Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 60

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*60*

*Masu turamin messages Ina godiya bisa kwarin guiwar da kuke bani nagode Allah yabar kauna, anty sofy, Binta,. Limsy , Balkees soyayyar da kukewa wanga buk daban ne Ina yinku irin sosai din nan*

Dakyar bacci ya dauketa sai faman Juyi take tare da tunani iri iri, can bangaren Ayman kuwa yayi matukar kewarta sosai he wish that kowane dare tana kusa dashi , Yana kwance Yana wannan tunanin Failuzaa ta kwata gefensa ta fara masa wasu abubuwan da ya dagula masa lissafi daga nan labari ya canza dama tayi missing nasa abin nema ya samu…

Washegari da wuri hajjo ta tashi saboda tana da lectures by 8 kitchen ta shiga ta dafa indomie da Scotch egg ta koma falonta sauri take gashi har yanzu bataji motsin mutanen gidan ba tabe baki tayi ta gama breakfast nata ta shirya lokacin 7:40 ta kulle part nata ta wuce harabar gidan . Kai tsaye side din Fauzan ta nufa tayi sallama ya Bude kofa ya fito Yana gaisheta cikin girmamawa tace ” don Allah school zaka saukeni Ina da class Kuma naga ya Ayman bai tashi ba ” “ok ba matsala bari na dauko keys ”
Ya koma ciki daga baya ya sameta jikin motocin ya Bude wata Lexus red color sai daukar Ido take ya Bude back seat yace mata Bismillah…ta shiga yayi dropping nata a school.
*9am* ya gama shirinsa cikin black suit da grean shirt sai army green tie da takalmin cover black color yayi fitting nasa sosai ya fito tamkar Wani bakin balarabe saboda gashin Kansa da yasha gyara, Bai tsaya yin breakfast ba saboda sun tashi a makare Failuzaa tana kitchen tana hada breakfast ya wuce part din Hajjo yayi knocking yakai sai 3 shiru ya cire waya ya kira layinta no answer, shiru yayi Yana tunani meyasa taki Bude kofa kodai fushi take har yanzu ya Duba agogo Yana da meeting by 10 yanzu after 9 donhaka ya wuce kawai ya fice daga building din. Fauzan na ganinsa yazo ya karbi bag din dake hannunsa Yana masa barka da fitowa ya amsa a takaice, wata hummer jeep Wrangler ya Bude masa gidan gaba ya shiga sannan ya zagaya zuwa bangaren driver maigadi ya wangale gate suka fita cikin speed, sai da suka baro layin ne Fauzan yace ” Allah ya taimaki Yarima anjima zanje daukar hajiya a school”
Ya juya Yana kallonsa da alamar tambaya Fauzan ya Gane meyake nufi yace ” Ina nufin anty amarya da safe nayi dropping nata tana da class 8_10 da Kuma 10_12 ” Wani boyayyen ajiyar zuciya ya Sauke na samun relief sannan ya furta ” okay” ahaka suka cigaba da tafiya Babu Wanda ya sake magana.

*Nnamdi Azikiwe international airport Abuja*

Sanye yake da brown t-shirt da black leather trouser sai black half cover shoe irin na Maza idanunsa sanye da black sunglasses, hannunsa rike da Fahad d’ayan hannunsa Kuma rike da trolley zee na rike da karamar bag sai uban tumbin da take turawa haihuwa ko yau ko gobe, sun Kara haske sunyi fresh baya son dawowa Amma an damesa a wurin aikinsa shiyasa ya dawo, wajen parking lot suka tsaya Yana waige waigen Neman driver din gidansu waya ya cire ya kira driver din bayan ya kashe call din ya Kalli zee yace ” u wait here…zanje na duba motocin Ayman dake wajen customs za’ayi clearing dinsu idan driver yazo ku wuce kawai so that I’ll not keep you waiting..” yatsina fuska tayi ” yanzu mu kadai zamu koma kenan kasan I need you yanzu kada labour ya taso min baka kusa ” ” c’mon zee kinsan fa da zancen motocin nan wai ya kikeso nayi ”
“Hmm …yanzu shi uban me zaiyi da wadannan motocin naga gidansa motoci sunfi 3 ”
“Ke kika siyo masa ne Ina ruwanki nifa banson gulma kinsani ” kwafa yayi ya juya ya tafi , Fahad ya koma kusa da zee ya tsaya, tabe baki tayi sai Kuma ta Ciro wayarta layin Failuzaa ta fara Nema bayan Yan seconds tayi picking…daga can bangaren Failuzaa ta fara magana
” Anty zee… oyoyo da alama kin dawo kenan naga wannan layin naki na Nigeria ne ”
” Yanzu shigowata ko gida bamu Kai ba nace bari na Miki albishir kunsamu sababbin motoci zafafa ” “haba dai anty zee .. a Ina kika gansu ” ” hmm billionaire husband naki yayi ordering lambos guda biyu zafafa gaskiya Failuzaa ki rike mijinki Yana jida naira what…Kinga motocin nan kuwa wen I mean Lambo fah I mean it Lamborghini Gallardo fah can you imagine kiyi searching kudin in dollars ki gani ” dariya Failuzaa tayi daga haka zee ta kashe wayar tana ta tunani inama a ce ita aka siyawa wannan motor da Abuja zasusan da zamanta y’ar VP da minister, Anya ba tisa Aman zatayi ya Siya mata kuwa idan yaso idan kudinsa bazai Kai ba ta nemi ciko gun iyayenta don gaskiya wannan motocin karshe ne Anya ma akwai Mai Hawa irinsu kuwa , tana nan tsaye tana lissafin banza har driver ya karaso tahau fada akan meyasa ya ajiyeta baizo da wuri ba Yana Bada hakuri ya dauki kayan su kafin ya Bude mata mota suka shiGa ya jasu suka tafi.

12 suka fito lectures a gajiye hajjo tace” ni gida zan wuce besty nagaji gashi yunwa nake ji wallahi ” Ummeey ta gyara tsayuwa tace ” ba sai kizo muje restaurant ba kici abinci mu huta kafin ki tafi ” dariya hajjo tayi” haba dai besty restaurant Kuma ai mun wuce wannan , tab har nayi imagining Ina cin abinci ya Ayman yazo ya sameni tab.. za’a ga drama kinsan mutumin nan da ra’ayi kuwa , yanzu ma yace Babu ni Babu gyale fah sai dai hijabi” tabe baki Ummeey tayi” tohh…masu miji manya yaushe akayi auren har zai fara kafa Miki dokoki, lallai yanzu a takaice zaki daina saka veils kenan ”
“Gaskiya idan a school ne yahana bansan ko unguwa ba ”
“Lallai kuwa kina da aiki wallahi idan nice bazan taba yarda ba , gara tun yanzu ki dakatar dashi idan bahaka ba zaki wahala a gidan ko don Yana ganin Yana da kudi ne oho ” ” haba ke kuwa meya kawo batun kudi Muna maganan hijabi” hada rai Ummeey tayi dai dai nan Fauzan ya karaso cikin hummer jeep din Ayman hajjo Bata Gane motar ba duk daliban Dake wajen suka juya suna kallon motar, yayi parking ya fito Ummeey tace” tohhh…kaga masu mota kala kala na safe daban na Rana daban, anzo daukar ki hajiya ”
Hajjo ta juya suka hada Ido da Fauzan ta Kalli Ummeey tace” toh sai jibi kenan gobe Muna free ki mana karatun c.a ”
“Ehh ga Mai rashin aikin Yi ba dole kice a Miki karatu masu miji ” dariya hajjo take ta dauki abi a wasa tace ” toh aikin me zakiyi nidai na tafi ”
ta juya ta tafi Fauzan ya gaisheta ta amsa ya Bude mata mota ta shige tana d’agawa Ummeey hannu. Wayar Ummeey yayi ringing anty zee ce cikin Jin dadi tayi picking
“Big anty an dawo kenan ”
“Ki sameni a gida yanzu duk abunda kike ki barshi ki taho Ina gida” dif ta kashe wayar Ummeey na murmushi ” Kai anty zee an dawo kenan uwar daru ” mota ta wuce driver yaja ta fada masa wuse zasu tafi gidan anty zee ba gida zasu koma ba nan ya dauki hanyar zuwa Wuse.

Fauzan na parking cikin gida Aman ya hango jingine jikin wata dalleliyar mota Ayman na tsaye a gefe gaban Hajjo ne ya Bada sauti Ras..ganinsu da tayi tsaye yasa gaba d’aya kafafunta sun mata nauyi dakyar ta fito tamkar munafuka tana rike da handbag nata tafiya take a hankali kanta na kallon kasa taki d’agowa bare su hada Ido, Ayman ya kura mata Ido Aman kuwa kallo d’aya ya mata yayi saurin dauke Kai ya cigaba da maganan da yake. Fauzan ya karasa inda suke ya mikawa Aman hannu suna gaisawa tazo ta wuce zata shiga cikin gida kamar daga sama taji muryan Ayman na cewa ” hey babygirl Babu gaisuwa ne ” cak! ta tsaya Bata tafi ba Bata Kuma d’aga kanta ba, sauri yayi ya karasa kusa da ita Yana karban bag nata fuskarsa dauke da murmushi ” welcome back ya school din ”
“Alhamdulillah Ina yini ”
“Shine kika tafi baki nemeni ba ” ya marairaice ta wutsiyar Ido take kallon Aman Wanda ya Maida hankali kansu, guntun murmushi tayi” sorry nayi leti shiyasa Kuma I was thinking that u guys were sleeping ne ”
“Ok..ga Aman baku gaisa ba ” Ido ta ware Yana kallonta yace ” c’mon wat is there komai kaddara ne daga ubangiji Kuma Hakan bazai Hanaku gaisawa ba he is my bro after all ” Wani miyau ta hadiye batasan ta Yaya zata fara magana da Aman ba donhaka ta wuce cikin gida, murmushi yayi ya juya rike da bag din nata ya komai wajen Aman suna kallon juna Aman yace ” Amma Kai shegen kayane fah, dama haka kayi zurfi cikin son yarinyar nan amma don tsabar zurfin ciki ka barni Ina ta hauka har sonta ya kusa kashe ka ba don Allah yasa Fauzan yayi jahadi ya tona asirika ba da yanzu tuni kana barzahu ” duka Ayman yakai masa ya kauce Yana dariya , ya koma nesa dashi yace ” dama ance shiru shiru mugun kaya ashe Muna tare da sharukhan bamu sani ba , har an iya fadan Wani babygirl ”
“Man are you jealous” hararinsa Aman yayi yace” ka gode min nabar Maka ita da wallahi kasan baka Isa tace tana sonka ba ”
” Hey..hey ya isheka matata ce please”
“Kai ka sani munafuki ni gida zan wuce” dariya Fauzan yake musu suna burgeshi yadda suke kaunar junansu, murmushi Ayman yayi ya juya ya koma kusa da Aman din ya rikesa a kafada yace ” thanks man gaskiya motoci sunyi Kyau nagode sosai”
“Your choice..ni dan aika ne , da alama yanzu har magana ka koya ”
“Banson iskanci Ina Maka rakiya idan baka so sai na koma ”
” Fauzan zaiyi dropping dina wajen Ammi kafin na wuce gida” “ok ka gaishesu anjima zan shigo Umma tace jibi zata koma ” “ok sai ka shigo ” Fauzan ya tada motar yazo daf inda suke Aman ya Bude front seat ya shiga suna d’agawa juna hannu sannan suka tafi.
Wanka hajjo ta shiga hade da alwala bayan ta fito ta saka wata free gown mara nauyi boubou style irin na Ethiopia ne Bata shafa komai ba sai turaruka ta duba time na sallah ya kusa ta fito falo kenan Failuzaa ta shigo nan suka gaisa ta ajiye mata abinci godiya tayi Failuzaa tace ” albishir anty amarya”
“Goro…”
“Kinga wannan motocin na harabar gidan wannan sababbin black n white din nan ?” “Wallahi ban kula ba dayake lokacin da na shigo suna tsaye ”
“ai Ina gindin window Ina kallonki Kinga mutumin naki kika sunne Kai kamar Baki gansu ba ” cike da mamaki hajjo tace ” waye kenan ?”

“Aman nake nufi ko zakice bakisan Yana wajen ba ” “seriously? Kinsan ni ban kula ko dashi da waye awajen ba kawai dai naga mutane shiyasa na dauke Kai”
“Allah Sarki Aman idonsa kaf Yana wajenki har yaban tausayi” Wani kallo hajjo ke mata tayi saurin canza magana tace ” toh motocin ashe mu aka siyawa naji Yana fadawa Aman din , nidai white din nake so ke sai ki dauki bak’in” hajjo dai na ganin iKon Allah murmushi tayi tana mamakin halayen Failuzaa wato bayan kissa harda gulma da saka Ido cikin lamuran mutane ta iya, shigowarsa falon ya katse hirar Failuzaa ta tashi tana cewa ” toh anty amarya ahuta gajiya bara naje nayi sallah ” ta juya ta fice Ayman Yana zuwa ya rungumeta Yana sauke numfashi lamo tayi tana Jin bugun zuciyarsa ” I really miss you baby girl, yau kadai da baki kusa dani I feel so lonely” batayi magana ba sai da ya gaji ya saketa suka koma kujera suka zauna Yana kallon kyakkyawar fuskarta natural beauty sai sheki take gyaran fata da aka mata ya dada fito da hasken ta na asali ga Kuma qamshin da take Yana saukar masa da kasala , Kiran sallah aka fara shiyasa ya tashi yace ” let me pray ”
“Ok ” ta amsa a gajarce , Yana fita ta Bude abincin faten doya ne yaji kifi sosai sai qamshi ke tashi nan ta dauki spoon ta zuba a plate ta fara ci tana lumshe Ido saboda ya mata dad’i sosai gaskiya Failuzaa ta iya girki idan batayi da gaske ba zata kureta wajen sarrafa abinci.

Back to top button