Adandi 17
*17*
Sun jima a cikin shopping Mall din suna siyayya duk wani abu da yasan zasu buqata saida ya siya musu hatta da part sannan suka fito yana riqe da hanunta suna dariya takai hanunta taja gemunsa daidai lkcn da Abdul ya dago kansa dagakan sitiyarin don cewa yayi da abokan nasa su tafi kawai shi zai taho idan yaga fitowarsu aikuwa wata qusa yaji ta caki qirjinsa data sashi dafewa da sauri jikinsa yana wata irin rawa a fili yace “kai! Kai!! Ina wlh da sake bude motar yayi kamar zai fita sai kuma ya fasa saboda yana bala’in tsoron jizginta ba kunyar jizgashi zataji a gaban Mus’ab ba shikuma zai iya daukar komai banda wannan a shigo har masarautar sa a jizgashi.
Mota suka shiga suka dauki hanyar komawa campus din sunata hirarsu ta masoya suna zuwa suka dauki Rahmah suka wucce ya sauke musu kayan a gdan sannan ya sake daukar kudi ya bata har naira dubu hamsin taqi karba daqyar ya lallabata ta amsa ya tafi sukuma suka shige suka zauna suna bude kayan ba zato babu tsammani sukaji an banko qofar an shigo suka miqe da sauri ganin Abdul yasata sauke ajiyar zuciya idanunsa akan nononta data sakesu ko bra babu saboda ita ba gwanar sanya bra bace indai ba fita zatayi ba ganin inda hankalinsa yake yasata daukar hijjab tasa.
Ya hadiye wani yawu me daci ya fara matsowa kusa da ita tana janyewa har saida sukakai qarshen bangon dakin ya sanya hanunsa ya riqe kafadarta idanunsa sun qara ciki saboda bala’i sai hawaye yake fitarwa bakinsa na rawa yace “wato bazaki gane abinda nake fada miki ba ko meyasa kikeson dole saikin wahalar dani meyasa bazaki rabu da wannan dan iskan mutumin ba wlh kinji na rantse miki Samha basonki yakeyi ba qarya yake miki akwai qudurinsa akanki Samha nasan wayeshi nayi abubuwa da yawa akansa aikina baizo kansa bane amma saboda dalilin rabani dake da yake shirin yi shiyasa na dakatar da wanda nakeyi nakai hankalina gareshi Samha zaki yarda ki auri mutumin da uwarsa take kallonki a matsayin karuwa kilaki yar DANDI mutumin daya kasa bayar da hujjar kare matsayinki a gurin iyayensa mutumin da yake boye miki abubuwa da yawa akansa nasan ya fada miki zai tafi Oxford University qaro karatu a zahiri ba haka bane ya boyewa matarsa da iyayensa aurenki ne saboda a karon farko sun nuna qin amincewarsu ga aurenki saboda tabon da gibin da kikayiwa tarbiyyarki matsalata daya ce Samha inada kishi kuma a gdanmu akwai al’adar da dole budurcinki shine zai fansheki kekuma kin zubar da naki a titi Samha idan kin amince min zan aureki amma zan nemi budurwa wacce bata taba sanin namiji ba na aura kafin ke inyaso ke saina aureki matsayin bazawara kinga babu wanda zai buqaci qyallen budurcinki da saf…..”
Bata bari ya rufe bakinsa ba ta daukeshi da wani gigitaccen mari jikake tasss tasss yayi saurin sakinta tare da ja da baya ya cije lebansa har saida ya fashe jikinsa da haqoransa na rawa baitaba sanin haka zafin mari yakeba sai yau da Samha ta mareshi dama haka takeji duk lkcn daya mareta amma bata taba nuna masa ba.
Bata bashi damar cewa komai ba tace “tur munafiki mayaudari meson bata sunnar ma’aiki na tsani maqaryacin mutum irinka a rayuwata Abdul meka mayar danine yar iska wadda batasan ciwon kanta ba Abdul kaima kasan ciwon kanka bareni to kayi gaggawar fita daga rayuwata na tsaneka Abdul na tsani mutum mara sanin darajar dan’adam irinka ka wahalar dani lkcn da banida yanda zanyi shine ya cetoni yasoni a lkcn daka qini akan wata hujjarka mara tushe ya kula dani yajani a jikinsa ya soni da raunina kuma kullum kalmarsa yana sona a yadda nake kaje ka auri yammata hudu ka baresu ka hudasu rana dayama domin cika jahilar al’adarku amma ni Samhanatu ko a qwarqwara bazani gdanka ba balle mata matar ma saboda tsabar ka rainani bazawara to ka gayamin da ubanwa aka taba dauramin aure ko kuwa dole akayi maka saika aureni so bari kaji na fada maka ko zan mutu babu aure ni Samhanatu Sa’ad Dandoki nafi qarfin auren me qaramar qwaqwalwa irink….” Daga mata hanu yayi jikinsa na wata irin tsuma yace “ya isa haka Samha kada ki zageni a garina kike wlh idan kika zageni saikin shekara goma a kurkuku”
Juyawa yayi ya fice a mugun fusace zuciyarsa kamar ta faso qirjinsa ta fito daqyar ya mayar da kansa gda ya shiga yana ya fita daga motar yana layi kamar wanda yasha dagga ya nufi cikin gdan bayi da kuyangi sunata kai gaisuwa amma ina babu amsa Mainah Abdu ya shiga cakwakiyar soyayya bayaji baya gani dakinsa ya shiga ya fada gado ya saki wani kuka me ciwo yanajin kamar ya cire zuciyarsa ya jefar tunda yake a rayuwarsa baa taba cimasa mutunci irin yau ba to wama ya isa yaci masa mutuncin shikuwa meye a jikin Samha da bazai rabu da ita ba ta tsaneshi fah tace saboda wani shege da yake da tabbacin bason Allah da annabi yakeyi mata ba ashe haka ciwon so yake meyasa Samha tayi masa haka yasan duk wannan badaqalar da ace ta tsare mutuncinta duk da haka bata faru ba gashi Mai martaba jiya yace masa lallai ya fidda matar aure nanda wata daya idan ba haka ba zai aura masa yar qaninsa Gidado wadda ko a hoto baitaba ganinta ba qarin tashin hankalinsa ya zaiyi da soyayyar Samha idan ya karbi Pretty Aysha kamar yanda Mai martaba ya ambata kuma Yaya zaiyi da qiyayyar uwarta Lubabatu da tunda Gidado Sa’ad ya aureta ta rabashi da kowa ta dauki qahon tsana ta dorawa zuri’ar masarautar Katsina shima sosai yakejin tsanar matar qanin mahaifin nasu dama yar tasu guda daya dabai taba gani ba…….
_Washhh! ashhh!! wannan cakwakiya da yawa take nasha gudu na gaji duk dan na kawo muku tsugumin wannan badaqala ta birnin masoya zanje nayi bacci na huta zuwa dare_
*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/11, 7:44 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*
*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*
*