Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 48

Sponsored Links

PAGE* 4⃣8⃣

Sultana sadiya dak’yar tasamu tad’an tsaida nutsuwarta sannan tad’an yi d’an murmushi mai kama da yak’e tace ranki yadad’e ya akayi kikasan cikine da ita kuma an tabbata shi d’inne?

Murmushi dada tayi sannan tace tabbas cikine da ita dan rannan k’arnin kifi kawai taji ammah saida tayi amai ke ko yanayinta zaki kallah sai kin gane hakan kuma ko jiya da yarima yazo gaisheni saida namatsa mai da tambaya sannan yafad’amin ashe cikin har ya kai tsawon wata hud’u, kinsan halin yarima ba komai yake fad’aba.

Sultana sadiya saida gabanta yayi wani irin fad’uwa, cikin zuciyanta tace wata hud’u??? batasan lokacin da tace hmm ai yarima ya iya munafunci.
Ganin yadda sultana bilkisu da dada suka zuba mata ido yasa tayi murmushi tace ya za’ayi ni a matsayina na mahaifiyarsa yak’i fad’amin, ai ya kamata tasamu kulawa sosai a wajenmu tunda mune matsayin dangi yanzu a wajenta saboda da mu take zaune.

Dada murmushi tayi tace tabbas maganarki gaskiya ce koda munso ace sumayya ce tafara haihuwa ammah bakomai tunda haka Allah yak’addara kuma dukkansu d’ayane tunda duk matansane,

Sultana sadiya cikin rashin nuna damuwa tace ai d’a nakowane da zarah da sumayya duk d’ayane a wajena.

Murmushi sultana bilkisu tayi tace nima haka ina sa rai nan ba da dad’ewaba my dota nima tahaifo mana baby.

Dariya sultana sadiya tayi sannan tace saidai daga baya dan mu nan ba da dad’ewaba zamu amshi jika.

Eh munji babu komai muma namu insha Allahu yana nan zuwa.

Dada ido tazuba musu cikin jin dad’i sannan tace Allah yakawo masu albarka.

Gabad’ayansu suka amsa da Ameen.

Mik’ewa sultana sadiya tayi tana murmushi tace ranki yadad’e zan wuce akwai bak’uwa da zanyi yanzu hakama ina sa ran ta iso, insha Allahu zan je induba jikin my daughter.

Cikin jin dad’i dada tace toh bakomai.
Sultana bilkisu tace sai anjima sultana.

‘Dan rissinawa sultana sadiya tayi sannan tace na barku lafiya, tana fad’in haka tajuya tafita.

Nan sultana bilkisu da dada suka cigaba da hirarsu, saida maraice yayi sannan sultana bilkisu tayi ma dada sallama takoma part d’insu cike da farin ciki akan cikin zarah.

A 6angaren sultana sadiya ko da tafita bak’in cikine yatokare mata mak’ogwaro, takaici duk yacikata ita kanta ta yi mamakin yadda akayi ta iya danne bak’in cikinta a gaban su dada.

Ko da ta isa part d’inta a parlour tayada zango nan tashiga kaiwa da kawowa ahankali take furta na shiga ukku ya akayi wata daga zuwanta tariga d’iyata samun ciki, kai da sake dole ne inbi ta kowace hanya wajen ganin na zubar da shi, taya wata d’iyar talakka zata fara aje jika a masarautar nan? Ba dai hakan yana nufin plan d’in da nashirya ya rugujeba? Inaaaa hakan ba zai ta6a yuwuwaba wlh, Tsanar zarah sa yarima ne taji ya k’aru a cikin zuciyanta.

Cike da 6acin rai tajanyo wayarta takira sumayya, sumayya na yin picking sultana sadiya cikin d’aga murya tace ke kina ina?
Daga chan 6angaren gimbiya sumayya tace ummah lafiya naji ki haka? Ina gida.
dan ubanki kizo yanzu kisameni ina jiranki.
Sumayya cike da mamakin mahaifiyartata tace toh ummah,
Sultana sadiya bata k’ara magana ba ta kashe wayar tare da wulli da ita saman cushin.

Daga chan 6angaren sumayya da mamaki tabi wayar da kallo ahankali ta furta lafiya? Kiran me ummah take min haka cikin gaugawa? Ba abinda yafi d’aure mata kai sai jin yadda ummah tayi mata magana cikin tsawa.
Ahankali tafurta Allah dai yasa lafiya, tana fad’in haka tamik’e tasaka alkyabbarta sannan tafito tanufi part d’in mahaifiyartata.

Ko da ta isa a tsaye tatarar da sultana sadiya tana zagaye d’akin tana cize le6e, cike da rud’ewa sumayya ta isa wajenta tace ummana lafiya me yake faruwa?
Ajiyar zuciya sultana sadiya tayi tace sumayya komai ma ya faru.
Cike da mamaki sumayya tace ummana ban fahimcekiba.
Taya zaki fahimceni sumayya bayan kinyi wasa da damarki? Toh gashinan abinda nake guje miki ya faru…”sultana sadiya tafad’i hakan cikin d’aga murya”
Sumayya tsaye tayi tana kallon ummanta cikin rashin fahimtar inda tadosa.
Sultana sadiya ajiyar zuciya tayi tace sumayya kishiyarki tana d’auke da cikin yarima na tsawon wata hud’u.

Wani irin fad’uwan gaba yaziyarci sumayya tsaye tayi cak tana jin abun kamar a mafarki, chan sai ta k’yalk’yale da dariya tace ummah ciki kuma tsawon wata hud’u? Kina nufin zata haihu da yarimana? Chan kuma sai ta fasa k’ara tare da furta wlh k’aryane hakan ba zai ta6a faruwaba.
Kallon ummah tayi tafashe da kuka tace ummana wlh ban yardaba babu yadda za’ayi inbar wacchan matsiyaciyar tahaihu da yarimana ummah wlh sai na kasheta saidai nima a kasheni.

Sultana sadiya jin d’iyartata tana surutai cikin d’aga murya gudun kar ajisu yasa tajanyo sumayya suka shige bedroom d’inta.

Suna shiga sumayya tafad’a jikinta tare da fashewa da kuka tace na shiga ukku ummana ya zanyi da rayuwata ummah na tsani yarinyar chan, ba zan ta6a yadda cin mutuncin da yarima yayi minba ace ‘yar talakkawa yayi ma ciki wlh ya munafunceni Allah ummah Sai na kasheta saidai shima yakasheni.

Sultana sadiya rungume d’iyartata tayi cike da tausayinta tace kidaina cewa haka sumayya kinga abinda daman nake guje miki yanzu gashinan kinyi wasa da damarki.

Sumayya cikin kuka tace ummana wlh ba zan ta6a yarda a zalunceniba inma haihuwarce ai ni yafi dacewa inyita.

Sultana sadiya rik’ota tayi sukaje bakin gado suka zauna cike da tausayi tace sumayya kiyi shuru hakanan muyi magana.

Sumayya share hawayen fuskarta tayi nan tazuba ma umman ido.

Sultana sadiya tace yauwa ko kefa, yanzu dai da farko inaso kikwantar da hankalinki kinutsu kar kice zaki kawo tashin hankali a gidan aurenki dan kinsan wannan mijinnaki ba zai d’auki hakan ba, sannan indai kinsan kina planning toh kidaina kisamu kema cikin nan kiyi sa, inyaso ita zarah kibarni da ita nasan yadda zan 6ollo ma lamarin.

Sumayya tace ummah toh cikin nata fa?

Tsiyata da ke Sumayya wani lokacin baki ganewa, tunda dai nace kibarni da ita ai nasan abinda zanyi, na dai fad’a miki kar kikuskura kice zakiyi mata wani abu da kanki.

Sumayya tace toh ummah.
Yauwa kokefa.
Murmushi kawai Sumayya tayi batare da tace komai ba.

 

A 6angaren sultana bilkisu kuwa koda takoma 6angaren su a bedroom d’in sultan Ahmad tayada zango lokacin yana zaune yana duba wata newspaper,

Bud’e k’ofan da tayi tashigo yasa yad’aga kai yakalleta ganin yadda taketa fara’a yasa ya aje newspaper d’in tare da yin murmushi yace da alamu yau matartawa tana cikin farin ciki.

Sultana bilkisu Ida k’arasowa tayi wajensa tazauna fuskarta d’auke da fara’a tace tabbas ranka yadad’e ka yi gaskiya domin yau ina cikin wani irin farin ciki.

Rik’o hannunta yayi yace toh nima afad’amin farin cikin da ake nima intaya.

Sultana bilkisu murmushi tasakar masa sannan tace ranka yadad’e mun kusan samun jika.

Jika fa kikace?

Eh ranka yadad’e, tabbas auren zarah da yarima akwai alkhairi a cikinsa, my son ya kusan zama daddy.

Sultan Abbas kasa 6oye farin cikinsa yayi yace Alhmdllh Allah abun godia, gaskiya naji dad’i kuma nayi farin ciki dan arayuwata inason ganin jinin yarima,

Dariyar jin dad’i sultana bilkisu tayi tace was yaga yarima da d’a.

Shima sultan Dariyar yayi yace Allah dai yasafke lfy, Allah yakawo masu albarka.

Ummi cikin jin dad’i tace Ameen farin cikina.
Gabad’ayansu suka sakarma juna murmushi, jin kiran sallar magrib ne da aka fara yasa suka mik’e, sultan Ahmad yayi alwallah yawuce masallaci.

 

Sumayya ko da takoma 6angarensu bedroom d’inta tashige tafad’a saman gado nan wani sabon kukan yakubce mata yi take babu k’ak’autawa tausayin kanta yakamata, saida tayi mai isarta sannan tajanyo waya takira zinat.

Zinat nayin picking babu ko sallama sumayya tace baby na shiga ukku.

Daga chan 6angaren zinat tace haba baby akan wane dalili zakice kin shiga ukku, me yake faruwa ne?

Sumayya fashewa tayi da kuka tace zinat dole ince haka domin ina cikin matsala bansan ya zanyi da rayuwataba.

Baby kinutsu kimin bayanin abinda yake faruwa kidaina kuka.

Sumayya tsagaitawa tayi da kukan da take tace zinat wannan bagidajiyar yarinyar daga zuwanta wai har ta samu ciki, wlh ba zan ta6a yarda ba.

Zinat cikin d’aga murya tace kina nufin wannan kishiyar taki?

Toh in ba itaba wa kike tunani ni wlh kasheta zanyi kowa yahuta inyaso nima daga baya akasheni.

Zinat ajiyar zuciya tayi tace kar kice haka baby kiyi hak’uri kijira zan shigo,
Har sai yaushe zaki shigo kina nufin inbari har sai ta haihu? Cewar sumayya
A’a baby ai very soon zan shigo, kijirani zuwa next month zan shigo wlh sai munyi silar zubar da cikin.

Sumayya tace toh zan gwada inga idan zan iya hak’uri har sai kin shigo.

Zaki ma iya baby, yanzu dai nidai burina kikwantar da hankalinki kar kije ki aikata abinda zai je yadawo.

Hmm baby kenan kidaina maganar kwanciyar hankali dan ayanzu hankali ya gama kwanciya kawai dai sai anjima yanzu zan d’an huta.

tana fad’in haka bata jira jin komai daga wajen zinat ba takashe wayarta.

 

Mik’ewa tayi taje tawatsa ruwa tayi shirin bacci tahaye gadonta dan yau cewa tayi babu abinda zai kaita wajen yarima saidai yayi baccinsa shi kad’ai dan shi kansa haushinsa takeji,
duk yadda taso tayi baccin kasawa tayi kalmar cikin zarah yatsaya mata a rai duk yadda taso tayi bacci kasawa tayi daga k’arshe saida tasha maganin bacci sannan tasamu bacci yayi awon gaba da ita.

 

_*Washe gari*_

Wajen 12 zarah zaune take saman cushin hannunta rik’e da waya tana chart sallamar da taji anyine yasa ta amsa tare da d’ago kai takalli mai sallamar, da mamaki take kallon sultana sadiya da take sakar mata murmushi, cikin sauri zarah tamik’e tsaye fuskarta itama d’auke da murmushi tace sannu da zuwa ummah.

Yauwa d’iyata, a’ah kice jiki ya warware, cewar sultana sadiya.

Zarah cikin Jin kunya tace bismillah ummah kizauna.
Zama sultana sadiya tayi har a lokacin fuskarta tana kan zarah, cike da jin kunya zarah tazauna k’asa tace ummah ina wuni?
Lafiya lou dafatan kina Lafiya, ya k’arfin jikin naki.
Cikin jin kunya zarah tace ummah ai na warke,
toh masha Allah, Allah yak’ara sauk’i, ai ba a fad’amin bakida lafiya ba sai jiya naji wajen dada.

Zarah shuru tayi tana wasa da yatsun hannunta tana murmushi, ahankali tamik’e tace ummah bari inkawo miki ruwa.
Murmushi sultana sadiya tayi tace kibarsa kawai saikace wata bak’uwa.

Wucewa zarah tayi tace ummah bari dai inkawo miki, sultana sadiya binta tayi da wani irin kallo har tashige kitchen, ahankali tafurta tabbas yarinyar nan cikine da ita.

Zarah ko da tashiga kitchen dafe k’irjinta tayi tare da safke ajiyar zuciya dan ta tsorata sosai da fari da taga ta shigo sai daga baya da taga ba da wata manufar tazoba sannan taji dad’i, ahankali tafurta Allah yasa umman sumayya ta shiryu.

 

Nan tacigaba da had’a mata kayan marmari da drinks kala-kala a saman tray ta d’aura tad’auko tafito.
A gaban sultana sadiya ta aje tace ummah kifara da wannan kafin ingirka miki abinci.

Murmushi sultana sadiya tayi tace a’a zarah keda bakida lafiya kibarsa kawai dan ni nan a k’oshe nake,
Zarah ruwan inibi tatsiyaya a cup tamik’a mata tace ummah toh ko yayane kisa albarka.

Kar6a sultana sadiya tayi tana murmushi tace nagode zarah, kur6a d’aya tayi ta aje sannan tace zarah kiyi hak’uri akan abinda nayi miki wlh sai daga baya nagane hakan ba daidai bane,

Murmushi zarah tayi tare da d’ago kai takalleta tace ummah bakimin komai ba wlh dan ke matsayin uwa kike a wajena.

Nagode sosai zarah, Allah yaimiki Albarka, Allah yasafkeki lafiya.

Zarah kasa amsa mata tayi saboda wata irin kunya da tarufeta.

Mik’ewa sultana sadiya tayi tace toh ni zan wuce.

Ummah tun yanzu?

Haba zarah me zan zauna inyi ni da nake matsayin suruka, yanzu dai indai kinsan kina buk’atar wani abu kidinga aikawa ana fad’amin insha Allahu ni kuma zan samo miki koma menene, yanzu haka ga zogale chan nasa ana dafawa na baro sun kusan gamawa, Indai angama zan aiko miki da ita nasan zakiso cinta..

Murmushi zarah tayi cikin jin dad’i tace toh ummah nagode.

Haba minene abun godia ai keda sumayya duk d’aya nad’aukeku, zansa a ma k’wad’a miki da k’uli-kul’i dan akwai wata baiwata data iya irin wad’annan k’wad’on masu dad’i ita zansa tayi miki.

Zarah duk’ar dakanta tayi tace nagode sosai ummah, Allah yak’ara girma da d’aukaka.

Sultana sadiya tace Ameen sai na aikon, tana fad’in haka tawuce nan zarah tarakata har wajen part d’inta tare da k’ara yi mata godia.

Sultana sadiya tace bakomai, nan tawuce cike da farin ciki dan ta san tarkonta ya kama kurciya…

 

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

 

_Masha Allah my dota *hafnan* Ina tayaki murnar kammala novel d’inki maisuna *FATALWAR MIJINA* hak’ik’a kin zuba basira sannan kin koyar da darasi a cikinsa gaskiya salon novel d’in ya burgeni, Allah yabaki ladar abinda kika fad’a daidai kurakuren da suke ciki Allah yayafe miki, ur mommo love you more_

 

_~Masoya sak’onku yana isowa agareni ina godia sosai Allah yabar k’auna, mutanen katsina ku ma sak’onku ya iso agareni nagode sosai nima ina gaisheku~_

 

Back to top button