Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 10

Sponsored Links

page 1⃣0⃣

 

_*After 3 days later*_
sumayya ce kwance tayi matashin kai da cinyar zinat tana waya da ummanta bayan sun gama sumayya d’aga kai tayi takalli zinat da take ta dannar waya da alama chart takeyi, tace baby mutuminki fa har yau bamuyi wayaba.

murmushi zinat tayi tace toh sai me minene abun damuwa tunda dai bai nemekiba toh kema kisharesa, ke ni jiya da nafita na ga Alhaji jamilu kuma nafad’a masa muna tare wlh bakiga yadda ya rikice min ba wai sai ya biyoni ya zo wajenki.

murmushi sumayya tayi tace ke dai kina son jona ni da Alhaji jamilu,

zinat tace toh ai nasan zamu samu cash masu tsoka a wajensa, ke nifa inda ke da kud’i a nan nafi wayau.

dariya sumayya tayi tace nima haka dear, wlh dan dai ina tsoron kar yarima yagane da nabi maganarki naje munyi sharholiyarmu da shi inyagi abinda nayaga.

Zinat tace haba baby kefa matsalata da ke kenan taya kike tunanin mijinki zaya gane tun farko ma bai ganeba sai a yanzu?

Sumayya jinjina kai tayi alamun gamsuwa sannan tace toh yanzu dai ta ina zamu fara?

zinat murmushi tayi tace ai ya bani number d’insa bari kawai inkirasa sai kuyi magana ko kuma inbaki number d’insa.

dasauri sumayya tagirgiza kai tace a’a kirawo min shi dai da wayanki kinga yanzu nayi aure kar wataran yakirani gaban mijina.

zinat tace hakane nan tafara dialing d’in number d’insa tanaji yad’aga dasauri tasa ma sumayya a kunne, jin muryarsa yasa sumayya yin murmushi tare da kallon zinat.

zinat alama tayi mata na tayi magana.
sumayya kwantar da muryar tayi tace Alhajina dafatan kana lafiya.

Alhaji jamilu da yake kwance jin muryar sumayya da yayi yasa yamik’e zaune tare da cewa sumayya daman kina nan?

sumayya murmushi tayi tace aikam dai ina nan Alhaji ya gida ya kake?

Alhaji jamilu cike da jin dad’i yace lafiya lou baby gaskiya naji dad’in jinki da nayi wlh daman nadad’e ina cigiyarki wajen zinat.

sumayya tace ayya kar kadamu yanzu ai gani.

yace baby toh inaso muhad’u ya za’ayi?

sumayya kallon zinat tayi sukayi murmushi sannan tace toh katuron address d’inka sai inzo

cike d’s jin dad’i Alhaji jameel yace yanzu ko zan turo miki ammah please kizo yau,
sumayya tace kar kadamu zan shigo da anjima, yanzu dai ina jira sai ka turo.
nan sukayi sallama suka kashe wayan.

sumayya kallon zarah tayi da tatsareta da ido tace baby nidai ko da na je gaskiya bana iya bari yayi sex da ni.

zinat zaro ido tayi tace haba baby saboda mi? toh kud’in fa?

murmushi sumayya tayi tace kar kidamu dolene ma sai na samo mana kasonmu kin d’auka a banza chan baya yamoreni?

dariya zinat tayi tace toh ai lokacin ma mun yagi kasonmu,
sumayya tace a yanzu ma dole yabamu, bari ma kiga inje inyi wanka, tana gama fad’in haka tamik’e tafara cire kaya.

 

bayan ta fito wanka shiryawa tayi cikin riga da skirt na atamfa sannan tayafa d’an k’aramin veil, kallon zinat tayi da tatsareta da ido tayi murmushi tare da jujjuyawa tace baby ya kika ganni?

zinat ma murmushi tayi tare da mik’ewa tace kinyi kyau sosai anya kau Alhaji mukhtar zai barki?

dariya sumayya tayi tace muje dai kiyi dropping d’ina.

wani dank’areren gida aka hangame musu gate suka shiga gefe guda zinat tayi parking sannan takalli sumayya da take bin gidan da kallo tace haba baby kema fa gidanki ya tsaru naga sai kallon wannan kikeyi

murmushi sumayya tayi tace balaifi yayi min kyau.

zinat tace toh kifita kishiga ni bari inje koma dai me kenan sai kindawo.

sumayya tace toh tare da bud’e motar tafita nan zinat taja motarta tabar gidan.

ahankali sumayya take takawa tanufi k’ofar da zata sadata a cikin gidan cikin karambani take bin hanya saidai ganinta tayi a parlour lokacin Alhaji jamilu yana kwance saman 3 seater yana kallo, jin anbud’e k’ofane yasa yad’ago ganin sumayya yasa yamik’e dasauri yanufi inda take tsaye, rungumeta yayi yace oyoyoo babyna.

sumayya janye jikinta tayi daga nasa tana murmushi tace baby kwana dayawa.

rik’o hannunta yayi suka zo saman 3 seater suka zauna har a lokacin idonsa cikin nata yace baby ban d’auka zan k’ara ganinki a yanzu ba saboda nisan da kikayi min kin 6oye.

sumayya murmushi tayi tace no ni ina gefe kune dai siyasa ta6oye.

Alhaji jamilu hannunsa na sark’e da nata yace mu muna gefe baby inkinson ganinmu zaki ganmu dan ba irinku muke 6oye mawaba, yanzu dai taso mushiga daga ciki.

sumayya mik’ewa tayi tabi Alhaji jamilu bedroom d’insa suka yada zango saman gadonsa, rungume yayi yakai bakinsa cikin nata suka fara kissing d’in junansu inda hannuwansa suke yawo cikin rigarta.

sumayya dai kawai tana biye masane har yarabata da kayan jikinta romance d’in sunansu suke son ransu daga k’arshe sumayya da taga yana shirin shigarta tadakatar da shi.

da mamaki Alhaji jamilu yake kallonta yace baby saboda me zaki hanani? Please kibarni inyi kinsan fa nakwana biyu banji d’umin jikinkiba.

murmushi sumayya tayi tace dear kayi hak’uri just dai muyi romance d’in juna ammah bana buk’atar sex, ganin yana shirin yin magana yasa tarufesa masa bakinsa da nata cike da kwarewa itama tadinga sarrafasa saida taga ya gamsu batare da sex ba sannan tabarsa.

Alhaji jamil kallonta yayi da take shirin tashi yace baby ina zakije?

murmushi sumayya tayi tace gida zan koma yace haba dan Allah kiyi min ko da kwana d’ayane

sumayya tace a’a Alhaji tafiya dai zanyi inyaso wani lokacin sai indawo.

Alhaji jamil ba dan yasoba yace toh atare sukaje sukayo wanka, duk yadda taso tatafi dawuri hanata yayi saida tayi dagaske sannan yad’auko yamaidata gidan zinat.

A mota ma bai bartaba rungumeta yayi inda hannuwansa suke yawo a cikin rigarta saida yagaji dan kansa sannan yabarta, cheque d’in 1.5 million yarubuta mata yamik’a mata.

cike jin dad’i sumayya takar6a tare da yin godia sannan sukayi sallama tafito daga motar tana d’aga masa hannu har yatafi sannan tashiga gida.

A parlour tatarar da zinat zaune da d’an k’aramin veil a gefenta da alama itama bata dad’e da dawowaba.

daga gefen zinat tazauna tare da cewa wash wlh na gaji.

dariya zinat tayi tace ya dai baby? ai nasan Alhaji jamil ba zai ta6a barinki hakanan ba.

ta6e baki sumayya tayi tace ke ni kawai dai na amince masane ammah banbari yayi sex da ni ba, wlh yarimana yafisa iya sarrafa mace saisa nace miki bana tunanin akwai namijin da zan iya jin dad’insa kamar yarima.

ta6e baki zinat tayi tace haka dai kike gani ammah wlh inkina so zan iya had’aki da guys d’ina zakiga banbanci sosai

sumayya tace bama naso.
zinat tace yanzu dai babu abinda yabamu kenan?
sumayya bud’e jakkarta tayi tafiddo cheque d’in tamik’a mata.

zaro ido zinat tayi tace baby yanzu Alhaji jamilu yabaki kud’in nan batare da yayi miki komai ba?

murmushi sumayya tayi tace kawai dai munsha minti ammah babu abinda yashiga tsakaninmu, ke ni sai bayan natafi nake tunani ai da nayi ma yarima magana da zai bani saboda duk abinsa ammah baya da rowa

zinat yamutsa fuska tayi tace ai k’arama da bakiyi masa magna ba dan banason mutumin nan saboda wulak’ancinsa.

sumayya tace zinat ammah wlh yarima baida rowa.
zinat ta6e baki tayi tace matsalarsa, nidai ynz tashi muje mukwanta inyaso gobe sai muje muciro kud’in mud’ibi kasonmu sai muyi order d’in wasu kayan da sauran kud’in, nima kinga ga 1 million nan d’azun nakar6esu wajen wani guy d’ina.

dariya sumayya tayi tace ai daman tunda nadawo naga veil d’inki a gefe nasan kin fita.

zinat tace ai ina dropping d’inki ban dawo gidanba nawuce chan, yanzu dai nidai agajiye nake muje daga ciki.

 

 

 

Tun daga ranar sumayya idan Alhaji jamilu yakirata take zuwa gidansa ammah bata bari yayi sex da ita tun yana k’orafin har yagaji, ahaka tacika 1 week a garin.

zinat rok’onta tayi kar takoma gida dakyar tasamu sumayya tazauna domin tak’ara ko da kwana biyu ne ammah saida takashe wayarta gudun kar su dada sukirata.

____________

Yarima suhail tunda sumayya tatafi bai damuba harkar gabansa kawai yakeyi domin a ganinsa da ita da babu basuda banbanci, ko da sau d’aya bai d’aga wayaba da zumar yakirata.

ahaka har tayi 1 week ammah bata dawoba,

Dada jin sumayya shuru bata dawoba yasa takirata a waya ammah wayanta a kashe dan haka ta aika aka kira mata yarima.

yarima yana kwance a 3 seater kujerar da take opposite d’insa Shaheed ne zaune duk yadda shaheed yaso suyi hira da yarima suhail ammah yarima ya k’i,

ganin haka yasa shaheed yaja bakinsa yayi shuru dan yasan halin mutumin nasa har korarsa ma zai iyayi, gajiya yayi da shurun daga k’arshe yakalli yarima da yazuba ma ceiling ido da alama tunani yake, yasheed yace yarima meyake damunkane?

shuru yarima yayi yakyalesa.

murmushi shaheed yayi yace ranka yadad’e ko kana tunanin gimbiyarkane.

yarima juyowa yayi yawurga ma shaheed harara sannan yamaida kansa ga kallon ceiling.

dariya ce takama shaheed ammah yadanneta yace Allah yahuci zuciyarka.

K’ofar d’akin aka shiga knocking, Shaheed ganin yarima baida niyar yin magana yasa yabada izinin ashigo.

wata baiwace tashigo dasauri tazube k’asa a bakin k’ofa tace ranku yadad’e Allah yaja da ran yarima mai jiran gado, daman sultana dada ce tace tana nemanka.

shaheed kallon yarima yayi yaga baida niyar yin magana kuma yana jin ta, shima bakinsa yaja yayi shuru.

saida aka d’au kusan minti ukku tana tsugunne sai chan yarima yad’aga mata hannu batare da ya kalletaba alamun tatafi.

dasauri tak’ara duk’ar da kanta tace ranka yadad’e afito lafiya sannan tatashi tafita tabar d’akin.

shaheed kallon yarima yayi yaga baida Niyar tashi, cikin ransa yace yau abun ya motsa kenan, nan yacigaba da kallon ball d’insa.

saida akayi kusan minti goma sannan yarima yamik’e tare da d’auko alkyabbarsa yasaka, batare da yayi ma shaheed maganaba yafita yabar d’akin,

nan mutane sukayita zubewa suna kwasar gaisuwa yau ko d’aga musu hannunma bayayi ahaka har ya isa turakar dada.

ko da yashiga dada tana kishingid’e anayi mata tausa, ganinsa yasa duk suka zube suna kwasar gaisuwa, tsaye yarima yayi har saida suka tashi suka ficce sannan yatako yazo yazauna bisa kujerar da take opposite d’in dada.

dakyar kamar bayason yin maganar yagaishe da dada.
dada cikin fara’a da sakin fuska ta amsa masa, gyara zamanta tayi sannan tace yarima daman akan maganar matarkane yaushene zata dawo?

Yarima kallon dada yayi sannan yamaida kallonsa akan wayarsa da yake dannawa cike da jin haushin maganar da dada tayi,

dada zuba masa ido tayi tana kallonsa baida niyar bata amsa,
sai chan yace ranki yadad’e ai nad’auka kunyi magana kinsan lokacin da zata dawo tunda nidai bata fad’amin kwanakin da zatayiba.

dada baki tasaki tana kallonsa har yagama maganar sannan tace suhail kana dai so kacemin bakuyi waya da itaba tunda tatafi.

yarima shuru yayi bai tankaba,
dada tace ammah wlh da kacika marar kirki har yanzu kana nufin baka huceba kenan.

yarima kallon dada yayi tare da yin murmushi yace dada kenan ni ba fushi nakeba, kawai dai nad’auka kinsan lokacin da zata dawone ammah kiyi hak’uri idan maganata ta6ata miki rai,

dada tace toh yanzu nafahimta ammah dan Allah kakirata kaji yaushe zata dawo saboda sati guda tace zatayi ammah yau kusan kwananta takwas.

mik’ewa yayi yace toh dada, bari inwuce ana jira.

dada tace toh shikenan nidai dan Allah kakirata.

yarima baice komai ba yawuce yafita cikin ransa yana cewa saidai kar tadawo indai sai na kirata zata dawo.

 

Bayan kwana biyu gimbiya sumayya tayi shirin komawa gida lokacin Kwananta goma, Alhaji jamil da zinat su suka kaita airport a chan ma Alhaji jamil yana manne da ita kud’i masu tsoka yabata, har saida sukaga tafiyarta sannan suka bar wajen.

 

Gimbiya sumayya ko da tadawo da su dada suka tambayeta akan rashin dawowarta k’arya tayi musu akan wai wata matsala ce tatashi akan business d’insu saida tajira komai yakoma normal sannan tadawo.

ko da tadawo sai da takwana biyu batasa yarima a idontaba dan tayi tunani zaizo d’akinta ammah sai gashi tsawon kwana biyu bai zoba.

dan haka da daddare shiryawa tayi taje 6angaren yarima domin ta san Indai ba ita tajeba toh ba zai ta6a zuwa wajentaba saidai idan yana buk’atarta.

lokacin da tashiga yarima suhail yana shirin bacci ko inda take bai kallaba, takawa tayi taje inda yake still dai bai kalletaba sai ma wucewa da yayi yahaye gadonsa yakwanta.

Sumayya cikin ranta tace toh yau kuma naga yadda zamu kwashe da wannan d’an jin kan, binsa tayi saman gadon takwanta gefensa tace my sweetheart ko welcoming d’in ma bazan samuba, tsawon kwana biyu da dawowata ammah ko kanuna ka damu.

yarima suhail batare da ya kalletaba yace ashe kini dawo?

da mamaki sumayya take kallonsa tace au da ba zan dawoba?

yarima bai tanka mataba yajuya mata baya.

sumayya ganin haka yasa tarungumosa ta ba tace haba yarima wai meyasa kake son wulak’antani ko dai bakaji dad’in dawowataba?

yarima banza yayi yakyaleta cike da k’ulewa.

gimbiya sumayya tace haba yarima wlh banason sharewar nan da kakemin.

yarima suhail yace sumayya ai da baki dawoba dan dabakinan hankalina ya fi kwanciya wlh, ni da kin taimaka kin tashi kinkoma d’akinki dan yanzu banason a dameni hutu nake buk’ata.

sumayya cike da k’ulewa tace kai wlh tsiyata da kai bakasan arzik’iba duk yadda mutum zai nemi yakyautata maka sai ka kushesa nifa kawai tausayinka nakeji ganin lokacin da nad’auka bana nan nasan kayi missing d’ina.

Yarima tashi yayi yazauna yana kallonta a wulak’ance yace sumayya me kika d’aukeni? na fa san abinda nakeyi ni a yanzu bana buk’atarki dan haka kitashi kifitarmin daga d’aki,

da mamaki gimbiya sumayya take kallonsa tace yarima ni kake kora? me nayi maka daga dawowata sai kahauni da fad’a?

wani mugun kallo yarima suhail yayi mata tare da nuna mata k’ofa.

tashi sumayya tayi tare da d’aukar alkyabbarta tasaka sannan tace naji zan fitar maka daga d’aki sauk’inma nima ina da nawa d’akin daman taimaka maka zanyi ammah tunda……

tsawa yarima yadaka mata cikin 6acin rai yace I said get out!!!

sumayya ta tsorata sosai da ganin yanayinsa dan haka dasauri taficce tabar d’akin cike da jin haushin wulak’ancin da yarima yayi mata daga dawowarta……

 

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

 

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_*Sak’on gaisuwata gareka M.B.A a duk inda ka kasance nagode sosai*_

 

_~Masha Allah Sis leemah nd my k’anwa Janaf ina tayaku murnar kammala novels d’inku masu suna *BABBAN KUSKUREN DA NATAFKA nd NATAFKA KUSKURE* hak’ik’a kunyi namijin k’ok’ari wajen baje basirarku da hikimarku kun wa’azantar, kun nishad’antar sannan kuma kun fad’akar gaskiya na yaba muku sosai Allah yak’ara basira da zak’in hannu, I heart u all~_

_*Ummun Meenal Mummyn fadyl nd my chubby kuna ina kumatso kusa yau filin nakune, wannan page d’in mallakinkune ku kad’ai kuyi yadda kukeso da shi*_

 

Back to top button