Auren Gado Hausa NovelHausa Novels

Auren Gado 19-20

Sponsored Links

1⃣9⃣&2⃣0⃣

 

………….. Naziya kuwa Abin kamar a mafarki haka take ganin shi, koda ta farfado manya suka natsar da ita sunayi mata nasiha, sai Ajiyar zuciya takeyi takasa koda fitarda hawaye, Saida Akace mata har an sallace shi an dangana shi da makwancin shi ne ta fasa kuka, shikenan yanzu bazata kuma ganin shi ba, haka rayuwar su tazama tarihi Auren ta dashi yazama tarihi, Wannan wace irin kaddara ce ta bullo a cikin Rayuwar ta? Istigifari ta farayi domin kar Imanin ta yayi rauni, Amma kowa yasan bakaramin ciwone a zuciyar taba rashin mijin da kukayi Aure wata biyu yatafi yabarka, kowa ya tausaya mata, har kanin Baban su Ahmed din na gidan sunzo, mommy kuka take tana birgima, cikin masifa Aunty Fatima tace “Wallahi bilkisu kukan ki baida Amfani ai saiki tashi kiyi farin ciki, Ahmed yatafi yabar miki duniyar, ba Auren kece raini ba! yau gashi yabar miki matan duka, kiyi Addu’a ma ko jika ace yabar miki jikin Y’ar talakar da bakyaso, kin hana yara sakat ai munsan komai kallon ki mukeyi kawai kijira Abinda zai biyo baya, wallahi sakamako na zuwa. Matar kawu ce uwar gidan tace “Aa Fatima kubarta haka rashin d’a tayi kuma kuzo ana zama kuna tada fitina. “Nayi shiru Matar yaya”.
Kuka Momy ta fasa, yanzu take data sani mara Amfani Ina ma Ina ma, Allah yasa Naziya tanada ciki, Allah yasa zata ga Abinda zai cire mata kewar d’an ta mai hakuri, Kuka takeyi mara Amfani domin batada damar maida hannun agogo baya.
Khaleel kuwa zazzabi mai karfi ya rufeshi Saida likita yazo ya kuma dubashi, su Malam na tausar shi tareda mai nasiha mai ratsa zuciya, kabi d’an uwan ka da Addu’a shine kawai soyayyar da zaka nuna mai yanzu.
Gefen Amare Fauziya tafi d’an natsuwa domin mutuwar ta taba zuciyar ta don duk shashancin mutum yau ace Wanda kasani yafadi ya mutu, dole kaji jikin ka yayi sanyi idan akwai Imani a tareda kai.
Gefen Amaryar Ahmed mommyn ta da y’an uwan ta nafama akan ta shirya takaba tace atafau bazata yimai takaba ba tunda ko kwana basuyi ba tare, maganar har taje kunnen mommy, bata iya cewa komai ba domin ta shiga rayuwar kurame na wucin gadi, Naziya kam bazata iya bude baki tace wai mijinta bai kusance taba, domin akwai Alkunya kuma ko saboda soyayyar datake mai tareda hakkin igiyoyin nan uku dake wuyan ta dole tayi mai takaba, in akwai Abinda yafi haka ma zatayi mai domin ita tasan tayi rashi babba Wanda maida irin shi zaiyi wuya, ita ai jitake ma ta rufe shafin Aure a rayuwar ta.
A cikin kwanakin uku zuwa bakwai bamasu sauki bane ga duk makusantan mamacin, tun daga kan mommy, Naziya, Khaleel da duk wasu masoyan Ahmed,
A dakinta take tanayi mai takaba mai tsabta tareda binshi da Addu’oi dare da rana, kuka kuwa kullum dare sai tayishi rayuwar da sukayi dashi batada tsawo Amma yabar mata memories da zasu rika tuno mata dashi har karshen Rayuwar ta.

Seven days

Khaleel Ko part d’in shi bai zuwa tun ranar da fauzy ta shigo ko kallon ta baiyi ba, Abinci ma baya iya ci ya rame a fuskar shi sosai daka kalle shi, Aunty zarah ce ta shiga dakin shi yana zaune rikeda waya karatun Alqur’ani mai girma natashi, idanun shi a rufe, sanye yake cikin jallabiya fara, “Ibrahim” kazo Alhaji na Kira ta fada tareda juyawa, tashi yayi yana sa stop tareda rike gefen jallabiyar shi ya fita, a katon falon ya samesu dukan su har Naziya tana nade cikin hijabin ta, gefe daya Maman Salifa ce da ta Fauziya duk suna hakimce sai kuma Amaren a gefe, Wanda shi tun ranar da aka kawo su bai sasu a idoba, Kawu da malam ne zaune a kujera sai kannin kawun mata biyu gefe, mommy ce tayi shiru kamar ruwa ya cinyeta, kana ganin ta kasan mutuwar ta tabata. Kawun ne yace “Malam Abubakar na taraku ne anan saboda Abubuwa uku na farko dai Ina Kara mika ta’aziya ta gareka Ibrahim domin kai Kayi rashi, Allah ya Kara maka dangana tareda ikon daukar nauyin da aka dora a wuyanka, na biyu akan maganar Matar Ahmed, sun kirani akan zasu tafi da ita gida domin bazata iya yimai takaba ba, don haka ga Malam muji shima idan zai tafi da Ita uwar gidan ne gida. Saurin dago kanshi yayi ya kalli gefen ta, sai yanzu yaga yanda ta rame tareda yin zuru zuru, gwanin tausayi, ya ce Kawu duk yanda kukayi daidai ne. Abinda ya iyacewa kenan,
Addu’a malam yayi kafin yabisu da nasihohi ya karayi musu ta’aziya, ya dora dacewa Idan so samune Naziya ta zauna a dakin ta, Amma a yanzu saboda dalilai masu yawa zan mayarda ita gida tayi takabarta, Allah ya gafartawa Ahmed.
Wani irin daci Khaleel keji a zuciyar shi, yarasa wane irin tunani zaiyi baida kalma daya da zai iya furtawa a halin yanzu,
Kukan mommy ne yasa suka kalle ta, ba Wanda yaji tausayin ta har Khaleel din ma, domin tsawon kwana bakwai din nan baya ko kallon gefen ta.

Toh Hajiya bilkisu Ahmed ya tafi, Amaryar da kika buga kirji kukayi mai yau tace bazata iya zama dashi ba, sannan Inada yakinin mugun halin ki ne yasa itama Matar tashi za a tafi da ita, domin ni Nafi kowa sanin halin ki bazaki taba canzawa ba, da zaki canza da mutuwar yaya na zata fara canzaki, mundade muna daukar mugun halin ki yau kinga ni, Allah yasa ki dauki darasin idan har akwai sauran kwakwal akan ki.

“Ya isheka Modu karka manta d’ana na rasa babban dana duk Wanda yayi kukan mutuwar nan Kara yayi min, sannan maganar bakin hali, naji abarni da kayana duk ko wacce tafi ruwa gudu cikin su, ni Abarni da zafin rashin d’ana kawai, tafada tana mikewa cikin zafi tayi daki tana kuka mara madafa.
Ko dago kai Naziya batayi ba Saida malam yace “su shukrah na nan zasu hada miki kayan ki su taho dake, ni zantafi dalibai na jirana a gida. Ya musu sallama yatafi. Saura y’an uwan kawai da iyayen matan, Maman Fauzy tace toh Saura mu yaza’ayi da yarinya tun da tashigo ace bata samu kwanciyar hankali ba.
Cikin zafi yace “Zaku iya tafiya da ita in kun so I don’t need her.
Yafada cikin fada da kuma iyakar gaskiyar shi, “dama momy ta Aurota idan kunga bazaku iya zama ba ga hanya.
Cikin rawar jiki tace ” no mommy please kuje ni Ina nan. Tafada domin tana matukar kaunar Khaleel, bayan ta aureshi da kyar ta yaya zatayi sake ta fita, don haka tuni ta kashe bakin uwar, salifa ce taja uwar ta gefe, “mommy nidai kinga kisa kawun su yasa Khaleel ya Aureni tunda anayin Auren gado, kinga yafi ma Ahmed din haduwa mommy wallahi zan zauna in ya Yarda. “Y’ar gari nima tunani na kenan ai kinga yaron ya Tara dukiya kan dukiya gatashi gata uwar shi gata d’an uwan shi yanzu, ke fa uwar shi duk cikin mu tafimu kudi shegiyar, bari mukoma inyi magana.

Jiki na rawa suka koma falon lokacin Naziya ta mike tayi daki inda su Aunty Raliya ke hada mata kayan ta, daga Khaleel sai kawu sai gwaggon nin shi, mommy dasu zarah na daki,
Zama Maman Salifa tayi tana Washe baki “Alhaji Inada magana. Suka zuba mata ido kafin yace “munajin ki. “Yauwa nace ba, tunda dai ga d’an uwan shi mezai hana ayi tunani mai kyau a bashi Salifa sai a hada Auren gado. Wani irin saurin dago kanshi yayi tareda watsa musu kallon kun haukace ya ce “kuna hauka wallahi kun haukace, toh kusani kune sanadin duk Abinda ya faru a rayuwar d’an uwana, koda ace mata sunkare a duniya bazan taba Auren Y’ar kiba, don haka kawu ni natafi Inka gama domin one more minutes a nan zanyi Abinda bashi bane. Yafada yana wucewa a zuciye,
“Toh kunji sai ku tashi kubamu wuri, inji daya daga cikin matan, shigewa dakin mommy sukayi jiki a sanyaye,

Dayar tace “yaya dakasa baki ya Auri Wannan Y’ar mai Hankali, itace Matar Aure ba wa’innan y’an barikin ba. “Zamuyi Wannan maganar ba yanzu ba kubari mu gama war ware rashin da mukayi sannan shima Khaleel baya cikin natsuwar shi yana bukatar natsuwa, company su ma manager din ne ke kulada komai tunda ba Ahmed.
Dakin mommy su zarah ke lallashin ta domin sunsan koma meye ita tafi kowa rashi, har suka samu tayi shiru tana Ajiyar zuciyar, Shigowar kawar tata yasa tace kuna nan Hajiya? Eh kawata ai na canja shawara, nace ai basai na dauketa ba kawai tunda zumunci mukayi niyyar hadawa tun farko ko yanzu bata baci ba tunda kanin shi na nan sai a hadasu Auren gado kawai.
Kallon su tayi kawai domin tasan Waye Khaleel kuma yanzu bata isa ta tunkare shiba sai bayan komai ya natsa, amma Ajiye mata biyu irin Salifa da fauzy Abun Alfaharin tane a matsayin surukai.
Zarah ce tace, “ai yanzu saidai abari komai yanatsa kafin Wannan maganar ta taso, kuma Karku manta yanada wata Matar fauzy kuma kinsan Y’ar waye. “Badamuwa nidai inzai Aure ni zan zauna da ko mata goma ne Salifa tafada, domin itafa kawai tasa rai.
“Oh Allah kasa mu zamo iyaye nagari ga ya’yan mu Amen.

Kwana ki natafiya Naziya yanzu tana gidan su duk kayanta dake gidan ankwashe har wainda bata moraba, tafara warware wa Amma kusan kullum cikin yiwa Ahmed Addu’a take da sadaka idan tasamu hali, har Azumi takeyi litinin da Al hamis domin Allah yakai ladan kabarin shi. Khaleel kuwa haryanzu bai dawo dai dai ba, fauzy tayi binshi har tagaji bai komawa kanta, ko fuskar shi bata gani. Yau yana kwance a katon falon mommy ta shigo ciki ita kanta ta rame, “Ibrahim, wai kai wane irin yaro ne, yazaka sawa yarinya ido tun kawo ta gidan ku bayan kasan akwai hakkin ta akan ka, kai bazakayi koyi da halin d’an uwan ka ba, Ahmed dina ba haka yake ba, idan har kaunar da kakewa d’an uwan ka gaskiya ne Kayi koyi da halin shi.
Dagowa yayi tareda cewa ” koyi nakeso inyi da Rayuwar da kika dora shi akai mommy, Ina ganin yadda yayi Rayuwa batareda Matar shiba, kuma kece kika sashi, ke kika hana yaya na ya sauke hakkin da ya dakko har yabar duniya, mommy kina tunanin Allah bazai tanbayi d’an uwana Wannan hakkin ba? Ta dalilin tsanar da kike yimata har tabar gidan nan bataji dadin rayuwa da mijinta ba why Mommy? Don haka itama Matar son taki tayi biyayya irin nata tagani.
Ibrahim banson rashin kunyar ka haka kaga Ahmed…. “Mommy enough, kidaina kwatance da yaya, ribar me yaci, kinga Amfanin Abinda duk yakeyi? See to avoid you and your wife, am going back to bangkok, zanje in kulada duk wani aiki da yayana yakeyi, bana ra’ayin zama anan, I don’t need her idan tagaji tasan hanyar gidan Uban ta.

“Ibrahim, zan hadaka da kawun ku inni bazakaji magana taba. Wucewa kawai yayi, dama so yake kawai ayi fourty days ya yi gaba Amma yanzu baijin zai iya Kara ko kwana daya a garin kano gwara yatafi ko zai dawo dai dai.
Duk gurmin da Akeyi Fauziya ta shigo tana kallo, yana wucewa a zuciye ta nufo mommy cikin kallon tsana da kece sanadi, tace Wallahi bantaba sanin Abinda kikayi zai shafi farin cikina ba dana taka miki burki, kuma zanje in shirya inbi mijina. Ta buga mugun tsaki, “Fauziya karfa ki manta ni uwar mijin ki ce kike fadamin maganar da kikaga dama. uwar miji uwata ce ko uwar ubana ce? I beg give me a break. Ta yi gaba zuwa dakin shi dake part d’in .

Yana hada kayan shi, tayi sallama yayi wurgi da Abinda ke hannun shi saboda haushin takurar ta, ya juyo cikeda haushi, “can’t you learn from Naziya, kintaba ganin tana bin yaya the way you are following me? Please have some shame.
“Oh baby yazaka hanani bin mijina, you are my husband Inada right akan ka, and ka daina hadani da Wannan village and stupid girl……. Wani irin kukan kura yayi a wuyan ta, tareda shake ta ya hada da gini idanun shi kamar na bakin kumurci, “what did you said? Cikin karaji, don’t repeat that again if not kin gama numfashi a duniya, I promise you, kin ce hakki ko kinada hakkina? gani ki diba in kinada karfi, hakkin na karfi ne kizo ki kwata, useless, now get lost. Ya saketa tareda hankada ta waje,

Da mugun kuka tafita falon Wanda mommy naji tayi Saurin tarar ta, Fauziya lafiya Me Khaleel din ya miki? karki tabani kuma wallahi sai na fadawa daddy na ke kikaja Wannan aikin da kike taka ma dashi sai kin barshi. Tafita tana kuka, hannu ta dora aka, kunga yaro zaimin salalar tsiya, Allah sarki Ahmed da kana nan kaine kadai mai iya takawa yaron nan birki, Allah ya jikan ka yaron kirki Allah yakai haske kabarin ka.
Ta share kwalla tabi bayan shi,
Lokacin yagama shirya jakar shi, kallon kayan tayi tareda zubamai ido, yanzu Khaleel bangama war warewa a rashin d’an uwanka ba zaka tafi kabarni bayan kasan banda kowa sai ku biyu kacal, yanzu shi yatafi kai kuma zaka tafi kabarni.

Baice mata komai ba yayi hanyar bathroom, fita tayi tana fitar da hawaye, wayar ta ta dakko tafara kiran number wayar kawun nasu, yana dauka tasa mai kuka tareda fadamai komai akan zaman shi da Fauziya, da kuma tafiyar da zaiyi. Yace mata Yana zuwa kawai ya katse kiran.
Bayan hour biyu kawun ya iso lokacin yaci Ado cikin manyan kaya Wanda rabon shi dasu tun kafin mutuwar yayan nashi,
Lekowa mai aiki tayi tace Ana kiran shi a falon, ya ce tace yana zuwa, fitowa yayi, yasamu mommy gwanin tausayi gefen kawu akasa yau tunda tana neman taimakon shi. Sallama yayi yagaida shi, zama yayi a kasa kanshi akasa, fuskar shi ba annuri ko kadan, kawu yayi gyaran murya yace “Khaleel tafiya zakayi batareda sani na ba? “Aa kawu yanzu ma gidan naku nake shirin zuwa infada maka.Toh Amma me zakaje yi kabar nauyin da yake wuyan ka anan, nafarko Matar ka, na biyu mahaifiyar ka na uku company, sannan wasiyar d’an uwan ka, ko bazaka cika mai burin shi bane, domin yafadamin tun ranar da zai rasu saboda rashin natsuwa banyi maganar da kowa ba, sai Malam, dago kanshi yayi domin jin wane magana akayi harda malam zai shiga ciki, “Ya bar maka Amanar Auren Naziya, kuma munyi magana da malam tunda zance ne na wasiyya ya Amince sai dai muyi Addu’a ta fita takaba lafiya sai a daura muku Aure da ita.

Wani irin zufa Kebin ta kowane kofa ta jikin shi, yakasa koda motsi baya iya koda daga yatsar hannun shi balle ta kafar shi,
Kukan mommy ne yasa yadawo hayyacin shi , wallahi bazai yuwu ba, yaza ayi yaya ya Aura ya mutu kanin shi ya Aura, kuma dole ne ni sai nayi Rayuwa da Wannan yarinya mai kamar mayya, nidai ban Amince ba gaskiya bada yawuna ba.
Kallon banza kawun yayi mata kafin yace ” ni nasan bazaki canja ba balkisu, kuma nasan ilimi yayi miki karanci da kin koma islamiyya, tunda bakisan Ibrahim zai iya Auren Naziya ba, kuma Ina so insani me yarinyar tayi miki, ko ince meye laifin ta? Ni tanada laifi A wurina kana ganin saboda soyayyar ta dana ya hadiyi zuciya ya mutu, banason ta kuma lashemin zuciyar Khaleel din da ya ragemin nidai bada yawuna ba.

“Yawun ki basuda Amfani a wurin mu don haka Khaleel gareka idan ka Amince kafin ka wuce kaje kaga malam Allah ya taimaka ya kuma tsareka, sannan zancen Matar ka Wannan kaidai ba jahili bane kasan hakkin Aure to don haka Kayi kokari Kayi Abinda ya dace ni natafi.
Yafada yana mikewa, tashi yayi jikin shi a sanyaye yabi kawun Saida ya shiga motar shi yadawo gidan, tana nan ta cika tayi tab. Kana jina Ibrahim, wallahi kar kasake inji kadawo min da Wannan yarinya mai farar kafa gida, karka sake ka Amince da Wannan Auren nafada maka.
Wucewa kawai yayi cikin dakin shi, ya datse key tareda zubewa akasa, wasu irin hawaye masu zafin gaske ne suka zubo mai, wainda baisamu yinsu ba tuntuni, Ashe maganar da Ahmed kullum yake fadamai zata kasance gaskiya, Wato akwai Abinda Allah ya boye shiyasa ya cusa mai muguwar soyayyar Naziya wadda bai taba yarda da itaba domin yasan is prohibited,
Yasha wahala yana kuma kan shan wahalar, zai iya rantsuwa da Al’qur ani yafi yayan shi son ta, Wanda baisan ya akayi soyayyar ta ta shiga zuciyar shi ba, how? when? Wani irin kuka yakeyi Am sorry yaya am sorry my brother da nasan zaka tafi kabarmin ita da na roki Allah ya cire min soyayyar ta ya barmin kai a rayuwa, Am sorry for loving your wife more than you brother, am sorry for feeling jealous idan kuna tare baka sani ba yaya, Inada kishin ta sosai yaya I use to cry behind door saboda zafin kishin ta, you are my brother but Ina kishin ganin ku tare, bansan ya akayi soyayyar ta ta shigeni ba, I love her more than the way you love her, I hate myself for that I swear to you, I control my feelings because of you.
You’re dead because of hidden destiny, hawayen shi ya share tareda hadiye kukan, “I will make her happy yaya zancika maka burin ka, zanbata farin ciki fiyeda yanda Kayi mafarkin bata, zansata dariya fiyeda yanda take dariya idan kuna tare. Mikewa yayi ya zari key din hadaddiyar motar shi tareda goge fuskar shi da kyau ya fita cikin hanzari a falon da yabar mommy a nan ya same ta tana waya tana fadawa y’an uwan ta bakin labari, Modu ya rantse sai ya cakuda jinin ta da talaka…….. . 🖊

 

“Comment share the free pages please and Wannan ne last free page ku biya ku karanta cigaban yanda zata kasance, ya za ayi da rayuwar Naziya shin zata Amince, shin zataso Khaleel, ya rayuwar su zata kasance da Fauziya, idan Naziya ta Amince da Auren Khaleel wace wainar mommy zata toya????? Muje zuwa yanzu za afara wasan this is just the beginning, let’s go my fans 💃, ga masu bukatar biya kofa a bude take chart me up 09011251444

 

*Matar Soja*
10/20/21, 7:33 AM – Fiddausi Yunus: 🌻🌻AUREN GADO🌻🌻

 

*Matar soja ce*

 

Daga marubuciyar
KUSKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK’ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA Y’AY’AN GATA
And now AUREN GADO,

 

Ga masu bukatar Wnn littafi ku turo kudin ku ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani hassan Fcmb ko katin wayar ku ta Wannan number 09011251444, sai kuma y’an 🇳🇪 Niger ku tuntubi Wannan number domin biyan naku, +225 0748153903, littafina Dari biyar ne kacal 500 sai najiku nagode,

Back to top button