Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 90

Sponsored Links

90….. Da yamma karfe biyar Ikram ta dame Momy xata koma gida ita, dama tun xuwanta gidan da ta ga Rukayya na nn ta ki sakin jiki duk ta wani hade rae taji bata son xaman gidan kuma duk da su Seeyama na nn, a daddafe tayi karfe biyar a gidan snn Momy ta sa Drivernsu ya maida ta gida, har bakin mota Rukayya da su Seeyama suka rakota duk ta hade rae ta daga ma su seeyama hannu kawae drivern ya ja motar suka bar gidan, shidda saura minti ashirin suka iso gida, ta fita tayi ma drivern gdya ya bude mata booth ta dauki tsaraban da Momy ta hada mata snn tayi cikin gida, bbu kowa falon sae TV dake ta aiki, jin kamshin girki yasa ta gane Jummai na kitchen ta haura sama xuwa dakin Mami, Mami bata dakin sae mata biyu da ta gani baxa su wuce shekaru ashirin ba duka xaune kan gadon Mami, farar ta daura mayafin da ke kafadarta xuwa kanta, Ikram ta dauke kai tace “ina yinin ku” duk suka amsa da lfya, ajiye ledan hannunta tayi ta fice daga dakin ta sauka kasa xuwa gun Jummai, don jin su waye matan don bata taba ganinsu ba, Jummai na parboilin din shinkafa tace “A’a yaushe kika dawo Ikram” Ikram ta gaisheta tace “Mama jummai ina Mami fa ban ganta a daki ba” Jummai tace “ki duba daya dakin tana ciki” Ikram tace “to suwaye wnn matan dake dakin Mami, naga suna min wani irin kallo a ina suka san ni?” Jummai bata ce komai ba tana ta aikin gabanta sae da Ikram tace “Mama Jummai” Jummai ta juyo tana kallonta tace “bakin Mami ne” Ikram bata ce komai ba ta juya ta bar kitchen din ta koma sama ta shiga dakin da Mami take, Mami na xaune dakin Ikram ta karaso ta gaida ta, Mami tace “har kin dawo” Ikram tace “ehh momy ma tace in gaishe ki,” Mami tace “ina amsawa” ta kwanta gefen Mami tace “baki kika yi Mami” Mami tace “ehh” Ikram ta mike tace “xan je gun Mama jummai” karfe tara saura Ikram na xaune dakin Jummai Mami ta shigo tace “Jummai ku je da Ikram ku siyo fruits inda kike siyo min, sae driver ya kai ku” Jummai tace “to” Mami ta mika mata kudi ta fita, Hijab kawae Ikram tasa suka fita da Mama jummai, suna fita Khaleel ya shigo gidan Mami na xaune falo, ya karasa ya xauna kasan carpet ya gaisheta ba tare da ta kallesa ba ta amsa, Mami tace “ka dauki matar ka ku bar min gidana ynxun nn” ya mike bae ce komai ba ya haura sama, tana xaune ita kadae a dakin tana danna wayarta don kawarta ta tafi da yake nn Abujan take, ya karaso ya xauna gefen gadon yace “a shirye kike? Xamu tafi gida” ba tare da ta kallesa ba tace “ehh” ya mike ya fita ya kuma sakkowa ya sami Mami a falo yace “ikram fa Mami” wani mugun kallo Mami tayi masa a fusace tace “Ikram? Me xata maka” yace “gida xa mu tafi” tana girgixa kai tace “tun kan in bata maka rae ka tashi ka ban waje, bana son magana, da wace Ikram din xaku tafi? Get out Khaleel” mikewa yyi ya haura sama, ba a dau lkci ba ya sakko yarinyar na biye da shi a baya fuskarta lullube da mayafi handbag dinta a hannunta, ta iso har gaban Mami ta durkusa Mami tace “to Allah ya kiyaye hanya, ya kuma bada xaman lfya” mikewa Khaleel yyi ya ma Mami sae da safe yarinyar ma hka snn ta bi bayansa, Mami na jin tashin motarsa ta jinginar da kanta jikin kujera a hankali, lallai Khaleel ya nuna mata iyakarta, bayan fitarsu da minti goma su Ikram suka shigo, ranar dae Mami ranta a dagule ta kwanta, Ikram kam ina tasan meke faruwa, ko tambayar rashin ganin Khaleel din ma bata yi ba tunda ba damuwa tayi ba tana ta harkar gabanta, washegari Mami tasa ta hada kayanta Jummai ta rakata Driver ya kai ta suleja gun Ammi tayi hutu. Karfe sha biyu jummai ta bar gidansu bayan tayi ma Ammi sallama da Driver, Ammi na kallon Ikram bayan fitar jummai tace “mijin ki fa ikram, ae ba mami ya kamata tace ki xo hutu ba” Ikram dae sae cin maiman da mmn altine ta aiko mata take bata ce komai ba, Ammi ta daka mata tsawa “ba magana nake maki ba” ikram ta turo baki tace “to nima ban sani ba Ammi” Ammi tayi shiru tana kallonta can tace “baki bar wnn dan iskan halin naki na turo ma mutane baki ba ko” ikram bata ce komai ba Ammi tace “ki tashi ga kayan miya can ki gyara ki kai nika ki dawo kiyi miyan, bbu abinda xanyi tunda ga ki” Ikram ta yo waje da ido tace “ae ban iya ba Ammi”
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikhram~ By Khaleesat Haiydar.

Back to top button