Yarima Suhail 49
PAGE* 4⃣9⃣
Haka sultana sadiya ta isa 6angarensu farin ciki fal a zuciyanta, cikin sa’a ko da ta isa tatarar angama dafa zogalen, nan tasa wata baiwarta tak’wad’a mata, sannan tawuce cikin bedroom d’inta inda tad’auko k’ullin maganin da tasa aka samo mata.
Bayan an gama kwad’on a parlour aka kawo mata cike da jin dad’i tabud’e taduba saida tad’ibi nata sannan tazuba ma sauran maganin tamotse yadda ba za’a ganeba sannan tajuye a cikin wata kula mai kyau, murmushin mugunta tayi tace zarah kinyi babban kuskure da kikayi saurin yarda da ni dan bakisan wacece ni ba,
Sallamar da akayine daga wajen d’akin yasa ta amsa saida tagama abinda take sannan tabada izinin ashigo, jakadiya ce tashigo cikin sauri taduk’a tagaishe da sultana sadiya cike da girmamawa.
Sultana sadiya kallonta tayi a wulak’ance saida tayamutsa fuska sannan ta amsa.
Jakadiya k’ara duk’ar da kanta tayi k’asa tace ranki yadad’e daman dada ce ta aikoni wajenki.
Shuru sultana sadiya tayi na d’an lokaci sannan tace ina saurarenki.
Jakadiya ledar da take hannunta ta mik’a mata tace gashi tace akawo miki.
Kar6a sultana tayi tabud’e batasan lokacin da Murmushi yakubce mataba ganin wata had’ad’ar sark’a da dada ta aiko mata da shi, cikin sakin fuska sultana sadiya tace kice mata nagode.
K’ara duk’awa jakadiya tayi tace Allah yaja da ranki nabarki lafiya,
Gyad’a mata kai kawai sultana sadiya tayi,
Har jakadiya ta wuce zata fita sultana sadiya takirata.
Cikin sauri jakadiya tadawo taduk’a tace ranki yadad’e na amsa kiranki.
Sultana mik’a mata kular tayi tace gashi kikai ma gimbiya zarah.
Cikin sauri jakadiya takar6a cike da mamaki tace ranki yadad’e gimbiya zarah ko gimbiya sumayya?
Harara sultana tawurga mata cikin fad’a tace zarah nace miki ko sumayya?
Jikin jakadiya yana rawa tace kigafarce ranki yadad’e gimbiya zarah zan kaimawa Allah yahuci zuciyanki.
K’ofa sultana sadiya tanuna mata, cikin sauri jakadiya tad’auki kulan tafito.
A chan 6angaren zarah bayan sultana sadiya ta tafi komawa tayi saman cushin tazauna tare da dafe kanta mamakin sultana sadiya duk ya kamata dan yau ne karo nafarko da tafara ganin fara’arta, tunowa tayi da duk wulak’ancin da take yi mata a baya, murmushi zarah tayi wanda ita kad’ai tasan ma’anarsa.
Jakadiya tafiya take ammah mamakine yacikata ahankali take furta miye had’in sultana sadiya da gimbiya zarah? Miyasa batace inkai ma gimbiya sumayya ba sai zarah? Anya ba wata k’ullalliya da matarnan take shiryawa?
Bari dai inje sai inji daga bakin gimbiya.
Lokacin da ta isa a parlour tasamu zarah zaune tana shan fruit salad, cike da girmamawa taduk’a tagaishe da zarah, cikin sakin fuska zarah ma tagaisheta tare da tambayarta su dada.
Murmushi Jakadiya tayi tace suna lafiya sannan tamik’a mata kular tace ranki yadad’e gashi daga sultana sadiya tace inkawo miki.
Murmushi zarah tayi batare da ta kar6a ba tace bud’e mugani.
Cikin sauri Jakadiya tabud’e, zarah lek’awa tayi tace ba laifi kwad’on ya min kyau saidai ba zan iya ciba.
Murmushi Jakadiya tayi tace ranki yadad’e wai miye tsakaninku dan nayi mamakin ganin ta bada kwad’o akawo miki.
Itama zarah murmushi tayi sannan takwashe komai tafad’a ma Jakadiya.
Jinjina kai Jakadiya tayi tace duk tak’are cikinki ne da taji ance kina da shi takeso taga bayansa.
Ta6e baki zarah tayi tace koma mekenen ta Allah ba tataba dan ni nafi k’arfinsu, ban yarda da kwad’on ba aje kawai azubar da shi a 6oye inda wani ba zai ganiba bare yaci.
Jakadiya tace angama ranki yadad’e, Allah yatsare mana ke.
Zarah jingine kanta tayi da kujera nan jakadiya tamik’e tafita tabar d’akin.
Bayan fitarta Zarah mik’ewa tayi tashiga bedroom d’inta, saman gadonta takwanta tana mamakin halin sumayya da mahaifiyarta, ji take da ace sumayya zata amince suyi zaman lafiya da zatayi farin ciki da hakan dan ita da zuciya d’aya take zaune da ita.
Tunowa tayi da gogon nata nan tayi murmushi dan ita kanta ta san tayi missing d’insa rabonta da shi kusan 3 day’s kenan, wayanta tad’auko talalubo number d’insa, lokacin yarima yana cikin duba patients d’insa ganin me kiransa yasa yamaida wayan silent yacigaba da aikinsa dan lokacin gab yake da yatashi yakoma gida.
Zarah ganin ta tsinke baiyi picking ba yasa ta aje wayar tare da maida idanuwanta tarufe dan tasamu tad’anyi bacci, ammah gefe guda ji take tana buk’atar son cin zogale da balango dan tunda taga wadda sultana sadiya ta aiko mata taji tana kwad’anta.
Mik’ewa tayi tafito parlour dan tasa asamo mata, daidai lokacin sumayya tashigo d’akin babu ko sallama.
Zarah tsaye tayi tana kallonta cike da mamaki dan sumayya had’e rai tayi sosai ba alamun fara’a a tare da ita daga gani kasan ba mutunci yakawotaba.
Ta6e baki zarah tayi tace haba baiwar Allah ya za’ayi kishigo min d’aki babu ko sallama saikace kin shigo d’akin arna.
Wata uwar harara sumayya tawurga mata cike da 6acin rai tace tunda gidan ubankine ai dole inyi sallama, ke ni nan bai min kama da d’akiba sai dai kongo dan haka ank’i ayi sallamar banza matsiyaciya, kuma cikin da kike tak’ama da shi indai ina numfashi bazaki ta6a haifesaba ke gidannan ma dole kibarsa dan yarima ba ajin aurenki bane, ni banga abinda yagani a jikinkiba har ya amince ya aureki, banza ‘yar matsiyata.
Murmushi zarah tayi cikin rashin damuwa tace sumayya ni yanzu banada lokacinki abinda yake kaina ya isheni, kuma ciki da kike magana Allah ne yabani baki isa kiyi min abinda Allah baiyi min ba.
Cikin k’araji sumayya tace kar kikuskura kiyi min gori dan wlh zansa kiyi nadamar da bakita6a yiba a rayuwarki, kinci sa’a ina rangwanta miki ammah wlh da tuni kinbar gidannan kuma cikine kirufa ki aje sai nayi silar zubar da shi.
Zarah shafa cikinta tayi tace malama kinfa dameni da haukanki, kifita kiban waje ko yanzu insa afitar min da ke.
Ta6e baki sumayya tayi tace duk yadda kikayi daidaine ammah inaso kisani ni sumayya na tsaneki, tsanarki bazata ta6a fita daga zuciyana har sai ranar da naga na cika burina, tana fad’in haka tajuya tafita daga d’akin a harzuk’e.
Zarah tsaye tayi tabita da kallo har ta fita, ahankali tafurta Allah yashiryeki sumayya.
Ringing d’in wayanta da tajiyo yasa cikin sauri takoma bedroom d’in tad’auko, ganin mai kiranta yasa tasaki murmushi tare da zama gefen gado saida tasaita nutsuwarta sannan tayi picking.
Gabad’ayansu shuru sukayi sai chan Zarah tayi sallama,
Daga chan 6angaren yarima amsa mata yayi.
Zarah murmushi tayi tace barka da hutawa, ya aiki?
Yarima saida yalumshe idonsa sannan ahankali yace Alhmdllh, y kk?
Cikin shagwa6a tace ina lafiya, saidai babynka da yake wahalar da ni.
Uhm sry, kawai yarima yace,
Zarah kamar zatayi kuka tace ni balango nakeson ci please katafo min da shi.
Yarima shuru yayi nad’an lokaci sannan yace yanzu duk nan gidan ace kin rasa naman da zakici, kuma baki iya sawa ayi miki?
Zarah kukan shagwa6a tasanya sai tace ni wlh nasiye nakeson ci na nan banason k’amshinsa.
Yarima jin kukan nata yake har cikin ransa dan duk ta kashe masa jiki, ahankali kamar mai jin bacci yace toh shikenan zan tafo miki da shi, kukan ya isa.
Zarah tsagaitawa tayi daga kukan da take tace toh nagode please kahad’o min da shawarma, sai kadawo.
Yarima tsinke wayar yayi tare da dafe kansa yana tunanin ta yadda zai fara tsayawa wajen me nama siyan nama, tsaki yaja nan yajanyo wayarsa yakira d’aya daga cikin yaransa yace yaje yasiyo mai balango mai dad’i da shawarma.
Yana gama wayan yamik’e yad’auki key d’in motansa yafito yanufi gida.
Zarah bayan sungama wayar dariya tayi sannan tatashi tashiga wanka.
Bayan ta fito simple makeup tayi nan tashirya cikin gown d’inta maikyau. Saida tayi sallah sannan tajanyo wayarta takira su mama dan sugaisa, hira sukayi sosai nan mama take shaida mata jibi za’ayi baikon Aysha da malam bello, Zarah murna tayi sosai dan har cikin ranta taji dad’in hakan dan tasan malam bello zai kular mata da k’anwarta, nan tace insha Allahu zata shigo ranar, bayan sun gama waya da mama takira Aysha sukasha waya tana tsokanarta daga nan kuma tasa taba yaya rauda wayar nan ma sukaita hirarsu sun dad’e suna hira sannan sukayi sallama.
Mik’ewa Zarah tayi tad’auko veil d’in gown d’in, a gaban dreesing mirrow tatsaya tatufke kanta tayi kamar gambo sannan tayi rolling d’in k’aramin veil d’in nata nan tayi gwanin kyau, tafito tanufi part d’in yarima dan tasan indai ba ita tajeba toh mawuyacine yakawo mata dakansa.
A parlour tasamesa zaune yana waya, gefensa sumayya ce sai wannan cika take tana batsewa, ganin zarah yasa tawurga mata harara tace malama lafiya zaki shigo ma mutane?
Murmushi zarah tayi tace malama ba fa wajenki nazoba.
Yarima da yake waya juyowa yayi yazuba mata ido, itama Zarah kallonsa tayi tasakar mai murmushi, muryar sumayya taji ta ce kedai wlh ban san wace irin natatta bace ke kullum kina manne da mutum, ta6e baki zarah tayi tace kanki akeji.
Yarima kashe wayar yayi batare da ya kallesuba yace kudai bakuda aiki sai fad’a.
Sumayya kwantar da kanta tayi a kafad’ansa tace dear itace tawani shigo ma mutane dan neman fad’a…tak’arashe maganar tare da wurga ma zarah harara.
Zarah murmushin mugunta tayi mata sannan ta ida isa gefen Yarima tazauna 6ata fuska tayi kamar zatayi kuka tace baby nifa zuwa kawai nayi inkar6i abinda nace kasiyo min wlh yunwa nakeji babynku yana wahalar da ni yau, janyo hannunsa tayi tad’aura saman cikinta tace baby kaji motsi yakemin….tak’arashe maganar tare da kashe mai ido d’aya.
Yarima janye idonsa yayi daga kallonta tare da safke ajiyar zuciya ahankali yace bari inkirasa.
Sumayya cikin 6acin rai tace babbar bura’uba ke wa zakiyi nuna ma duniyanci? Wlh baki isaba kanki farau cikine?
Zarah murmushi tayi tace sorry Auntyna wlh ba kaina farauba kawai dai ina buk’atar ci ne,
Yarima mik’ewa yayi tare da yin dialing d’in number d’in yaron nasa yana shirin kira, knocking d’in k’ofa da akayine yasa yabada izini ashigo.
‘Daya daga cikin guards d’insane yashigo d’auke da leda d’an rissinawa yayi yace ranka yadad’e sak’one aka kawo maka.
Kar6a Yarima yayi batare da yayi magana ba, nan guard d’in yajuya yafita.
Yarima juyowa yayi ya kallesu duk sunci face, yanayin yadda sukayi ya so yabashi dariya, tsaye yayi da ledar sai chan yabud’e yaduba ganin kashi biyu ne yasa yad’auki kashi d’aya yamik’a ma sumayya yace ga naki.
Yamitsa fuska sumayya tayi tace duk naman da yake gidannan sai ansiyo na waje, ni gaskiya bazan iya ciba.
Ta d’auka yarima zai lallasheta kawai sai gani tayi ya mik’a ma zarah duka ledar yace gashinan.
Kar6a zarah tayi tare da yin murmushi tace nagode sosai baby, nan tamik’e tare da kallon sumayya da tacika tayi fam tace Aunty sumy kiyi hak’uri idan na 6ata miki sai anjima, tana fad’in haka tajuya tafita tabar d’akin.
Yarima komawa yayi yazauna tare da d’auko remote yana canza channel, sumayya kallonsa tayi tace yarima kana ganin abinda yarinyarnan take min ammah baka iya yi mata magana.
Wani irin kallo yawurga mata kamar ba zaiyi maganaba sai kuma chan yace sumayya akan me zanyi magana bayan a da tana baki girmanki kece dai kikak’i kirik’e girman naki kinga kenan laifin nakine dan haka in zaki gyara toh kigyara.
Sumayya haushine yakamata gani take kamar ya goyi bayan zarah, yamutsa fuska tayi tace ya dai kamata kadinga adalci a tsakaninmu dan mu dukanmu matankane kuma ita d’in da kake ma rawan kai ai…….wata irin harara da yawurga matane yasa tayi shuru batare da ta k’arashe maganartaba,
Cigaba yayi da kallonsa inda Sumayya tamik’e cike da jin haushi taficce tabar d’akin.
Cikin rashin damuwa yarima yayi kwanciyarsa saman kujerar, dan shi yanzu halayyar Sumayya har ta daina bashi mamaki.
A chan 6angaren sultana sadiya koda jakadiya tadawo mata da kular tambayarta tayi zarah ta ci kwad’on? Jakadiya saida taduk’ar da kanta k’asa cike da girmamawa sannan tace eh ranki yadad’e dan dukansa tacinye ta ce tana godia sosai.
Murmushin jin dad’i sultana tayi sannan tace kai haba toh menene abun godia a ciki? Ai taimakon kai ne, yanzu zaki iya tafiya.
K’ara duk’awa jakadiya tayi tace toh ranki yadad’e atashi lafiya, tana fad’in haka ta tashi cikin sauri tabar d’akin.
Bayan ta fita sultana k’yalk’yalewa tayi da wata irin dariya tace yarinya bakisan wacece ni ba wayace miki koda da second d’aya zan iya sonki? Kallon agogon da take manne ga bangon d’akin tayi sannan tace nan da minti talatin cikinki zai tashi aiki, tana fad’in haka tayi murmushin mugunta sannan tajanyo wayarta takira sumayya nan tafad’a mata komai.
Sumayya murna tayi sosai har da ‘yar taka rawarta nan tanemi 6acin ranta tarasa.
Yau ko da taje d’akin yarima da dare shi kansa saida yayi mamakin ganinta cikin farin ciki bai dai tambayetaba yashareta yai kwanciyarsa haka tazo bayansa takwanta yanajinta tarungumesa nan yamaida idanuwansa yalumshe ahaka bacci yai awon gaba da su.
Da safe sumayya sa wata kuyangarta tayi takular mata da duk wani motsin zarah dan ta yi tunanin za’a fito da ita aje asibiti ammah da mamakinta har wajen 10am ammah shuru dan haka tashirya da kanta tanufi part d’in zarah dan tagane ma idonta abinda yake faruwa, cikin ranta tace ina ma insameta kwance tana fama da ciwo, murmushine yakubce mata tace Allah yasa haka, daidai lokacin tad’aga labulen d’akin zarah tashiga, curus taja bakin k’ofa tatsaya ganin zarah da tayi zaune saman lallausan carpet d’in da yake shimfid’e a tsakiyan parlourn hannunta rik’e da waya tana dannawa da ka ganta kasan tana cikin k’oshin lafiya.
‘Dago kai zarah tayi takalleta tare da sakar mata murmushi sannan tace sannu da zuwa Aunty sumy, kishigo man.
Ta6e baki sumayya tayi cike da mamaki tace bashi yakawoni ba.
Zarah ma kallonta takeyi tace toh me yakawoki?
Cikin nuna isa sumayya tace wannan ba matsalarki bace malama saidai inaso ink’ara tunatar miki akan mijina babu abinda ban iyayi, dan haka a kowane lokaci kisaurareni, tana fad’in haka tajuya tafita tabar d’akin.
Zarah binta tayi da kallo har tafita sannan tayi murmushi tace Allah yashiryaki sumayya, A kullum ba zan ta6a yin k’asa da gwiwaba wajen addu’a Allah yakareni daga dukkan sharrinku.
Sumayya tana fita bata zarce ko’inaba sai part d’inta a parlour tayada zango tashiga zagaye d’akin cike da tashin hankali nan takira wayan ummanta.
Ummah tana d’aga wayan sumayya tace ummah na shiga ukku wlh waccan matsiyaciyar tana nan lafiya lau babu abinda yasameta anya kuwa ummah kin zuba mata?
A firgice sultana sadiya tace sumayya me kikace? Tana nan lafiya lau fa kikace kai ba zan ta6a yaddaba.
Gimbiya sumayya kamar tafashe da kuka tace wlh ummah tana nan babu abinda yasameta ummah gaskiya cutarki akayi ba maganin zubar da ciki bane aka baki.
Cike da jin haushi ummah tace ke gidanku sumayya da me zanji da rashin zubewar cikin ko da banzar maganarki marar amfani, ni babu wanda yacuceni wannan maganin na sanshi kuma nasan nazubar da cikine dan da anyi amfani da shi ba’ayin rabin awa sai ciki ya fita , toh inhakane ya akayi cikin nata bai zubeba?
Shuru ummah tayi tana nazari sai chan tace kenan hakan yana nufin zarah bataci k’wad’onba? Tabbas bataciba.
Sumayya cike da mamaki tace ummah kina nufin bata ciba? Toh ko tasan k’ullalliyar da kikayi matane?
Ummah girgiza kai tayi kamar tana a gaban sumayya, tace batasan komai ba akan haka saidai idan wani dalili yahanata ci.
Toh fa ummah yanzu ya za’ayi wlh banason cikinnan nata kokad’an…sumayya tak’arashe maganarta cikin kuka.
Ajiyar zuciya sultana sadiya tayi tace kidaina kuka sumayya kikwantar da hankalinki yau zansa ashirya mata wani kwad’on ni zanje da kaina inkai mata taci.
Sumayya fashewa tayi da dariya kamar ba ita bace take kuka cike da jin dad’i tace ummah hakan kawai za’ayi gaskiya da kin gama min komai dan ni yanzu wlh cikinta ya fi aurenta da yarima d’agamin hankali.
Hmm duka dai da matsala sumayya ammah dasannu zamu magance komai.
Sumayya cikin jin dad’i tace Allah yabar min ke ummana.
Dariya sultana sadiya tayi tace Ameen shalelena yanzu dai bari inje inyi abinda yadace.
Toh ummana sai najiki, nan sukayi sallama kowa yakashe wayarsa.
Sultana sadiya k’wala ma d’aya daga cikin kuyanginta kira tayi, cikin sauri tashigo jikinta yana rawa taduk’a cikin girmamawa tace ranki yadad’e na amsa kiranki.
Yamitsa fuska sultana sadiya tayi sannan tace kije kisami baiwata sabura kice nace yanzu tahad’amin kwad’on zogale yaji kayan had’i sai takawo min nan ina jiranta.
Kuyangar tace toh ranki yadad’e angama, cikin sauri tamik’e tafita tabar d’akin.
Sultana sadiya maida kanta tayi ta jingine ga kujerar da take tana murmushin mugunta.
_Comment_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja’art✍_
_*YARIMA SUHAIL*_
_*Written By~Sis Nerja’art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔
_Masha Allah my friendy *Sadiya Sidi S* Ina tayaki murnar fara sabon novel d’inki mai taken *RAYUWAR MATA* yadda kika fara lafiya Allah yasa kigama lafiya, Allah yabamu ikon d’aukan darasin da yake cikinsa, kurakuren da suke ciki Allah yayafe miki, I hrt u over dear_