Hausa NovelsKurkukun Kaddara Book 2 Hausa Novel

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 3

Sponsored Links

_~*BossLadiesWriters*~_

*KURKUKUN ƘADDARA*

 

_The Prisoners E3_

*Daga alƙalamin Hafsat Bature*

~Middle step~

 

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._

 

A yayin da Angel ta ke A Cikin mawuyacin Hali Idan muka koma 6angaren ƴan uwanta da ke ta tsammanin dawowarta, wani mummunan abu Ya faru dasu!! Tun lokacin da suka fuskanci cewa gari ya waye bata dawo ba, Hankulan su su ka tashi matuƙa, Sun kasa fitowa daga Cikin ɗakin tsohuwa Tamira, gudun kada asirin su Ya tonu, tun da ana kallon duk wani motsinsu.

“Yanzu ya zamu Yi? Nifa ina tsoron mu fito daga ɗakin tsohuwa Agan mu dole su zargi wani abu” Deeja ce tai maganar

Haris yace”Zaman mu kuma acikin ɗakin yafi komai haɗari, Idan Giant su ka zo kawo mana abinci zasu ga babu mu aɗaki zasu Iya zargin mu”

Damuwace ƙarara akan fuskokinsu, Kowa yana tofa albarkacin bakin shi, jemimah da ke a ruke da hannun Batul idanuwanta sun kumbura suntum saboda rashin baccin da bata samu damar yi ba adaren Jiya, jikinta hada zazza6i,

“Mun tsaya muna kallon juna, Yakamata Muyi wani abu akai,” eve ce ta yi maganar, fuskokin su duk sun kumbura musamman idanuwanta saboda rashin baccin da ba su yi ba a daren jiya.

Numfasawa Batul ta yi tare da cewa”mu fita kawai” ta ambaci hakan tare da ɗaukar jemimah saman Jikinta, ƙofar fita ta nufa ta sanya hannu ta tura ta, Zura ƙafarta ke da wuya Cikin ɗakinsu Ta yi arba da tsohuwa Zafreen A tsaye hannunta ruke da sandarta fuskar nan ɗauke da murmushi, A gigice Batul ta koma Cikin ɗakin Zuciyarta na bugun uku uku, Ganin yadda ta Faɗo masu yasa su ka haɗa ba ki wurin tambayarta”Lafiya? Me yasa ta dawo”? Muryarta na ruwa ta ambaci sunan tsohuwa Zafreen!

“Wlh ita ce naganta a cikin ɗakin mu, Wayyo Allah mun shiga uku”! Cikin shessheƙar Kuka ta ƙarasa maganar, Kafin wani ya kuma cewa wani abu tsohuwa zafreen ta faɗo cikin ɗakin da su ke a ciki, A firgice Azeeza ta 6oye bayan Gabriel Jikinta nata kerma, Tashin hankali ne tsantsa akan fuskokinsu.

Ɗaya bayan ɗaya ta ke bin su da shu’umin kallon nan nata

“Halan Ƴar uwar ku ku ke Jira ta dawo”? Shiru su ka yi babu wanda Ya tanka mata,” Idanuwan su azazzare jin ta gane me su ke jira, hakan ya tabbatar masu da cewa Sun yi aran gama da Angel, Zuciyoyin su ba ƙaramin karaya su ka yi ba. Dama saida ransu ya basu cewar fitar Angel ba alkhairi bace.

Tuntsirewa ta yi da dariya mai sautin gaske kamar zata fasa masu kunnuwan su, har saida suka sanya tafin hannayen su wurin toshe kunnuwan su.

Lokaci ɗaya ta dakata da yin dariyar tare da ɗaure fuskarta tamau babu annuri ko misƙala zarratin.

Wahalallan Yawu su ka haɗiya, Daƙyar Deeja ta samu damar buɗe baki Muryarta na kakarwa ta soma magana”Dan Allah Ki yi haƙuri kada ki cutar mana da ƴar uwar mu, duk abunda ta aikata ba laifinta bane, Laifin mu ne, ta yi ne saboda mu…..” bata ƙarasa maganar ba, Haris yai saurin toshe mata bakinta gudun kada ta tona masu asiri, A hasashen shi Tsohuwa zafreen bata san zancen shirin guduwar su ba, Iya abunda ta sani shine Shigar Angel kurkuku.

Muryar jemimah Cikin shessheƙar kuka da 6acin rai tace”Wlh idan ki ka ta6a mini Genie ɗina saina rama mata, bata ma ku komai ba ku ke cutar min…..” a hanzarce Batul ta toshe mata bakinta da hannu, Hankalin su yai matuƙar tashi ganin irin kallon da tsohuwa Zafreen ta ke bin Jemimah.

“Dan Allah Ki yi haƙuri da kalaman da ta yi maki, yarinya ce bata son komai ba, kuma bata acikin hayyacin ta,” Atare suka haɗa baki suna bata haƙuri, da buɗar bakin ta sai cewa ta yi”Sorry for ur self! Ku ya cancanta in ba haƙuri saboda kune rayuwar ku ta ke acikin matsala, Ni bani da damuwa”

A matuƙar ruɗe suke binta da kallo

Cigaba da yin magana ta yi cikin shaƙiyanci da izgilanci”Na jima inason kasancewa tare da ku ban samu damar Yin hakan ba sai yau, Ganin ku da nayi ahaka yayi matuƙar tayar mini da tsohon tsumina, ya za’ai? Zaku bani haɗin kai ko kuwa zan ƙwaci haƙkina ta karfi”? Ta yi tambayar tana ɗage masu gira.

Kallon kallo su ka soma jefa ma junan su, sam basu fahimci me ta ke nufi ba.

“Au Na manta kufa dabbobine ba ku san komai ba, dole sai ana yi ma ku magana da yaren da zaku iya ganewa,” ta ambaci hakan tare da tunkarar su, bayin Allah sai ja da baya baya suke Ke yi.

“Abunda na ke nufi shine zan kwanta da ku In biya buƙatata, idan ku ka bani haɗin kai salin alin zamu rabu lafiya, har ma In bada umarnin akawo maku lafiyayyan abinci, kuma daga rana irin ta yau za’a daina baku ganye kuna Ci”

Hankalinta akwance ta ke kora masu Bayani, Cikin shessheƙar kuka Deeja tace”Wlh ba zamu ba ki haɗin kai ba” ta ambaci hakan tare da kallon su Hibba

“Kada ku yadda da ita so ta ke ta yi mana irin abunda akayiwa unaiza wanda yaja har ta mutu tabar duniya……” Maganar da Deeja ta yi ne ya fargar dasu, sai yanzu su ka fahimci abunda tsohuwa zafreen ta ke nufi. Ƴan matan cikin su tuni sun fashe da kuka suna roƙonta akan karta ta6a su ta ƙyale su, Baiwar Allah Azeeza ta ƙanƙame Gabriel kamar zasu koma mutun ɗaya. tsananin tausayin kansu ne ya kama su, don basu ga alamun sassauci akan fuskarta ba.

Tsawa ta daka masu tare da nuna mazansu da sanadar hannunta”Maza ku fuce ku bani wuri, ba da ku zanyi ba, Matan na ke kwaɗayin kasancewa dasu” kaitsaye ta basu umarnin fita, kamar sakarkaru haka suka haura ƙafafuwan su su ka nufi ƙofar fita, Azeeza da ke ruƙe da Gabriel tuni ya yi wurgi da ita ƙasa saboda basa acikin hayyacin su, ta yi amfani da sihirine wurin basu umarni su fita, fucewar su ke da wuya ƙofar ɗakin ta datse ta yadda ba zasu Iya tsere mata ba.

Jikin su sai kerma ya ke yi, da gudu Azeeza ta shige ƙarƙashin gadon tsohuwa tamira, ganin ta yi hakan yasa Batul sauke Jemimah tare da turata ƙarƙashin gadon, tace da azeeza ta rungumeta a jikinta, bayan ta ɗago ta jera da sauran ƴan uwanta suka haɗu suna yi mata magiya akan ta ƙyale su kada ta cutar dasu.

Shu’umin murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, A hankali ta jefar da sandar hannunta, Dama lafiyar ƙafarta lau, ruƙe sandar da ta ke yi na ado ne. Yatsun hannayenta ta ɗaura kan doguwar rigar da ke a jikinta, Ta zame ta nan take tsiracinta Ya bayyana babu kyan gani jikin ta duk tamoji tamoji kamar jikin faskaran Icce, Undyn da ke a jikinta shara shara ya ke kamar net kana iya ganin komai, uban gashin gabanta gwanin ban ƙyama, Tsayin shi ya kai na ciyawa, wani abun tashin hankalin ma Halittar gabanta sak irin na Namiji ce hakan na nufin tsohuwa zafreen Mata maza ce! Nonuwanta kamar silifas har saman Cikinta. Runtse idanuwansu su ka yi don ba za su Iya jurar kallon tashin hankalin nan ba. Ajikin bango suka ƙanƙame juna kamar zasu tsaga shi su shige ciki saboda tsabar yadda su ka manne mashi.

Bayan ta kammala cire doguwar rigar ta jefar da ita ƙasa.

“Ku kwantar da hankulan ku Ni ba da ku zan fara ba, Na ƙarƙashin gadon su nafi sha’awa” jin wannan maganar yasa suka bubbuɗe idanuwansu azazzare suke kallonta, Kafin su ka kai idonsu kan gadon tsohuwa Tamira da ƙarfi Deeja ta furta sunan Jemimah da Azeeza, Kafin su yi yunƙuri zuwa gare su tsohuwa zafreen ta cimma ƙarƙashin gadon da hannu Ta janyo ƙafar azeeza da ta jamimah da ƙarfi ta fusgosu waje kawunansu ba ƙaramin buguwa su ka Yi ba, A saman gado ta kwantar dasu Sai faman lashe baki take tana ƙokarin cure masu kayan jikin su.

Kukan kura Su Batul su ka yi da gudu gaske suka haye saman gadon, Da iya ƙarfin su na ƙarshe su ke kai mata naushi duk don ta ƙyale masu Ƴan uwansu, sai dai ina ko kaɗan tsohuwa zafreen bata Ji bugun nasu ba, batasan ma su na yi ba don tuni ta tsuduma cikin biyan buƙatarta dasu azeeza, ta raba su da kayan jikin su, sautin kukansu Ya karaɗe Cikin ɗakin wani irin raɗaɗin azaba su ke ji a jikinsu, sai da ta tabbatar ta lala masu rayuwa, tun numfashinsu na fita a wahalce har ta kai ga sun daina motsi, gaban su sharkaf da jini, tukunna ta ƙyalesu ta koma kansu Batul da ke bugun bayanta, wata irin wawura ta kai masu da hannayenta masu faɗi ta dinga Rabasu da kayan jikinsu Zir ta yi masu Mutun biyu ta damƙa acikinsu Sarah da Yasmin Ta kwantar dasu ƙasa ta hau kansu taci gaba da biyan buƙatarta, wa’iya zubullah Tashin hankalin da suka fuskanta Bazai misaltu ba, basu ta6a ganin Masifa ido da ido ba sai yau, Suna ji suna gani ta gama amfani dasu sarah ta koma kan su Rubina ɗaya baya ɗaya ta ke kwantar dasu ƙasa ta hau kansu tana Biyan buƙatarta. sautin koke kokensu da gurnanin tsohuwa zafreen Ya cika kunnuwansu Haris, waɗanda tuni sun jima da haukacewa, Don tun bayan fitar su daga cikin ɗakin ƙofar ta datse, Tunaninsu ya dawo, Sun yi kuka har sun gaji, yayin da su ke jiyo sautin muryoyin su Deeja cikin mawuyacin hali su ke ƙwala masu kira donsu zo su cece rayuwar su sai dai sun gaza yin hakan, basu da wata hanya da zasu iya taimakon su, ji su ke kamar su haɗiyi zuciya su mutu, sun yi fatan ace mafarki ne ba gaske ba.

Mutun ɗaya ce ta rage A tsaye Fuskarta jaga jaga da hawaye ta rasa ya za ta yi don tasan itama zata dawo kanta ne idon ta gama dasu Deeja gani ta ke kamar ƴan uwan su sun mutu saboda wasu daga Cikinsu babu numfashi atattare dasu Musamman jemimah da Azeza zaiyi wuya su rayu. zafreen ta gama kashe masu rayuwarsu ta wulakanta su kamar dabbobi.

A haukace Batul ta nufi table ɗin da ke ɗauke da Tunkunyar shayin nan ta ɗaɗɗago shi da hannu biyu, tana haki ta nufi tsohuwa zafreen da ta duƙufa asaman su Rubina, ta daddage ta buga mata shi, Ko gizau batayi ba, Komawa ta yi tare da ɗauko kujerar table ɗin ta dawo ta kuma buga mata ita saman kanta, still bata ɗago ba.

A fujajan ta koma cikin ɗakin tana neman abunda zata ƙwala mata, Duk ta bi ta haukace sai waige waige ta ke yi fuskarta sharkaf da hawaye, har zata juya ta wutsiyar idonta ta hango Rigar wuƙa da ke a so ke a tsakanin littattafan cikin Book shelves ɗin ɗakin.

Tsohuwar ajiye ce wuƙar da tsohuwa Tamira ta ba Danish Kyautarta a lokacin da ya buƙaci yana son datse sumar kan shi, ashe ya maida mata ita shiyasa ko lokacin da Angel ta yi mashi magiya akan ya bata wuƙar Yaƙi bata saboda bata atare da shi, da gudu Batul ta nufi book shelves din ta zura hannu ta ɗauko rigar wukar ta zaro ta Jikinta har salƙi ya ke yi saboda tsabar kaifinta, wuƙar sihiri ce mai haɗarin gaske, Cikin zafin nama ta watsa aguje bata nufi ko’ina ba sai kan Tsohuwa Zafreen a lokacin ta gama da su Rubina juyowar da za ta yi ke da wuya Batul ta daddage ta Luma mata wuƙar Cikin idonta, kafin ta yi wani yunƙurin yin amfani da sihirinta Batul ta ja wuƙar Tun daga kan idonta har zuwa saman wuyanta ta tsartsarga mata Jikinta, Wani irin ƙarfine yazo mata, Dama jinin ta akan akaifa ya ke, Zuciyar ta bushe, Gaba ɗaya tsohuwa zafreen ta gigice saboda azabar zafin da taji na shigar wuƙar, Ta yi ƙoƙarin Buge Batul sai dai Allah bai bata Ikon Yin hakan ba, ba ƙaramin Illah Batul ta yi mata ba, Sai dai duk da haka wani abun mamaki babu ɗigon Jini da ya fito daga idonta, duk inda Batul ta fasa mata da wuƙar kamar ana ɗinke fatar wurin haka ta dinga haɗewa tamkar ba’a ta6a tsaga ta ba.

So ta ke ta lalubo sandar hannunta saboda ƙarfin sihirinta yana a jikin sandar, Idan har babu ita Sauran sihirin da ke a jikinta ba lallai Ya iya yi mata tasiri ba, Daƙyar ta samu ta yi wurgi da Batul gefe ɗaya gaba ɗaya ta kife ƙasa kanta ya daku, wuƙar hannunta ta kufce mata, yunƙurawa zafreen ta yi tare da miƙewa tsaye Jikinta na kakarwa ta soma tafiya tana tunkararta, so ta ke kawai ta kashe ta har Lahira, Cikin fitar hayyaci Batul ta miƙe zaune daga kwancen da ta ke a ƙasa, Ja da baya ta dinga Yi har sai da ta ƙurewa bango.

Tuni tsohuwa zafreen ta cimmata, tafin ƙafarta ta ɗaura saman Yatsun hannun Batul ta murjesu, tsabar raɗaɗin da Batul ta ji ne yasa ta fashe da matsanancin ku ka na fitar hayyaci, wata irin zufa ta soma tsasstafo mata

“Kafin ki kashe Ni, Ni zan fara kashe ki, Dabba kawai, Kin yi kuskure da ki ka soka mini wuƙa A cikin idona, Angaya maki cewa Ni Mutunce da zan mutu farat ɗaya? Tana huci ta yi tambayar, janye tafin ƙafarta tayi daga kan yatsun hannun Batul ta ɗaura ƙafar saman jikinta da ƙarfi ta danna shi tare da murza ƙafar, Jini ne ya soma gangarowa ta cikin bakin batul Nan ta ke Numfashinta ya soma kokawar ɗaukewa…..

Ba zato ba tsammani tsohuwa Zafreen Taji an buge mata kanta da ƙarfi gaba ɗaya ta kife ƙasa, ta baya aka shammace ta, A hanzar ce ta ɗago don ta ga wanene, a matuƙar ruɗe ta ke kallon fuskarta, Ba kowa bace face TSOHUWA TAMIRA.

“Ban yi mamakin ganin ki ba Dama na jima da zargin cewa ba ki atare damu Tamira!” zafreen ce tayi maganar muryarta akausashe, saboda tsabar 6acin rai facial musles din tsohuwa tamira har kerma su ke yi, Hankalinta yai matuƙar tashi ganin yadda zafreen ta lalata rayuwar Yaran da ta raina gaba ɗaya ta gama da rayuwarsu, ta yi danasanin zuwan da ta yi amakare da duk hakan bata faru ba, idanuwanta sun yi jawur dasu tamkar garwashin wuta, wani irin hu ci ta ke futarwa

Yunƙurawa tsohuwa zafreen ta yi tare da miƙewa tsaye, Ido cikin ido su ke kallon juna babu sassauci akan fuskokin kowannan su.

“Ni dama ba ki ta6a burgeni ba, Muguwa azzaluma baƙar kafura, Ban ta6a ganin dabba Jahila daƙiƙiya irin ki ba, Wai ke baki da hankali ne? Ke fa mutunce waɗannan yaran da kika lalata rayuwar su mutanene fa ba dabbo bi ba, Laifin me su ka yi maki da har su ka cancanci wannan hukuncin daga gare ki”? Rai amutuƙar 6ace ta jefa mata tambayar.

Ɗaure fuska tsohuwa zafreen Ta yi, idanuwanta sun kaɗa jawur dasu, Babu ko alamun imani akan fuskarta

Tana magana tana huci kamar mayun waciyar zakanya” Ni kike gayawa magana? Ka da ki manta ke bakowa bace a gidan kurkukun nan face ƙasƙantacciya mai rainon Yara, dole Ki yi mini biyayya saboda ni ke agaba da ke, Nafi ƙarfin ki Tamira nesa ba kusa ba, Idan har kina son ki tsira da ranki to ki gaggauta barin wajen nan tunkafin In yi maki mummunar Ill……”Bata kai ga ƙarasa maganar ba, tsohuwa Tamira ta daka mata tsawa har saida ta furgita, karo na farko kenan da taga Rashin tsoro acikin idon Tamira.

Nuna ta ta yi da yatsan hannunta”ko da can baya da na ke girmamaki ba dan ina jin tsoron ki bane sai don Ƙudirin da na ke dashi na son Rushe Baƙin tarihin da kuka kafa, Ajali ne ke kiran ki shiyasa har ki ka yi gigin shigowa cikin ɗakina, A yau inaso in nuna maki ƙarfin ikon da na ke shi wanda na samu awurin rainon yaran da nake yi, Zafreen Yau zaki yaba ma aya zaƙinta, Ko da zan rasa raina ne saina fara ganin bayanki wulaƙantacciya kawai”a fusace ta ambaci hakan idonta akan fuskar zafreen ga dukkan alamu mamaki da al’jabi ne ya hana ta mayarwa Tamira martanin maganarta. bata ta6a tsammanin tsohuwa Tamira zata Iya yada mata magana ba tare da jin shakkarta ba.

“Tsautsayi da ƙaddara ne suka jefo waɗannan Watsastsun ƙafafuwan naki cikin ɗaki na, Kin ga babu mai kallon mu bare aji sautin mu, Yau zan huce haushina akan ki….” Tunkan ta ƙarasa maganarta, tsohuwa Zafreen ta 6ace ma ganinta, Hankalin tsohuwa Tamira Ba ƙaramin tashi yai ba, babban abunda ta ke ji ma tsoro kada ace ta bar ɗakin, In kuwa haka ta faru zasu fuskanci azabtarwa domin kuwa za ta je ne ta fallasa su.

Jin motsin mutun abayanta yasa ta yi saurin Juyawa, Har saida gabanta Ya ɗan faɗi ganin tsohuwa Zafreen ta bayyana cikin shigar jajayen kayanta hannunta ruƙe da sandarta, ashe 6acewar da ta yi don ta ɗauko sandar hannunta ne ta kuma mayar da suturarta.

“Na yi tsammanin kin ji tsoro kin gudu ne”; acewar tsohuwa Tamira

Mahaukaciyar dariya zafreen Ta saki tare da cewa”Babu tsoro a cikin zuciyar tsohuwa Zafreen! Tamira kin shiga Uku! Kin tsokanowa kanki Bala’e da masifar da ba za ki Iya jurarsu ba, Zan kashe ki har lahira bayan na gama da ke zan ƙarasa kashe waɗanda basu mutu ba a cikin Yaran can naki, Zan sha Jinin su In ci tsokar naman su”

Tana kai ƙarshen maganar ta, ta yi kukan kura tare da Afkawa tsohuwa Tamira, gaba da gabanta Aljani Ya taka wuta, Domin kuwa Zafreen tafi Tamira ƙarfin sihiri, Faɗane ya kaure a tsakanin su kamar dawakai, ba ka iya jin komai sai sautin buge bugen su da gurnaninsu uwa namun dawa, Ƙura ta karaɗe cikin ɗa ki, Kusan atare su ka canza suffofin su, Tsohuwa Zafreen ta rikiɗa ta koma Damusa, Tamira ta koma kura, Ko a namun dawa Damusa ba abokiyar karawar Kura bace, Faɗan nasu Ya canza salo, kamar a filin daga su ka cigaba da kaima junan su Hari duk suka raunata kawunan su.

*ANGEL*

Tsawon lokaci tana a sume saman Gadon da aka kwantar da ita, fatar jikinta jawur da Jinin da su ka yi mata wanka dashi duk ya daskare mata, zai yi wuya yabar Jikinta, saukar ruwan sanyin da ta ji ajikinta ne ya farkar da ita a firguce ta farka, sai dai ta kasa buɗe idanuwanta saboda nauyin dasu ka yi mata, hatta bakinta Yaƙi buɗuwa la66anta sun kumbura suntum wani irin zogin azaba su ke yi mata.

Ba zato ba tsammani kunnuwanta su ka jiyo mata muryar SALSABEEL.

“Meyasa ki ka yi gaggawa? Kin manta me na faɗa ma ki? Sai da nace ku yi takatsantsan idan ba haka ba za ku ja ma kan ku ne damu kan mu….” Sam ta ƙasa motsa bakinta, Idanuwanta kaɗai ta iya samun damar buɗe su akan jikin shi, Yana atsaye Cikin shigar Giant ko’ina na jikin shi arufe kamar yarda ta ganshi a shekaran Jiya. Ta yi mamaki sosai saboda a tattaunar da su ka yi da ita ya faɗa mata cewa ba zata sa ke ganin shi ba, sai ga shi Ya dawo yau, hakan ya tabbatar mata da cewa suna acikin haɗari gaba ɗayan su, taja masu bala’e.
Rushewa ta yi da matsancin kuka raunin da ke abakinta yaci gaba da fitar da jini

Tsananin tausayin ta ne Ya kama shi, ganin yadda suka raunata Jikinta sun gur6ata mata tsaftatacciyar fatarta, tsabar takaici da danasanin gaggawar da ta yi ne yasa ta yin kukan, tana so ta yi ma shi magana sai dai ta kasa saboda sautin muryar ta yaƙi fita ko da tana yin kukan babu sauti.

“Ban faɗi hakan don na fama maki ciwon da ke acikin zuciyarki ba, Nasan kina yi ne duk don ki cece rayuwan ƴan uwan ki, don kuma ki cika mana alƙawarin da ki ka ɗaukar mana, sai dai kash gaggawar da ki ka yi ta yi silar jefa rayukan mu cikin haɗari, Zai yi wuya mu tsira sai dai bazan bari Ki rasa ran ki ba, Zan yi maku ƙoƙari Ayau ɗin nan ku fuce daga cikin kurkukun nan kafin Hankalin Matsafan ya dawo kanku, Mun ci sa’a shuwagabannin kurkukun basu aciki, Sauran da suka rage Giant ne masu haɗarin gaske, Ni kaina da na ke da sihiri a jikina bazan Iya ja dasu ba, A yanzu haka da nake Yin magana da ke nayi ƙoƙarin Sarrafa ɗakin Da ke ɗauke da madubin tsafin su shiyasa ba zasu Iya ganin mu ba, Nan da Awa ɗaya Zamu Aiwatar da komai Idan har lokacin nan ya cika kuna acikin kurkukun nan mu dukan mu zamu Mutu bayan azabtarwa da zasu Mana.”

Baiwar Allah duk da raɗaɗin da bakinta ke yi mata ahaka ta daure ta cije ta soma Yi mashi magana muryarta araunace daƙyar sautin ma yake fita

“Sun cire min uniform ɗina, Ruwan zamzam din Yana a cikin aljihun wandona bansan Ya zanyi ba” cikin ƙunar rai ta ambaci hakan

“Zanje na ɗauko maki Uniform ɗin ki, cikin minti ɗaya” Yana ambaton hakan ya 6ace ma ganinta.

Yunƙurawa ta yi daƙyar ta miƙe zaune, Ƙarnin Jinin jikinta ya addabi hancinta, bargon da ke shimfiɗe saman gadon ta janyo ta yafa ma jikinta, Zuciyarta acunkushe take da damuwar halin da ƴan uwanta su ke a ciki, Ita ba ta damu da kanta ba, sune damuwarta. Fatanta Allah yasa tsohuwa zafreen bata cutar dasu ba kamar yarda ta faɗa mata.

Durowa Cikin ɗakin salsabeel Yayi hannu shi ruƙe da uniform ɗinta, Jar vest ɗinta da wandon ta Ya miƙa mata su, yatsun hannayen ta na kerma ta kar6e su, Agaban shi ta zura kayan bayan ta kammala sanya su ta zaro ƴar ƙaramar robar zamzam daga cikin aljihun wandonta, Idanuwanta acike tab da ƙwala ta kalle shi tare da cewa”Ta ya ya zan Iya ganin Danish har in bashi ruwan zam zam ɗin”?

“Bamu da isasshen lokaci, A saman bayana zan goya ki in kai ki inda Ya ke kuma zan taimaka maki mu bashi ruwan, ya kai ƙarshen maganar tare da Juya mata baya ya zuƙunna daga bakin gadon, matsowa ta yi tare da kama bayan shi ta haye, Ya yunƙura Ya miƙe, Daga inda ya ke goye da ita Ya 6ace 6att….

Ba su dura a ko’ina ba sai A wani katafaren Ɗaki mai tsawo da faɗi komai na cikin shi launin Ja ne, hatta dogayen labulayen da ke a kewaye dashi red colour ne. wani irin sanyi ne ke ratsa sassan Jiki acikin ɗaki kamar sanyin A.c, daga gani special room ne na kurkukun ƙaddara, Tsadaddun furniture ɗin da ke a cikin ɗakin kaɗai abun kallo ne.

Jin shiru bata motsa daga saman bayan shi ba yasa shi yi mata magana muryarshi cikin raɗa ya furta” Mun ƙaraso, Ki tashi ki ga ɗan uwanki” yanayin yadda ya yi mata maganar ne yasa taji gabanta Faɗuwa shi kanshi Salsabeel ɗin A tsorace Ya ke da abunda zai Biyo baya balle ita kuma da ta ke Ƴar ƙwaruwa wadda bata taka kara ta karya ba. Tsoro ya hana ta ɗago ta kalli inda Danish ɗin Ya ke duk irin kewar shi da ta yi, Sosai ta runtse idanuwanta Hannayenta ƙanƙame da Salsabeel.

“Na faɗa maki bamu da isasshen lokaci ki sauka mana” yai maganar tare da zuƙunnawa don ta sauka, Kamar wadda ƙwai ya fashe mawa akai jiki na kerma ta sauko daga saman bayanshi, sai lokacin ta samu damar Ware idanuwanta sosai Tana ƙarewa ɗakin kallo tun daga kan labulayen dake a cikin shi har zuwa kan shimfiɗaɗen Carpet ɗin dake a ƙasa Ga wani ƙayataccen table mai ɗauke da Dinner set, plate ta gani na tangaran mai ɗauke da kayan marmari, ga wani apple da aka datsi saman shi, hada sawun haƙoran mutun, Ga wani glass cup mai ɗauke da wani abu acikinsa ruwane amma launin shi yayi bright red kamar an surkashi da wani abu. Duk fa wannan kalle kalle da ta ke yi ba ta yi tozali da shi ba, saboda ta hana idonta kaiwa gare shi, Har sai da Sabsabeel yai mata gyaran murya tukunna ta soma Juyar da ƙwayar idanuwanta a hankali ta ɗaura su kan katafaren king sized bed ɗin da ke kafe a cikin ɗakin, Gado ne irin na sarakuna launin shi Golden Colour an shimfiɗe shi da lallausan Bedsheet launin Ja, slowly ta sauke idonta akan dogayen ƙafafuwanshi wa’iya zubilla tsabar ruɗu yasa ta dabarbarce saboda ta kasa yadda cewa shine, Halittar Jikin shi gaba ɗaya ta canza, Ya zama jibgegen ƙato, Samun Namiji mai irin ƙirar ƙarfin shi zaiyi wuya, ƙira ce mai matuƙar tsoratarwa, rikitarwa da kuma jan hankali, Ga dukkan alamu bacci ya ke yi a giant ɗin ma bai bar halin shi na yin bacci ba, Dogon wandone Baƙi A jikin shi, Sai Jar t shirt ta matse jikin shi, ta bayyana ainihin surar shi, musamman damtsen hannayen shi tamkar zasu fasa rigar saboda tsabar ƙarfi.

Sun canza shi sosai Farar fatar wuyan shi hada zanen tattoo launin baƙi da Ja wanda ya kasance Tambarin kurkukun ƙaddara ne duk wani Giant yana da Zanan a wuyan shi, sun rage mashi tsayin sumar kanshi, Anyi mashi kitson zane guda shida, wutsiyar kitson ta sauka har saman Broad-shoulders ɗin shi, Ya koma kamar ƴan iskan turawan nan, waɗanda tun daga suffarsu zaka shaida cewa, ba bu Ɗigon Imani A zuciyar su.

Zafafan hawaye ne su ka wanke fuskarta a yayin da ta ke ƙare mashi kallo, Ta gaza yarda da abunda idanuwanta su ke Nuna mata, Wai Danish ɗinta ne Ya koma haka? Hankalin shi kwance ya ke sharar bacci babu alamun damuwa atattare da shi, duk irin kewar shi da ta yi shi baisan ma da zaman ta ba balle sauran ƴan uwan shi, saboda zalunci na mutanan nan sun rabasu da ɗan uwansu.

Cikin shessheƙar Kuka Ta furta Sunan shi”Da..Nish..” walking nervously ta nufi bakin gadon ta zauna daga gefe tana ƙare mashi kallo, Ya yi wani irin haske mai kyan gaske, tsabar kyan fuskarshi tamkar zai kashe mata ido, la66ansa sun yi jawur dasu kamar na Jinjiri, Dogon hancin shi ya tafi tsaye ba lanƙwasa, kwarin idon shi ta zuba ma ido, dogayen eye lashes dinshi masu kyau da tsari.

“Don’t waste Our time! Mintuna kaɗan suka rage mana,” Muryar Salsabeel ce ta fargar da ita, Ji ta ke kamar ta faɗa mashi ta rungume shi a jikinta ko ta samu sassauci a cikin zuciyarta.

Matsawa kusa da ita sabsabeel yai “Ki buɗe murfin robar, Ni zan hau saman gadon In ruƙe shi gudun kada ya farka ya ham6are ki, naushin giant yana da haɗari sosai Bugu ɗaya su ke Yiwa mutun ya mutu In ba wani iko na Allah ba’ Wannan maganar da ya yi ta ɗaga mata hankali, ta ƙara jin tsoron shi.

Yatsun hannunta na kerma ta soma ƙoƙarin buɗe murfin, tana dab da zata Ƙarasa cire shi, Kamar An ce ta kalli fuskarshi taga ƙwayar idon shi na motsi ta saman kwarin idon shi, da ƙarfi ta furta”Ya farka”

Sautin miryarta ne ya daki dodon kunnanshi, Aiko kamar an zungure shi Ya ware manyan idanuwanshi launin russet brown akan fuskarta, wani irin ƙwar jini yai mata a furguce Ta miƙe daga gefen gadon Tana ja da baya, idanuwanta azazzare, Salsabeel da ke yunƙurin ruƙe kafaɗun shi don Ya hana shi miƙewa A zafafe Yai wurgi dashi tun daga saman gadon Ya ƙundumo ƙasa Ji ka ke tummm, Hankalin Angel fa ya ƙara tashi ganin yarda ya jefar da babban mutun kamar Salsabeel yadda kasan kallon tamola haka ya jefar dashi wanda a haife salsabeel zai Iya haifarshi, Durowa yai daga saman gadon Yana huci Kamar mayunwacin zaki, breast ɗin shi har motsi su Ke yi, Wani matsiyacin kallo da taga yana binta dashi yasa ta haɗiyi yawu mai zafin gaske, kallon da Danish ke yi mata kamar ma baisan wace ce ita ba, Tunkararta Ya soma yi Yana gurnani har wani jijjiga jikin shi ya ke yi, babban abunda ta ke ji ma tsoro kada Ya rikiɗa Ya canza halitta don ta fahimci abinda ya ke shirin Yi kenan, Juyawa ta yi da gudu tana neman inda zata 6oye kanta don kada ya cimmata, saida ta gama shan wahalar kewaye ɗakin Kwatsam taga Ya bayyana agabanta. Ɗagowa ta yi a tsananin tsorace ta ke kallon shi tana girgiza mashi kai haɗi da marairaice mashi fuska don Yaji tausayin ta amma ina ai ko kallo arziƙi bata ishe shi ba, Muryar Salsabeel ce ta karaɗe kunnuwanta a kausasace ya ke bata Umarnin ta gudu daga gabanshi kada ta bari ya Damƙe ta.

kafin ta yi yunƙurin Canza hanya Cikin rashin sa’a ta ji Ya damƙi qugunta Kamar ɗiyar roba Ya ɗaga ta sama Muddin kuwa Ya bugata da kasa sai qugunta Ya 6alle saboda ƙarfin dake gare shi bana Mutun bane na baƙin shaiɗanin aljani ne, Yana ƙoƙari makata Da ƙasa Salsabeel ya cimma shi Gaba ɗaya yai wurgi da ita ƙasa ta kife robar zamzam ɗin da ke a hannunta tuni ta gangara ƙarƙashin table ɗin da ke a ɗakin gashi murfinta ya fara zamewa zai cire saboda buɗeshin da ta fara Yi, ruwan da bai wuce Kur6a ɗaya ba Ya kare idan ya zube shikenan sun rasa damar da su ke da ita.

Faɗane ya kaure a tsakanin Salsabeel tsohon ƙashi da Danish garkuwar kurkuku, Yadda Danish Ya ɗaga salsabeel Ya buga shi da kasa ba ƙaramin gigita Angel yai ba, lamarin ya tsoratar da ita babban abunda take jima tsoro kada Ya kashe shi da bugu, da ko ta shiga uku, ƙarfi ba ɗaya ba Danish ya zarce salsabeel Nesa ba kusa ba saboda shi matsayin babban giant ke gare shi masu haɗarin gaske, Salsabeel Kuwa Ko star ɗaya bai da ita a muƙamin Giant, ta inda Allah ya taimake shi ƙwarewar da ya samu A fannin sarrafa tsafi, ba don haka ba da tuni Danish ya jima da karkarya ƙasusuwan jikin shi, Bugun da ya ke yi mashi da ace Lafiyayyan mutun ya yi mashi wanda baida sihiri a jikin shi da tun a bugun farkon, ga6o6in jikin shi zasu daina aiki.

Ta rasa ina zata tsoma ranta ta ji daɗi faɗansu ya yi matuƙar ta6a ƙwaƙwalwarta, Ku ka ta dinga yi hannayenta daddafe da kanta, wani irin matsanancin ciwon kai ne ya farmata, muryar Salsabeel taji a raunace ya ke faɗa mata ta ɗauko zam zam ɗin, da sauri ta rarrafa ta nufi table ɗin har ta kusa ƙarasawa Taji an Janyo ƙafarta da ƙarfi Yai wurgi da ita gefe ɗaya har saida kanta ya bugu da bango tsabar raɗadi Yasa nan ta ke ta sume. Sai faman huci ya ke yi yana gurnani, gaba ɗaya ya gama naƙasa ƙwarin gwiwarsu , shi kanshi Salsabeel Yana durƙushe ƙasa kanshi Ya bugu sosai ga6o6in jikinsa sun rauna, akan idon shi Danish Ya jefar da table ɗin da ƙafarshi, Kayan marmarin da ke asaman shi duk su ka tarwatse ƙasa, Ashe yana sane da robar Zam Zam ɗin hannunta, Kafarshi Ya ɗaga da niyar ya ta ke ta don ta fashe, A kiɗime Salsabeel Ya fasa ƙara tare da Miƙewa Yana jan kafarshi Ya nufi Danish.

Shu’umin murmushi ne Ya bayyana akan fuskar shi hada juyowa ya kalli Fuskar Salsabeel Ya ɗaga mashi gira muryarshi tamkar ta mashayin giya ya furta”What?”

“Kada ka fasa ta na roƙe ka ko dan saboda ƙaunar da ke a tsakanina da kai danish, Nifa ne Ya yan ka, Yau da hannun ka ka ke buguna kamar zaka kashe ni? Sai ka ce baka sanni ba? Laifin me muka aikata maka? Kalli kaga yadda ka Bugi ƴar uwarki Angel kamanta irin ƙaunar da ke atsakaninka da ita”? Ta6e la66ansa yai”who is she”? Tambayar daya jefa mashi kenan

Muryar Salsabeel tamkar zai fashe da ku ka Ya ce “Ka kalle ta da kyau yar uwarka ce Angel, Ba ka yi kewarta ba? Idan bazan manta ba lokacin da ka ke rashin lafiya saboda matsalar da idon ka ya samu sunanta ka ke faɗi acikin sambatun ka ko ka manta ne”? Kwa6e fuskarshi yai Alamar bai tuna komai ba.

Salsabeel sai Jan hankalin shi ya ke yi da surutu A yayin da ya ke tunkararshi duk don ya samu damar ɗauke robar zamzam ɗin da ya ke Yunƙurin fasawa.

“you’re trying to deceive me” Danish Na ambaton hakan Ya dire ƙafarshi saman robar, kukan Kura Salsabeel Yai tare da cakumar Wuyan shi Da iya ƙarfin shi na ƙarshe Ya daddage Ya janye Danish gefe ɗaya, A gaban robar Sabsabeel Ya zuƙunna Yana Kallon Yadda ruwan Cikin ta ya tsiyaye ƙasa, Tsabar takai Ci yasa shi Fashewa da kuka kamar ƙaramin Yaro, ƙululun baƙin ciki ne ya addabi zuciyar shi, Damar da su ke da Ita ta ƙare, zaiyi wuya su tsira.

Jikin Salsabeel na tsuma Ya yunƙura tare da miƙewa Ya ɗaura idanuwanshi akan Bayan Danish wanda ke ƙoƙarin Tunkarar Angel don Ya ƙarasa kasheta, A hankali ya ɗaura yatsun hannun shi saman rigar jikin shi ta kakin Giant, For the fast time da yai nufin bayyana ainihin suffar shi, Cire Rigar jikin shi yai tare da jefar da ita ƙasa, Faffaɗan ƙirjine dashi Irin na sadaukan Ya ƙi, 6an6are mask ɗin da ke akan fuskarshi Yai tare da jefar dashi saman rigarshi.

Namijin Duniya Kyakkyawan gaske, fatar jikin shi Jawur ta ke, Ya fito a baturen shi, Idan ka kalli fuskar shi ba za ka ta6a yarda cewa shi jinin tsohuwa Tamira ne, saboda ita mummunace tsufa Ya 6oye kyanta.

“Na bika ta lalama ka ƙi banin haɗin kai yan zu zan yi maka ta tsiya, Danish ko ni ko kai A yau ɗin nan” Jin miryarshi yasa Danish dakatawa da yin tafiyar, cikin Takun Qasaita Ya waiwayo yana kallon shi, ganin ya tu6e rigarshi yasa ya fahimci shirin faɗa Ya yi, jijjiga jikin shi yai nan ta ke ya rikiɗa ya koma Jibgegen zaki ƙosasshen gaske sai gurnani ya ke yi yana wage bakin shi.

Hankalin Salsabeel Yai matuƙar tashi ganin ya rikiɗa, saboda shi sihirin shi bai kai ƙarfin da zai Iya rikiɗa ya canza halitta ba, ganin yadda ya ke tunkaro shi a fusace Yasa shi ja da baya ya soma tunanin me yakamata yayi don Ya dakatar dashi, idan ba haka ba A kashe zai kashe shi har lahira.

Waige waige ya dinga yi yana bin ɗakin da kallo har idon shi ya sauka akan Wuƙar yanka kayan marmarin da ke yashe saman floor, Ba zai iya ɗaukarta ba don bai son Ya cutar dashi, Lallashinshi ya soma yi yana faɗin”Am sorry Danish ni ba faɗa zanyi da kai ba, Pls ka saurare ni Danish dan Allah ka canza halittarka zuwa ta mutane ina son yin magana da kai…..” Magiya ya dinga yi mashi amma ɗan tahalikin nan yaƙi sauraron shi, Juyawa yai da gudu ya nufi saman gadon ɗakin Ya daka Uban tsalle Ya haye saman shi tare da sanya hannu ya rarumo bargon dake nannaɗe saman shi, dai dai lokacin da Danish Yai kukan kura Ya daka tsalle da suffar Zaki Zai kai mashi hari Yai saurin Rufe shi Da bargon Ya nannaɗe shi a ciki, Allah ne ya taimake shi Ya bashi ƙarfin da shi kanshi yasan bana shi bane, a saman floor suka faɗo, Sosai Ya matse Danish Acikin bargon, ruƙo bana wasa ba kamar zai kashe shi, tun yana jin sautin gurnanin shi har ta kai ga yai shiru babu motsi alamar ya suma.

Tsabar farin Ciki yasa shi sakin dariya yayin da hawaye ke bin fuskarshi, tunawa da lokacin su da ke shirin ƙarewa saura Mintuna 30 ya rage masu kacal, A hanzarce Ya zame bargon da ya lullu6e shi a ciki, har ya koma suffar shi ta mutane a ƙasa ya kwantar dashi, Miƙewa Salsabeel yai da sauri ya nufi robar zam zam ɗin da ya tsiyaye, Ya ɗauko ta a tsakiyar tafin hannun shi ya dawo ya zuƙunna agaban Danish, a hankali ya buɗe mashi ƙaramin bakin shi ya dinga matsar robar ta ƙarfi kamar zaiyi hauka daƙyar ya samu ɗigon Ruwan Ya faɗa bakin shi, Ɗigo ɗaya kacal, Gani ya ke kamar ba zai isa ya dawo hayyacin shi ba, hakan yasa shi cigaba da matsa robar duk don ya samu ruwan ya ƙara ɗigowa a ƙarshe da ya gaji ya jefar da robar ƙasa, ya dafe kanshi da hannu biyu zuciyar shi na harbawa da matsanancin sauri.

faɗuwar da gaban shi ke yi ya tabbatar mashi da cewa wani mummunan abu na faru da wani nashi ko dai mahaifiyar shi, ko kuwa yaran da ya ke ƙoƙarin taimakon rayuwar su, Miƙewa yai a zabure Jiki ba ƙwari ya nufi Angel da ke yashe ƙasa tun ɗazu da Danish ya jefar da ita ta sume bata ƙara motsi ba, hannu biyu ya sanya tare da ɗaukar ta, Ya dawo ita gefen Danish Ya kwantar da ita, kafin ya ƙara miƙewa Ya nufi Kayan saman table da Danish Ya watsar dasu ƙasa, A cikinsu ya samu robar ruwa, ya ɗaukota tare da dawo wa gaban su Ya zuƙunna yana faman fitar da huci Shi kanshi a raunace ya ke daurewa kawai ya ke yi duk don ya samu ya ƙarasa taimakon su.

A Saman fuskar Angel Ya watsa ruwan a Firgice ta farka haɗi da miƙewa tsaye tana Faman zazzare idanuwanta fuskarnan jawur ta kumbura suntum.

“Unaisah” Cikin sanyin murya Salsabeel ya ambaci sunanta ko da ta kalle shi a tsoroce Ta furta”wanene kai”! Ras Ya ji gaban shi ya faɗi, Can kuma sai ya tuna da fuskarshi daya cire, shiyasa bata gane shi ba.

“Salsabeel ne” kallon shi ta dinga yi kamar yau ta fara ganin shi, ita kanta ba haka ta yi tsammanin zata ga fuskarshi ba.

“Ga ɗan uwan ki nan, Na yi ƙoƙarin ɗiga mashi ruwan zamzam ɗin sau ɗaya abakin shi bansani ba ko zai farka acikin hayyacin shi ko kuwa akasin hakan, Ba zan Iya jiran farfaɗowarshi ba, hankalina ba akwance yake ba, Ina tsoron wani abu ya sami mahaifiyata Don haka zan tafi wurin ƴan uwanki nasan tana atare dasu” Angel na ƙoƙarin buɗe ba ki tace mashi ya tafi da ita kada yabarta anan gudun kada Danish ya farka a matsayin Giant ya kasheta sai dai kash kafin tayi maganar Salsabeel tuni ya 6ace ma ganin ta…

A 6angaren Su tsohuwa zafreen kuwa Dambe su ka yi bana wasa ba, Saboda tsabar zalunci sai da ta cire mata kunnuwanta duka biyun ta cinye su, Jini duk ya wanke jikin tsohuwa tamira, duk yadda taso ta ƙwaci kanta ta kasa saboda rashin ƙwarin Jikinta, har sai da zafreen ta kwantar da ita ƙasa ta dinga buga kanta Ga ƙasa tuntuna motsi har ta kai sumewa.

Mahaukaciyar dariya zafreen ta saki ganin ta yi nasara akanta, Faɗa da aljani ba riba maganar da zafreen ta furta a yayin da take miƙewa ta nufi wuƙar da batul ta yi amfani wurin yi mata Illah, Jinin da ke a jikin wuƙar ta lashe kafin ta juyo ta dawo kan tsohuwa Tamira, Ta zuƙunna tana Shafa Jikinta da tsinin wuƙar”Na jiye maki baƙin Ciki, domin kuwa ayanzu ɗin nan zar farke Cikin ki, In kwashe ƴan hanjin dake a cikin ki In cinye su, idan kin isa Ki kwaci Kanki, ƙazamar banza har ni za ki kalli idona Ki gaya mini magana kamar bakisan wacece ni ba…..” ta ambaci hakan tana mai sakin murmushi

Yunƙurin caka mata wuƙar ta yi ba zato ba tsammani taji an buge kanta da wani abu mai nauyin gaske tamkar dutse kafin ta yi yunƙurin juyawa don taga wanene taji an ƙara buga mata shi akanta, nan ta ke kanta ya juye Ta kife ƙasa,.

Batul ce a tsaye Tana haki, Hannunta ruƙe da sandar Zafreen da ta jefar ƙasa, ƙarfin sihirin da ke a jikin sandar ne yasa har ta yi nasarar kwaɗeta da ita, daddagewa tayi da ƙarfi taci gaba da buga mata sandar, Jijiyoyin wuyan ta duk sun furfuto waje saboda tsabar 6acin rai, babu sassauci atattare da ita tun tsohuwa zafreen na motsi har ta kai ga idanuwanta sun Juye, Jefar da sandar Batul ta yi ƙasa tare da ɗaukar wuƙar da zafreen ɗin ta jefar, Saman ruwan cikinta ta haye ta daddage ta dinga luma mata wuƙar Jini yadin ga ambaliya kamar an kunna fanfo harta saman fuskarta, Kacaca tayi mata sai da ta farketa, A ƙarshe dai Baful ta yi nasarar kashe tsohuwa Zafreen ko shura wa ba ta yi ba nan ta ke rai yai halin shi, harta mutu batul bata daina farke jikinta da wuƙar ba, saboda bata acikin hayyacinta, kuka ta ke yi tamkar ana zare ranta.

Farfaɗowa tsohuwa Tamira ta yi a hankali ta buɗe idanuwanta da suka ruƙida su ka yi jawur dasu, ta wurga su kan Batul da ke a zaune saman Zafreen tana aikin fiɗa.

Muryarta na rawa ta ambaci sunanta”Ba..tul..” Sai lokacin ta jefar da wuƙar hannunta, jiki na rawa ta sauko daga saman jikin zafreen ta rarrafo Zuwa gaban tsohuwa Tamira.

Fuskarta jaga jaga da hawaye hada majina, taci gaba da yin kuka tana faɗin”Ta zalunce mu ba mu yi mata laifin komai ba, ta kashe mana ƴan uwan mu ta gama da rayuwar mu…..”

Hannun tsohuwa na kerma ta ɗaura shi saman sumar kan Batul da ke a tarwatse daƙyar take iya yi mata magana”Batul babu wasu kalmomi da zan iya yin amfani dasu wurin baku haƙuri akan irin jarabtar rayuwar da kuka fuskanta, Ku yi haƙuri kuyi haƙuri Allah yana atare da ku…….” Da numfashinta na ƙarshe ta ƙarasa maganar nan ta ke rai yai halin shi, A matuƙar kiɗime Batul ke Fuskarta………

 

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

Back to top button