Auren Gado 23-24
2⃣3⃣&2⃣4⃣
………….. A katon filin jirgin yafito yana Takawa daya bayan daya kamar wani prince, sheki yakeyi yana wani irin haske, idanun shi dauke da katon eye glass, baka ko ganin kwayar idanun shi, fuskar shi dif take ba Annuri yakara haiba da cika ido, watannin hudu sunyi matukar taimaka mai wajen warkar da damuwar rashin dan uwan shi kadan, driver ne tare da manager dinsu ya tareshi, gaisawa sukayi ya shiga motar suka zuba mai duk kayan da yazo dasu, suna tafiya yana discussing harkar business din su Wanda an samu cigaba sosai a cikin watannin fiyeda shekarun baya, domin shi mai zafine kuma baida sanyi kamar yayan shi, yana bin diddigin komai ma’aikatan sun san an samu canjin boss ba wasa, kuskure kadan yagani ko yaji tun yana China zaisa ayi firing mutum a aiki.
Kamar daga sama suna zaune dai dai itada mommy suna hira mommy na Kara lallashin ta tareda alkawarin komai zaiyi dai dai idan yadawo tunda yafara sauraran ta. Kawai sukaji sallamar shi sama sama, wani irin zabura sukayi duka tareda sakin baki, suna mai welcome, zama yayi kawai gefen mommy ya gaida ita tareda dan sakin fuska, domin uwa uwace koda kuwa abola take yawo, he missed her domin fushin da yakeyi da ita yasa tunda yaje baya kiranta baya son ko jin muryar ta sai in ita takirashi, he know she is wrong, kuma shima he is wrong, domin ba Wanda yabashi damar watsar da uwar shi, riko Hannun ta yayi tareda sakin murmushi, “mommy am back. I’m glad my son, ya harkokin ina ji a bakin manager komai na tafiya normal. “Yeah Alhamdulillah. Wani irin rawar kafa Fauziya keyi ta matso tareda zama gefen shi tadafa cinyoyin shi dake cikin blue jeans dinshi sabo dal, “Baby wannan irin surprise haka dama kafada, am happy wallahi. Ture hannun ta yayi tareda mikewa yace” OK bari inshiga ciki zanyi wanka in huta, mommy please am hungry. Jikin ta narawa tace bari in hada maka meal din ka just five minute,Ta wuce murna fal cikin ta, tarar shi Fauziya tayi tace “darling muje part din mu mana nan akwai takura ba sakewa”.
Mugun kallo ya watsa mata kafin cikin zafin rai yace “uban waye zai takuraki anan, now listing I know exactly what you are doing, ko ki dawo nan ko ki yi ta zama acan ke kadai, saboda bana ra’ayin zuwa wanna gidan if you are ready ga dakin ki can! Ya wuce abun shi.
“Kutumar uba wato dakin da Y’ar kauyen nan ta zauna yakeso ta dawo wallahi bazata dawo nan ba sai dai duk Abinda zai faru ya faru. Bin bayan shi tayi bayan ta gama dogon tunanin ta, lokacin harya tube ya daura towel, tuni taji wani irin feeling ya taso mata domin khaleel fa namiji ne complete ba algus ya ginu ya keru, wani fesar da zafin bakin ta tayi kafin ta matsa tana karairaya zata rungume shi.
Hannu yadaga mata “please, bana son disturbance, nagaji now get out.
Haba khaleel wane irin daukar Alhaki ne wannan? you’re my husband why All this?, ko bankai mace bane, Auren mu wata hudu Amma ace ko hug baka bani damar yiba. “Go and ask mommy idan ta Amince da hakan saiki dawo now out. Yafada yana wucewar shi bathroom. Fita tayi kawai rai abace taci karo da mommy, me yafaru kuma kinfito da bacin rai? “Ba dole ba, yaza’ayi ace wai sai na tanbayi izinin ki zan rungumi miji na? gaskiya kekam a bincike ki kina wa yayan ki asiri ne wane irin biyayya ce suke miki kike cutar dasu, so kikeyi nima inyi rayuwa irin ta Naziya? wallahi ko kina so ko bakyaso sai kinganni da cikin khaleel. “Haba Y’ar lelen mommy zo kiji, ke baki iya siyasa ba keda zaki caba ado ki makalewa mijin ki, ya zakice banason hada iri dake Fauziya, duk soyayyar da nake nuna miki haba ki rika ragamin mana. “Nidai kiyimai magana yadawo gefen mu Ina jiran shi. “Jeki zanturo shi kin ji. Ko sauraran ta batayi ba ta fice, saida ya dauki kusan minti talatin yana kwance tareda runtse idanun shi a cikin ruwan, shi kadai yasan tunanin zuciyar shi, wani irin murmushi yayi na gefen baki, kafin ya fito ya dauraye jikin shi, ya daura towel ya fito, mommy da ya gani zaune da Abincin shi tana jiran shi yasa yace “oh my mommy am coming tank you, I really miss your cooking.
“Oh son kayi kasa kaya kazo kaci. Kananan kaya yasaka kafin yadawo yazauna, akaron farko yafara bata labarin komai kafin yayi shiru, domin tuno da dan uwan shi da yayi, “I promise, Yaya zanyi duk Abinda kake burin yi kafin nawa. Shiru tayi tareda dafashi, “khaleel, mutuwar Ahmed gibi ne babba a rayuwa ta and all tanks to wannan Y’ar gidan talakawan, look son kaga idan Har na isa dakai kar inji ka yarda da Auren yarinyar nan, idan kana so ka ciremin kewar dan uwan ka kabi Abinda nakeso. kallon ta kawai yayi ya janyo Abincin shi yafara ci, bai kuma cewa komai ba har ya cika cikin shi fal ya kora da juice, “mommy zan kwanta domin nagaji sosai, later zamuyi magana.
Kallon dan rainin wayau tayi mai kafin ta kwashe kwanonin ta tafita, wato duk maganar ta bata bukatar Ansa, saida yaga ta fita yaja numfashi, “am sorry mommy she is my wife now! Auren mu ya dauru tundaga ranar da tafita takaba, don haka soon zata tare agidan nan.
Baccin shi ya shaka bayan ya rufe kofar saboda bai son damuwar Fauziya.
Tana can ta cika tab tana jiran mijin ta ga mommy ko zancen batayi mai ba saboda damuwar Auren Naziya yafi tsaya mata arai. Bai tashi ba sai la’asar yayi sallah ya shirya yafito domin yanada Abunyi, part din yayan shi ya leka yaga ba kayan salifa, wayar shi yaciro tareda kiran manager yabashi umarni, akan ya nemo mai best company na furniture’s a kano saboda he want to renovate the house, baya bukatar tsohon Abu a ciki, saida ya gama tsara komai ya fita daga gidan.
Tun fitar ta takaba ta murmure tayi tas da ita ba ruwan ta da komai fitama batayi dama kuma ita bamai yawo bace, tana cikin gida tana taya inna aiki ko tana chat a wtstp domin yana rage mata tunani da kewar Ahmed dinta, a kullum ta kalli yanda baya duniya Amma ya inganta rayuwar su Abin na mugun faranta mata zuciya, hatta da dakin su an saka musu gado da sabuwar katifa, dama basuda talaucin Abinci domin Malam ba mutum bane da ke zama, nema yakeyi iya karfin shi, a zaune take yanzu a karkashin bushiya itada shukrah suna hira sama sama tana chat, tana cikin adon ta cikin riga da sket na shadda orange sabuwa da Aunty Raliya ta dunka mata na fita takaba, dinkin yayi kyau sosai yayi cib a jikin ta, jikinta ba ko mayafi dankwalinta yadan zame kadan kana hango kwantacciyar sumar ta agaban goshin ta, yanzu Almajirai basa shigowa gidan saboda duk Anfitar dasu waje, suna sakewa sosai, Inna ce ta fito dauke da robar gyada mai bawo ta zauna itama a wurin, “Shukrah sa hannu mu bare gyadan nan da ita zamuyi sanwar dare, waccan inta dauki waya bata ji bata gani. Ajiye wayar tayi tana Dariya, “kai inna ai zan Ajiye tunda ga aiki, Amma inna me yasa bakya son a bare miki gyada a injin sai barar hannu? “Kyuiya ke damun ku yanzu” mu da Ina mukaga wainnan Abubuwan, ko nikan masara sai mu niketa a dutse, Yanzu aiku yan gayune, inkai gyada ta injin a farfashemin rabi yabi bawo. Sallamar da akayi ne yasa suka amsa tareda dagowa, Inna ta saki baki tareda cewa” maraba da mutanen ikko, mai sunan Malam kaine a gari?, dukan su sakin fuskar su sukayi, Shukrah ce tafara cewa ” Yaya Sadiq oyoyo kaine? Matashi ne kyakyawa ba laifi ya matso wurin da suke Shukrah ta Bashi wurin zama ya zauna ya gaida Inna tareda gaisawa da Naziya tareda yimata gaiduwar rasuwar mijinta, Sadiq Almajirin Malam ne da yazauna a gidan kusan tun yana yaro yataso hannun Inna kamar d’anta, har makaranta yayi a hannun su yanzu yana business a Lagos kuma Alhamdulillah ya samu Abun rufin Asirin shi, shima don har gida da motar hawa ya mallaka na kanshi, yanada rufin asiri dai dai gwargwado, hira sukeyi tsakanin su domin ya zama dan gida basa mai kallon bare infact matsayin Yaya suke kallon shi,
Sallamar da Malam yayi ne tareda kuma khaleel yasa Inna ta tashi saboda kunyar taga khaleel, Wanda Naziya bata lura ma da shi ba, dariya takeyi har dimple dinta na lotsawa, saboda sun saba da Sadiq sosai,, saida ya zo gab dasu ta shaki kamshin turaren shi, dago kanta tayi sukayi two eyes ido cikin ido tuni Annurin fuskar ta ya dauke kamar yanda nashi ya dauke dif, dama ba wani fara’a yakeyi ba, mikewa tayi kawai ta dauki robar gyadar tayi kitchen zama sukayi su uku a wurin Shukrah na gaida su ta wuce itama, fuskar shi tamke suka gaisa da Sadiq, Malam yafada mai koshi waye a wurin shi, “Ibrahim Mai suna na kamar su Naziya yake a wurina, yana kasuwanci a ikko yau ya shigo. “Sadiq wannam shine mijin Naziya na yanzu”. Saurin kallon Khaleel yayi domin yana ganin shi yasan wani ne kuma ya tara ko kuma dan wani, wani iri yaji yace “Malam andaura ne? “Eh kamar yanda nafada maka rasuwar mijinta wannan dan uwan shine. Shiru yayi kawai shi yasan Abinda ke ranshi, fuskar khaleel a tamke yace “Malam zan iya ganin ta? “Bismillah ai gidanku ne ga dakin ta can kuje kuyi magana. Yafada tareda juyawa suna magana da Sadiq, “yanzu dai baka komawa sai ka kawomin Matar Auren ka Sadiq tunda dai kasamu rufin Asiri Bana son zaman magidanci ba iyali. “Insha Allahu Malam” kafin intafi zan nema.
Wucewa khaleel yayi hannun shi sanye cikin pocket din manyan kayan nashi, shadda ce fara Y’ar gaske, tayi matukar haska shi, dama ga iya wanka,
Zaune take tana cewa Shukrah” shi kuma wannan daga Ina? kalla yanda ya fadowa mutane cikin gida. “Kai Aunty bakya ganin tare yakeda Malam kuma karki manta kin kusa zama Matar shi tunda ki ka ganshi yanzu, ni Ina tunanin ma kamar baya garine tun zuwan dayayi bai kuma zuwa ba sai yau. “I don’t care da yazo da kar yazo kinsan da Allah zai taimakeni Malam ya fasa zancen Auren nan da nafi kowa farin ciki. “You are too late. Yafada bayan ya daga labulen dakin nasu ya shigo, saurin tashi Shukrah tayi, ya kalleta” sister excuse us please. Yafada yana murmushi kadan, tace “tom” da sauri ta fice, karasa shigowa yayi, taji kamar ta zura da gudu, juyawa tayi tareda daukar katon hijabin ta ta zura. “Hmmm. Kallon dakin yayi dakyau yaganshi fes yana kamshin turaren wuta ba wani tarkace daga gadon su sai Karamar waldrp da akwatunan su sai mirror dake dauke da kayan kwalliyar su.
Matsawa yayi gaban mirror batareda yace mata komai ba, ya dauki turare daya ya kalla ya Ajiye. Kallo take binshi dashi kawai domin rainin wayan shi yawa ne dashi, kuma so take taji ya karasa maganar daya faro tun farkon shigowar shi. Ganin baida niyyar cewa komai gashi haibar shi duk ta cika mata daki, duk taji she is not comfortable at all. “Malam ka taimaka ka fadawa Malam baka ra’ayin Aure na, domin ni bana ra’ayin Aure yanzu, musamman dakai. “Sai da wancan kazamin ko da kike wa dariya kamar wawuya right? Yafada yana juyowa tareda matsowa kusa da ita. “Nidai koma meye ni bazan Aureka ba”. Hmm Ashe igiyar Auren a hannun ki zata zauna idan an daura? dago kanta tayi tareda kallon cikin idanun shi domin fadamai magana, “wane irin cin Amana ne zaisa ka Amince da Auren Matar yayan ka, kuma bayan kasan ba kaunar juna mukeyi ba? That’s your opinion not mine! and listing, Aure an daura shi tun daga ranar da kika fita takaba, don haka ko kiso ko kar kiso you’re under me, kina karkashin inuwar Aure na, sannan kina maganar cin Amana ko what ever, ai kece mai cin Amana har kin manta da Yaya na kin fara sakewa wani banza fuska kina dariya, listing to me, am not like my brother ni ba zakiyi min Abinda kikaga dama ba, wannan rayuwar da kikayi a baya ki gogeta this is Ibrahim khaleel, you better change your way, be a responsible house wife, if not bazakiji dadi naba.
Wani irin zafi zuciyar ta ke mata yanzu ji take da tana da karfi shakeshi zatayi har sai ya daina numfashi domin irin maganar dayake fada mata a sulale.
“Malam idan kana tunanin Naziyar daka sani ce a baya you are mistaken, inada nawa tsatstsauran ra’ayin idan naso, don haka karkayi mafarkin zanyi irin rayuwar da nayi da Ahmed a gidan ku, naso Ahmed shiyasa na jure wulakanci kuma kai kasani ba zaman dadi a rayuwar da baso sai tsana a cikin ta. “Hmm that means you hate me? “We hate each other. Tafada tana murguda baki, “ni bazanyi zaman Aure dakai ba. “OK naji kuma duk na haddace and lokaci ne zai fada mana komai, Malam ya tanbayeni yaushe zandauke ki da nace end of the month, yanzu nafasa so nake kitare a gidana domin inga ra’ayin waye zaiyi tasiri. “Nidai bazanje ba don Allah ni ka sakeni kafada musu kafasa. Har ya juya zaifita kalmar saki tasa ya juyo, tareda Kara tamke fuska, ” in your dream. “Ni bazan zauna da wata kishiya ba ai Kanada mata, ni kuma bazan zauna da namiji mai mata ba, Tafada ne kawai badon Abinda ke ranta kenan ba sai don ta rasa wane irin excuse zata kawo mai.
“get ready domin zama zakiyi da kishiyoyi ba kishiya ba, and saboda careless baki kosan bana gari ba, anyway am back tsarabar ki sai kin tare, bye. Ya fice cikin hanzari, tabishi da kallon mamaki, duk zafin nan da take ganin yanada shi bai nuna mata ba, wai da gaske an daura mata Aure dashi? Ya bata sani ba? Shukrah ce ta shigo tace “Aunty da gaske fa Malam ya daura muku Aure da khaleel ya sadiq kefada min yanzu. Zama tayi kawai tareda dafe kanta, ta Ina zata fara zama dashi, wace irin rayuwa zasuyi, yazata zauna da Ahmed yanzu shima ta zauna dashi?
“Aunty nidai karki sa tunani kiyi Addu’a Allah yasa kiji dadin Auren nan fiyeda na farko. “Hmm Shukrah, bakisan halin shi bane, ni bazan taba sonshiba. “Aunty kin sani fa bakyau kaki mutum da yawa in zaki so mutum kiso shi don Allah haka in zaki k’i shi ki k’i shi don Allah.
Bansan wane irin zama kukayi da Yaya Ahmed ba Amma ki kyautata zatonki kisawa zuciyar ki hakuri zakiyi farin ciki. Shiru tayi tareda mikewa ta fito domin tana bukatar Amsa wurin inna..
Zama tayi a kitchen din tareda daukar Alayyaho tana gyarawa “Inna yaushe aka daura min Aure ban sani ba? Dago kai Inna tayi tace “kije ki tanbayi Malam ai kin San baya magana biyu, don haka karki manta da furucina, kuma kar inji musu ko jayayya akan zancen nan, kinji nafada miki kiyi ki yanka kitashi ki tuka tuwon nan ya dahu. Ta fada tana fita tabarta, wasu hawaye ta share masu zafi tareda ci gaba da aikinta, tayi Alkawari koma meye zai faru atsakaninta da shi ne zaiyi daya sanin Amince wa Auren ta.
Sai dare ya koma gidan su domin bai bar gidan Malam ba sai bayan magrib daga nan yayi gidan kawu, suka tattauna kafin yayi isha’i yadawo gida.
Lokacin Fauziya na zaune a falon cikin gida tana jiran taga inda zai bullo, mommy tuni ta shige domin batason rigimar ta, tsawon rana tana korafin yaki komawa gefen su, shigowa yayi da sallama, “me kikeyi a falo ke kadai Ina mommy? ” ta kwanta, Ina kafito inata nemanka a waya baka picking? Tsayawa yayi tareda kallon ta ” yaushe wannan yafara a tsakanin mu dake? Aike na ki kayi ? OK naje wurin Amaryata ne. “Wace irin Amarya, khaleel Aure zaka Kara? “Don’t act like you don’t know about it,” salifa ka Auro min again ko wata ka samu? Wadda bakyaso ki fada dai itace kuma ba Aure nake nema ba Aure an riga an daura in kina lissafi daga ranar da zata fita takaba daga ranar ni mijinta ne, don haka next week zata tare nan gidan.
Wani irin ihu ta buga tareda zubewa ta zabga Ashar ” kutumar ubancan ni zaka wulakanta duk halaccin da nayi maka sakamako na kenan kishiya da wannan yarinyar, Wayyo ka cuceni wallahi bazan hada miji da wannan ba. “Toh sai ki bar mata dama itama bata ra’ayin kishiyar kuma in zabe za ayi kinsan bazan zabe ki in barta ba, saboda Amanar Yaya na ce, zanyi komai domin in kulada Amanar shi.
“Wallahi Khaleel baka isaba Indai nono na kasha saika saketa” Aure aka daura muku bada yawuna ba, lallai Modu ya kai karshen mugu kuma munafuki, na fada maka bana son hada iri da talaka bazaka gurbata min zuri’a ba, kuma zanyi fito na fito da duk munafukin da keda hannu a cikin hadin Auren nan , sun samu nasarar lashe min kurwar yaro na babba kaima sun fara galaba akan ka, ai dole akuma likamaka tunda anga daula ba’aso abarta wallahi khaleel zakusan koni wacece muzuba nidaku da duk Wani dangin ubanka. Wucewa yayi kawai daki domin maganar ta isheshi kuma baida Abunyi akai Aure dai an daura ba fashi shi yasa yace kar kawu yafada mata,
Kwana sukayi da fauziya basu runtsa ba, zata iya Yarda asiri akewa dan ta shi yasa suka samo kanshi inba hakaba me zaiyi da ita………. 🖊
*Matar Soja*