Cuta ta Dau Cuta Hausa NovelHausa Novels

Cuta ta Dau Cuta 1

Sponsored Links

*_Typing_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_ _

 

_Shafi na ɗaya_

 

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ƙai._

……..“Ango! Ango!! Ango!”. Itace kalma mafi rinjaye da tafi fita a bakunan taron matasan dake cike da ƙofar gidan. Yayinda wanda suketa faman kira da angon bakinsa ya kasa rufuwa dan farin cikin da yake a ciki a wannan rana data kasance ta aurensa da masoyiyarsa mafarkinsa. Magana da ɗaya daga cikin abokansa ya gwargwaɗa masa a kunne ta saka shi jan hannunsa suka koma gefe. Cikin ɗan nuna yanayin damuwa da hasala ya ce, “MB ya akai haka kuma? Nifa bana son matsala wlhy, duk abinda zan ɓatama Love rai bana son shi musamman a wannan ranar ma data kasance mana ta daban…..”
“Na sani kwantar da hankalinka, kaima kasan dai bazan bari wani abinda zai ɓata farin cikinka faruwa ba JJ. Na faɗa maka ne kawai dan kar kaga an samu canji, dan yanzu haka ma nariga na daidaita matsalar, wajen da aka samu yanzu ɗin ma yafi wancan komai…”
“Amma karka manta wajen farkon muka saka a invitation card”.
“Hakan bazai zama matsala ba shima, dan kusa-da-kusa suke, dabarar da zamuyi zamu ajiye su Nure a ƙofar wancan hall ɗin duk wanda yazo sai su turosa inda aka canja ɗin. Yanzu sai ka sanarma amarya kawai, ko hakan baiyi ba?”.
“A yayi, kunyi ƙoƙari, ALLAH ya bar zumunci bari na sanar mata”.

*_DINNER HALL_*

Matuƙar ƙyau da ƙayatuwa wajen yayi tamkar dama tun farko nan suka shirya yin shagalin. Kalar decoretions ɗin wajen kalar ankon ƴammatan amarya da suka sha ƙyau har suka gaji, haka suma abokan ango shar da su. Shigowar ango da amarya ta shafe duk wani ƙyawun kowa a wajen, dan adonsu na musamman ne. Atake hasken flash ya shiga tashi tako ina, tsakanin wayoyi da camaras, a gefe mc na faman kwarzantasu, yayinda dj ya saki wani cool music mai ratsa zuciya. Ta ko’ina dai taro ya cika taro kam sai masha ALLAH, abokan ango da ƙawayen amarya nata taka rawar gani irin na bajinta tare da dangi takowace ɓangare. A yanda aka tsara komai zaka iya saka masu bikin a layin masu hannu da shuni, sai dai sam ba haka bane ba, ana dai tsaka tsaki, wato babu tsiya babu hamshaƙin arziƙi. Sai dai akwai rufin asirin ALLAH ta kowanne ɓangarorin guda biyu. Anyi taro an tashi lafiya kusan ƙarfe ɗayan dare, ango na son maida amaryarsa gida da kansa yayarta tace karya damu yaje gida ya huta zasu wuce da ita. Babu yanda ya iya dole ya haƙura suka dunguma shi da abokansa zuwa hotel da suka kama. Amarya da danginta suma suka wuce nasu gida dan sai gobe in sha ALLAH za’a miƙata gidan mijinta…..

*_WASHE GARI_*

A kaf ƴan rakkiyar amarya babu wanda baiyi santin gidan da aka kawota ba. Dan kuwa dai gida ya cika ya tunbatsa komai zam. Tabbas angon yayi ƙoƙari sai kuma fatan a zauna lafiya. Bayan kammala ƴan kai da kawo na al’ada da rabe-raben kayan gara kowa ya kama gabansa aka bar amarya da ƙawayenta. Sune suka sake gyare mata gida ana faman raha da wasa da dariya komai ya koma kan saitinsa. Sai dai amarya bata da wani kuzari tattare da ita, ba komai ya jawo hakan ba sai ƴar fargabar da aka san duk wata amarya kamila da ita a irin wannan ranar, dama ita gata bamai yawan hayaniya bace, ko ƙawayen ma ba wasu ne daban ba, daga ƴan uwa sai maƙwafta da aka tashi tare. Bayan idar da sallar magrib kowacce ta shiga sake gyara kwalliyarta sukai zaman jiran abokan ango. Ƴan halak ɗin kam basu taushe hannu ba, dan idar da sallar isha kaɗan suka iso gidan. Amarya dai na lulluɓe, yayinda ango yay tsallen turare ɗan goma zuwa inda take ya zauna kusa da abarsa kamar zai rungume, itako tana ta faman matse jiki waje guda abinka da farin shiga ga kunyar baƙunta. Suko abokan ango nata faman masa shaƙiyanci da ido yana musu daƙƙuwa ta ƙasan riga da sakin murmushi. A haka dai akai ƴan abubuwan daya dace tsakanin abokan ango da na amarya, zuwa tara da rabi ango da yaga basu da niyyar basu filin ya murje idanu ya korasu waje. Sun fito suna dariya, yayinda MB babban amininsa ya sinna masa wasu ƙwayoyin magani tare da miƙa masa gorar ruwan hannunsa yana faman ƙyafta masa idanu da masa magana a hankali. “Adai yi tuƙi a hankali, dan wannan motar ƙirar larabawa ce, idan bakai wasa ba amaimakon horn ƙira’ar Alkur’ani zakaji”. A tare suka kwashe da dariya tare da cafkewa bayan ya afa maganin batare da tambayar na miye ba ya kora da ruwa. Ango JJ ya ce, “Shege abokina, kune malaman duniya, dan shugaban mai jan ƙyalli ma a ƙarƙashin koyarwarku yake baza komarsa”. Dariyar suka sake kwashewa a tare, MB yay gaba yana saɓa babbar riga da faɗin, “Idan da matsala kai dai kai kirana da wuri na turo makanike dan ka samu damar fita shan iskar yammaci, na barka lafiya a tuna da maƙota kar’a ishesu da…” bai ƙasa ba ya wani kashe masa ido ɗaya yana ficewa a gate ɗin. Shi dai ango JJ rufe gate ɗin yay yana cigaba da dariyarsa. Kafin ya juya cikin gidan ransa fes yau ranar baje koli ta duniya a cikin rayuwar sa…
Shuuu!! Aka gitta kamar ta gefensa a dai-dai yana kai hannunsa ga handle ɗin ƙofar, kamar zai share da tunanin iskar sanyi data fara kaɗawa ce sai kuma dai ya ji an sake gitta masa yana ƙoƙarin tura ƙofar. Wawwaigawa yay damansa da haggu sai dai kuma babu kowa, cikin nuna halin ko’in kula ya ɗage kafaɗu da taɓe baki ya ƙarasa shigewa a falon.
“Amarya kin sha ƙamshi, amarsu baƙya laifi koda kin kashe ɗan masu gida!”. Ya jero kalaman kirarin tamkar shine ya fara ƙirƙirarsu saboda tsaruwarsu a bakinsa kai kace waƙace a bakin shata ko barmani coge. Bai damu da jin ba’a amsa mar ba, ya murzawa ƙofar key harda gyara labulaye da ƙyau. Turus yaja ya tsaya ƙirjinsa na bada wani irin turururumm tamkar sautin gangar Ado gwanja a tsakkiyar filin biki. Wayam falon babu komai, duk kayan alatun nan da aka ƙawata falon da shi  tamkar wata almara babu su babu alamar su. (Kai ina, wannan almara ce JJ dawo hankalinka) wata zuciya ta ayyana masa. Yawu ya haɗiye da ƙyar, tare da sakin murmushi mai kama da kuka shi adole yana son dawo da hankalinsa jikinsa. Bakinsa na rawa da karkarwa ya furta, “L-o-v-e!” a rarrabe yana runtse idanunsa da ƙarfi. Ba’a amsa mar ba yanzun ma dai, dan haka ya sake ƙarfin halin buɗe ido ɗaya da ƙyar, da sauri ya sake buɗe ɗayan ma ya shiga waige-waige yana haɗiyar yawu da sauri-da-sauri. Yanzu kam falon komai ya dawo kamar yanda yake a da, sai dai kuma kalar kayan ta canja. (JJ! Farin ciki fa ke neman juyar maka da brain, ka daidaita kanka mana). Kansa ya shiga gyaɗawa kamar tsohon ƙadangare cike da son gamsar da kansa akan dole, sai kuma kamar wanda aka ingiza ya nufi bedroom da sassarfa, yana tafiya yana waigen falon. Har ɗan datse hannunsa yake wajen ƙoƙarin rufe ƙofar bedroom ɗin da danna mata key saboda yanda jikinsa ke rawa. Cikin dauriyar azabar dake ratsa masa hannun da ya datsa ya jingina da ƙofar yana sauke nannauyar ajiyar zuciya irin ta na sha da ƙyar ɗin nan. Yakai minti ɗaya a haka kafin ya dai-daita kansa da ƙyar yana sauke ajiyar numfashi a jajjere. Kasancewar sai ka ratsa ɗan lungu daga jikin ƙofar kafin ƙarasawa tsakkiyar bedroom ɗin sosai saboda bathroom dake a wajen ya bashi damar share gumin ɗaya tsatstsafo masa da dai-daita yanayinsa da ƙyar sannan ya cigaba da tafiya a takun da bai gaza huɗu zuwa biyar ba. Bedroom ɗin ƙato ne, ga kayan gado yaji masu ƙyau dan iyayen amarya sun taka rawar gani suma. Ƙoƙarin hana kansa kallon komai yake saboda abinda ya baro baya, dan haka ya nufi gadon kansa tsaye dan yasan dai anan zaiga amaryar tasa sarkin kunya da nutsuwa. Sai da ya kai zaune yana faɗin, “Afuwan Love na barki ke ɗaya, na sallami waɗan nan ƴan matsalar ne, kin san in su MB na waje bakin mutum baya hutaw……”
Ya kasa ƙarasawa sakamakon abinda idonsa ya gane masa. Wata irin murɗaɗɗiyar macijiya ce baƙa ƙirin an mata wata kwalliya da kalar jaja-jaja mai haske kamar ƙwan lantarki. Ba’a labaran tatsuniyoyi da wasanni ba, ko’a film ɗin ƴan India da suka sabayin na macizai bai taɓa cin karo da irin wannan maciji mai girma ba. Rawa jikinsa ya farayi kamar mazari, har takai yana zamewa a saman gadon zuwa ƙasa batare daya farga ba. Gab ya kusa kaiwa ƙasa daɓar yaji an riƙoshi…
“D lafiya kuwa? Miya faru kake irin wannan kakkarwar har kana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa?”.
Nutsatstsiyar muryar amaryarsa ta ratsa masa kunne, yayinda lallausan tafin hannunta da tunda ya riƙesa a wajen dinner jiya abin ya kasa barin ransa ke riƙe da shi a yanzu ma. Kusan a tare ita da shi suka zube a ƙasan, dan ya riga ya taho gaba ɗayansa, sannan ya fita nauyi. Faɗowarta jikinsa ya sakashi sakin wani irin ihu tamkar wanda aka farkar a barci da ruwa mai sanyi. Yay wani irin mamuƙeta illahirin jikinsa na rawa. A hankali ta saki ƙara da faɗin, “Wayyo D zaka karya min awazzu.”
Kafin yau idan yaji wannan zazzaƙar muryar tata ji yake yafi kowa sa’a a duniya. Amma a yau maimakon hakan wani irin rawa da kakkarwa jikinsa keyi, ga zufa ta wanke masa illahirin jikinsa tamkar wanda yay wanka. Zumut ya miƙe tamkar wanda aka zabura ya shiga waige-waige, sam babu komai a gadon, sai ma gyaran da yasha na musamman ga filos da aka jera a kansa tamkar an zana a takarda. Sake juyowa yay da sauri yana kallonta da nuna gadon da yatsa, sai dai bakinsa ya kasa furta komai, sai ma rawa da pink lips ɗinsa sukeyi. Cikin rashin fahimta take kallon gadon itama, sai kuma ta dubesa da alamar tashin hankali a tattare da ita. “D! dan ALLAH miya faru, wlhy kana sake rikitani nikam. Jibafa yanda kake zufa. Kana nuna min gado kuma ni banga komai ba a wajen.”
(JJ ka nutsu, karfa ka ɓata wannan daren mai muhimmanci a gareka mana) wani ɓangare na zuciyarsa ya faɗa cikin tsawatarwa. Kansa ya shiga jinjinawa tamkar zuciyar tasa na kallonsa ne, ya haɗiye busashen yawu tare da sakin murmushin yaƙe ga amaryar tasa. “B..ba komai Love, dama fa ina gwada ki ne kawai naga amaryar tawa jaruma ce ko matsoraciya.” ya ƙare maganar yana damƙo hannunta cikin nasa da ƙyau. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi, sai kuma ta duƙar da kanta tana ƙoƙarin janye jikinta daga nashi dan kunya. Yanayin nata ya sake sakashi dawowa hayyacinsa da tuna masa shi ɗin fa ango ne. Ƙoƙarin haɗiye komai yake yi, duk da hakan abune mai wahalar gaske a garesa, amma dai zai gwada yin wannan jarumtar ya gani. Ayatulkursiyyu ya karanta a zuciyarsa yana tattofawa a kaikaice. Sai da ya tabbatar ya ɗaure ɗakin ɗamm acewarsa, kafin ya ƙara ɗan samun nutsuwar sake maida hankalinsa ga amaryar tasa da kanta dai ke a sunkuye.
A karo na farko ya jawota jikinsa ya rungume tsam yana sauke tagwayen ajiyar numfashi, yayinda ita kuma ta shiga masa rawar jiki irin na farin shiga, sai dai bata hanashi ba ko yunƙurin janye jikinta har kusan mintuna biyu daya saketa dan kansa. “Yau dai ga ni ga Love a gida ɗaya, ɗaki ɗaya a matsayin ma’aurata”. Ya faɗa yana sake riƙo hannunta duk biyu cikin nasa da ƙyau tare da gyara zamansa ya fiskanceta. Murmushi ta saki tana ƙara ƙasa da kanta tare da jan mayafinta ta rufe fuskarta. Shima sai ya saki wata ƴar siririyar dariya cike da nishaɗi, hannu ya kai ya yaye mayafin yana mai ɗago haɓarta ta yanda zaiga fuskanta da ƙyau.. Wata muguwar zabura yayi baya yana mai waro duka idanunsa waje jikinsa na karkarwa batare da ya ma sani ba ya furta, “Anoosha!!”.
Cike da salo tai masa luuu da idanu tare da sakin sassanyan murmushin da a fuska ɗaya ya sanshi kuma ya taɓa ganinsa, bai kuma sake ganinsa ba. Tsabar kiɗimewa da shiga ruɗani har yana bugewa da gado wajen zabura da ƙoƙarin tattara babbar rigar jikinsa alamar zai kwasa a guje yaji caraf an riƙesa…….✍️

*_Tofa babbar magana, wai ango JJ mijin amaryar da ko sunanta bamu sani ba mi shika hwaruwa ne hakanga kuma? Anya kuwa ba….Bara dai na iya bakina abinga walle bana hiɗi bane._*

_Alhamdullahi inata alƙawarin gareku na yin free book ALLAH bai ƙaddara hakan ba sai yanzu. To Amin afuwa gani zan cika alkawarin in sha ALLAH. Ina fatan wannan littafi zai ƙawatar da ku tako wace fiska, cakwakiya, nishaɗi, ƙalubale, ƙaddara, son zuciya, kai abubuwane da yawa ya wawuso tako wace fuska, zakuma ku fahimci saƙon da yake son isarwa, dan salon na musamman ne, idan nace na musamman ina nufin na musamman a gaba ɗaya musamman ɗin.

*Kumuje zuwa gidan ango muji yaya zai ƙare da wannan daren farko nasa, dan naga na musamman ne fa .*

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

Back to top button