Auren Gado Hausa NovelHausa Novels

Auren Gado 25-26

Sponsored Links

2⃣5⃣&2⃣6⃣

 

……………… Kuma kasaurare ni idan har kai ka nuna isarka ta Auren wannan yarinyar nima ka jini da kyau, saika Auri salifa itama. Wani irin Kallo yake musu daga ita har Fauziya, “mommy kinayin duk wannan Abubuwan saboda wannan useless woman din ne ko, Toh ki fada mata itama tolerating dinta kawai nakeyi a gidan nan badon Ina son ganin taba, kin san cewa ba Wani Abu da aka doramin akai mai nauyi samada igiyar Auren ta? Wallahi in kun Auro wata tare zasu tafi, wallahi bazan hana ku daura Auren wata ba, Amma igiyar a hannu na take, I won’t hesitate to cut it all. Ya nuna ta da tuni tayi tsit saboda jin maganganun shi, “try and make another commotion here” zakiga true colors dina one by one now move out of my way ya fada cikin tsawa, ta fita da gudu saida ya ga tabar part din ya zauna tareda riko hannun mommy yace “sit my mommy let’s talk. Ibrahim kar ka maida ni Karamar yarinya na san me kake shirin yi, Auren salifa bazan fasa ba ehem. “Mommy mommy mommy”, please ki saurare ni baso nake ki canja ra’ayin kiba domin nima nawa bazan canja ba kawai mu zauna mu fahimci juna, kinga ba Abinda nake kokarin yi sai cika burin Yaya Ahmed, bazan taba wasa da Abinda yake matukar kauna a duniya ba, nafarko ke nabiyu kuma Naziya, mommy Yaya Ahmed nason ki haka Matar shi, kun Aura mai salifa batareda yana so ba, ranar da ya rasu wasiyyar in Auri Naziya yabari ba salifa ba, mommy akwai alkawarin da Yaya Ahmed yayi a gabana akan Naziya, idan har kika dawo da salifa zaki taimaka min wajen cika mishi wannan Alkawarin, forgive your only son Mommy, Ina kokarin yimiki biyayya ne domin ku Amanar Yaya Ahmed ne a wurina. “Khaleel na dade da sanin akwai raini a tsakanin mu dakai. Zamewa yayi tareda rungume ta ” ba raini a tsakanin uwa da dan ta, sai soyayya da neman Albarka. “Toh in Albarka ta kake nema ka saki yarinyar nan ka zauna da zabin zuciya ta.
“Ita Naziya meye laifin ta? “Kasan matsala ta akanta bana kaunar hada jini da ita idan ka sake ka Auro Y’ar nan bazakuji dadi naba Khaleel.
Tashi yayi kawai saboda ya lura tayi nisa kamar yanda shima yayi nisan, kuma ba wanda zai kirashi ya dawo baya, wannan Alkawarin zuciyar shine, he is ready for them tundaga kan naziya mai cewa bata Son shi har fauziya da uwar gayyar. Wucewa yayi kawai yayi dakin shi tareda rufewa gam yayi baccin shi mai dadi, wanda Naziya bata samu ba, ta Kwana kukan Auren ta da shi, tareda tunanin yanda zasu zauna inuwa daya, yaza’ayi ta Amince ko hannun ta ya rike.
ta kwana Alkawarin yanda zata gasa mai Aya a hannu yanda ba abarta ta rayu da mijin da takeso ba shima bazata yi zaman jin dadi da shiba, mommy kuwa ta Kwana tsara yanda zatayi da Naziya a gidan,

Washe gari ganin kawai sukayi Ana fitarda tsoffin kayan gefen Ahmed Ana shigo da wasu na yayi masu tsadar gaske da kyau, fauziya ce ta fito da sauri tana kallon gefen, tasan halin khaleel kamar yunwar cikin ta, wato da gaske yakeyi sai ya kawo wannan yarinyar gidan nan, gidan ta shiga da gudu saboda bakin ciki mommy na zaune tafado falon kamar saukar Aradu, saida mommy ta dafe kirji saboda tsoron da taji, “oh ni Balkisu” Fauziya ki rika tunawa inada hawan jini kirika yin Abu a hankali kar kisa wata rana in zube a banza, “ba damuwa ta bane ni yanzu damuwa ta itace kifito kiga irin uban kayan da khaleel yasa ake sakawa a gidan Ahmed saboda wannan Jakar yarinyar. Tashi mommy tayi tareda cewa wane irin kaya kuma bayan wainda ke ciki ko morar su ba ayi ba? Dukiyar da muka tara zai narkawa Y’ar talak……., shiru sukayi domin ganin Ana shigo da wasu irin new designer boxes wainda basu dade da fitowa ba wajen saiti uku, sunyi tsaye kamar ruwa yacinye su, kafin ya shigo da wata katuwar Leda a hannun shi, sanye yake cikin kanan kayan nashi na fama, fuskar shi a sake yace musu suje part din shi a store zasuga wasu set biyu su kwaso su, zama yayi yana murmushi yace “mommy ki ga kayan Auren Naziya kisa Albarka. “Khaleel” zan matukar bata maka rai fiyeda tunanin ka, wannan Y’ar matsiyatan kake kashewa irin wannan Dukiyar haka kana hauka ne?, sannan duk wannan uban kayan way’enda kake cewa a kwaso kuma na uban waye? “Momy ki duba mana Abinda baiyi ba a karo mata. Ya duka tareda bubbude akwatunan, kayane na gani nafada karshen kudi kowane akwati kalar kayan da ke ciki, komai har nighties nasu akwatin daban, gefe daya Wani dan madaidaicin kit ne shakeda sarkokin gold, diamonds Harda tsadaddun passion way’enda sunyi kudin Wani zinarin, sakin baki momy tayi tace “khaleel”, way’ennan kayan ko Fauziya Y’ar gidan Wani ba akai mata irin suba, don iskanci kasan kayan mata shine kabarni da siyan na fauziya?, ko kwandala baka bayar ba, yanzu akan wannan yarinyar ka narkarda Dukiyar ka haka khaleel? Shiru tayi lokacin da suka shigo da wainnan akwatunan, way’enda ya siyo ma Ahmed da niyyar ya hada a lefe suka boye, English wears ne masu matukar kyau da tsada da dogayen riguna way’enda har hango yanda zasuyi a jikin ta yakeyi, Wani irin hawaye ne ya ciko idanun shi yana tuna yanda ya yi da yayan shi akan akwatunan, a zuciyar shi yace “Yaya she is going to wear them insha Allah.
Fadan mommy yasa ya dawo daga tunanin shi, “khaleel” ka nuna min ban isa ba ko ka nuna min kai kafi dan uwanka mallakuwa ko? yayi kyau, wallahi zakaga mai zaifaru muddin ka kawo Y’ar nan cikin gidan nan. Ta wuce fuuu. Fauziya ce dake fitar da hawayen bakin ciki ta matso “Allah ya isa tsakani na dakai khaleel , wato akwatin Auren ma da sadaki na duk bakasan zafin suba, no wonder bakasan mutunci na ba banda wata kima ko daraja a idanun ka…. Wani irin hankada ta yayi baya tareda mikewa ya nuna ta, zaman yan bori tayi har tana dafe kugu, “look ba macen da keda damar fadawa khaleel magana sai mutum biyu daga mommy sai Naziya sune keda Iko da khaleel, thank God kin gane inda hakkin Auren ki yake, that’s hannun mommy so from today don’t ask me your hakki go ask mommy. Ya Kira masu aikin yace su kwashe mai kayan zuwa part din shi, idan masu aikin sa kayan sun gama su sakasu ciki, karku bar wurin domin za’a iya saka musu wuta saboda bakin ciki.
Suka kwashe suka fuce, yana tsaye, “khaleel” nasan me ka keso dani infita in bar maka gidan ka wataya da Amaryar ka, wallahi yadda baka bani kulawa ba itama bazata samu kulawar ka ba, mu zuba cikin gidan nan. Tayi waje tana kuka,
Girgiza kai yayi tareda cewa “let me shower and go to her, am coming baby, kema zan zo inji kalar naki salon maganar naji na nan ya isa, now is up to you.

 

A tsakar gidan suke tana hira dasu Sadiq yau ma ya shigo suna taya inna tsinke zogalen da zatayi musu dambu domin sadiq nason danbu sosai, hirar su sukeyi suna dariya, Malam yayi sallama, tareda khaleel yana cewa “iso Ibrahim kaima dan gidane ai basai ka jira iso na ba. Jin maganar shi baisa ta daina hirar ta ba infact bata ko dago kanta ta kalle shi ba, sanye take cikin doguwar rigar atanfa mai kyau dinkin ya matukar fito da yarintar ta da kyanta, idanun shi akanta suka sauka, zama yayi gefe tareda gaida Inna, ta amsa ta kwashe zogalen ta ta mike, tabarsu dama ba Shukrah agida tana makaranta,
Malam yace “Sadiq kana cikin mata kuna aiki inka gama kafito muyi magana. Yafada yana fita, yi tayi kamar bata san Allah yayi ruwan tsiyar shi a wurin ba,
Har suka gaisa da Sadiq, taci gaba” ya sadiq kasan Ina son in karanta mass com, saboda aiki a gidan redio ko tv Abun na burgeni sosai. Tafada tana dariya, Wanda ke karawa fuskar ta kyau, da zaka kalli fuskar khaleel da zaka hangota kamar manja saboda ja, “kai haba ai mace tafi mutunci da aikin likita Naziya, ni da badon anyi min kafa ba da tuni na jefaki school of nursing ma. Dariya tasa, wadda saura kiris ta tafi da numfashin khaleel, mikewa yayi tareda fita a zuciye, ya samu Malam a zaure, “Ibrahim harka fito? “Eh Malam magana zamuyi. “Bismillah Toh. “Nace ba laifi idan yau nadauke ta ta koma gidan mu? “Aa kaida Matar ka ai bawani laifi kawai ko yanzu ka so zaku iya wucewa, bari in fada ma mahaifiyar ta. “Toh zan tafi zuwa dare zan dawo in tafi da ita, ai badamuwa idan ba arakata ba ko? “Babu hakan shine daidai ma tunda ba Auren farko bane, Allah yabaka ikon rike Amanar dan uwan ka tareda sauke dukkan hakkin da ke wuyan ka. “Amin yace, yabi Malam suka koma ciki lokacin ta mike tsaye zata shiga dakinta, bin bayan ta yayi kawai,
Tana shiga taji mutum a bayan ta saida ta zabura, tayi baya kamar zata zube saboda tsorata datayi daganin shi, saurin riko hannun ta yayi domin zata fadi, ya fisgota zuwa jikinshi Wanda saida ta runtse idanun ta kafin tayi saurin ja baya tana fisge hannun ta, jitayi kamar ta warta mai mari, “me yasa zaka tabani? Ta fada jikin ta na rawa, “oh ba atabaki ne? Ai bansani ba, yafada yana bata Wani irin kallo mai cikeda ma’anoni tun daga sama har kasa.
Saurin bin jikinta tayi da kallo tareda juyawa tana shirin daukar mayafi, yayi saurin matsawa, ” akwai Abinda zan iya yi idan har kika aikata Abinda ke cikin zuciyar ki, ni ba shashashan namiji bane, kina iya tsayawa a gaban Wani banza yanda kike so idan kinganni saiki rika neman Abun rufe jikin ki me kikeso ki boyemin?
“Kaga Ina jin kunyar ka don haka karka bari inbude baki infada maka maganar da bazaka manta daniba. “Say it am ready to hear. “Kaga kana cin Albarkacin Ahmed shi yasa kake yi mun Abinda kaga dama Ina kyale ka, not anymore, tunda kace zaka wuce gona da iri, karka manta kai kanin mijina ne, matsayin mijin da kake kokarin dorawa kanka zuciya ta bata karba ba ban Amince ba.

“Hmm first in history, naji mace na deciding yanda zasuyi zaman Aure itada mijinta, yafada yana rike gemun shi cikeda rainin hankali, “husband, yes I am your husband believe it or not, and secondly, ni nake tsara rayuwar da nakeso inyi, inaso kije ki bincika tarihi na kiji bana daukar ra’ayin Wani, I only did what I think is right, ya zakiyi rayuwa me kikeso me zaifaru dake, duk nine zanfada miki yanzu, wannan rufe rufen jikin da kike yi idan naso zan iya hanaki saka ko pant da breziya a cikin gida na, watch out wannan mijin da kike gani bakisan waye shiba, and third, later in the night you are going to my house, enough of all this hira da kikeyi da katon banza, so get ready in time, first in history miji zaizo ya dauki Amaryar shi, ya matsa gab da ita tareda cika mata fuska da hanci da tsadadden kamshin jikinshi ya hura mata iska yayi ficewar shi kamar Wani walkiya,
Ya sumar da ita da kalaman shi, saida ya fita ta zube akasa tana hade jikinta, she can feel his presence up to now, a dakin jikinta kamshin shi duk ya Kama, kalmar shi na ko pant da breziya sai yana ra’ayi zata sa ya tsaya mata arai, lallai tantiri take gani a gaban idanun ta na bugawa a jarida, zata iya rantsuwa kalmar bazata taba futowa daga bakin shi ba, yanda yake behaving like gentle man, now she is mistaken, infact batasan me zai yi nan gaba ba, kallon tsintsiyar hannun ta tayi tanajin nashi haryanzu a nata, Wani irin Yar takeji fiyeda yanda takeji idan Ahmed ya riketa, hannun shi kamar Wanda yake massaging dinshi da baby oil, saboda softness ko ita mace hannun ta baikai nashi laushi ba, she can still feels his heart beat, lokacinda ta fada na second biyar, zuciyar shi bugawa take da mugun karfi. Tashi tayi tareda kwabe kayan jikinta ta zubar akasa, ta datse kofar ta koma zubewa akasa, kallon shape dinta nayi, ta tsaru dakyau jikinta nada tsari da Wani irin kyalli abunka da fara, juyowa tayi ta zubawa tukunyar fulanin ta ido nasan cewa yes Ahmed yayi rashi babba da bai more way’ennan Abubuwan ba, a cike suke tam a girke zaune Alamar bazasu taba kwanciya ba, tashi tayi ta kalle su tasa kuka ” am sorry Ahmed dana sani nabari kayi yanda zakayi dasu da nasan bazaka rayu da ni ba, bazan kasa kai maka hakkin kaba, yanzu tayaya zan iya bawa dan uwan ka kulawa, bazan iya ba kaine ka dace da duk wannan Abun ba kanin kaba, murje idanunta tayi tareda daura kuduri mai girma. Kiran da taji Inna nayi mata yasa ta zabura ta mike, wasu kayan tasa domin ta tsani way’ennan saboda kamshin shi da sukeyi, ta fita idanun ta sunyi ja. “Toh” Malam yace Anjima zaki tare gashi wannan Karon ko shiri ba’ayiba don haka na Kira yayar ku tace tana zuwa kije ki hada Abun bukatar ki. “Toh” tace kamar zatayi ihu saboda damuwa, gwara zama da mommy sau dubu da zama da khaleel a wurinta, a tunanin ta tagama zama a wannan gidan sai gashi rayuwa takuma juyawa da ita ta bahagon hannu.

Tunda yafita gidan su yana barin unguwar yayi tafiya mai nisa yayi parking a gefen titi wajen da ba hayaniyar komai ya Dora kanshi a jikin sitiyarin motar shi, wani irin numfashi yake fitarwa da sauri da sauri, yanajin kamshin turaren wutar da take Amfani dashi akaya, he can feel her chest a nashi har yanzu, runtse idanun shi yayi da karfi yana dukan iska, fauziya tasha rungume shi by mistake bai taba jin haka ba, wani irin racing zuciyar shi keyi, itace mace ta farko da ta fara sashi yaji shi a namiji, bayaso ya nuna mata rayuwar Aure sai yakoya mata sonshi, sai ya cire mata bakin cikin zamanta na baya sai ya bata dukkan farin ciki, so yake yazama bawan mace a Karon farko, Amma sai yayi amfani da nashi salon, “Am sorry Yaya, zuciya batada k’ashi, batada limit, I don’t know when and how? I think tun ganin ta nafarko yes that’s it, love at first sight.
“But kai take so, bana bakinciki because she love you, zan tayaka bata farin ciki I promise you bazan taba cutar da itaba that’s my promise to you my brother.
Hour guda cur ya kwashe yana tunani a wurin kafin ya wuce ya samu kawun shi yafada mai yau zata tare, yasa Albarka tareda Bashi shawara akan zaman Aure, da kuma akan mahaifiyar shi, sai kayi da gaske, ina fatan kasan halin Hajiya balkisu fiyeda ni yanzu, don haka Allah yabaka ikon sauke duk wani hakki.
Godiya yayi yatafi tareda wucewa gidan,
Bakowa duk sunfita, mommy taje wurin zarah domin neman mafita ita kuma Fauziya tayi gidan su,

Tabe bakinshi yayi ya shige dakinshi ya kwanta yana murmushi, yana hango yanda maganar shi ta sa takoma kamar gunki, “this is just the beginning baby. Tafin hannun shi ya kalla, yana jin kamar har yanzu yana rike da tsintsiyar hannun ta, yasan dole taji yanda yakeji shima, ya dauki lokaci yana tunani kafin yayi bacci mai dadin gaske,
Gefen Naziya kuwa tana zaune batada zabi Shukrah ta zana mata lalle jada baki gefe Aunty Raliya ta shirya mata lafiyayyar kaza tasata ci, zama tayi ta nagi kayarta tasan aikin banza sukeyi kawai yanda Ahmed yatafi haka shima zai gaji ya sallamo ta, ba Abinda zai shiga tsakanin su, sayi sa gama. Haka ta murjeta da dilka tas, zuwa magrib ta yi wanka da ruwan kamshi da yaji hade hade, suka bata sabon kaya ta saka, tayi sallah,
Ta dade a sujudarta tana neman Allah ya taimaketa kar ya bawa duk wani makiyinta sa’a akanta, bayan isha’i Malam ya shigo gidan ya zaunar da ita tareda yimata nasiha mai ratsa jiki.
“Naziya nasan zakiji a zuciyar ki banyi miki adalci ba, nasan bakya son wannan Auren, kuma nayi matukar mamaki da kike kokarin bujurewa hukunci na, shin kin manta bana yin Abu dakai, kin manta duk Abinda nake nema sai na nemi zabin Allah, na hango miki farin ciki Naziya idan har kin daure kin karbi kaddarar rayuwar ki, kije Kiyi biyayya Albarkar mu tare da Addu’ar mu tana tare dake, Allah yayi miki Albarka. Kuka takeyi kasa kasa hawaye sharkab a idanun ta, Inna ma tayi nata tareda sa ma rayuwar ta Albarka.
Sallamar shi ce tasa Malam ya fito tareda tarar shi cikin murna “sannu Ibrahim ka iso. “Eh Malam. “Toh Hauwa fito da ita ga mijinta, “wani irin nishadi yake jinshi a ciki, tun bayan mutuwar dan uwan shi yau ne yake jin kamar Ana wanke mai zuciya da ruwan madara.
Cikin manyan kaya yake sky blue yard na maza yanada wani kyalli kyalli kana iya hango farar singlet dinshi, gayen yasan sirrin ado, kuma duk shigar da yayi kyau take mai saboda cikar zatin shi, ko dago kai batayi ba data fito cikin katon hijabi kalar kayan jikinshi, Wanda yana kallon ta yayi murmushi cikin duhun daren, wannan fitinannen kamshin nashi duk ya cika musu tsakar gida,
Inna gaisawa sukayi tace bari insa Shukrah ta kwaso kayanta. “Abar kayan zandawo inkwashe su gobe. Yafada tareda yi musu sallama ya fita, komawa tayi ta rungume Inna tasa kuka, jikinsu duk yayi sanyi, Malam fita yayi yana cewa idan kungama Shukrah ta rakota waje,…….. 🖊

 

*Wacce wainar zamu soya a gidan khaleel my fans, wane irin rayuwa ce zatayi tareda wainnan mutane ukun fauziya momy and khaleel, meye ra’ayinku akan kudurin Naziya? Waye zaiyi nasara a wnn tafiya khaleel or Naziya? ” muje zuwa time will tell insha Allah*

 

*Matar Soja*
10/20/21, 7:33 AM – Fiddausi Yunus

Back to top button