zuba mata ido, saidai wani gefen kishin ta kamar yasa ya sume yanda tayi kyau gashi ba KO hijabi wani na ganin ta, tuni yayi wani irin fici fici da ido,dole tabar gidan nan yau bazai yuwuba don baya kaunar KO yaro ne ya kalleta bare wannan katon mutum……… 🖊

Back to top button