Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 51

Sponsored Links

PAGE* 5⃣1⃣

Zarah tana fitowa nan kuyanginta suka take mata baya har cikin gidansu, Zarah dagudu ta isa wajensu mama da suke zaune suna ‘yan soye-soye, jikinmama tafad’a tace cikin murna tace oyoyoo mamana.

Mama ma rungumeta tayi cikin jin dad’i tace oyoyoo Zarah na.

Yaya rauda kallon Zarah tayi tace ikon Allah kedai har yanzu baki girmaba.

Zarah turo baki tayi cikin shagwa6a tace yaya rauda na fa kwana biyu banga mamanaba, mama janye Zarah tayi daga jikinta tace rabu da ita zarahna,

Daidai lokacin kuyangin zarah suka iso suka duk’a cikin girmamawa suka gaishe da su mama
Cikin sakin fuska su mama suka amsa musu tare da tambayarsu gida sukace Alhmdllh, kallonsu zarah tayi tace zaku iya tafiya amaidaku gida, duk’awa sukayi sukace to ranki yadad’e angama, mama leda tasamu tak’ulla musu su donut tabasu, nan sukayi sallama da su mama sannan suka mike suka tafi.

Zarah kallon mama tayi da tazuba mata ido, murmushi Zarah tayi tare da duk’awa tagaishe da ita.

Mama amsa mata tayi cikin sakin fuska tare da tambayarta mijinta da mutanen gida
Zarah cikin jin kunya tace duk suna lafiya mama.

Juyowa tayi tana dariya tace yaya rauda ina kwana? Harararta yaya rauda tayi tace yanzu k’arfe sha biyu zaki kira mana kwana.

Afuwan yaya rauda ina wuni?
Murmushi yaya rauda tayi tace lfy lou ya gidan?
Zarah tace Alhmdllh komai daidai.

Sai a lokacin zarah taji k’amshin soyen ya daki hancinta, yamitsa fuska tayi jin zuciyanta yana shirin tashi tace wai banga amaryaba,

Mama tace tana nan d’aki tana k’ullah kunun aya, cikin jin dad’i zarah tace wow bari inje insha har na ji ina son sha, cikin sauri tawuce tanufi d’akin.

Mama da yaya rauda binta sukayi da kallo cike da sha’awa dan ko ba’a fad’a musuba sunsan zarah cikine da ita.

Tana shiga d’akin taja tatsaya, Aysha da take zaune tana k’ullin kunun aya ganinta yasa tataso dagudu tarungumeta tana oyoyoo Aunty zarah, zarah ma dariya tayi tace ke zaki karyani ni sakanni,

Aysha janye jikinta tayi tana dariya tare da zuba ma zarah ido tace Auntyna kinga yadda kika koma kamar ba keba

Murmushi zarah tayi tace ke banson tsokana, amaryarmu ya shirye-shiryen bikki? Allah yasa kar asa mana bikkin nesa.

Dariya Aysha tayi tace wlh Aunty zarah nima addu’an da nake kenan.

Da mamaki zarah takalleta tace lallai Aysha ashe bakida kunya toh Allah yakyauta,,,,tana fad’in haka tawuce tanufi wajen kunun ayan tabar Aysha tana ta dariya.

Zarah zubawa tayi sosai tasha har saida taji ta k’oshi sannan tabarshi.

Duk yadda taso tataya su mama girki kasawa tayi saboda k’amshin tayarmata da zuciya yake, dole tahak’ura tayi zamanta.

Abbah ma koda yadawo ya yi murna sosai da ganin ‘yar tasa.

Wajen k’arfe ukku ‘yan neman aure sukazo anmusu tarbar mutunci, inda aka tsaida maganar akan nan da watanni hud’u masu zuwa.

Sun kawo su biscuits su alewa bakin gwalgwado sun bada sai kud’in nagani inaso da na neman aure.

 

ko da abbah yazo musu da labarin su mama sunyi murna sosai nan sukaita fatan alkhairi.

Nan aka zauna aka k’ullah kayan aka d’ibi na dangi sannan aka aika mak’ota nasu.

Mama duk yadda taso zarah taci abinci k’iyawa tayi daga k’arshe saidai tabada aka siyo mata awara nan tazauna taci.

 

Bayan sallar isha’i suna zaune suna hira zarah handbag d’inta tabud’e tad’auko dubu d’ari biyu tamik’a ma abbah tace gashinan Abbah ko kayan kitchen anfara siya mata.

Abbah girgiza kai yayi yace a’a zarah akwai kud’i hannuna dan na ware wanda zan cika incanza mana gida, kud’in da suka rage ne nasamu nabud’e shago ina kasuwanci dasu nakeso inmata siyayyarta.

Zarah cikin jin dad’i tace hakane Abbah ammah dan Allah kataimaka ka amsa kuk’ara sai asamin albarka.

Kar6a yayi nan sukaita sa mata albarka.

Aysha da take cikin d’aki tana waya fitowa tayi takalli zarah tana murmushi tace Aunty zarah kizo kugaisa da malam bello yana nan k’ofan gida.

Zarah girgiza kai tayi tace a’a Aysha kinga ban tambayaba, marairaicewa Aysha tayi tace iyakarki fa zaure nan zaku gaisa,,,tafad’i haka tare da mik’ama zarah gyalenta.

Zarah kar6a tayi tayafa ba dan tasoba tamik’e tabi bayan Aysha.

Daga waje suka hangosa tsaye zarah wajen k’ofar gidansu tatsaya, malam bello kallo d’aya yaimata yad’auke kai fuskarsa d’auke da murmushi yak’araso wajen da suke yana mai cewa a’ah ashe yayarmuce.

Murmushi zarah tayi tace malam ina wuni?
Lfy lou zarah ya gida da mai gidan.

Cikin jin kunya tace kowa yana lafiya, kallon Aysha tayi da taketa murmushi tace malam ga dai amanar k’anwatanan akularmin da ita.

Dariya malam bello yayi yace kar kidamu yayarmu insha Allahu zanyi iya bakin k’ok’arina.

Zarah cikin jin dad’i tace Allah yasa malam mungode sosai, Allah yakaimu lokacin.

Gabad’ayansu sukace Ameen.

 

Daidai lokacin motar yarima ta iso wajen da suke, yana yin parking saida gabansa yafad’i ganin zarah tsaye da wani, baima lura da Aysha ba datake gefe, suna had’a ido da zarah wata irin harara yawurga mata, zarah saida gabanta yafad’i cikin ranta tace nashiga ukku, dakewa tayi tataka ta isa inda yake fuskarta d’auke da murmushi tabud’e mai k’ofan tace sannu da zuwa.

yarima wani irin kallo yaimata yace wanene wancan kuke tare da shi?

Koda ta tsorata da hararar da yai mata ammah tadake tayi murmushi sannan tace mijin da Aysha zata aurane…shine dan bakida hankali kike tsaye da shi ke kad’ai kina ta yimai dariya?

Zarah da mamaki takallesa tace bafa ni kad’ai bace baga Aysha chan ba.

Sai a lokacin idonsa yakai ga su Aysha dasuke tafowa inda suke, ajiyar zuciya yasafke sannan yafito daga motar daidai lokacin su Aysha suka iso wajen da suke,

malam bello cikin girmamawa yarussina zai gaishe da yarima.

Cikin sauri yarima yarik’o hannunsa sukayi nusabaha fuskarsa a sake yace Allah yasa alkhairi ango,
Malam bello duk’ar da kansa yayi cikin girmamawa yace Ameen ranka yadad’e nagode,
Aysha ce tace yayana ina wuni?

Kallonta yayi fuskarsa a sake yace k’anwata kin wuni lafiya? Sai mukaji labari, Allah yasa alkhairi,

Aysha cikin jin kunya tarufe fuskarta, malam bello ne kawai ya amsa da Ameen.

Dariya zarah tayi tace magulmaciya kawai.
Yarima kallon zarah yayi yace menene kuma abun gulma? Daga tana jin kunyan yayanta.

zarah fari taimashi da ido.
Yarima janye idonsa yayi daga kallonta yace k’anwata bari mushiga ciki ingaishe da su abbah.

Aysha murmushi tayi tace toh yayana afito lafiya.

Zarah jerawa sukayi da Yarima suka shiga gida inda sukabar malam bello da Aysha suna ta hirarsu.

Koda sukazo shiga yarima ja yayi yatsaya, zarah kallonsa tayi tana shirin yin magana yace muje mana.

Zarah murmushi tayi sannan tawuce gaba yarima yabi bayanta har suka shiga cikin gida, har a lokacin su mama suna zaune tsakar gida, zarah tabarma tad’auko tashimfid’a mashi yazauna cike da girmamawa yagaishe da su abbah,

Fara’a bayyane a fuskarsu suka amsa mashi tare da tambayarsa mutanen gida, yarima saddar da kansa yayi k’asa yace Alhmdllh, Ya hidima?

Alhmdllh,,cewar su abbah.
Masha Allah, Allah yasa alkhairi, Allah yakaimu lokacin.

Cikin jin dad’i suka amsa da Ameen y rabb.

Yaya rauda kallonsa tayi tace ranka yadad’e barka da dare.

Murmushi yarima yayi yace yayarmu anwuni lfy?

Yaya rauda tace lafiya lou Alhmdllh, y hak’uri da mu?

Murmushi kawai yarima yayi.

Zarah mik’ewa tayi taje tad’auko abinci takawo mai, ganin haka yasa su abbah suka tashi suka bashi wuri dan yasamu yaci.

Bayan su Abbah sun tashi zama tayi gefensa dan tazuba mai, kallonta yarima yayi yace kindai san bana cin abinci da dare.

Zarah ma 6ata fuska tayi takallesa kamar zatayi kuka tace abincin gidan namu ma bazakaciba?

Yarima kallon kunun ayan da takawo mai yayi yace zuba min wannan dai.

Toh tace sannan tatsiya mai a cup tamik’a mai, kar6a yayi yafara sha kad’an kad’an, wayarsa da ya aje gefe zarah tad’auka tana wasa da ita, yarima baice mata komai ba ahaka har yashanye, kallonsa tayi tace ko ak’ara ma?
Girgiza kai yarima yayi sannan yace kije kiyi ma su mama sallama kizo mutafi dare yakeyi.

Mik’ewa Zarah tayi, yarima kallonta yayi yace wai ke yau kin ma ci abinci?

Zarah yamitsa fuska tayi tace na dai ci awara.
Shuru yarima yayi baice komai ba,

wucewa tayi taje tasanar da su mama zasu tafi nan tafito tare da su mama,
Nan suka yi sallama suka fito daidai lokacin Aysha zata shigo gida, kallonsu tayi tace ba dai tafiya zakuyiba.

Yarima murmushi yayi yace ko mukwana?
Dariya Aysha tayi tace eh ranka yadad’e.

Zarah kallonta tayi tace ina angon har ya tafi?

Susa kai Aysha tayi cikin jin kunya tace uhm.

Dariya Zarah tayi nan Aysha tarakasu har wajen mota sukayi bankwana takoma gida.

 

Tunda suka fara tafiya tsit motar tayi, ahankali yarima yajuyo yakalli zarah da tajingine kanta a sit d’in da take zaune ta zuba ma waje d’aya ido kamar mai tunani, janye idonsa yayi daga killonta yacigaba da tuk’insa duk sai yaji babu dad’i yanayin da yaganta.

Ahankali yace akwai abinda kike buk’atane?

Zarah juyowa tayi takallesa taga ba ita yake kalloba idonsa yana a titi, shuru tayi tana kallonsa jin tayi shuru yasa yarima yad’an juyo yakalleta karaf suka had’a ido, zarah duk’ar da kanta tayi sannan tace ice cream nakeson sha.

Yarima janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace meyasa kikeson shan kayan sanyi, ya kamata kidaina tunda yanzu ba ke kad’ai bace.

Zarah 6ata fuska tayi kamar zatayi kuka tace toh.

Yarima saida yabiya yasiyo mata sannan suka wuce gida, yana yin parking Zarah tabud’e tafita, kallonta yarima yayi yace wannan fa wa zai kawo miki?

Murmushi Zarah tayi tace sorry mancewa nayi nan tad’auka sannan tawuce cikin gida.

Yarima ma fitowa yayi yawuce fada dan sugaisa da memartaba.

___________

A 6angaren sultana sadiya ranta a 6ace takoma part d’inta a parlour tatarar da sumayya zaune tana jiranta dan sumayya tunda taga shigar sultana part d’in zarah yasa tafito tazo turakar iyayenta dan tasamu labari wajen ummanta idan tadawo,, ganinta yasa sumayya tamik’e cikin murna tace ummana angama komai ko?

Kallonta sultana sadiya tayi tare da jan tsoki tace sumayya wanchan banzan mijin naki ya 6ata min duk wani plan nawa.

Sumayya a tsorace tadafe k’irji tace ummah kar dai kicemin asirinmu ya tonu?

Sultana sadiya zama tayi saman kujera cikin 6acin rai takwashe komai tafad’a ma sumayya duk abinda yafaru.

Sumayya ajiyar zuciya tayi sannan tace ummah wlh banji dad’in faruwar hakanba, yanzu saboda Allah ido zansa mata har tahaihu? Yanzu ita zata aje ma yarima magaji?,,,sumayya tafad’i haka tare da fashewa da kuka, cikin kuka takalli sultana sadiya da abun duniya yadameta tace ummah ko kid’au mataki ko kar kid’auka wlh ba zan ta6a barin zarah ba sai naga bayanta.

Sultana sadiya jawota tayi tazaunar da ita gefenta tace sumayya banaso kije kiyi abinda zai jawo abinda za’ayi da ansani,

Sumayya shigewa tayi jikin ummanta tana kuka tace ummah a kullum ina fad’a miki bandamu da abinda zai faruba indai burina ya cika.

Sultana sadiya d’ago kan sumayya tayi tana share mata hawaye tace kidaina cewa haka sumayya kibari abi komai a sannu, sumayya mik’ewa tayi tana ja da baya tace a yaushe duk za’ayi hakan bayan ta haihu? Girgiza kai tayi tace ummah kibarni kawai, tana fad’in haka tajuya tafita daga d’akin.

Sultana sadiya k’walah mata kira tashiga yi ammah ina sumayya tafiyarta tayi.

Dafe kanta sultana tayi tace wannan wace irin rayuwa ce?

 

Sumayya koda takoma part d’inta batabi ta kuyanginta da suke gaishetaba dagudu tashige bedroom d’inta tamaida tarufe, jingine kanta tayi da k’ofar tashiga rusa kuka, tana jin wayanta tana ringing tashare tacigaba da kukanta, daga k’arshe takoma saman gadonta takwanta nan tak’ara sautin kukanta saida taji kanta ya fara ciwo sannan tatsagaita kukan nata.

Wasa-Wasa ciwon kai da zazza6i suka rufeta haka tajanyo blanket tarufa ahaka tayi ta juyi har cikin dare sai daga baya bacci yayi awon gaba da ita.

Da safe ko da kuyangarta zabba’u tazo tayita knocking jin shuru yasa tatura k’ofan tashiga cikin sauri ta isa inda Sumayya take k’udundune da bargo tana rawan sanyi,

Kallonta zabba’u tayi a firgice tace ranki yadad’e mi yasameki?

Sumayya dakyar tabud’e baki muryarta na fita ahankali tace je kikira min yarima.

Cikin sauri zabba’u tamik’e tace toh ranki yadad’e.

Yarima zaune yake yana breakfast inda zarah take gefensa tana shan ruwan lipton wanda yasha kayan yaji, knocking d’in k’ofa akayi zarah kallon Yarima tayi da yature cup d’in tea d’insa gefe yamik’e saida yabaro dining area sannan yace yes,

Guards d’insane yabud’e yashigo saida yad’an russuna sannan yace ranka yadad’e gimbiya sumayya ce tayo aike,

Yarima saida yazauna saman cushin sannan yabashi izini yabarta tashigo.

Kuyanga zabba’u koda tashigo zubewa tayi k’asa takwashi gaisuwa wajen yarima, hannu kawai yarima yad’aga mata, zabba’u k’ara duk’an da kanta tayi tace ranka yadad’e daman gimbiya sumayya ce batada lafiya tana chan kwance yanzu haka ita ta aikoni inzo insanar da kai.

Zarah jin an ambaci sumayya batada lafiya yasa tamik’e tabaro dining area,
yarima nuni yayi mata alamun tatafi, zabba’u k’ara duk’awa tayi takwashi gaisuwa sannan tamik’e cikin sauri tabar d’akin.

Zarah kallon yarima tayi da yamik’e cike da jin tausayi tace meyake samunta?

Shima yarima kallonta yayi yace bari inje indubata, Zarah bayansa tabi tace muje tare.

Yarima baice komai ba nan suka fito suka nufi part d’in sumayya duk inda suka ratsa bayi da Kuyangi duk’awa suke suna kwasar gaisuwa,

ko da suka shiga parlournta nan ma kuyanginta suka zube suka gaishesu, hannu yarima yad’aga musu cikin sauri suka fita sukabar d’akin.

Bedroom d’inta suka nufa, nan Zarah tayi knocking d’in k’ofan, zabba’u da take tsugunne k’asa tana jera ma sumayya sannu, mik’ewa tayi taje tabud’e k’ofan ganin su yarima ne yasa cikin sauri taja gefe tare da d’an rissinawa tace ranka yadad’e sannunku da zuwa,

Yarima baibi takantaba yawuce yanufi wajen bed d’in sumayya, cikin sauri zabba’u tafita tabar d’akin.

Zarah ma bayansa tabi suka isa, sumayya d’ago kai tayi takalli yarima sai hawaye, daga gefen gadon yarima yazauna yace sumayya bakida lafiya? Meyake samunki.

Sumayya d’agowa tayi tarungume yarima tare da fashewa da kuka,
jikinta yaji da zafi ahankali yace zazza6i kike? Gyad’a mai kai tayi, sorry yace nan yashiga shafa bayanta.

Zarah da take tsaye kamar zatayi kuka saboda tausayi, cikin muryar tausai tace sannu Aunty sumayya ya jikin naki?

Sumayya cikin sauri tad’ago takalli Zarah dan kwata-kwata bata lura da itaba, duk ciwon da takeji ammah hakan baihata wurga ma Zarah hararaba sannan takoma jikin yarima talafe.

Tsaye Zarah tayi duk jikinta ya yi sanyi,

Yarima janyeta yayi daga jikinsa tare da maidata yakwantar yace bari inje ind’auko drugs kinji?.

Gyad’a mai kai sumayya tayi, mik’ewa yayi yakalli Zarah yace kisa ahad’a mata breakfast bari indawo.

Toh Zarah tace sannan takalli sumayya da taketa rawar zazza6i tace Aunty sumayya Allah yasauke.

Banza sumayya tayi takyaleta, Zarah bata damuba tawuce nan tasa kuyangin sumayya suka had’o mata breakfast takar6a tadawo bedroom d’in, a saman bedside ta aje sannan takalli sumayya tace intaimaka miki kitashi kiyi breakfast d’in?

Kallonta sumayya tayi cikin tsana tace ba ruwanki da ni malama.

Daidai lokacin yarima yadawo kallon Zarah yayi yace batayi breakfast d’inba?

d’aga kai kawai Zarah tayi batare da ta yi magana ba.

Yarima wucewa yayi yazauna gefen gadon yace sumayya kitashi kiyi breakfast sai kisha drugs.

Yamutsa fuska sumayya tayi tace na k’oshi, taimaka mata yarima yayi tatashi zaune yace kidaure kici ko kad’an ne.

Sumayya jikinsa tafad’a tace ni bana iya ci,
Kallon Zarah yayi da take tsaye yace zuba mata breakfast d’in.

Zarah toh tace sannan tazo tazuba chips cikin plate sannan tahad’a tea mai kauri tamik’a mai cup d’in.

kar6a yarima yayi sannan yace ma sumayya kidaure kisha ko kad’anne, sumayya ganin yadda yarima yake lalla6ata yasa ta amince zatasha dan tasan halinsa idan yaga tana haka zai iya shareta yayi tafiyarsa, haka tabud’e baki yashiga bata tanasha ahankali tana k’ara langwa6ewa saida yaga ta d’an sha nakirki sannan yabarta,

Kallon zarah yayi da take rik’e da plate d’in chips tana yamitsa fuska dan k’amshin ya fara isarta, ganin haka yasa yarima yakar6i plate d’in yad’aura saman bedside nan yad’auki fork yad’ibo yafara bata, kad’an taci nan yabata drugs d’in tasha.

Zarah cike da tausayi tace sannu Aunty sumayya, banza sumayya tayi tak’yaleta.
ganin haka yasa yarima yace sumayya tana miki magana fa.
Wani irin kallo tayi ma zarah sannan ciki-ciki tace yauwa.

Yarima ganin tana shirin komawa takwanta yace sumayya kitashi kid’an watsa ruwa ko kinji dad’in jikinki.

sumayya langwa6e kai tayi tace toh kataimaka min ban iya yi.

yarima kallon zarah yayi da take kallonsu, murmushi tasakar mai tace bari inje inhad’a mata ruwan wankan, bata jira jin abinda yarima zaiceba tamik’e tanufi toilet d’in sumayya.

yarima binta yayi da kallo har tashige sannan yamaida kallonsa ga sumayya da tatsaresa da ido ganin yadda yake bin zarah da kallo Wani irin takaici yacikata.

Ahankali yace akwai abinda kike buk’ata?
Girgiza kai kawai sumayya tayi, daidai lokacin zarah tafito daga toilet d’in kallon yarima tayi tace ga ruwan chan na had’a,
Yarima kallon sumayya yayi yace muje kiyi wankan.

Marairaice fuska tayi kamar zatayi kuka tace bana iya tashi jiri nakeji please kad’aukeni,,,tafad’i hakan tare da kallon zarah.

zarah d’auke kanta tayi kamar bataji abinda taceba.
Yarima shuru yayi kamar ba zaiyiba, zarah juyowa tayi takallesa nan suka had’a ido, cikin rashin damuwa tasakar mai murmushi , janye idonsa yayi daga kallonta babu yadda ya iya haka yad’auki sumayya yanufi toilet da ita.

 

zarah tana ganin sun shige bata kawo komai a rantaba nan tagyara mata bedroom d’inta tas sannan tafita takoma part d’inta.

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

 

Back to top button