Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 39

Sponsored Links

PAGE* 3⃣9⃣

Zarah zamanta tayi nan tafara gyangyad’i saida taji baccin yana cinta sosai sannan tamik’e tana turo baki tashiga bedroom d’in yarima,

Har ta kwanta saman gadonsa sai kuma taji bata iya yin bacci haka dan haka tatashi saida tacire kayan sannan tashiga toilet d’insa cikin sauri tayi wanka tafito d’aure da towel, saida tatsane jikinta sannan tafara tunanin abinda zata sanya, raba ido tafarayi daga k’arshe da taga ba yadda zatayi yasa taja tsaki tace nasan halinsa ina iya zuwa zan fita yayi min wulak’anci
saman gadon tahau takwanta tare da k’udindine jikinta da blanket bata kawo komai a rantaba takashe gloves ahaka bacci yad’auketa.

Wajen 12 yarima yakashe kallon yatashi yashiga bedroom kunna gloves d’in yayi tare da kai kallonsa a bed d’insa zarah k’udindine take tana baccinta hankali kwance murmushi yayi sannan yacire kayansa yawuce yashiga bathroom

Bayan ya fito shiryawa yayi sannan yakashe gloves d’in yakunna marar haske sosai yaje yakwanta gefen zarah,

Zuba mata ido yayi yanayin yadda take bacci tana burgesa, ya dad’e yana kallonta sannan daga baya yajanyo blanket d’in zai rufa shima, zaro ido yayi ganin yadda jikinta yabayyana dan gaba d’aya towel d’in ya rabu da jikinta, k’irjinta yazuba ma ido yana kallo sannan daga baya yaruntse idonsa yana jin wani iri a jikinsa, duk yadda yaso yadaure kasawa yayi ahankali yabud’e idonsa tare da yaye dukkan blanket d’in.

Rungumota yayi jikinsa zarah baccinta kawai take hankalinta kwance ahankali yafara zagaye hannuwansa a jikinta daga k’arshe yamaida yakwantar da ita sannan yacigaba da wasa da kowane sashe na jikinta,

Zarah cikin bacci taji kamar wani abu yana bin jikinta dan ji tayi kamar ana mata tafiyar tsutsa, dak’yar tabud’e idonta tare da safkesu akan yarima da yake a k’irjinta,

Zaro ido tayi tare da d’aura hannunta a kansa tana nema taturesa muryarta tana rawa tace pppplease yarima kadaina,

Yarima duk yafita hayyacinsa ahankali yad’ago kai yakalleta da narkakkun idanuwansa batare da yayi mata magana ba yahad’a bakinsu yafara kissing d’inta, inda hannuwansa suke yawo a kowane sassa na jikinta nan da nan Zarah tamik’a wuya dan dama ita kanta tasan tayi missing d’insa.

Sun dad’e suna abu d’aya har Zarah tagaji ammah yarima bai k’yaletaba saida yagaji dan kansa sannan yabarta.

Zarah tana turo baki takalli yarima da yake kwance idanuwansa a lumshe yana maida numfashi tace shine katasheni daga baccina? Chan k’arshen gado takoma takwanta tare da janyo blanket tarufe jikinta ita kanta wani irin sanyi takeji a ranta fuskarta d’auke da murmushi a haka bacci yayi awon gaba da ita.

Yarima ma yadad’e a haka shi kansa yasan yana cikin farin ciki dan ji yake kamar yau yafara sanin Zarah, ahankali yabud’e idonsa yakalleta chan k’arshen gado ta k’udundune jikinta, jawo wayarsa yayi yaduba time lokacin 1:50am.

Dak’yar yasamu yamik’e jikinsa ba k’wari yashiga bathroom dan yatsarkake jikinta.

Bayan ya fito komawa yayi yakwanta tare da juya mata baya fuskarsa d’auke da murmushi ahaka bacci yayi awon gaba da shi.

Zarah ko da yarima yatayar da ita tayi sallah tana ganin ya tafi masallaci tasaka kayanta tafito takoma part d’inta, tama yi tunani safiya nan takwana ammah sai taga bakowa, saida tatsarkake jikinta sannan tad’auro alwallah tazo tayi sallah.

Bayan tagama saman gadonta tahau tayi kwanciyarta ahaka bacci yayi awon gaba da ita.

Wajen 10 safiya tatashe dak’yar Zarah tatashi dan ji take baccin bai ishetaba, kallon safiya tayi tace kekuma yaushe kika shigo?

Dariya safiya tayi tace tun d’azun nashigo ina parlour jin shuru baki fitoba yasa nashigo, Zarah maida idanuwanta tayi talumshe tace please safiya kibarni inyi baccina.

Janye blanket d’in da Zarah take rufe da shi safiya tayi tace ank’i d’in tunda kinje kunsha love da prince shine har yanzu baki tashiba,

Zarah tunowa tayi da darensu na jiya nan tabud’e idonta tana murmushi tace toh ina wuranki?

Hararta safiya tayi cikin wasa tace aikam dai daruwana tunda kika hana babban abokin ango zuwa dinner, mutane suna ta nemansa.
Da munsa rai tare zakuzo sai mukaji shuru ashe kina nan kin rikitamana prince dan tunda naga gayun da kikayi nasan dak’yar idan prince zai iya barinki kitafi batare da wani abuba

Ta6e baki Zarah tayi tare da tashi zaune tace kinsan dai halin yarima indai yasa kansa toh babu wanda zai iya hanasa dan haka nidai bani nahanasa zuwaba daman chan baiyi niyaba.

Safkowa tayi taje tashiga toilet tayi wanka bayan ta fito zama tayi tatsantsara kwalliyarta sannan tad’auko super English blue colour tasaka nan tamurza d’aurin kallabinta, sark’arta ta gold tasaka nan kyaunta yak’ara fitowa.

 

da k’arfe biyu daidai aka d’aura auren rahma da shaheed, auren da mutane dayawa suka hallara.

Saida su zarah sukayi sallar azuhur sannan suka shiga cikin gida da yake cike da jama’a.
Safiya jan Zarah tayi suka shiga part d’in sultana sadiya dayake a chan rahma tazauna,

A parlour suka tarar da sultana da sumayya sai wasu abokan sultana sadiya a zaune suna hira.
Cike da girmamawa su zarah suka gaishesu, nan abokan sultana sadiya suka amsa ammah banda ummah da sumayya da suka had’e rai.

Safiya ce takalli sumayya tace Aunty sumayya ina adda rahma?
Ta6e baki sumayya tayi tare da cewa kin bani ajiyartane?
Safiya murmushi tayi tace yi hak’uri dan naga tare kukene saisa natambayeki.
‘Daya daga cikin k’awayen ummah ne tace kai sumayya miye nabak’ar magana? Kikasani ko k’awayen amaryane?

yamutsa fuska sumayya tayi tace nasan baku gane wacchan ba? tanuna zarah
Eh gaskiya bamu santaba wacece ita?

Ummah ce tace toh wacece banda munafukar kishiyarta.
‘Daya daga cikin matan ne tace tace wlh sumayya banga laifinkiba toh waima ubanmi tazo yi mana a nan?
Sumayya tsaki taja tace gulmar da tasaba ko?

Safiya da zarah tsaye suke suna kallon ikon Allah , k’arama zarah da bata wani damuba dan tasaba da wulak’ancinsu Ummah.

Safiya ce tace haba bayin Allah daga tambaya sai cin mutunci? Sumayya cikin 6acin rai tace ke safiya kikiyayeni ko ranki ya6aci.
Ta6te baki safiya tayi tace Allah yabaku hak’uri sannan takama hannun zarah suka wuce wani room da taga wata abokiyar rahma ta shiga.

A chan saman gado suka hango amarya zaune taci k’walliya tasha kyau har ta k’oshi, gefenta k’awayentane suka zagayeta sunata hira.

Safiya jan zarah tayi sukaje suka zauna bakin gadon.
Zarah fuskarta d’auke da murmushi tace sannunku? ina wuninku?
Gabad’ayansu suka amsa sannan tacema rahma amarya kinsha kyau Allah yabada zaman lafiya.
Murmushi rahma tayi sannan tace Ameen nagode sosai,

‘Daya daga cikin ‘yan matan amaryace tace gimbiya wannan ma friend d’inki ce?
Girgiza kai rahma tayi tace matar Bro ce.
Kallonta sukayi sukace ba dai yarima ba?
Shi man amaryarsace 2 months kenan yanzu da aurensu, cewar rahma.

Gabad’ayansu suka juyo suka kalli zarah d’aya daga cikinsu tace ashe matansa biyu, masha Allah gaskiya tana da kyau sosai kamar prince.
Wata tace saisa baya kallon mata ashe yasan ya aje mata kyawawa a gidansa.
Sai tayita haifo mana kyawawan yara, cewar safiya.
Zarah da kanta yake sunkuye d’ago kai tayi tagallah ma safiya harara.

Dariya safiya tayi tace daga fad’in gaskiya sai harara?
shuru zarah tayi tak’yaleta, tanajib wasu daga cikin ‘yan matan suna ta maganar yarima har taso taji haushi, sai daga baya suka canza hira.

Saida sukayi sallar la’asar sannan suka fito sukaje part d’in dada basu wani dad’eba suka koma na ummin yarima nan suka zauna suna hirarsu.

Saida akayi sallar magrib sannan aka d’auki amarya aka kaita gidanta da yake kusa da masarautar, zarah cikin motarta sukaje gidan amarya, kowa saida yayaba tsari da kyaun gidan anzuba mata gaya na’azo agani dan room nd bedroom 3 akayi mata, nan akaita santi daga k’arshe kowa yayi Allah yabada zaman lafiya sannan aka watse aka bar amarya da wasu abokanta.

Shaheed kallon yarima yayi da yake shirin barin gidansu yace haba yarima yanzu kana nufin bazaka rakani wajen amaryataba?
Harararsa yarima yayi yace akace maka dole sai naje? Idan su muhammad sukaje ai ya wadatas,
Cike da jin haushi Shaheed yace shikenan duk yadda kayi daidaine daman jiya k’in zuwa dinner kayi.
Wai kai baka ganin rahma k’anwace agareni akanme zan dinga shige muku.
Ta6e baki Shaheed yayi yace nikuma abokine wanda bakada kamarsa, toh laifine dan kaje?
Rik’o hannun yarima yayi yace please yarima kataimaka karakani d’akin amaryata.

Murmushi yarima yayi yace toh shikenan naji jeka ka ida shiryawa kazo muje dan ni yau dawuri nakeson komawa gida saboda agajiye nake.
Shaheed yace angama ranka yadad’e.

 

Wajen k’arfe tara suka raka Shaheed gidansa, Tunda suka shiga d’akin da amarya take yarima bai d’aga kai yakalli kowaba dannar wayarsa kawai yake, nan abokansu da na amarya sukaita tsokanar ango da amarya, duk yadda wasu sukaso yarima yayi magana ko sunsamu shiga ammah baiyiba dan nunawa yayi kamar baisan da zamansu, nan aka k’ara yi musu nasiha sannan suka tashi sukabar gidan,
yarima yana shirin shiga motarsa saiga wasu mata biyu sun iso cikin kwantar da murya sukaimasa sallama.
Rik’e yake da murfin motar ya amsa musu ciki-ciki.
Ahankali d’aya tace dan Allah in bazaka damuba munaso kayi dropping d’inmu.
Ta6e baki yarima yayi sannan yace ba hanyarmu d’ayaba kudaije wajen wad’anchan su k’ila hanyarku sukayi.
Matan kallon juna sukayi sannan d’aya tace toh please zamu iya samun phone number d’inka?
Wani irin kallo yarima yayi musu sannan yashiga motarsa yaja yabarsu nan tsaye.
A k’arshe saidai suka koma wajen sauran abokan ango suka shiga motocinsu Cike da takaicin abinda yarima yayi musu.

Yarima ko da yakoma gida wanka yayi sannan yabi lafiyar gado yakwanta.

Zarah ko daman koda tadawo dak’yar tasamu tayi wanka takwanta batayi tunanin daman zuwa part d’in yarima ba dan agajiye take.

_Toh mudai saidai muce amarya rahma da ango shaheed Allah yabada zaman lafiya_

 

*BAYAN SATI ‘DAYA* ‘yan bikki duk suka watse zarah tayi missing d’in safiya dan ‘yan kwanakin nan da sukayi sun saba sosai, yanzu saidai zaman kad’aici kuyangintane suke d’ebe mata kewa tahanyar bata labarai masu dad’i.

Yau kasancewar girkin zarah ne kwance take saman bed d’inta kanta yana kallon ceiling da alamu tunani take, ringing d’in wayantane yakatseta ganin mai kiranne yasa tasaki murmushi dan rabonta da yarima tun lokacin bikki, saida takusan tsinkewa sannan tayi picking, yarima baijira tayi maganaba yace kihad’o min coffee yana fad’in haka yakashe wayarsa, fuskar zarah d’auke da murmushi tamik’e tanufi kitchen dan ko bakomai tasan yau zata sakasa a idanunta.

Bayan tagama had’a masa hijab d’inta tasaka kasancewar daman har tayi shirin kwanciya,

Ahankali tabud’e bedroom d’insa tashiga yarima dasauri yad’ago kai yakalleta sannan yamaida kansa yacigaba da dannar laptop d’insa, zarah k’arasawa tayi kusa tashi tare da zama gefensa sannan tace ga coffeen.
Yarima batare da ya kalletaba yace ina zuwa,
Haka yabar zarah rik’e da cup har kusan 5 minutes sannan yakar6a,
Mik’ewa zarah tayi zata tafi, batare da ya kalletaba yace ina zakije?
Murmushi zarah tayi tace zanje inkwanta ne.
Ban baki iziniba, cewar yarima da yake dannar laptop.
Marairaicewa tayi tace wlh bacci nakeji.
Ko inda take yarima bai kallaba.
Zarah turo baki tayi sannan takoma tazauna,
Yarima tagefen ido yana kallon yadda take ta fushi.

Zarah ita kanta har tagaji da zaman cikin ranta tace lallai mutumin nan ya raina min wayau miyake nufi da ni ne? Chan kuma sai tayi murmushi tare da cire hijab d’inta nan gashinta yabazu kallon yarima tayi da ya aje cup d’in yana cigaba da dannar laptop, amsar laptop d’in tayi ta aje gefe, yarima binta yayi da kallo cike da mamaki Ahankali tafad’a jikinsa tare da rungumesa cikin shagwa6a tace please kazo muyi bacci kaga har 11 fa tayi.
Wani iri yaji a ransa ammah yadake yace kikwanta mana ni sai nagama abinda nake.
Zarah d’ago kai tayi tana kallon cikin idonsa ahankali takai bakinta cikin nasa yarima daman kamar jira yake nan yacafke nan suka fara rikita junansu sun dad’e a haka sannan zarah tazare jikinta takwanta tare da jawo yarima jikinta dak’yar yasamu yakashe gloves.

yau makara sukayi sallar asuba har saida gari yafara haske sannan zarah tafarka duba time tayi taga 6:15am zaro ido tayi sannan takalli yarima da yake kwance yana bacci har takai hannu zata tadasa sai kuma tafasa, rigarta tajanyo tasaka sannan tafara k’ok’arin janye blanket d’in da yake rufe ciki,
Jin ana jan blanket yasa yafarka, zarah saida tasafka daga saman gadon sannan tace katashi yau munyi late.
Tana fad’in haka tazura hijab inta tafita tabar d’akin.

Yarima janye blanket d’in yayi cikin sauri yamik’e yashiga toilet yana mamakin yadda yamakara yau baisamu jam’i ba, chan kuma yaja tsaki da yatuno basuyi bacci da wuriba.

Zarah ma ko da takoma part d’inta saida tatsarkake jikinta sannan tayi sallah, bayan tagama kitchen taje tashiga nan tafara tunanin me zata had’ama yarima na breakfast, chan kuma sai tayi tunanin tahad’a mai kunun gyad’a dan tasan yana sonsa sosai.

Nan tad’aura ruwan kunun sannan tafere doya tadafa, bayan ta dafu tadaka tayi yamball.
Bayan ta gama wanka tashiga tayi da tafito tashirya cikin swiss less d’inta, veil tayafa sannan taje tad’auki basket d’in taba wata kuyangarta tarik’e suka nufi part d’in yarima

A gaban dressing mirror tagansa tsaye yana fesa turare, d’an rissinawa tayi tagaishesa, tacikin mirror yarima yake kallonta saida yagama fesa turaren sannan ya amsa.
Fuskarta d’auke da murmushi tace breakfast d’inka na dining,
Shuru yarima yayi har ta juya zata fita ahankali yarima yace kije kishirya in ajeki gida.
Dasauri zarah tajuyo cike da jin dad’i tace yanzu?
Eh, ammah idan baki shirya zuwaba shikenan.
Zarah cikin sauri tace na shirya kagani?
Yarima kallonta yayi sannan yazo yawuce yafito yanufi dining,

Zarah bayansa tabi har yaje yazauna nan tayi serving d’insa sannan itama tazauna tayi serving d’inkanta,
nan sukacigaba da breakfast d’insu ba wanda yai magana, zarah saboda zumud’i bataci abun kirkiba tatashi, yarima kallonta yayi yace shi kuma sauran wa zai ida cinye miki?
Itama kallonsa tayi tace nak’oshi ne,
Wani kallo da yayi matane yasa takoma tazauna tacigaba da turawa ba dan tana jin dad’insaba yarima yarigata tashi yabar wajen, nan zarah tabisa da kallo har yashige bedroom d’insa, sannan takalli plate d’insa ahankali tace shi bai cinyeba ammah ni shine zai ce incinye,
Mik’ewa tayi tatattara kayan tasaka cikin basket tad’auka tafita tabar d’akin.

Ko da takoma part d’inta cike da farinciki tashiga bedroom d’inta tad’auko handbag d’inta sannan tacanza veil saida tak’ara gyara fuskarta sannan tafito.

Daidai zata shiga part d’in yarima sai gashi ya fito, kallonta yayi sannan yace muje, a tare suka jero suka fito, guards d’insa har sun taso nan yarima yad’aga musu hannu, d’aya daga cikin motocinsa suka shiga dakansa yayi driving d’insu tunda suka fara tafiya ba wanda yayi magana zarah ko k’agare take su isa gida taga iyayenta wani irin nushad’i takeji dan fuskarta takasa 6oye farin cikinta,
Yarima ta mirror yakalleta yaga tana ta murmushi ta6e baki yayi sannan yamaida kallonsa ga titi, gudu yake sosai cikin k’ank’anin lokaci suka isa gidansu zarah,
zarah cikin sauri tabud’e k’ofar tafita sannan takalli yarima da shima yake kallonta tace zaka shigo kugaisa?
Yarima duban agogon hannunsa yayi sannan yace saidai in nadawo,
Toh sai kadawo Allah yakiyaye,
Ameen yace sannan tarufe motar har saida taga ya tafi sannan tashiga gida da gudu ba ko sallama tana k’walama mama kira,

Mama dasauri tafito d’aki tana cewa muryarwa nakeji kamar ta d’iyata, zarah rungume mama tayi tace oyoyoo mamanmu,
mama dariya tayi tace kai zarah har yanzu dai dasauran k’uriciya atare da ke, dariya zarah tayi tace mamanmu nayi missing d’inki fa, daidai lokacin yaya rauda da rahma suka fito daga d’akinsu sukace wa mukeji kamar zarah?
Zarah kallonsu tayi tana dariya tace nice dai, Aysha ce tazo tarungumeta tana murna mama tace sakarmin ita kar kikayar da ita.
Aysha sakinta tayi tana turo baki tace kai mamanmu ya za’ayi inkayar da ita.
mama jan hannun zarah tayi sukaje suka zauna saman tabarma.
Aysha da yaya rauda kallon juna sukayi sukai murmushi sannan suma sukaje suka zauna.

Cike da girmama zarah tagaishe da mama, nan mama ta amsa mata tare da tambayarta ya mutanen gida?.
Duk suna lafiya lou suna gaisheku.
Mama tace muna amsawa,
Sannan zarah takalli yaya rauda tagaisheta.
fuskar yaya rauda d’auke da murmushi ta amsa, zarah tace ya k’arfin jikinki?
Yaya rauda tace ai jiki ya warke,
Nan Aysha tagaisheta, zarah tace ‘yar k’anwata ya gidan?
Dariya tayi tace Alhmdllh, ya yayana?
Zarah murmushi tayi tace yana gaisheku,
Aysha tace nad’auka ma tare zakuzo.
Eh shi yasafkeni yana saurine zaije hospital saisa bai shigoba ammah da anjima zai shigo.
Toh Allah yakawosa lafiya, sukace Ameen.

Daidai lokacin Abbah yashigo d’auke da leda yace a’ah yau mune da manyan bak’i?
Zarah cike da jin dad’i tace abbah sannu da dawowa, ina wuni?
Lafiya lou ya gidan da mijin naki?
Lafiya lou abbah kowa yana lafiya,
toh masha Allah.
kallon mama yayi da takar6i ledar hannunsa yace bari inje insamo abinda za’a dafa ma d’iyata mai d’an dad’i-dad’i.
Zarah murmushi tayi tace a’a abbah kabarsa agirka abinda ke akwai.
harararta rauda tayi tace toh baki isa kiyi mana buk’uluba sannan tace abbah ahad’o da kaji,
Dariya abbah yayi yace toh d’iyata yanzu kau dan yau dole aci dad’i.
gaba d’ayansu dariya sukayi sannan abbah yace sai nadawo, sukace adawo lafiya.
Nan suka zauna suna hira.

Mama shinkafa tabada aka 6arzo mata tad’aura burabusco, bayan abbah yadawo su rauda suka gyara kayan miya nan suka d’aura miyar dage-dage wadda tasha naman kaji, hadad’en kunun zak’i suka had’a.

Bayan sunyi sallar azuhur gabad’ayansu suka had’u saman babbar tabarma suka had’u suna ci cike da nishad’i.

Bayan sun gama atare sukayi wanke-wanke sannan suka zauna hira,

Abbah ne yace zarah rauda tafad’a mana yadda kukayi da wannan saurayin nata saidai banji dad’iba da kika amsar masa kud’insa, murmushi zarah tayi tace abbah kadaina cewa haka hak’intane fa na amsar mata kaduba kaga irin wahalar da tasha ai dan taci kud’in bawani abu bane,
jinjina kai abbah yayi yace hakane to yanzu ya kuke gani ya dace ayi da kud’in?
Mama ce tace nidai atawa shawarar ina ganin yafi dacewa shine kasiyar da wannan gidan kasamu gida wanda yad’anfi wannan girma ko mai d’akuna ukkune kasiya mana tunda akwai sauran kud’i a wajenka,
Gabad’ansu sukace hakan ko za’ayi,
Abbah yace bank’i ta takuba toh yanzu idan maganar auren Aysha tatashi ya za’ayi?
Zarah ce tayi karaf tace aure kuma abbah?
Murmushi sukayi gabad’ayansu sannan abbah yace kiyi hak’uri bamu fad’a mikiba malam bello ne yazo yasameni yace yanaso abashi aurenta,
Zarah a firgice tace malam bello?
Mama ce tace Malam bello dai naki,
Zarah kallon Aysha tayi tace daman soyayya kukeyi?
Aysha dasauri tagirgiza kai tace wlh bahaka bane Aunty zarah shine yace yana sona da nak’i amince masa sai yasamu abbah yafad’a masa kuma nanashi labarin rayuwata yace ba matsala daman yasan komai tunda yanzu nadaina toh yana sona yanaso inmaye gurbinki, yanzu haka har danginsa sunzo sati guda da yawuce sun nemi aurena,
Zarah farincikine fal yabayyana a fuskarta cike da jin dad’i tace gaskiya nayi murna sosai kar kidamu ‘yar uwata ni tuni nacire malam bello daga cikin zuciyata gaskiya nayi murna Allah yakaimu musha bikki.
Sukace Ameen,
bud’e jakkarta tayi tad’auko cheque d’in 500,000 tamik’a ma abbah tace abbana nima ga tawa gudunmawar ataimaka acanza mana gida insha Allahu ko da bikkin Aysha ya zo Allah zai rufa mana asiri.

Abbah yace a’a zarah baza’ayi hakaba ki aje kud’inki rannan ma fa kin aiko mana da kud’i kema kisamu abu mai amfani kisiya.

Zarah tace abbah bana tunani zan iya tara kud’i alhalin ku kuna nan kune yafi cancanta kutara baniba, ban ta6a tunanin samun naira d’ayaba batare da kun fad’omin arai ba, k’wallah ce tacika mata ido tace abbah dan Allah kataimaka kakar6a kusanya min albarka.
Dukansu tabasu tausayi yanayin yadda tayi maganar nan abbah yakar6a shi da mama sukaita sa mata albarka suna jinjina halin ‘yar tasu tabbas sunsan sunyi sa’ar d’iya kamar zarah.
Abbah yace toh shikenan kuban lokaci zanyi tunani akan maganar canza gidan ammah fa kuyi hak’uri dan bawani babba za’a siyaba.
Sukace eh bakomai mun amince.
Abbah yace toh masha Allah, Allah yayimuku albarka gabad’ayanku.
Cikin jin dad’i sukace Ameen y rabb.
Nan abbah yamik’e yace bari inje wajen Yaya muda mugaisa.
Sukace Adawo lafiya.
Bayan ya fita nan suka cigaba da hirarsu.

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

 

_Sak’on gaisuwa da jinjina agareki yayata takaina *SADNAF* kinfi k’arfin page a wajena kema kin sani ina ji dake irin sosai d’innan, nagode sosai da soyayyarki agareni saidai ince Allah yabarmu tare, I hrt u dear_

 

Back to top button