Adandi 14
14
Kallonta Mamy takeyi cikin tsananin mamaki da tsoro tace “au cewa yayi keba Varging bace to ubansa ne ya budamin ke da zaice keba Varging bace kinga Samha ki rufawa kanki asiri kifita daga sabgar taqadirin yaron nan idanma bazaki auri Na’im ba to kibawa malaminki dama yazo kigani idan yayi miki mana ki manta dashi nifa banga ribar son abinda baya sonka ba” tana gama fada mata haka ta miqe ta fice ita kuma taci gaba da kukanta sai dare sannan ta fitar parlourn Dad dinta ta tarar zaune yana aiki a system dinsa ta zauna kusa dashi ta dora kanta a kafadarsa tace “Dad ko missing dina ma bakace kayi ba”
Murmushi yayi ya tallafo fuskarta yayi kissing kuncinta yace “nayi missing dinki sosai daughter love amma kece naga kamar bakiyi murna da dawowa garemu ba jiya naje Katsina naga yan’uwanki Yarima Farooq yanata tambayarki nace kina mkranta shine yace idan ya dawo daga Rasha zasuzo da Mainah Abdu tunda shima ya gama project din daya kaishi Kano ne ko Kaduna tsakanin B.U.K da A.B.U dai yake kinsan dake jami’in leqen asiri ne na qasar England amma yana musu aiki anan yafi yi musu aiki a makarantu cikin dalubai yakan samu department din da yakeso yayi register dasu ya shiga a matsayin dalubi ke har bautar qasa yasha zuwa States da dama na qasar nan duk a cikin aikinsa ne hakan shine yake bashi damar yin bincikensa cikin sauqi babu mesa masa ido bashi da yarda ko kadan kuma bashi da sauqi yanada zafi sosai Mainah Abdu dan rikici ne na qarshe da yana kirana daga baya kuma ya zubar da wayoyinsa amma na karbo number sa so shi wayarma ba dagawa yakeba saboda tsabar rashin yarda dakai Samhatu zan hadaki dai da yan’uwanki kuyi zumunci na lura suna sonki musamman Yasmin da duk zuwan da zanyi sai ta tambayeni kw har hotunanta tabani tace na kawo miki kuna kama sosai saidai ita farinmu tayo su dukkansu fararene zubin fulanin katsina mallawa kema kina yanayi dasu sosai fatarki ce dai ba irin tasu ba”
Lagwabar dakai tayi tace “ni nagaji da wannan lbrn da kake bani kullum Dad ka kasa kaini Katsina ni banma san hanyarta ba gashi har ana shirin turamu service Imo State” shafa kanta yayi yace “karki bata ranki zan kaiki kiga yan’uwanki sunada yawa Daughter wadannan da nake baki lbr dai sune shaqiqanki da babansu dani Babarmu daya babanmu daya” turo baki gaba tayi tace “ni bazanma ce ba tunda baka nunamin suba tun Ina qarama sai yanzu da kake shirin auraddani” dariya yayi sosai yace “yawwa dama wannan sakaran yaron Na’im yaxo da mgnr aurenku nace masa sai kin gama bautar qasa yace ya fasa aurenki saboda haka ki fitar da mijinki da kanki” rungumeshi tayi tana dariya shima dariyar yayi ta tashi ta shige kitchen ta dauko abinci ta zauna gaban Dad din nata tanaci tana bashi a baki itadai Mamy tana zaune tana kallonsu tana dariya tace “wlh Dad saika tashi tsaye akan Samha lamarin yaron nan data qwallafa rai akansa yana neman zautata” murmushi yayi ya lakace mata hanci yace “so abinki Yata ya cancanci asoshi na Allah dai yasa rabonki kine….” Dagowa tayi da sauri ta kalli Dad din kawai sai hawaye ya balle mata cikin damuwa ya janyota yana share mata hawayen yace “kici gaba da hqr zakiyi nasara my daughter hqr mabudin rabone kinji” daga masa kai tayi ta miqe ta shige dakinta ta kulle ya dube Hajiya Lubabatu yace “kinada matsala Hajiya na fada miki baa qwacewa yaro garma ki sakar mata da kanta idan ta sheqa taji babu qwaye zata zubar”
Haka kwanaki sukayita shudewa watansu biyu a gda cikin watannin Dr Mus’ab yazo Abuja yakai sau biyar tun tana zulle masa hardai ta rungumeshi hannu biyu saboda itama zuwa yanzun auren takeso da gaske shine yake cire mata kewar Abdul saboda yasan duk ta yanda zaiyi yabawa fulawarsa ruwa sosai.
Tunda kuwa yaga ta sake jiki dashi ya fara bijiro mata da mgnr aure yauma suna zaune a garden din gdan nasu cike da kulawa ya dago ya kalleta tayi murmushi tace “Sir yada kallone?” Ajiyar zuciya yayi yace “inajin tsoron wani ya kwacemin kene My love don Allah ki bani dama na turo magabatana asan dani a gdanku idan da halima a banike in yaso a tsayar da lkcn aurenmu zuwa lkcn da zaku gama bautar qasa in yaso sai ayi biki abani matata my love kada kicemin a’a don Allah wlh Ina buqatar aure shekaruna sun fara nauyi 37 year’s ba aure haba Samha a tausaya mini mana kinga fa kema kina buqatar auren nan nasan dai kinfi 20 year’s yanzu ko?”
Tunda ya fara mgnr idanunta suka ciko da qwallah inama ace Abdullah ne ke roqonta haka da taji dadi zamewa yayi daga kujerar da yake kai yace “don girman Allah kiyi hqr My love wlh bansan kalamaina zasu bata miki raiba da bazan fara ba nayi miki alqawarin bazan qara maki wannan mgnr ba harsai sanda kika buqata don kanki…”
Rufe masa baki tayi tana girgiza masa kai tace “ba kalamanka ne suka batamin raiba hasali ma dadi naji na sani kuma na yarda kaidin masoyinane na haqiqa wanda nakeda yaqinin bazan taba danasanin rayuwar aure dashi ba na baka dama Sir na baka dama ka turo….” wani ihun murna ya saki yace “oh gud! Na gde my love naji dadi sosai insha Allahu zanyi miki adalci kuma zanci gaba da sonki har abada” janye hanunta tayi daga nasa ta miqe ta nufi cikin gdan da gudu tanaji yana kiranta amma taqi tsayawa murmushi yayi yanajin qaunarta na nunkuwa a zuciyarsa miqewa yayi ya fita ya samu taxi ta kaishi airport ya hau jirgi domin sanarwa da iyayensa kyakkyawan labarin.
Tana shiga ta fada gadonta ta fashe da sabon kuka shikenan yanzu ta tabbata ta rasa Abdul dinta? Mamy ce ta shigo ta zauna tana shafa gashinta cikin lallashi tace “meye yake damunki ne pretty?” Cikin kuka tace “Mamy na bawa Dr Mus’ab damar turo magabatansa yanzu shikenan na rasa Abdul Mamy shikenan na tabbata mallakin wani bashi ba” murmushin farin ciki Mamy tayi tace “nidai Ina tunanin shegen yaronnan asiri yayi miki Samha to wlh ki kiyayeni kinji na fada miki yaron kirki irin Mus’ab gashi babanshi me kudi ne ke nifa banason kaiki inda zaki wahala ke baki hutaba nima ban hutaba nafiso a fitar dake gdan arziqi akaiki gdan arziqi Mus’ab shine ya dace dake wanda yake sonki saboda Allah yo wancan wawan yaron idan kika kuskura kika aureshi ai kinshiga uku don ko ya sameki Varging yana tande zakin zaiyi jifa da kwalin tunda bake yakeso ba budurcinki yakeso shashasha dake da bakisan me sonki ba”
Tashi Mamy tayi ta fice daidai lkcn da wayarta tayi ring Dr Mus’ab ne yake fada mata yanzu zai hau jirgi sukayi sallama Kiran da akayi mata ta rinqa dubawa biyu na Rahmah ne uku na Abdul na Rahmah tabi saboda tana ganin kamar zaifi muhimmanci a gurinta nashi bai wucce gaisuwa ba da qaryar yana kewarta tana dagawa tace “wai Samha me yake faruwane?” Cikin rashin fahimta tace “game dame ba?” Sake katseta tayi da cewa “yanzu Dr Mus’ab ya kirani yake fadamin nayi masa gdy a bisa matsayin da kika bashi wanne matsayi ne?”
Ajiyar zuciya tayi tace “nabashi dama ya turo magabatansa gdanmu ayi mgnr aurena dashi ne kawai” hamdala Rahmah tayi tace “amma naji dadi sosai gsky ki godewa Allah Samha Mus’ab yana sonki sosai kuma zakiji dadin rayuwa dashi” hawaye ta share tace “inata qoqarin cusawa zuciyata soyayyarsa amma na kasa” rarrashin ta Rams tashiga yi tana bata kalamai masu kwantar da hankali nan take fada mata cewa ranar juma’a ana nemansu a makaranta zasu karbi posting latter su tace “nayi farin ciki da aka hadamu guri daya Samha” haka sukaci gaba da hirarsu bawai don tanajin dadin hirar ba saidon ragewa kanta tunani da damuwa sannan sukayi sallama tana sauke wayar a kunnenta wani Kiran ya shigo My Abdul tagani a saman wayar yana yawo tayi kamar bazata dagaba saidai wata zuciyar ta umarceta da dagawa ta kara a kunnenta tare dayin sallama ajiyar zuciya ya sauke tare da amsa Mata yace “laifin me nayi da kikaqi dagamin waya My Samha?” Cikin raunin murya tace “wataran dole zanbar iyayena da yan’uwana da qawayena na koma qarqashin mulki wani shiyasa na fara qoqarin sabarwa da kaina rayuwar kadaici” duk yanda yaso ya fahimci kalaman nata ya kasa dole ya nemi qarin bayani ta hanyar cewa ban fahimci abinda kikeso kicemin ba Samha” ajiyar zuciya tayi ta sake matse teddy bear din dake hanunta tace “ina nufin yau ta kasance rana ta musamman a rayuwata saboda yaune na bawa wani da namiji damar shigowa rayuwata ta hanyar qulla relationship na aure wanda ya kasance bakai bane Abdul nabawa Dr Mus’ab damar aurena….”
Cikin wata rikitacciyar murya yace “ya isa haka Samha banason jin wadannan munanan kalaman naki da suke neman tarwatsamin zuciya” harga Allah taji babu dadi amma data tuna irin wulaqancin daya rinqayi mata tsayin shekaru yana jizgata sai kawai ta share taci gaba da harkokonta zuciyarta cunkushe da damuwa.
Kwana biyu tsakani iyayen Mus’ab sukazo suka nema masa aurenta Dad yaji dadi kuma yasawa abin albarka suka tsayar da lkcn aurensu wata bakwai shima saboda service din da zasu tafi da bazaisa samada wata biyu ba wai ranar Dr Mus’ab kamar ya goyata saboda farin ciki yana wani marairaice mata waishi babu don babu yanda zaiyi ne amma lkcn yayi masa tsayi tayi dariya cike da tausayinsa tace “saurin me kakeyi Yallabai abinda baasa masa lkc bama zuwa yake ya wucce balle wanda aka sanyawa lkc tasha fama dashi kafin ya qyaleta ta kwanta da sharadin gobe shine zaizo ya taho da ita gurin Indection din.
Da asuba wayarsa ce ta tasheta ta daga ta kara a kunnenta tayi sallama ya sauke wata ajiyar zuciya yace “Wayyoh My love wannan sexy voice din take sumar dani zatayi” murmushi tayi tace “bancika son tsokana bafa” yayi dariya yace “babu tsokana gsky ce Allah my love duk lkcn dana ganki sai naji yanayina ya sauya dalilin da yasa na taba kiranki nayi miki nasiha akan ki rinqa suturtamin jikinki amma kika rufe idonki kika cinyemin mutunci tsaf” dariya tayi tace “kayy Sir nice na cinye maka mutuncin inama na ganshi balle na cinyeshi?” Dariya sukayi sosai yace “bazaki gane ba sai ranar da kika jiki a qasana Ina sukuwa a kanki sannan zaki fahimci inda nake Samha inasonki aduk yanda kike” duk sanda ya furta mata kalmar nan sai jikinta yayi sanyi tausayinsa da tausayin kanta abinda wanda takeso ya kasa yi mata a kenan sadaukarwar da Abdul ya kasa yimata a rayuwa kenan gata Dr Mus’ab yayi mata yana sonta a duk yanda take kalmarsa kenan kullum.
Wasu hawaye ne suka zubo mata tace “yaushe zaka taho?” Ya fahimci damuwa a muryarta don haka ya saisaita murya yace “yanzu wanka kawai zanyi na taho amma naji damuwa a muryarki meye ya kawota cikin rayuwar matata?” Ajiyar zuciya tayi tace “soyayyarka gareni itace take sanyayamin jiki da kuma bani mamaki ka tayani da addu’a Allah yasa nasoka kamar yanda kake sona Sir” numfashi ya sauke yace “ta daina baki mamaki kinji my wife ganinan zuwa yanzu ki tanadarmin breakfast dakanki nakeso kiyimin saboda ki fara samun ladan aure tun yanzu” murmushi tayi tace “angama ranka ya dade” sukayi dariya tare da ajiye wayoyin a tare…….
. *UMMUH HAIRAN CE…* ✍
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*
*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*