Auren Gado 57-58
……… Tunda ya shiga ya hango ta a zube a gadon ya shiga tashin hankali, idanun ta ta bude a karon farko ta zuba mai idanu, so take ta motsa jikinta amma bazata iya ba, bakinta takeso ta bude bazata iya ba, domin har d’an karkacewa yayi kadan, ta rame a cikin Kwana kadan, wasu irin hawaye ne masu zafi suka biyo kumatun shi, for the first time yana regret na bijirewa umarnin ta koda zai mutu, saboda soyayyar uwa da d’a sai Allah, da kyar yaja jiki ya matsa wurin ta tareda dafata yasa kuka mai ciwo, “Am sorry mommy na am sorry”, nasan da yaya Ahmed ne bazai taba barinki a cikin wannan halin ba, gashi ni na barki mommy, am not a good Son mommy am sorry.
So take ta lallashe shi tare da nuna mai baida laifi amma bazata iya ba, sai hawaye da kebin kuncin ta itama, dagowa yayi cikin sauri, ya share mata hawayen ” please don’t cry momy”, zanfita dake ko ma wacce kasa ce zaki warke da izinin Allah. Yayi saurin tashi ya koma wurin likitan.
“Doctor zan iya tafiya da ita China kai tsaye ba wata matsala? eh babu saidai mun dorata akan medication na tsawon sati daya, muna so muga ni idan maganin ya karbeta nan da Kwana uku munga cigaba basai ka Fita da ita ba, so have some patience sir khaleel.
Haka ya fito a sanyaye idanun shi sunyi jawur, tundaga nesa taji ba dadi tana ganin Yanayin shi tasan ba lafiya,
Har ya matso tareda bawa manager umurni kai tsaye fuskar shi ba walwala, “take my wife home”
Ya juya yana Kara yiwa kawu bayani, jikinta yayi mugun sanyi y’an da yaki ko kallon ta kuma tana ganin damuwa karara a fuskar shi, daga dawowar su mommy tafara shiga tsakanin su ne ko kuma ciwon tane yasa ya shiga wannan mood din?
Kasa tafiya tayi ta matsa ina dakin inganta kafin in tafi? Tafada cikin kwantar da murya,
“Kije gida no need, batada lafiya banason Abinda zai daga mata hankali kuma.
Kallon tuhuma take mai ba tare da ta gano manufar shi ba ta juya cikeda sanyin jiki domin batada zabi,
“Hajiya ina zan sauke ki? Shiru tayi kadan tana tuna ai ba a gidan shi ya dauketa ba don haka ko yanzu gidan Aunty Raliya tace suje domin batasan me zata fada ba in taje gidan malam.
Tunanin Yanayin shi takeyi a zuciyar ta, they are just fine kafin suzo Asibiti, meya faru? Haka take ta tunani har suka isa gidan Aunty, akwatin ta ta cire tace yaje da nashi kawai.
Aunty Raliya tayi matukar mamakin ganin ta kamar daga sama Saida ta tsorata.
“Naziya saukar yaushe? “Yanzu muka shigo”… Tayi mata bayanin mommy ce ba lafiya tabar shi a Asibiti, “to ke meyasa baki wuce gidan kiba?
“Aunty ba anan ya daukeni ba da zamu tafi ko kin manta meya faru? toh Naziya naga kuna lafiya kalau da mijin ki me zaisa ki dawo gidana? ” ko in tafi gidan malam ne ? Tafada cikin fushi kadan da ya hadu dana khaleel ga tanbayoyin Aunty Raliya ga wata irin anger da takeji a zuciyar ta, “Aunty Matar shi na cikin gidan wadda akeso ya Aura mezan je inyi a can?
A’a kanwata duk dai haka bata tasoba, welcome back little sister, irin wannan fushi daga ganin ki kinyo mana tsarabar d’an China ne ko bangkok?
Kinga y’an da kika koma kamar atabaki jini ya fito jikin ki kamar wadda aka saka a engine, ai da badon nayi miki kyakkyawan sani ba bangane ki Naziya.
D’an murmushi tayi kadan, duk da haka zuciyar ta nakan khaleel, Sai da ta huta, Aunty Raliya ta bata Abinci taci kadan ta watsa ruwa, Aunty Raliya ta zauna gefen ta “Naziya akwai matsala na lura, meke faruwa ne meke damunki? Shiru tayi da kamar bazata yi magana ba Amma bata iya boyewa Aunty damuwar ta, da in ina tafada mata Abinda ke damunta.
“Mtsww kin dagamin hankali a banza, kika sani ko ciwon nata yayi zafine shiyasa kika ganshi haka, banson shirme ni banga Abun damuwa a cikiba.
Ajiyar zuciya tayi, badon ta gamsu ba imfact fushi ma takeyi dashi, don haka baccin ta ta shaka sosai don tagaji da zaman jirgin.
A Asibiti sai bayan ta wuce ya bita da kallo yana hango reaction dinta yasan ta shiga damuwar canjawar shi, and he can’t help it domin ganin mommy cikin wannan Yanayin duk ya dagula mai lissafi, sannan gashi yanzu Yanayin da yaga ta tafi ya kuma hargitsa mai tunani, bayason barin mahaifiyar shi kuma he wants to go to Naziya, haka yayi ta sintiri gasu kawu sun wuce gida yace sutafi su huta tunda yazo, dama ba azama damai jinya don haka suka tafi.
Ko yunwa bayaji duk da baici Abinci ba ko a jirgi, wallet dinshi ya ciro tareda wayar shi ya canja layin shi zuwa na gida yafara tunanin kiranta, lokacin tana bacci kuma tunda suka sakko 9ja batabi takan wayar ba don haka bata kunnata ba, jin ta switch off ya dafe kai, malam yakira suka gaisa, “Ibrahim kun dawo gidane naga number kasar mu? ” eh malam mommy ce ba lafiya shiyasa muka dawo ba shiri.
“Assha subuhanallahi toh kuna ina yanzu? Yafada mai Asibitin da suke.
Malam na kashe wayar ya tashi daga wajen ya shiga cikin gidan yasamu Inna kulu, yace ” Hauwa bari inje Asibiti mahaifiyar Ibrahim aka kwantar harma sun dawo suma. Ta jajanta Abun kafin tayi mai adawo lafiya, wani Almajirin shi babba da yazo gaida shi ya kaishi a roba roba har Asibiti.
Cikin girmama surukin nashi ya tarbeshi suka shiga har dakin mommy, malam ya jajanta tareda gaida ita tabisu da ido,
“Um um Ibrahim wannan ciwo nata tun yaushe ne? “Jiyane suka kawota Asibiti Amma bansan yaushe tafara ciwon ba. Yafada yana dukar da kanshi, “Assha, toh me likita yace akwai sauki ko Alamar samu? Ya mayarmai da yanda duk likita ya fadamai, ya girgiza kai yace Allah ya sauwake zata mike da izinin ubangiji karka damu ciwo jarabtace daga Allah Kuma jinya na kankare wa bawa zunuban shi don haka kataya ta da Addu’a, Ina ita Naziyar? Yace tana gida, ga shirme itada zata tsaya tayi jinyar mahaifiyar taku me ta tafi yi gida kuma?
“Ni nace taje ta huta zata dawo. Yafada kawai. Sannan malam yayi shiru.
Zuciyar shi shima tana wurin ta dan ba halin yabar Asibitin ne, bayan tafiyar malam ya koma dakin tareda zama ya zuba mata ido, zuciyar shi ta Kara karye wa “Am sorry Mommy for leaving you behind, ban kula da Amanarki da yaya Ahmed yabarmin ba. Hawaye ne suka zubo mai har kan hannun ta, ta bude idanun da su kadai suke aiki tana juyawa Alamar yadaina kuka, da tanada bakin magana da ta fada mai duk Abinda yafaru zatayi Amma babu, haka yayita kula da ita sai magrib ya fito domin bin dokar Asibitin ya shiga motar shi da yasa manager ya kawo mai,
Gidan shi ya tafi kai tsaye batareda tunanin komai ba, lokacin su Salifa sun baje a falon Mommy har da kawayen ta y’an iska ga mommyn ta a gefe tana waya akan akawo Mata sabbin gold tunda duniya tasu ce, sai da ta gama ta juyo tana kallon kawar Salifa da hannun ta ke cikin rigar salifan tace ” kufa bakuda kunya Ko kadan ina wurin don iya shege bazaku bari intashi ba, ku yaran zamani bansan meke damunku bane ga maza agari ga Alhazai ga d’anyun jini kubi, don iya shege junan ku kuke lalubewa, kuma ku kashe min hayakin nan ya ishheni haka kuyita bankadar shisha kamar Abinci.
“Old lady bazaki gane dadin bin jinsi bane sai kin d’ana yaseen. “Aa barikin da nayi baikai can ba kudai kuje kuyita yi ni yanzu tunda dukiya tasamu banda matsala kuma kusa ido kwanan nan zata karasa domin boka yafadamin ya fara aiki ya sakar mata ciwo a hankali zata karas………… Kasa karasawa tayi ta maida kalmar ta ta hadiye mukuth kamar ta hada da makogoron ta, tayi saurin mikewa tana diri diri don ko motsin mutum basuji ba. Tun shigowar shi gidan yasan akwai matsala domin yayi horn har yagaji ba mai gadi yatafi yawon shi, don haka da kanshi ya bude ya shigo tareda rufewa da katon kwado,
Salifa tayi mugun nisa don ba karamin jin dadin tabawar takeyi ba har wani cije lips takeyi idanun ta sun sauya tuni,
Taji salatin mommy, cikin zin zafin yanda take kokarin hanasu jin dadi tace ” my God mommy please ki bar nan munaso mu huta if you can’t wat……. Ai tafi mommy firgicewa ta tattaro rigarta ta na rufe kirjin ta da kyar ta zabura, mommyn ta na rawar kafafu da murya tace “khaleel yaushe ka.. Ka.. Da… Wone? Kagan mu nan muna d’an jajanta jinyar balkisu ne zanyi girki muje dubata banaso mubar part din ba kowa ayi sata. Tanayi tana kame kame.
Tunda ya shigo yake kame a jikin kofar falon ko motsi baiyi ba tunfara maganar mommy har zuwa yanzu, bazai iya misalta tafasar da zuciyar shi takeyi ba, nade hannun shi suke Saida ya gama kare musu Kallo tsaf idanun shi sunyi mugun kadawa, dukkan su bamai fuskar mutunci ko shigar Arziki, ya juya ya kulle kofar da key tareda cirewa ya jefa pocket ya nufo tsakiyar falon yana karewa ko ina Kallo.
“Hmmm I gave you ten minutes kafin inyi fresh up I want you to clean all this mess. Ya fada yana nuna musu falon da yayi kaca kaca domin sun maida shi dandalin iskancin su.
Shigewa yayi domin akwai tsananin gajiya a jikin shi, sai da ya tube ya shiga bathroom ya hada hot water ya shiga, zama yayi ya runtse idanun shi, ” mommy kinga me kika janyo mana ko? kinga irin zabin naki. Yafada yana mai zubo da hawaye, yanzu yaji zuciyar shi ta samu sukunin da zaiyi Abinda yake ganin ya dace don dazu inya biye zuciyar shi kisan kai zaiyi, ya tuna da maganar Hajiya sharefa. Zabura yayi ya dauraye jikinshi ya fito daure da towel.
Waldrp dinshi da yasan akwai kaya ya bude ya ciro kananan kaya guntun wando da Riga T-shirt bakake an rubuta handsome and Arrogant, da farin Zane,
Shigowa tayi cikin karairaya wai ita mai miji, domin sun zugota taje ta yi mai kissa tunda baice komai ba, baiga komai ba, don haka Jakar ta biyoshi dai dai yana daukar wayar shi yaji maganar ta.
“Darling welcome”… wani irin juyowa yayi a hargitse tareda sa kafa ya bata wani irin shoot da bata san yana zuwa ba, don haka wani irin tumbling tayi har jikin kofar ta buga kai Tim, ba shiri tasa Kara.
Wandon da ya cire ya dauka yasa cire belt din jikin shi. Ya rike wutsiyar Alamar da karfen yake son yin hukuncin, tuni har sun shigo a tsorace saboda ihun salifa.
Idanun shi a rufe yace ” kuma kunshigomin dakin ne da dattin ku”? toh duk sai kunci ubanku yau sai kungane kun shigo inda bai dace da iskancin kuba,.
Rufe ido yayi yana musu kan mai uwa da wabi har mommyn ma tana zuba salati, “d’an nan zaka iya dukan balkisu Ashe ? Indai zaka b…ai wani irin hambarin da yabata Saida tayi zaman y’an bori, kin saka mahaifiyata cikin ciwo bayan ita ba Abinda take nufinki dashi sai Alkhairi kinzo kin kawo min karuwai cikin gida har gefen uwata kuna iya shege, a kuma gabanki suke lalacewar su don kina tsinanniyar uwa, I think my mother is worst, Alhamdulillah nasan bazata taba aikata irin wannan halin nakiba, domin ta bamu tarbiya mai kyau but you, look at your daughter in front of your eyes……..
Wani irin bakin ciki ya kuma tokareshi ya Kara rufesu da duka sukayi falo suna zuba ihu, mommy da rarrafe da jan gindi ta Fita tana ” ni ka daka khaleel ina Suruka….. “Kina karasawa sai na sumar dake wallahi” surukin uban wa ni na Auri Y’ar ki ko kitanbaye ta ko yatsar ta na taba Kallo, ke har kinada Y’ar da Khaleel zai Aura? look nace ku gyara gidan nan kunki wallahi billahi idan Nafita nadawo bakuyi ba zakusha mamaki na…. “Ya isa don Allah malam kai din wa da zaka zo kana dukan uwata da kawayena? Toh bazamuyi ba ka kashe mu kuma kokaki ko kaso ni Matar kace igiyata na wuyanka kuma bazaka biyamin bukata ba dole in nemawa kaina mafit…… Wani irin kwashe ta yayi da kafafun shi ” tir Allah ya tsare ni in hada tsalkakakken jikina da najasa, wallahi da in zauna dake a matsayin mata gwara in mutu gauro, kuma inke kadaice mace khaleel bazai taba Aure ba, igiya ko na datseta duka ukun aje acigaba da karuwancin da license dama kin saba ko da mijin ki zai baki kulawa ba isarki zaiyi ba dabba Alade tunkiya kawai, and ke kuma, ya nuna mommy, “ba Wanda zai Fita wannan gidan sai mahaifiyata ta warke idan bata warke ba ko naga wani Abu yasameta wallahi za ayi gudu, don duk sai na nakasa ku. Ya bankada ta ya wuce tareda bude kofar ya Fita ya kuma kulle su a ciki.
Gefen Naziya ya nufa yana nan a garkame a y’an da yabar shi, ya rike kai that means ba nan tazo ba. Wayar shi ya ciro ya Kira manager yace” ina ka kaimun madam?
“Tana janbulo can tace inkaita.
“Nan ne gidana why zaka kaita can kuma bazaka fadamin ba. “Sorry sir bansani ba ne. Ya datse kiran cikin haushi ya Kara gwada kiranta ko yanzu shiru, ya nemi number Aunty Raliya, lokacin suna hira abinsu sun gama cin Abinci,
Daurewa kawai takeyi Amma zuciyar ta na wurin shi tayi mugun sabo dashi zaman su a can tsawon satunkan nan baya Fita ko ina suna likeda juna yasaba mata yau daga dawowa nan ya shareta, zata rama ne itama.
Karar wayar Aunty ce tasa ta kalla taga number shice ta basar Aunty tace “bani wayar to ni in dauka in baza ki daga ba.
Picking tayi tareda sallama, ya gaida ta cikin girma ta tanbaya mai jiki yace Alhamdulillah jiki, kafin yayi shiru yakasa tanbaya ko tana nan. Aunty tace ” ga mutuniyar nan. Ta Ajiye mata wayar tareda Fita Abinta tana cewa nabarki lafiya nayi wurin neman lada tsaya yanga ke.
Tana kallon wayar taki dagawa ya katse ya kuma Kira taki dauka, yace ” tofa khaleel ka shiga uku yau. Ya Kira yafi sau goma taki dagawa haka ya hakura ya kyaleta dole yaje karbar hukunci in yana son yazauna lafiya da zuciyar shi, a daren dukan su basu runtsa ba, khaleel Kwana yayi tsuki ga takaicin su Salifa ga kuma fushin Naziya, ga wani horo da jikin shi kemai wai bazai runtsa ba tunda bata kusa saboda sabo da yayi, zaune ya tashi yanajin kamar yayi tsuntsu yagan shi a gaban ta saboda kewar ta, “kin lalatani kinaso kuma ki gujeni baby no way wannan fushin is unacceptable, bazai yuwuba dole gobe kidawo nan I can’t take it.
Daren ya mugun yimai nisa, haka itama Amma saboda Yanayin kasalar da takeji daga baya tayi baccin ta, Assalatun farko yayi masallaci da badon kar ace lafiya ba zuwa zaiyi yayi gadin ta har gari ya waye ya ganta hankalin shi ya kwanta. Zama yayi yana gadin safiya, sai yanzu ya tuna da su Salifa ma, ya koma ciki tareda dakko key ya nufi kofar ya bude, suna shahsheme a kasa, Hajiya sharefa kugu yayi tsami ko motsi bata iyayi salifa kuwa hannun ta a kunbure Kwana tayi kuka saboda azaba daga gani ta targade ne. Suma sauran sai nishi sukeyi zasu iya rantsuwar ba mahalukin da ya taba musu irin wannan wulakancin na khaleel.
Taka hannun salifan da yayi ne yasa ta saka Kara mai karfin da ta tashe su har mommyn tana “wannan y’a akwai ki da shegen raki saikace nima ba ciwon nan ne dani ba wannan akwai tambadadden…. Tayi tsit ganin shi duk suka mike tareda fara bashi hakuri ” khaleel kabarmu mutafi yanzu kaga mun gyara ko ina wallahi bazamu kuma shigowa gidanka…. “Kuma nafada muku bazaku bar gidan nan a banza ba bayan kunyi sanadin kwanciyar mahaifiyata Asibiti”, Kujera ya samu ya zauna tareda dora kafa daya kan daya yace yanzu inaso inji duk Abinda yafaru bayan bana nan kafin inbarku kufita gidan nan oya I’m all ear’s. kayi hakuri bab…. “Kul kika kirani da wannan sunan ni ba sa’anki bane, call me sir khaleel ko sir Ibrahim. “Sir khaleel nidai naso in tafi mommy ce tasa ni zama wallahi ni na hakura da Auranka tunda naga baka damu dani ba, Amma mommy….. Ta bude mai bakin Jakar tsab momyn ta na mintsilin ta karta fada maganar takardaun Amma Kash tuni tayi b’ara, “takardun ka da managern ka yakawo suna nan ban tabasu ba wallahi. Dafe baki yayi yana mamakin greediness dinsu duk Abinda suke dashi wato bai ishesuba nashi suke hari da Dukiyar mommyn shi. “Wato 419 kuke yi kenan? Shine kukazo har gidana zakiyi in the name of Auren hadin zumunci, you know what? mommyna harga Allah so take zumuncin ku ya kullu shiyasa ta matsa mana domin Y’ar ki dagani har Yaya na, Ashe ku zuciyar ku sharri kuke nufin ta da shi, alright zaku ga karshen cin Amana kuwa. “Wayar shi ya ciro ya Kira manager yace ya zomai da police yanzu yanada y’an 419 a gidan shi. Tuni suka fara kuka mommy na rokon shi kawayen nacewa ” mudai meye namu aciki kawai mu masoyane abarmu mutafi ba ruwan mu da rigimar gidanku, salifa kinga kunjefa mu a matsala daga Zuwa hutawa. Karku damu zaku huta a bayan kanta. Ya mike tareda Fita ya rufesu ganin suna kokarin biyoshi suna roko. “Mommy kinga masifar da kika jefamu ko nafada miki halin khaleel kingani bantaba zuwa prison ba yau zaki sa in shiga bayan inada Abinda zai isheni Rayuwa ta ko wacce kasa nakeso inada manyan babe da zasu kaini in more, now look what you have got us in to, wallahi bazan yafe miki ba mommy.
Ga Y’ar banza don wa nake duk wannan abun badon ke nake yi ba saboda banaso ki wahala…. “Oh really? All tanks to you now we are going to rot in jail”.
Ke kibarni inji da kwankwaso na dakeyi kamar ya fita da gangar jikina.
Kuka tasa tace ” ni hannu na bakya gani ya kunbura dakyar nake dagashi wallahi, nidai Allah ya isar min. “Gawa? Inji mommyn. “Ga duk Wanda ya tsargu. Tafada tana murguda bakin ta saboda tsantsar rashin tarbiya.
“Toh mu muyiwa wa Allah ya isa ke Ko uwarki ?, saboda jarabar ki yau kinja mana masifa mu bamuci ko fucika ba. Amma kunci ni shegu matsiyata la’anannu kawai jarababbun ba.. ai tuni dambe ya kaure suka fara jirgar ta mommy na ihu gashi bata Iya kwakkwaran motsi. Karku kashen ya’. Basu daina ba Saida khaleel ya bude kofar, sunyi mata lilis duk sun jijjimata da kunba, police yabawa izinin shigowa yace duk su kwashe su. Tana numfashin wuya dakyar haka aka jasu keeeee, aka watsa bayan mota, mommy sai rokon shi takeyi yayi biris, yanzu burin shi yaje yaga farin cikin zuciyar shi ko a wane halin take?
Wanda tunda ta tashi suka hada lafiyayya breakfast da Aunty suka shirya a basket, ta kintsa cikin wata tsaleliyar doguwar Riga Y’ar Oman ta nade kanta da mayafin, ba fushi yakeyi ba na ba dalili zai sha mamakin ta tayi kyau na fitar hankali dole duk Wanda ya ganta yasan Matar wanice, mijin Aunty a lokacin da zai Fita ya saukesu a Asibitin, tundaga harabar take baza idanun ta ko zata hango shi, Saida suka tanbaya dakin aka nuna musu, bashi ba Alamar shi yana can yana dealing dasu mommy, takara cika, sai a lokacin taga mommy, tayi matukar tausaya mata har wasu hawaye taji sun zubo a kuncin ta, kai Rayuwa d’an Adam ba bakin komai yakeba yanzu mommy Y’ar gayuce haka kwance ko motsi bata iyawa, matsawa sukayi bakin gadon ta dafa hannun ta, tace “Sannu mommy Allah yabaki lafiya. Ta bude idanun ta ta zuba mata ido sai hawaye, so take ta bude baki tafara bata hakuri Amma ba hali, hannu Naziya tasa ta goge mata hawaye, nurse ce ta shigo ta tanbaye ta za a iya bata Abinci? Tace eh su bata mai ruwa saboda bakin daya d’an juya.
Dama sunyi kunun gyada, “Aunty Raliya ta zuba mata, da taimakon nurses Suka d’an dagata saboda nauyin jikin ta jingina mata filulluka, cokali tasa tafara bata kunun Tanayi tana gogewa saboda dawowa yakeyi kamar jaririyar da ake koyawa cin Abinci, ido kawai take binta dashi da hawaye, sai sannu sukeyi mata, Aunty Raliya tace ” kinga shirmen ki Naziya ki tsaya tunjiya saboda kula da ita kin kama kin tafi. “Aunty laifin shine ko bari baiyi na gantaba Ashe jikin yayi tsanani har haka ne, yanzu bazan koma ba zan tsaya da ita anan inkinje ki sa akawomin ko Kala biyu ne masu saukin sawa.
Tunda yagama dasu cikin gaggawa yayi wanka ya shirya cikin d’an kareriyar shadda Arsh guntun Riga tasha dinkin gayu na maza, ya fito yafada mota, hankalin shi ya kasu kashi biyu, mommy da Naziya, don haka ya yanke hukuncin zaije Asibitin first ya dubata don yasan inyaje wurin Naziya zai iya mantawa da kanshi acan, koda ya isa Asibitin yasha mamaki, Wanda tundaga kofar dakin kamshin ta yafara yimai welcome, wani irin Ajiyar zuciya yayi tareda murmushi kadan yace ” my happiness tunkafin ya ganta……. 🖊