Hausa NovelsKurkukun Kaddara Book 2 Hausa Novel

Kurkukun Kaddara Book 2 Page

Sponsored Links

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

 

_The Prisoners E8_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

 

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._

 

*Obie Estate*Haɗaɗɗiyar Daular arziƙi, Aljannar duniya da babu tamkarta a faɗin nahiyar Africa, Hamshaƙin Estate Ne Da ya haɗa tanƙama tanƙaman luxury Villas, da duk wani Ababen more rayuwa, Kayan alatun da ke a cikinsa kaɗai abun kallo ne, dollar ta yi kuka awurin ƙera ginin, yana da 6angarori da dama, kama daga katafaren Gate ɗin shiga Estate ɗin wanda Jami’ae ne ke tsaron shi Sojoji da ƴan sanda Ko sauro bai isa Ya ƙetara ƙofar shiga gidan ba saboda tsaron da ke gare shi, ba iya mutane ba hada na’urorin da ke sanya ido ga duk wani mai shige da fuce, kowace kusurwa ta villas ɗin tana maƙale da na’urorin cctv camera, daga bakin faffaɗan gate ɗin Santalelen titi ne zai isar da kai ga Interior ɗin daular, akwai Harabar ajiye motocinsu, Gardens da swimming pools area, Ga zoo wurin da ake kiwata dabbobin gidan. Kowani Villa na estate ɗin Yana da nashi kayan alatun na more rayuwa, parts ɗin da ke a cikin kowani gida ya haɗa da Haɗaɗɗun falullukansu waɗanda suka ji jigunannun furniture, Bedrooms, Dining rooms, Kitchens, Bathrooms, Laundry rooms, da sauransu, akwai Ƙayatattun dogayen benaye zubin twin stairs da U-shaped stairs, Idan ma mutun baida ra’ayin Hawa Benan Kowane Villa yana ɗauke da residential elevator wadda aka fi sani da lifter, tun daga Hawa na farko zata ɗauki mutun har izuwa hawa na Uku, dai dai da cokalin amfani na gidan babu wanda aka ƙera a ƙasa Nigeria, kaf kayansu daga ƙasar waje ake shigo dasu, mai karfin imani ne Kaɗai zai iya rayuwa acikin estate dinsu ba tare daya shagala daga yin ibadarshi ba, sai dai ta inda masu rayuwa cikin gidajen zasu burge ka Allah ya hore masu baiwar Ilmin duka na addini dana zamani, wayayyun mutanene masu daraja da ƙima a idon duniya, Sun Iya takun su ba zaka ta6a Iya aibatasu ba, saboda kyawawan ɗabi’unsu da halayansu, komai nasu is Extraordinary.

Tun da garin Allah ya waye masu aikin gidan su ke ta kai komo, kowaccensu ta yi dressing cikin chef’s uniform launin farare, ƙwararru ne a 6angaren girke girke da gyaran gida, basu wasa da aikin su, Suna ba lokacin mahimmancin sa, kuma suna takatsantsan wurin kula da buƙatun mutanan gidan.

A tsastsaye su ke a Cikin Katafaren Kitchen ɗin gidan mai girman gaske, A shaƙe ya ke da kayan Amfani, ko’ina a tsaftacensa ya ke tamkar ba amfani su ke yi da shi ba, aiki su ke yi tuƙuri babu kama hannun yaro, Matasan Ƴan mata da manyan su, wasu suna aikin wanke nama wasu suna yanke yanken kayan lambu agaban cutting board, yayin da wasu su ke agaban manyan gass cooker suna kula da girkin da suka ɗaura, akwai waɗanda ke a tsaye in front of kitchen microwave suna aiki.

Ƙamshin girkinsu ya karaɗe ko’ina tun daga cikin kitchen ɗin har izuwa Babban falon gidan.

Babbar macace ta shigo kitchen ɗin domin duba masu aikin don ganin yadda komai ke gudana, A ƙalla za ta kai shekara 40 a duniya, Ta kasance ɗaya daga cikin Masu yi masu hidima a gidan, ita ce head maids shugaban ma’aikatan Cikin gidan, Macace mai yawan fara’a ga son mutane, ma’abociya son Shigar fararen Kaya, A yanzu haka pakistan ne a jikinta riga da wando farare ƙal anyi masu adon duwatsu launi daban daban, ƙafarta na sanye cikin flat shoes, bakowa bace wannan face *DIVYA* ba’indiyace amma sunfi kiranta da *HAJJATY* tun da ta shigo kitchen ɗin masu aikin suka fahimci itace tazo dubasu nan fa suka ƙara dage damtse suna aiki duk don su ku6uta daga faɗanta.

A hankali ta ke zagaye Kitchen ɗin, Hannayenta a goye saman ƙirjinta, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, na ɗan wani lokaci kafin tayi masu gyaran murya, kusan atare su ka ɗago suna kallonta, Hannu ta tafa masu

“Aikin ku yana kyau, You ladies Are doing a fantastic job, everything smells delious, i’m sure ɗanɗanon girkin zaiyi daɗi kamar yadda ƙamshinsa ya ke da daɗin shaƙa, Ina ƙara jinjina ma ku,” ta ƙarasa yi masu maganar tare da ɗaga masu babban yatsan hannunta na dama alamar Jinjina.

Murmushi ne Ya bayyana akan fuskokin su, ba ƙaramin daɗi suke ji ba, Idan hajjati ta yabe su, suna matuƙar sonta kuma suna girmamata saboda kyawun halayanta da ɗabi’unta.

“Dame dame aka kammala ne”? ta yi tambayar tana kallon faces ɗinsu, Abla ce ta soma Yi mata jawabi

“Kebab with chips, Beef shawarma, burger and pancakes,…” kusan abu goma ta lissafa mata, Jinjina kai Hajjaty ta ɗanyi kafin ta ɗaura da cewa”Kada na katse maku aikin ku, lokaci Yana ƙurewa, Ku hanzata ku kammala, ”

“An aikawa Hajiya saratu Breakfast ɗinta!”? da sauri Safa tace”yanzu nake shirin zuwa in kai mata, Nice nike duty part ɗinta” Gyaɗa kai Hajjaty ta yi.

“Okey, shirya min fresh fruit ki haɗa min da kakkauran tea,” Wadda aka kira da Sarah ta amsa mata da toh, ba tare da 6ara lokaci ba ta shirya mata kayan marmari a cikin ƙayataccen wooden tray, tare da cup of tea, ta miƙa mata hannu biyu tasa ta kar6i tray din tare da juyawa ta fuce.

Bayan fitarta, Fira ta 6arke a tsakaninsu

“Safa ashe ke ce kike duty a part ɗin Aunty jarabatu zaki sha Masifa, ” Abla ce tai mata maganar, murmushi suka saki, sophia tace”Ai hajiya saratu ba daga baya ba, In dai wurin Iya masifane, Last time fa da naje kai mata abinci cewa ta yi wai na gutsiri ƙafar kaza, hada cewa ita bata yarda damu ba, wama ya sani ko mun saka mata guba acikin abinci donta ci ta mutu,” dariya suka saka

“Tana da wuyar sha’ani bata yarda da kowa ba, In ba wannan Mijin nata ba, Uban son banza suruki da zaman gidan surukai Ko kunya babu” sophia ce tai maganar, Safa tace”Ai koni na samu wurin zama agidan nan abunda zanyi kenan, waman taraka bati siddan, shiyasa a kullum nake roƙon Allah ya bani bugun zuciyar family ɗin, Wlh idan na Aure shi nadaina sakin baki ina bacci, nafilfili zanta yi akan Allah ya dawwamar da auran mu don nasan maƙiya da mahassada ba zasu bar mu mu zauna lafiya ba, Musamman Mahaifiyarshi uwar Ji da izza, kinga matar nan bata ɗaukar raini batason Mu’amala da bare….” tun da ta fara zuba suke binta da kallon rainin wayau saida takai aya tukunna Abla tace”you don’t ave sense, Dama najima da zargin kwakwalwarki ba dai dai take aiki ba, Ko Jazz da muka raina wlh yafi ƙarfinki, Ni kaina ba zance bana son Owais ba, amma ance abunda yafi ƙarfinka ka haɗa shi da baka so” kwa6e fuska Safa tai”kiyi min fatan alkhairi kawai, Nima a hausa novels ni ke jin irin hakan na faruwa, mafi yawanci zaki ga ƴar aiki ta auri ɗan masu gida, wani sa’in ma mai gidan ta ke aurewa….” sautin dariyarsu ne Ya hana ta ƙarasa maganar, suna fira suna aiki,

“Safa kina atare da wahala, in dai ko zaki cigaba da tunanin zaki samu abunda ki ke so kamar yarda ki ke karantawa ahausa novels, Ni Bance baya faruwa ba amma Allah a zamanin da mu ke ciki zaiyi wuya, mai kuɗi sai ƴar mai kuɗi, talaka sai ɗan talaka, Ina jiye maki tsoron heart attack ya kama ki silar son wanda bai son Kina yi ba, a ƙarshe ki ƙare a emergency room”

Dariya suka saki gaba ɗayan su, kwata kwata firar da suke yi bata ɗauke masu hankali daga yin aikin su ba, manyan cikin su ne kadai basa magana sai dai idan sun faɗi abunda ya basu dariya su ɗan murmusa.

“Ni takaici na magadan gidan nan basu da yawa, duk irin tarin dukiyar nan ace Iya mutun goma sha biyar ne ke da gadonsu” Abla ce tai maganar.

Abla tace”Nikaina abun na damu na, Yana yi mun ciwo a zuciya, na rasa gane meyasa basa son haihuwa, daga mai ƴa’ƴa biyu sai mai ƴa’ƴa uku, Allah ya hore masu wadatar arziƙi sai ƴa’ƴa ne zasu gagare su? Abun na ƙona mun rai, komai nasu na rayuwar turai, Mu da zasu taimaka su Aure mu, duk bayan ƴan watanni zamu dinga sakar masu ƴa’ƴa tuni zamu cika famiy ɗin”

Maganar Abla ba ƙaramin dariya ta basu ba, Sofiya tace”Sannu kaza suma ai suna son ƴa’ƴan, sannan bada son ransu bane ba su haihuwa, Ƙaddarar su ce ta zo masu ahaka, naji labari a bakin Hajjaty saboda tafi mu daɗewa a gidan, Suna haihuwa amma ƴa’ƴan basu zuwa da rai, A mace ake haihuwarsu yawanci da zarar sun yi haihuwar fari da ta biyu zaiyi wuya kiga sauran sun rayu a matattu su ke haihuwarsu, Allah ni tausayi suke bani, Musamman prime minister Hateem shifa Bai ta6a haihuwar ɗa Namiji ba, shi da matarshi Gimbiya mujeedat, ƴa’ƴa biyu duka mata, rashin haihuwarsu ba ƙaramin gi6i yai masu ba arayuwarsu, Ki duba fa hateem shine yafi kowa arziƙi a family ɗinsu daga shi sai sharafudeen,” mamakine akan fuskar Wasu daga cikinsu waɗanda basu daɗe da fara aiki ba

“Abun da ɗaure kai, Kuma an duba lafiyarsu? Ko dai wata lalurar ce da suka gada tun kaka da kakanni”?

“Ko ɗaya, Tun daga ƙasa Nigeria har zuwa ƙasashen waje an bincika lafiyar kowan nan su, Ba su da wata matsala da ta shafi ƙwayoyin haihuwarsu, lafiyar su ƙalau, har manyan malaman addini saida kakansu ya sanya don su bincika mashi meke faruwa a zuri’arshi, Sakamakon ɗaya ne dana asibiti, basu da wata lalura,”

Jikin su duk yai sanyi, Basu ta6a sanin zancen haihuwar da matansu keyi yara suna zuwa ba rai ba sai yau da sophia ta sanar da su.

“Allah mun tuba ka yafe mana, shiyasa akace zato zunibi koda ya kasance gaskiya, Gulma ba ta yi rana ba, Mune kullum tsegumin mu akan suna yin irin rayuwar turai ba su son haihuwa ashe ba laifin su bane, jarabtace daga Allah” murya asanyaye Safa Tayi maganar.

Abla tace “Na tausaya masu, kuma In sha Allah zamu ta ya su da addu’a, akan Allah ya yaye masu lalurar da ke damun su” shiru suka ɗanyi Na wani lokaci, daga bisani Safa ta shirya Kayan breakfast ɗin Hajiya saratu A Babban tray ta jera mata su, Bayan fitarta daga Cikin kitchen ɗin su ka ɗaura da wata firar, sam basa gajiya da firar Familyn Obinna.

“Muna fa da gagarumin bikin ranar zagayowar Haihuwar Obie, Nasan za’ae shagali na kece raini, za’a yi 6arin Dollar da pounds, Aranar zamu ga Zaratan ƴa’ƴan Obinna da Jikokinshi waɗanda basa a ƙasar, Ina da tabbacin Owais ma zai halarta”

Fuskar Sophia ɗauke da farin Ciki tayi maganar, Abla tace”Anya ko Owais zai zo? Kinsan fa halinshi, samun lokacin shi abune mai wuya”

“ai ko baiyi niya ba sai obinna Ya matsa mashi akan ya zo, Kinsan fa kaf cikin jikokinsa yafi ƙaunar Owais, kowa yasan da wannan zancen, Kinga ko ba zai so ayi shagalin nan ba tare da Owais Ya halatta ba,” acewar Abla

Murmushi Sopy tayi “Can’t wait to see Allah Ya nuna mana Lokacin, Dole naje ayi min wankin ido, don na samu damar ƙare Mashi kallo”

“Da rabon kisha mari, Owais baya son Kallo Idan Yana magana mutun bai isa Ya ɗaga ido ya kalle shi ba, Sannan ba’a katse shi, Sauƙin shi ɗaya Idan har kika karanci halayanshi da ɗabi’unsa tsaf zaku zauna lafiya, mutunne mai sauƙin kai baida girman kai, Yana da tausayi ga taimakon na ƙasa dashi…..” tun da ta fara jera masu Kyawawan halayanshi bata tsagaita ba har saida Landline ɗin dake a bakin ƙofar fita kitchen ɗin ta yi ringing tukunna ta dakata da yin magana, da sauri Sophia ta fuce ta je ta ɗauki landline ɗin Ta ɗaga kiran daya shigo, Cikin girmamawa tayi sallama, Jikinta sai 6ari yake yi.

“Cofee….” Iya abunda Taji an furta mata acikin wayar, jin yayi rejecting yasa ta zame ta daga saman kunnanta ta ajiyeta saman table, Dawowa Cikin kitchren ɗin Tayi Hankalinsu gaba ɗaya ya dawo kanta.

Har suna haɗa baki wurin tambayar ta “Wanene Ya kira” kwa6e fuska tayi tare da cewa”Nakasa gane muryar wanene acikinsu, Zaid ne ko Zayn, Coffee su ke buƙata, wa zai kai masu”? Ta yi tambayar tana kallon sauran. Shiru babu wanda yace zai kai, saboda Mugun tsoron shiga part ɗinsu suke Yi, saboda masifarsu,”

“Kinga tun da ke kika ɗaga Kiran nan Ki lalla6a ki je kawai ki kai masu awuce wajen” Acewar Abla, Yamutsa fuska marwa ta yi, Ba yadda ta Iya don dole ta haɗa masu coffee acikin mugs guda biyu ta ɗaura saman Plate ta fuce daga cikin kitchen ɗin.

Tun lokacin da Able ta fita hannunta ɗauke da tray Na breakfast ɗin Hajiya Saratu, Kai tsaye ta nufi Part ɗinsu, Tun kan ta ƙara sa gaban ƙofar ɗakin ta daddaɗan ƙamshin turarenta Ya daki hancinta, macace mai son ƙamshi ga iya ɗaukar Wanka, A bakin door ɗin Ta tsaya tare da Yi mata sallama, daga cikin ɗakin tajiyo muryar Hajiya saratu

“U can come in” A hankali ta tura ƙofar ta shiga, Hajiya saratu tana azaune tsakiyar Katafaren gadonta, jikinta na asanye da jallabiya, Kanta babu Kallabi Kitson zanene all back Wutsiyar gashin ta sauko har saman kafaɗarta, fararen idanuwanta suna a manne da farin glass medicated, tana da duhun fata mai kyan gaske, Hutu ya zauna mata, Hankalinta gaba ɗaya yana akan tsadaddar Apple Laptop ɗin da ta ke yin operating, ga dukkan alamu aiki ta ke yi.

“Once you’re done looking at me, please put the food on the table and leave my room.” Muryarta ce ta fargar da Safa daga kallon ƙurullan da ta ke bin ta da shi, Adabarbace ta gaishe da ita”Ina kwana Hajiya,” Guntun tsoki taja ba tare da ta amsa mata ba, ko kallo ba ta ishe ta ba, asaman front table din bakin gadon, Safa ta ɗaura mata tray din

“ko akwai wani abu da ki ke buƙata “? cikin Jin shakkarta Safa ta yi mata tambayar don tasan halinta, in har bata ba mutun iznin tafiya ba, yai yunƙurin Juyawa zai tafi atsawace zata ce mashi da Iznin wa!

Safa har ta gaji da tsayuwa shiru bata tanka mata ba, tamkar bata san da mutun awurin ba, Halinta ne share mutane, sai da ta mula ta sha iska tukunna ta ba ta zinin tafiya, bayan fitar Safa daga ɗakin, Ta dakata da yin aikin laptop ɗin, Yunƙurawa tayi tare da kai hannu ta damƙo Burger Ta soma turata abakinta tana ci, Bata wasa da Cikinta, Cikin ƙanƙanin lokaci ta handameta, ta kuma janyo Chicken wings tana ci, baya tagama ta ɗauki bowl ɗin dake shaƙe da plaintain chips hannu baka hannu ƙurya kamar mai fama da cutar yunwa, Saida ta lamushe komai, a ƙarshe ta kora da ruwan lemu mai sanyi.

“Daɗina dake bakya wasa da Cikin ki,” Jin muryar Mijin nata yasa ta ɗago da eye balls ɗinta akan fuskar shi, Daga cikin toilet ya fito waist ɗinshi ɗaure da towel, Ƙirarshi tamkar ɗan wrestling, Kakkarfan mutunne Jibgegen ƙato, Kyakkyawan ba’indiye Sumar kanshi akwance luf saman kanshi, Ga wani kwantaccen saje gefe da gefen doguwar fuskarshi, ‘ ta6e mashi baki Tayi”meye haka? Bana hanaka yawo da towel a qugunka ba? Yanzu da ace mai aikin nan tana acikin ɗaki ka fito fa? Fuskarta aɗaure tayi mashi maganar, Matsawa yai kusa da ita yaɗan ranƙwafa saitin fuskarta”yaushe zaki daina kishina? Murga mashi baki tayi”Bansani ba, Ni dai na faɗa maka, Karka kuskura ka ƙara fitowa ɗaure da guntun abu a qugunka bana son ta6ara” Ido cikin ido suke kallon Juna.

“Ƴa’ƴan mu Uku, kowan nan su Ya mallaki hankalin shi, Na yi tsammanin zaki rage kishi na da kike Yi” harara ta watsa mashi”pls Ka wuce ka je ka sanya suturarka, bana son ganin ka ahaka” Hannu ya kai yana ƙoƙarin warware towel ɗin gabanshi da sauri ta damƙi hannayenshi aɗan fadace tace”Pravin meye haka? Yarinta ce fa wannan”? Kashe mata ido ɗaya yayi fuskarshi ɗauke da murmushi yace”indai ina atare dake bazan ta6a girma ba, saboda tsantsar ƙaunar da kike nuna min” ta6e baki Saratu Tayi”naji yanzu kaje ka sanya suturarka, Sannan me kake son Ci insa akawo maka” Murmushin fuskarshi bai washe ba yace”abunda kika ci shi nake sonci abar ƙaunata, naga ma har kin kammala naki breakfast ɗin why ba ki bari na fito munci atare ba?” Ɗaure mashi fuska tayi “Pravin mu fa ba ƙananun yara bane da zaka tsaya kana gayamin kalaman Soyayya, ko da ya ke nafa tuna kufa indiyawan nan bautawa soyayya kuke yi har ku tsufa kuna abu ɗaya” cikin Zolaya ta ƙarasa maganar, gyaɗa kanshi yai”komi zaki ce bazanji haushin kalamanki ba, Amaryata kuma uwargidana, sannan uwar ƴa’ƴana abun alfaharina,” lumshe ido ta ɗanyi idan zata biyewa pravin ba zai barta taci gaba da yin aikinta ba, gwanine a fagen Iya soyayya da daɗin baki, Ya ƙware wurin Iya jan hankalin mace.

“Romeo, now your Juliet is at work, I’m almost done, zansa a kawo maka breakfast ɗin ka, Ni da kaina ma zan baka abincin abaki” Amsa mata yai da Okey, Daƙyar ta lalla6a shi Ya miƙe ya nufi Cikin ɗakin Yana tafiya tana satar kallon Bayanshi, a gaban closet ɗin kayanshi Ya tsaya tare da kai hannu ya buɗe

“My Juliet ba ki faɗa min kayan da ki ke so In sanya ma”! Murmushi ta saki”Yau babu aiki, ka samu hutu don haka Nafi sha’awar ganinka Cikin shigarku ta al’ada, Ya gane me take nufi, riga da wando Ya curo kalar na mazan Indiya ya sanya su ajikinshi, sun bi shape din jikinshi yadda kasan matashin saurayi saboda haɗuwarshi.

Bayan ya kammala Shirya kanshi, Hajiya saratu tasa aka kawo mashi breakfast, Da kanta take bashi abaki Yana ci, mugun son shi ta ke yi, ta mutu akan pravin, kamar yadda shima yake ƙaunarta, Allah Ya hada jininsu. Babu mai cin moriyarta irin Mijinta, komai nata mallakin shi ne.

Lokacin Da Sophia ta ƙarasa Bedroom ɗin twins dake acan Upstairs Second floor, Jikinta na kakarwa ta yi knocking ƙofar, almost 3 times kafin tajiyo muryar ɗaya daga Cikinsu “you can come in” Numfashi taja kafin ta tura ƙofar Haɗaɗɗen bedroom ɗinsu, Sanyin A.c da ƙamshin Turarensu ne Ya daki hancinta har sai da ta lumshe idanuwanta saboda tsabar yadda ƙamshin Ya kurɗaɗa ta ƙofofin Hancinta, tunkan ta shiga ciki Ta hango Ɗaya daga Cikinsu A tsaye Gaban tanƙameman dressing mirror Daga shi Sai short a jikinsa launin ja, Yayin da twin brother ɗin shi yake a kwance saman gado rabin jikin shi lullu6e da duvet. Kyawun surarsu sak irin na mahaifinsu Pravin, tamkar yayi kakinsu.

Muryarta na ɗan rawa tace”Barka da safiya yalla6ai, Ga coffee ɗin Ina zan aje’ ba tare da ya juya ya kalle ta ba yace “On my head” tuni tasha jinin jikinta, Batasan Ya zatayi ba, Zaid dake a kwance saman gadon Ya ɗaura ƙafarshi ɗaya saman front table ɗin gaban gadon.

“Is that how your parent taught you to enter a room without saying ‘Assalamu Alaikum ? Ɗakin kafurai kika shigo”?

Muryarshi tamkar ta mashayin giya

“Afwan yalla6ai, kafin in shigo saida na fara yin sallama, wata’ƙil baka jini ba ne” A sukwane Ya juya yana binta ɗan iskan kallo

“Am I deaf?” girgiza mashi kai tayi muryarta na kakarwa tace “That’s not what I meant, sir…” bai bari takai ƙar ƙarshen maganarta ba, ya nuna mata ƙofar fita
Aɗan tsawace ya furta “Oya Go back ki sake yin wata sallamar”
fuskarshi a murtuke yayi maganar, Idanuwan sophia tuni sun ciko tab da ƙwalla, Jiki asanyaye ta juya ta koma waje.

Kware Murya tayi”Assalamu alaikum” shiru bai amsa mata ba, shiga ciki tayi”Sir nayi sallamar in shigo? Coffee ɗin Yana hucewa”

Kafin Ya bata amsa Zayn dake kwance saman gado ya furta “I didn’t hear it. Go back and make another greeting”

Tayi mamakin Jin muryarshi duk a tunaninta bacci yake yi, ashe idonshi biyu, ” Maƙoshinta tamkar zai 6allo ta ƙara kware murya wurin Yi masu Sallama, Tun tana yi da marmari har ta fara gajiya, idanuwanta sunyi luhu luhu, A ƙalla tayi masu sallama kusan sau Goma sha biyar ba tare da sun bata iznin shiga ɗakin ba, Har saida Coffeen hannunta Ya salafce, sai da suka tabbatar Ta jigata sosai tukunna Zaid yace da ita ta shigo ciki, hawaye nabin kuncinta ta shigo.

Kishingiɗe ta samu zayn ya ɗaura kanshi saman pillow, Ko kallon arziƙi bata ishe shi ba, jiki na 6ari ta nufi Table zata ɗaura plate ɗin, Kakkausar Murayar zayn ce ta dakatar da ita

“Don’t you dare put that on the table! Ki koma ki canza wani coffee ɗin, wa zai sha abu ya salafce” juyawa marwa tayi tana kuka ta fuce daga Cikin ɗakin, ko a jikinsu, sun Iya rashin mutunci da mugunta idan suka so, duk rana ta Allah sai sun sanya ɗaya daga cikin masu aikin gidansu zubar da hawaye.

“Bro, when are we going back to America?” Zaid ne yai maganar while sitting on the dressing table chair.

Yatsina fuska Zayn yai “we have no way out, Zaid, seriously, naji takaicin tursasa mana dawowa Nigeria da obie yai, Ya hana rayuwarmu sakat, mu kaɗai mu ka tsone mashi ido, ga Owais can kamar tsuntsu Yana shawagi a ƙasashen waje sai mu da muka tsone mashi ido, nifa na gaji da halin dattijon nan, na rasa zaman me yake yi acikin duniyar nan, duk shekara sai na sayi sabon likafi da miski na mutuwarshi but yaƙi tafiya” Ranshi a6ace yake magana

Zaid dake kallon ɗan uwan nashi yana murmushi yace” I know what you’re mad about” Yatsina fuska yai”Kai ma ɗin itace damuwarka, Ummin america ce silar komai, ” Yana magana a harzuƙe ga dukkan alamu an fama mashi raunin dake acikin zuciyarshi.

“Everything about her is different. From the first day I saw her, I knew she was a classy woman with a magnetic personality that could captivate any man.” lumshe ido zayn yayi, bakomai yake tariyowa ba face farkon haɗuwarsu da ita.

“Naso ace ta amince min, ba abunda zai hana in aureta, zan tattara dukiyata gaba ɗaya data mahaifiyata, da ta Dattijon can duka In bada a matsayin sadakinta, sai dai kash ta nuna bata buƙatar aure arayuwarta, Zaid ya zanyi da raina? Ta sanya min jarabar da bazan Iya gogeta ba” cikin jin shauƙi yake magana.

Harara zaid ya watsa mashi”nifa ban gane ba, Taya zaka dinga yi min magana akan macen da nake son in mallaka? Kasan dai haramun ne muyi sharing mace ɗaya a gidan aure ko?, awaje ne muke da ikon yin hakan duk da shima yin hakan haramun ɗinne” ta6e la66ansa yai”Zaid ni ba zan yi jayayya dakai ba, just Kada kamanta ni ne gidan kuɗi, na gaban goshin mommy, mata kuma saida kuɗi”

Dariyar shaƙiyanci zaid ya sakin kafin yace “Nima ina da daddy, kada ka manta komai na mommy mallakinsa ne” Sakin baki Zayn yai saida Zaid ya karasa maganar tukunna yace”Daddy ai ɗan koren mommy ne, mutumin da ke zaune agidan surukansa? Mommy ce fa silar arziƙinsa, tayaya zaka hada kan ka da Ni? baya kasan Mune ke da dukiyar Ku kuma Bayin mu ne, Sai mun ɗan watsa maku hatsi tukunna kuke samun wanda zaku tsastsaga…..” Kallon al’ajabi Zaid yake bin ɗan uwansa dashi, yadda yake magana Yana kushe mahaifinsu yai matuƙar ɗaure mashi kai, da ace wani bare ne yai wannan maganar, hada shi za’a haɗu wurin cin ubansa, don sun tsani gorin da akeyiwa mahafinsu akan yana zaune gidan surukansu.

“Assalamu Alaikum” Muryar Sophia ce ta katse masu firar tasu, daga wajen bakin ƙofar ta tsaya”Yalla6ai ga coffee din na canza wani” har suna haɗa baki wurin furta”we don’t need it!” ranta ya 6aci, duk wahala da tasha a ƙarshe sunce basu sha, gyaɗa kai ta yi tare da juyawa ta bar part ɗin nasu.

“Zayn ba ka da mutunci, daddyn namu ka ke yi wa gori? Yunƙurawa yai tare da mikewa zaune A harzuƙe yace”ƙarya nayi ne?ni ban ta6a ganin Mutun mai matattar zuciya irinta daddy ɗinmu ba, har yau in na tuna gorin da akeyi mana raina 6aci yake yi, Allah ya hore mana komai na rayuwa amma daddynmu yaja mana abun magana” Jinjina kai Zaid yai”Nima fa abun na ƙona min rai yana yi min ciwo a zuciya, amma ya zamuyi dole mu rungumi ƙaddararmu” saukowa Zayn yai daga saman gado Ya nufi toilet ya shige, ya rage saura Zaid a ɗakin ya tasa mirror gaba yana kallon fuskar shi, bakomai yake tunanowa ba face fuskar *UMMIN AMERICA*.

*MIDDLE STEP*

Daga alkalamin Boss✍️

Kishingiɗe yake saman lallausar Darduma, a Cikin Haɗaɗɗen Garden ɗin gidansa, jikinsa na asanye da Voile sky blue riga da wando, Kayan sun zauna mashi, Fari ne Ba irin sosai ɗinnan ba, dukkan wasu alamun tsufa sun bayyana akan fuskarshi da jikinshi, A ƙalla zai kai shakara tamanin a duniya, daga ganin fatarshi hutu ya zauna mashi, kan shi babu hula, tsufanshi bai 6oye mashi Kyawun fuskarshi ba, tsabar kyan Da Allah yayi mashi zaiyi wuya mutun yai mashi kallo ɗaya ya kauda kai, saboda haɗuwarshi da iya ɗaukar wankanshi, sumar kanshi akwance take tasha gyara hurhura duk ta lullu6e ainin launin gashin nasa, daga gaban goshin sa akwai siraran hurhura, da akayi gayu da ita, ba ƙaramin kyau ta yi mashi ba,Yana da tsayin fuska, da Manyan idanuwa, Launin gray mutunne shi ma’abocin son ƙamshi, tamkar Da ruwan turare ya ke yin wanka saboda tsabar yadda jikin shi ke fitar da daddaɗan fragrance mai kwantar da tarzoma, Dogon gemun shi fari fat ya sauko har saman ƙirjin shi, Yana da yalwatacciyar suma.

Dattijon Arziƙi kuma gwarzon Namiji mai ɗauke da suffofin Jagoranci, waɗanda su ke da Jan hankalin Jama’a, mutunne shi mai daraja, Wadatar Arziƙi, kaifin basira da bajinta, Jajircewa, Mai cikar kamala, ga iya mu’amala Da mutane, kaifi ɗaya ne kuma bai Sa6a alƙawari,Ta ko’ina Allah Ya hore mashi, Kuma duk mun tarin dukiyar da ya mallaka Hakan bai gusar dashi daga Yin ibadarshi ba, Hakokin Ubangiji kama daga fidda zakka, sadaka, Da kyautatawa al’umma, mutun ne mai jin ƙan talaka, Shi nashi arziƙin bai ɗaura mashi Girman kai da maƙo ba, Da kuma ƙyamar Talaka, kowa Nashi ne wannan kenan.

daga bayan shimfiɗar shi Sandar shi ce jingine da bishiya wadda aka ƙerata da zallar Gold kuɗin ta kaɗai sun ishi bawa yai maganin talaucinsa, Yayin da iskar Garden ɗin take ratsa sassan Jikin shi, A hankali ya ke ɗan lumshe idanuwanshi yana buɗesu haɗi da ƙarewa ƙayatattun kayan alatun da ke a garden ɗin kallo, a duk lokacin da kewar jikanshi ta addabe shi yakan ke6ance kanshi daga Cikin Jama’a, ba tare da sanin kowa ba, ya ke shigowa garden shan iska, yasan muddin masu kula da lafiyarshi suka gan shi shi kadai agarden sai sun kira ya’yanshi sun faɗa masu daga nan su kuma zasu rasa kwanciyar hankalinsu, har sai sunzo sun duba shi, sun tabbatar da lafiyarshi tukunna hankalinsu zai kwanta, shi kuma bayason ya katse masu aiyukansu, saboda suna ƙoƙari wurin zuwa ganinshi akai akai, Suna matuƙar ƙaunarshi, Babbar damuwarshi a yanzu Jikanshi daya mutu akan ƙaunarshi yayi nesa dashi, ya kwallafa rai akan son shi, ko ƴa’ƴanshi da ya haifa baya yi masu irin son da ya ke yi mashi, gaba ɗaya hankalin shi na akan, kyawawan furannin cikin garden ɗin, Da Halittun dake yawo acikinsa irinsu ɗawisu da filfilo Yana matuƙar son ganin su.

Shu’umin ƙamshin Humran Jikinta ne ya daki Hancinsa, tun kan ta ƙaraso Ya ɗago da idanuwanshi Ya kalle ta kafin Ya kawar da idon shi gefe ɗaya sam babu walwala akan fuskarshi

Ƙarasowa tayi daga gabanshi Ta ɗan russina ta gaishe shi cikin girmamawa, shiru bai tanka mata ba, hakan da yai mata yasa ta fahimci babu lafiya, ba ta ta6a ganin damuwa akan fuskar dattijon ba sai yau, cikin sanyin murya tace”Yalla6ai na duba acikin gida baka nan shiyasa nazo duba ka a garden, fresh fruit ne na kawo maka” tai maganar tare da ɗukawa ta ajiye mashi kayan marmarin.

Da buɗar bakinsa sai cewa yai”Owais Ya dawo gidan nan”! murmushin gefen fuska Hajjaty tasaki”yalla6ai owais Ai baya a ƙasar Ko kamanta ne” yamutsa fuskarshi yai” Oh toh na manta, “har zata miƙe ta kuma cewa”Ko kana buƙatar wani abun ne”? Girgiza mata kai yai”bana son kowa yasan ina a garden”! amsa mashi tayi da toh kafin ta kama hanyar fucewa Kaitsaye ta nufi Entry hall na shiga gidan, Zuciyarta a cunkushe take da tunanin meke damun dattijon? Ta ya ya zata Iya sani? Duk ta damu kanta akanshi saboda Kyautatawar da yake yi masu bazata so ta gan shi a irin wannan yanayin ba.

Adai dai Ƙofar shiga Falon suka ci karo da matashin dake ƙoƙarin fitowa, Dogo siriri bai da ƙiba ko misƙala zarratin, Fari sol dashi daga ganin shi farar fata ne bai haɗa komai da jinsin baƙaƙe ba, Jikinshi na sanye da Kayan likitoci farin wando, Farar shirt daga sama ya ɗaura Lapcoat, Fararen idanuwashi na manne da farin glass, Masha Allah Kyakkyawan gaske, Sumar kanshi har saman wuyanshi,

“Jazz! ” yanayin yadda ta ambaci sunanshi ne yasa shi cin burki, Yana kallonta, fuskar shi a ɗaure yace “Me kike buƙata? Allura ko tiyata”? Dariya ta ɗan saki har fararen haƙoranta suka bayyana.

“Kinga sauri nakeyi Yanzu aka kirani awaya, Ina da patient” yai maganar yana ƙokarin bi ta gefenta Zai je wuce, ruƙo Hannun shi da tayi ne yasa shi yamutsa fuska Hada bubbuga ƙafarshi atakure Yake kallonta

Cikin sanyin murya ta soma magana”Jazz kana araye obinna ya ke6ence kanshi a garden? Hankalina ya tashi ganin damuwa akan fuskarshi….” Tunkan ta ƙarasa maganar Jazz Ya zame glass ɗin idon shi, Yanayin fuskarshi Ya canza sosai, ba tare daya ce mata uffan Ba ya nufi garden ɗin gidan, bin bayanshi tai da kallo fuskarta ɗauke da murmushi don tasan muddin Jazz yaje garden, damuwar obinna ta ƙare, Saboda kaifin basirar dake gare shi Tsab zaiyi mashi solving matsalar shi.
Kamar yadda Hajjaty Tabar Obinna haka Jazz ya same shi a kishingiɗe saman darduma, ya ɗan lumshe idanuwanshi, bai ta6a kayan marmarin da ta kawo mashi ba.

Sautin muryar Jazz ce ta daki kunnanshi”ina gwanin wani ga nawa!Kai ni fa bani da tamkar dattijon nan aduniya, Akanshi zan iya faɗa da kowa, duk mutumin da bai daraja gemunshi ba babu mutunci tsakanina dashi….” Cikin ɗaga murya ya ke yin maganar.

Hakan ba ƙaramin faranta zuciyar obinna yai ba, a tsanake yake kallon shi,

Kashe mashi ido ɗaya Jazza yai”ku fa tsaffin nan sai ana lallashinku ana tarairayarku, da zarar mutun ya haura shekara 70 a duniya sai kaga ya fara ɗabi’u irin na Yara, haba Uban mu maganin kukan mu, Idan Yunwa kake ji ba sai kai magana abaka abinci ba? Shine don rigima zaka ke6e kanka cikin garden salon ka jamana bala’e ace bamu baka kulawa yadda ya dace”? fuskarshi a ɗaure yai maganar, still murmushine akan fuskar obinna, A faɗace Jazz Ya nuna mashi hanya da yatsan hannun shi”maza tashi ka koma gida idan ba so ka ke Kaji ɗanyar geza a jikin ka ba, ” Wannan maganar da yayi tayi matuƙar bashi dariya sosai Obinna ya tuntsire da dariya yana kallon shi, jinjina kai Jazz yai hada ruƙe qugu yace”Na fahimci rashin mabugi ne ke damun ka, ” yai maganar tare da juyawa yana neman bulalar da zai buge shi, Dariya hada dafe ciki obie yake yi, Yayin da yake kallon shi,

“Mutun bai rasa ci da sha ba, Sutura Allah ya hore mashi, wadatar arziƙi da ta ƴa’ƴa mai yafi wannan aduniyar nan”? A faɗace yai maganar, kamar wanda aka 6ata ma rai, alhalin nan duk cikin zolayane, ganin yayi nasarar sanya shi farin ciki yasa shi matsawa kusa dashi.

Hannayenshi ya ruƙe acikin nashi”haba sanyin idaniyata, Dan Allah kafaɗin menene damuwarka? Ashirye nake dana sanyaka farin ciki,” fuskarshi amarairaice yai mashi maganar,

Lumshe ido obie ya ɗanyi kafin a hankali ya waresu kan fuskar Jazz

“Shi ne damuwata, Kafi kowa sanin hakan, bansan ya zanyi ba, inason ganin shi, ban ta6a tunanin zai ɗauki tsawon lokacin nan batare da yazo kawo min ziyara ba,” farin ruwane kwance acikin idanuwanshi, Hankalin Jazz ba ƙaramin tashi yai ba.

“Kamar yadda ka damu dashi, shima haka ya damu dakai! Ayyuka ne suka yi mashi yawa, pls ka yi mashi uziri….”

“Jazz Inaso Owais Ya halacci shagalin da za’ayi na murnar zagayowar ranar haihuwata, Amma nasan abune mai wuya ya iya zuwa” shiru Jazz ya ɗanyi yana kallon fuskarshi.

“Idan zaka Iya bani dama zan sa shi yazo, Nayi maka alƙawarin hakan,” Yai maganar tare da kai hannu ya ɗauki 6arin kanka Cikin kayan marmarin da hajjaty ta kawo ma Obinna, Abaki Ya tura yana sha.

“Na bar maka komai a hannunka, Indai zaka Iya cikamin burina na ganin Owais Ya halacci taron nan,”

“Kada ka damu dattijo, ko babu mota ba abun hawa sai owais yazo kasar nan, ” yai maganar tare dakai hannu zai ƙara ɗaukar Ayaba, Obie Ya ka6e mashi hannu

“Jazz ka raina girman gemuna, Kowa yana jin shakkar tunkarata amma kai Ko kaɗan ba ka Jin kunyar kallona ido cikin ido, ” dariya yasaki tare da cewa’Suma don basu son ainihin wanene kakana ba, shiyasa suke jin shakkarka, ”

“Ba aiki zaka je bane”? zaro ido waje yai sai lokacin ya tuna da mara lafiyan da zaije dubawa, da sauri ya mike yana faɗin”Rigimamman tsoho ni nayi nan Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana, ‘ har ya miƙi hanyar zai bar garden ɗin ya kuma dawowa ya zuƙunna a gaban farantin kayan marmarin ya ɗibi mai uban Yawa Kafin ya mike yana faɗin”Allah yaja da ran dattijon arziƙi tsoho mai ran ƙarfe, An buga dakai an barka, Namijin zaki uban dawa”

Murmushi ne ɗauke akan fuskar shi, idanuwanshi akan bayan Dr jazz har saida ya 6ace ma ganin shi tukunna ya ɗauke idon shi.

 

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

 

First bank

 

3196407426,

 

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

Back to top button