Auren Gado Hausa NovelHausa Novels

Auren Gado 61-62

Sponsored Links

 

 

…………….Bai fada mata komai ba akansu kawai gyada mata kai yayi, sukaci gaba da magana kasa kasa, tana tanbayar shi me yasa yake son takurawa Naziya, “khaleel kabi yarinyar nan a hankali karka kure mata hakuri fa. “Momy so kike ki shagwaba ta inkina fadar irin haka please karki fada Agabanta taji, nifa ba Abinda nayi mata impact ita yakamata kiyiwa fada tana juyani y’an da takeso. Yafada yana d’an daure fuskar shi, murmushi MOMY tayi na farin ciki da kwanciyar hankali ta dafashi da hannu mai lafiya. ” kasan bazan bari kasa min ita kukaba, wannan yarinyar farin ciki yakamata tayi ba kuka ba, khaleel kataba ganin ta daga kai tamun koda kallon banza, duk da Abubuwan da na rika yimata? Ka duba yarinyar nan iya zuciyar ta ta tsaya jinyata batareda ta duba duk cin mutuncin da nayi mata ba a rayuwa. Takarasa wasu hawaye na nadama na biyo kuncin ta, “duba kagani mahaifin ta batareda ya duba duk halin da na jefa Y’ar suba ya kuma daukar ta yabaka, saboda karfin Alkwari da soyayyar da sukeyi wa d’an uwan ka, yau maganar da nakeyi Albarkin Naziya nakeyin ta, da bata cikin rayuwata nasan wulakanta zanyi khaleel Hajiya sharefa tayi mun Abinda bantaba zaton kawa zata iya yiwa kawarta ba,All I want zumunci tsakanin mu ya Kara karfi Ashe…. Hmmm Salifa kuma..
Takarasa kalmar kuka na kufce mata. Tashi yayi ya rungume ta ” is OK Momy please komai ya wuce ki manta dasu, kuma nima ki yafemin da na bijire miki kuma natafi na barki.
“Aa bakayi laifi ba khaleel hakan shine ya kubutar min da Rayuwar ka da lafiyar ka nagode da baka Yar da ka hada Rayuwar ka data Salifa ba, danayi danasani na har abada da hakan ya faru domin sam batada tarbiya. “Please Momy ki kwanta ki huta ya isa haka. Yafada yana gyara mata kwanciya ya rufeta tareda komawa kan kujera ya zauna, dafa fuskar shi yayi yana shafawa tareda kallon gefen Naziya dake juyi duk tanajin hirar su takasa bacci saboda farin cikin canji da saukin momy.
Ya dauki lokaci kafin ya ja numfashi ya mike ya koma inda take kwance, gefenta ya rab’a tayi dif kamar tana bacci ya kwanta yana kallon saman dakin na tsawon lokaci kafin ya juya ya rungume ta tsam yana Ajiyar zuciya.
Kai khaleel maye ne wallahi tafada a zuciyar ta, wato koda da idon momy dai sai yayi y’an da yakeso, bakin shi ya Dora dai dai kunnen ta cikin rage murya sosai yace “I no you are not sleeping Hajiya, are you happy momy na takamin birki akanki, Hmm duk wayan Amarya dai sai ansha manta don haka ki gama gudun ki zamu hadu. d’an motsawa tayi domin gadon karami ne Wanda ta zungureshi badon taso ba ya Kara manneta yana runtse idanun shi, “kinsan dai baki kyauta min ba ko? This is the worst punishment for me, gaskiya ina kwaruwa Umm.
Shiru tayi mai Saida taji hannun shi ta saman rigar ta yana kokarin zurawa tayi saurin juyowa domin bashi gargadi da ido, yayi saurin cafke lips dinta, yana kallon kwayar idanun ta, tareda juya mata ido Alamar tayi mai shiru. Ya dade yana shan bakinta kamar mayun wacin Zaki tana kallon tsantsar jaraba kafin ya cire ya dora bakinshi saman wuyan ta yana lasa tareda mayarda numfashi nadan lokaci. Tashi yayi ganin hakan bazai taba yimai ba ya dagata tareda cewa ” let go. batason hayaniyar su dashi a gaban momy don haka tabishi tana mai gyara mayafin rigarta, ta dauki wayarta tana dubawa kusan karfe daya na dare.
Cikin Asibitin shiru sai hasken wuta ta ko ina ya bude motar shi ya zaunar da ita kafin ya shiga ya rufe ruf, fuskantar ta yayi tareda janyota zuwa kafar shi ya dora kanshi saman kirjin ta yana Ajiyar zuciya.

Related Articles

Ganin bazai ce komai ba tace” please meye haka wai? Idanun shi da sukayi ja ya dago tareda kallon ta na d’an lokaci kafin ya sanya hannu ya kwantar da kujerar motar yace ” keep quit my friend, tunda bakisan damuwa ta ba Allow me to sleep OK. Kwanto da ita yayi kan kirjin shi ya rufe idanun shi Alamar baccin zaiyi da gaske. Kafin kace me yayi bacci ta tsaya tareda sauraran Ajiyar zuciyar shi a natse,. Mamaki ya bata batareda ya tabata ba yasha baccin shi har Asuba, Wanda momy ma batasan fitarsu ba tasamu bacci mai cikeda kwanciyar hankali da kuma saukin da taji a jikin ta,
Ganin Ana kiran salla ga jikinta yayi ciwo domin ya kanan nad’eta ya hanata motsi sam, ta d’an bubbuga shi, ya bude idanun shi, baccin bai ishe shiba tace “Ana kiran salla fa. Mika yayi tareda ita a jikinshi yayi salati tareda karanto Addu’ar tashi daga bacci. “You see is All your foult jiya bansamu bacci ba yau ma bai isheni ba saboda rashin jinki da munje gida nasan zanyi bacci mai dadi.
Batace mai komai ba tafara kokarin sauka a jikin shi, riketa yayi ” wai ke meke faruwa ne? Kin zama kurma ne da kike bina da idanu ba magana, ko fushin ne da bansan laifina ba haryanzu? “Muje muyi sallah mutane sunfara fitowa. Sakinta yayi saboda lokacin sallah suka koma dakin, har lokacin momy bata tashi ba sabon brush ta bude tayi kafin tayi alwala ta fito. Tasamu baya ciki, domin dole sai yaje gida he can’t pray batareda yayi wanka ba domin yasan ya fitarda Abubuwa duk da bai samu Abinda yake soba.
Sallah tayi ta zauna akan dadduma tayi ta Azkar dinta har gari yayi haske.
Likita yayi matukar mamakin saukin jikin momy lokacin da ya shigo, yace is a miracle a dare daya ansamu improvement sosai domin duk nauyin jikinta ya sauka saura gefe dayan kawai Wanda yace a hankali shima zai warke idan taci gaba da shan magani. Tayi godiya da kanta.
Karfe takwas Aunty Raliya ta kuma zuwa da basket din Abinci ta ga Naziya da momy suna hira sama sama ta rashin sabo domin Naziya kunyar momy takeji ita kuma so take tajata a jiki sosai.

Abun ya matukar farantawa Aunty Raliya rai, ta ko saki jiki da momy sukasha hirar su tanata godiya da sa Albarka, ta sake ta d’an ci Abincin da Raliya ta kawo,zuwa karfe goma Tace zata tafi sai ta kuma dawowa, Naziya ta mike tace zataje tayi wanka ta canja tadawo ta Kira nurse tareda bata umarnin ta kula da momyn kafin tadawo, suka fita tare, momy taso tace ta Kira khaleel mana ya kaita Amma batason ta kuma yi musu katsalandan a rayuwar Auren su tasan komai zai tafi dai dai, Allah dai yabata lafiya.

Saida suka fita aunty Raliya tafara yimata fada, meyasa zata ce zata bita? “Aunty ai yasan zan bukaci wankan yatafi batareda niba don haka bazanje gidan ba nidai muje gidanki, ai kayana da na dawo suna can. Shiru tayi kawai kanin mijinta da yakawota ya mayarda su, koda ta tafi tayi wanka ta shirya ta natsu ta karya. bata samu bacci mai dadi ba jiya saboda nacin khaleel don haka Saida ta kwanta na kusan hour biyu.

Khaleel kuwa bayan ya shirya Saida yaje office dinshi yaga meke tafiya domin baisamu sukunin lekawa ba ya d’an dauki lokaci kafin ya dawo Asibitin, Samun momy yayi da Aunty Zarah da tadawo jiya ta samu labari a wurin Aunty Raliya domin duk ta damu bata samun wayar momyn Kwana biyu, fuskar shi ya tamke ya shigo kamar yaga kashi don Allah yagani ya tsani Matar nan shiyasa ya mugun raina ta, hawaye takeyi tana Sannu aunty Allah ya wulakanta sharefa da zuri’ar ta matsiyata. Sallama yayi ciki ciki ya samu gefe daya ya zauna ta juyo cikin fada ” khaleel Amma wallahi kai bakada kishin mahaifiyar ka, yaza ayi ace Suyi ma Aunty irin wannan Abun Amma ka zuba ido ka kyale su?

“Zarah kije ke kidauki mataki da kanki dama kece mai babban kaso a duk Abinda yake faruwa a rayuwar gidan mu, don haka karki manta inkin tashi yimusu hukunci ki hada da kanki kema kina bukatar hukuncin.

“Kingani ko Aunty wallahi Ibrahim ya mugun raina ni sai kace ba kanwar uwar ka nake ba kayita zuba min magan ganu son ranka, wallahi zandauki mataki akanka mtsww. “Hope dai badani kike wannan zancen ba da kuma tsakin, domin Zaki iya fuskantar bacin raina fiyeda tunanin ki, girma na kikayi ko kece kika haifeni da zanbaki girma? Look we don’t need you here just leave, go and fix your life first, don munafunci ina kike lokacin da ita yayar taki ke bukatar taimako? Were are you? Sai bayan ta samu sauki ki debo dogayen kafafunki kizo kina kawo mana sanabe were are all your relatives, sai lokacin da munafunci ya tashi ku cikawa mutane gida, look am not like Ahmed duk wadda tasan ba zumunci zai kawota gidan muba she is not welcome, kowace ta tsaya gidan tsohon mijinta, especially you Amara.

Tuni Aunty Zarah ta hadiye bala’in ta ganin ya hau yana faman surfa mata that means ajiraye yake da ita, momy ce tace ” khaleel that enough OK. Yace “Sorry Momy were is that girl? “Taje ta yi wanka ta canja tadawo. Dama yasan zatayi hakan wato bazata iya fada mai Abinda take bukata ba sai kawai Tayi Abunda taga dama don taga yana sonta yana lallaba ta, OK zai nuna mata koda yana son mace kuma baya daukar wulakancin ta why take mai yawo da igiyar Aure any how? Haushin ta ne ya saukewa Zarah tass tun ma baiji meya faru ba.
Komawa yayi kan kujera yana Danna wayar shi fuskar shi kamar hadari, momy ta kalle shi tace ” khaleel bansan me ke ranka ba, Amma na rokeka haukar da kamun yanzu ta iso kar yarinyar nan tadawo ka rufemin ita dafada.
Shiru kawai yayi domin yakai wuya, zarah kuwa mamaki take ciwon ne ya janyo momy har take damuwa da Naziya haka?
Kallon ta Tayi tareda yin murmushi kawai. Domin ta Riga tadawo hanya sambal bata fatan ta kuma karkacewa,

Aunty Raliya tasa aka dawo da ita bayan ta tashi ta shirya cikin kana nan kayanta ta zura katon hijab saboda shigar domin duk native wears dinta na gidan khaleel, harda socks ta sa baki,
Bayan ta zura after dress a sama saboda koda zata bukaci cire hijabin a Asibiti,
Wata irin uwar kasala takeji da tashin zuciya, da batasan dalilin shiba don haka duk sai jikinta ya mugun mutuwa, koda ta shigo cikin Asibitin zuciyar ta tashi takeyi sosai musamman kamshin pharmacy dake tashi a Asibitin,
A cikin natsuwa ta shiga dakin bakinta daukeda sallama yana nan zaune a wuri daya, muryar ta da yaji tuni zuciyar shi ta sauka yaja numfashi tareda zuba mata ido, ta matsa tareda gaida momy da Aunty Zarah da ta zuba mata ido itama tana ganin mugun canji da murjewar da Naziyar Tayi,
Ta koma kusa dashi ta gaidashi tana yamutsa fuskar ta domin jitake kamar ta koma saboda tashin zuciya,shikuwa kallon al amarin ta yakeyi yana noticing komai duk Tayi sanyi lakwas, tana zama cikin ta ya mugun murdawa Amai ya taso mata, da gudu Tayi bathroom suka bita da Kallo dukan su kafin ya mike yana mamakin ta ko lafiya?
K’ak’arin Aman da takeyi yasa momy ta daka mai tsawa ” kabi yarinyar nan kataimaka mata ka tsaya k’ik’am kamar sabon soja. Jefa wayar shi Aljihu yayi tana rikeda washing hand basin sai kwara Amai takeyi ya karaso tareda dafata yana mata sannu, yitakeyi kamar zata Amaye y’an hanjinta dama tea kawai ta karasha bayan ta tashi baccin, Saida ya bata ruwa ta wanke bakinta ya fito da ita, momy jitake kamar ta mike ta taimaka mata da kanta, kwantar da ita yayi akan extra bed din tana maida numfashi, ya zare mata hijabin, “ka Kira likita ya dubata ka tsaya nan kana kallon ta banson shirme. Momy ta fada, duk da zuciyar ta tagama fada mata damuwar bataso Tayi farin ciki saita tabbatar, inko cikine da tafi kowa farin ciki. Yana fita Zarah tace “Aunty ai wanna dagani ba tanbaya ciki ne da ita, don ni tun shigowar ta naga yellow din da Tayi nasan juna biyu ne. “Allah ya Y’ar da da zancen nan Zarah. Momy tafada tana shafa hannun ta mai lafiya,
Likita ya biyoshi ya shigo tareda nurse, yafara tsokanar ta ” mai jinya ta koma patient. Jinin ta ya deba yabawa nurse yace taje takai lab ayi P T test.
Bayan minti talatin ta dawo da result,
Khaleel na zaune ya na mamakin what is wrong with her, ta rufe jikinta da hijabinta ta juya mai baya domin kamshin jikinshi ma is killing her, likitan ne ya shigo fuskar shi a sake, ya mikawa khaleel hannu “congratulations sir, a zuciye ya mike kamar mai jiran a taboshi “my wife is sick and you are congratulating me? “Relax Sir Ibrahim, your wife is pregnant.
Yafada yana Kara Washe baki, saurin juyowa Tayi idanun ta a waje “pregnant? Ciki kenan fa? Ita keda ciki? Ciki fa??.
Momy dake jingine ta gyara zama kamar ta sakko takeji ta daga Naziya ta goya sai kabbara takeyi, zata samu Karin zuri’a, zataga jikan ta Wayyo dad’i.
Khaleel kuwa d’askarewa yayi kamar Wanda ya suma, bai taba imagining ciki ba a Auren su yanzu bawai don baiso ba no sai don Abubuwan daketa faruwa da shi na farko rashin Ahmed nabiyu rigin gimun momy,
Yakasa koda motsi yanzu shine keda cikin jikin Naziya? That means he is going to be a Dad? Allahu Akbar. Yayi sujud shukhur, batareda ya duba inda yake ba. Kafin ya tashi ya rungume likita “likita da gaske am going to be a dad? Ya juya wurin momy da gudu ya rungume ta “momy Zaki zama granny. Wasu irin hawayen farin ciki ne suka zubo musu su duka itada khaleel din, Aunty Zarah Tayi dariya tace ” congrats Son Allah ya inganta. Sakin momy yayi ya dawo tareda rike hannun Aunty Zarah “Sorry Aunty for all the trouble tank you for your prayers Amen Allah ya inganta min.
“Oh mun shiga uku khaleel bako kunya cikin farko? Koda yake kalli Aunty ma jikan Fari harda hawayen murna lallai zamusha Kallo. Tafada cikeda tsokana, ” eh bakomai kifada duk Abinda zakice.
Naziya kuwa reaction din su ya taba mata zuciya sosai har batasan lokacin da itama hawaye ya zubo mata ba, ita bata tabaji ko ganin dokin ciki irin nata ba ace har momy na kukan murna wannan ciki ai Alkhairi ne a gareta, Allah sarki Ahmed Ashe bashi bane uban ya’yan ta Allah mai yadda yaso.
Matsowa yayi cikeda farin ciki yaganta tana hawaye. Da mugun sauri jikin shi na rawa ya karaso “Innalillahi baby ya Zaki fara kuka bayan kinada ciki please don’t hurt my baby stop it. Hannun shi akan marar ta yasha yanajin wani irin farin ciki, ya dago kanshi “baby cikina na nan please ki kulamin dashi kidaina yawo ki natsu basai kinyi komai ba ko wanka zanrika yimiki kinji no need ki wahalar min da yarinya.
Gaba daya ya manta da duk mutanen dake dakin likita kuwa Abun ya matukar burgeshi, don haka bai tafi ba, Saida momy tace “doctor ka sallame ni zanje gida inkarasa warkewa idan akwai Abinda za arika yimin zan rika zuwa checkup.
“Tab bansan Wanda yafi wani doki ba keda khaleel Aunty. “Zarah gwara inkoma gidan tunda kinsan halin d’an naki kar yaje ya hana min ita sakewa yajamun Asara. “Tofa kaji likita. “Eh ba wani damuwa sai medication dinta kawai dama ba Abinda muke yimata shi irin wannan ciwon warkewar shi gaba daya dama sai a hankali. Amma Hajiya kiyi hakuri har zuwa karshen satin nan. “No likita discharge me. Juyowa khaleel yayi “no momy please kibari ki Kara samun sauki zan kula da ita karki damu.
Shiru Tayi na d’an lokaci Saida likita ya fita tace “khaleel kana ganin zan kuma shiga Rayuwar ku ne domin inkara hanaku zaman lafiya? So nakeyi inkasance tareda Naziya nasan wahalar laulayi tunda tafara da Amai ga gida bakowa at least ina kusa hankalina zai kwanta.
Gwanin tausayi Naziya ta sakko duk da batajin karfin jikin ta ta matso kusa da MOMY, ” momy ina nan tareda ke Sai kinji sauki ba inda zanje. “Aa Naziya gida Zaki koma ki kula da kanki kinji” nidai tare zamu tafi. Tafada tana marai raice wa kamar zatayi kuka. Fita kawai yayi yabi likitan yace ” doctor you have to discharge my momy kafin matata ta jamun Asara please, zaku iya hadamu da nurse da zata kulamin da ita kafin ta karasa warwarewa,and inaso ayi mana Ultrasound insan watan cikina da kwanakin shi da kuma lafiyar shi. ” that’s not a problem dama yakamata hakan, maganar nurse munada kwararru,madam ko yanzu zaka iya kawota muyi ultrasound din.
Godiya yayi ya koma tareda cewa ” get ready Aunty Zarah zamu tafi gida baki daya bari muga doctor da Naziya, let go. Yafada tareda dagata suka fito yana makale da ita kamar gold takun ma ji yake kamar yayi mata shi, nan take akayi mata, cikinta kimanin sati bakwai zuwa takwas.
Abu daya ke takura ta shine kamshin perfumes dinshi, is killing her dauriya kawai takeyi, koda suka shiga mota juyawa tayi gefen window ta danna domin iska ya rika shigowa, kokafin su isa gida duk ta bata jikinta da Amai, da kuma motar shi, sai sannu suke yimata duk ta galabaita, don haka suna isa daukar ta yayi MOMY kuwa wheel chair sabuwa Aunty Zarah ta taimaka mata ta turata zuwa gefen ta, da mai aikinta ta gyare fess, taji dadin ganin masu aikin su duk sundawo, gidanta yadawo dai dai, mai aikin tafara tanbaya ko Salifa na gidan? Tace koda tadawo basa nan batasan me yafaru ba. “Ai Aunty kinsan halin khaleel kila yayi musu Abinda ya dace, what ever dai tunda basa gidan Alhamdulillahi.

Gefen Naziya kuwa daukar ta yayi ya kaita bathroom ya mata wanka tsab yana hadiyar yawu domin Allah yagani ya mugun yin kewar ta, dan komai yakara Masha Allah…. Yana mata wanka yana murzar ta duk ya rikice yana mata sannu, “please ka kaini dakin momy banason wannan pefurmse din naka, gaba daya gidan nan kamshin ka yakeyi zuciya ta na tashi I can’t stay here please kafitar dani kafin in Amayar da y’an hanji na….. 🖊

 

“Wnn Abu dai bamai sauki bane wurin khaleel akwai rigima kuwa, baruwana, but I understand ur situation Naziya 😞

Back to top button