Kurkukun Kaddara Book 2 Hausa Novel

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 20

Sponsored Links

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

~Middle step~

_The Prisoners E20_

 

*Daga alƙalamin Boss Bature*

 

 

Hankalinta a matuƙar tashe take kallon fuskarshi, Numfashinta na hauhawa zuciyarta na bugawa da sauti mai ƙarfin gaske tamkar zata tsaga ƙirjinta, tsabar tsoratar da ta yi, Nurse Jessica da ke a zaune ta rasa gane meke faruwa ne? taga dai tun da Angel ta yi mashi rumfa taƙi motsawa, kamar an daskarar da ita, idanuwanta ba su hango mata hannun Danish da ya damƙi Qugun Angel da shi, sakamakon Sumar Kanta da Hijabin jikinta sun lullu6e shi.

“masoyiya Angel, Ke nake Jira, kusan ƙarfe goma na dare, Yakamata Muje ki kwanta ki kwanta ki huta” Cikin Kulawa ta yi mata maganar Tana leƙen fuskarta sai dai bata samu damar ganinta ba, saboda wuyan Hijabinta Ya zame tuntuni sumar kanta ta zazzago gefe da gefen fuskarta, ta rufe su.

Yunƙurin kubcewa tayi daga ruƙon nashi sai dai ko gizau wannan bai yi ba, kuma bai motsa ba, Ya matseta A jikinshi, tamkar an ɗaureta da igiyoyi, duk da sanyin A.c na room din hakan bai hana ta zubda gumi ba, zufar dake wanko fuskarta kaitsaye take sauka saman fatar face nasa, idanuwanta azazzare, yayin da acan cikin zuciyarta ta ke ta ambaton”INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHIRRAJI’UN”! Ba ƙaƙƙautawa.

Muyar Nurse Jessica ce ta ƙara fargar da ita”Lafiya kuwa Angel? Ya akai naji Kinyi shiru? Ko kinyi bacci ne a jikin shi” ta ƙare maganar tare da yunƙurawa ta miƙe daga saman chair ɗin ta nufi gaban gadon ta tsaya tana ci gaba da yi mata magana, tsabar yadda la66anta ke yin kerma ta kasa buɗe baki ta faɗa mata Halin da take a ciki.

Miƙa Hannu nurse jessica ta yi da niyar ta ɗago da Angel, saboda ta yi tsammanin bacci ne Yai awon gaba da ita, Sai dai Kafin ta ruƙo ta, Angel Ta yi ƙoƙarin Yin magana Muryarta A hargitsa ba natsuwa ta furta”ɗan Uwana Ya farka! Shine Ya ruƙe Ni”

Mamaki Ne Yasa Nurse jessica Zaro Ido haɗi da buɗe Baki, Ta Furta” Are u serious Ya farka?

“Ya farka, but he didn’t open his eyes. He held me so tightly that I couldn’t separate myself from him” cikin shessheƙar Kuka Angel ta furta maganar.

Jin haka Yasa Nurse jessica faɗin”Bari Na taimaka maki ki miƙe”

Hannu Biyu ta sanya ta ruƙe Angel ta soma kiciniyar 6an6arota daga Jikin Danish da Iya ƙarfin ta na ƙarshe sai dai takasa ta6uka komai, Mugun ruƙo Yai mata, Hatta dogayen nails ɗinsa sun yi mata shatu saman bayanta, Lamarin ya ɗaurewa Nurse Jessica kai, ganin ta sanya Iya ƙarfinta na ƙarshe Amma abanza, hakan ba ƙaramin ruɗar da ita yai ba, Muryarta na rawa ta furta”Bari naje na kira doctor”

Da sauri ta fuce daga Cikin ɗakin hada ɗan gudunta

A lokacin da bata Yi tsammani ba, Sexy voice ɗinsa ta ratsa kunnuwanta muryar da ta daɗe tana mararin Jinta

“My Angel” Iya abunda ya furta mata kenan.

nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, jin ya ambaci sunanta, hakan na nufin Yana acikin Hayyacinsa, ƙura ma fuskarshi ido tayi ganin yana mutsu mutsun buɗe idanuwanshi, sannu A hankali yake ƙoƙarin ware su, sunyi mashi nauyi saboda baccin da yai na tsawon kwanaki, Ta yi matuƙar ƙagara da son Yin tozali da kyawawan Reddish-brown eyes ɗinsa, kaɗan Ya buɗe su bai ƙarasa ware su ba, sun ciza launinsu, hakan ba ƙaramin kyau suka ƙara ma shi ba, Tsabar farin ciki batasan sa’adda ta fashe mashi da kuka mai tsuma zuciya, tana haɗawa da dariyar farin Ciki, ya natsu yana kallonta da wata irin kasala a jikinshi, sam bai san a ina suke ba Iya fuskarta Yake Iya gani.

Cikin shessheƙar kuka haɗi da shagwa6a take faɗin”Nayi missing ɗinka My man, sai yau zaka farka? Kabarmu da kewarka da fargabar a wani hali zaka tashi, sannan kuma ka tsoratar dani sosai….” lumshe idanuwanshi ya ɗanyi tare da ware su saman fuskarta, Hawayenta sai jiƙa masa face dinshi suke Yi, har cikin bakinsa, hakan bai dame shi ba, tamkar ya samu ruwan sha, haka ya ke yin swallowing dinsu.

Kallon da ya ke yi mata kallo ne dake nuni da tsantsar ƙaunarta da kewarta da yayi, hucin numfashinsu sai gaurayewa yake yi dana juna, hakan bai sha masu kai ba.

Idanuwanta sharkaf da hawaye sun rune jawur taci gaba da cewa”dan Allah ka faɗamin ba abunda ke damunka? Naga kanata kallona kaƙi kula ni” ta ƙare maganar still da shagwa6a, yamutsa fuskarshi yaɗanyi haɗi da motsa tausasan la66ansa calmly ya furta

“ke ce damuwata, kinsan bana son zubar hawayenki, ki daina yi min ku ka or else I’ll go back to sleep

yai maganar yana ƙoƙarin lumshe idanuwanshi da zolaya yai mata hakan aiko da sauri ta shanye kukanta, tana faɗin”na daina My man, kaine ka ƙi kwantar min da hankali na” ba zato ba tsammani taji ya manna mata peck saman fore head dinta, farin ciki duk ya cikata.

Muyarta har shaƙewa ta ke yi saboda kukan da tasha”ka sake ni, Ka matse ni” tayi maganar tana ƙoƙarin kubcewa daga ruƙon da yai mata, so ta ke yi ta nuna mashi sabon wurin da suke acikin shi, ƙanƙameta Ya ƙara yi yana faɗin

“Ki jira, zan sake ki, ina samun natsuwa atare da ke”

ƙayataccen murmushi ta saki, ta ɗan dakata suna kallon cikin idon junansu, lokaci ɗaya taga Ya haɗe face dinsa.

“Lafiya”? Tai tambayar tana cigaba da kallon shi

“Namanta, ban sama maku abincin da zaku ci ba, Na bar ku da Yunwa”

Murmushin gefen fuska ta sakar mashi”Ka kwantar da hankalin ka, Muna cin Lafiyayyan abinci har sai mun ture, shiyasa nace ka sake ni inason nuna maka wani abu” slowly ya zame hannunsa daga ruƙon Da yai Mata, Light bulb ɗin ɗakin Ya haske mashi ido, saukowa tayi daga saman gadon ta fuskanci gabas Ta duƙa tayi sujjada tana godewa Allah daya farkar mata dashi cikin ƙoshin Lafiya ba tare da wani abu ya same shi ba.

Alhamdulillahi Ala kulli Halin.

Ya yi matuƙar Yin mamakin ganin room ɗin da ya ke aciki, a kasalance ya yunƙura Ya miƙe zaune yana ƙarewa ko’ina Kallo, tunani ya shiga yi Ina ne nan? Waye ya kawo su? Fuskarshi da alamun ruɗani ya Tura yatsun hannunshi cikin yalwatacciyar sumar kanshi yaci gaba da cakuɗata tamkar yana sosata, saukowa ya yi da ga saman gadon.

Jikinshi yayi mashi nauyi daƙyar yake taka ƙafarshi, yayin da yake ƙarewa ɗakin Kallo, Angel tana a duƙe tun da tayi sujjada bata ɗago ba, addu’o’i take tayi masu.

Yana ƙoƙarin buɗe baki da niyar ya yi mata magana, Sai ga doctors da nurses sun shigo ɗakin da saurin su, Kusan atare su ka ci uban burki suna kallon kallon a tsakanin su da shi, Mutumin da suka daɗe suna mararin ganin Ya farka, sai yau Allah ya nufa zai tashi, Sun yi matuƙar girgiza da ganin Shi a tsaye kan ƙafafun shi, kyan fasalin shi Ya yi masu ƙwarjini.

Da hannu Yai masu Alamar su wanene su? Sai Ƴan kame kame suke Yi An rasa me Iya buɗe Baki Yayi mashi magana.

Juyawa yai da sauri Yaje gaban Angel da ta yi sujjada, Da hannu ɗaya ya ruƙo damtsen ta, Ya ɗago da ita tsaye kamar wata ƴar baby, nuna mata likitocin Ya yi da hannun shi

“Who are they, and where are we?”

daƙyar ta samu natsuwar Fayyace mashi komai tun daga kan Yadda aka tsunto su a daji aka zo da su asibitin kamar yadda Gabriel Ya sanar da ita.

Bayan ta gama kora mashi jawabi ta kalli fuskokin likitocin tace “ku ta ya ni murna ɗan uwan mu Danish Ya farka”

murmushi kowan nan su Ya saki Nurses din dake a cikinsu kamar sun samu tv haka suke Binshi da mayataccen kallo, ba mazan ba ba matan ba.

“Muna ta ya ki Murna masoyiya Angel, munga brother ɗinki Ya farka cikin koshin Lafiya” nurse jessica ce Tayi maganar

Daƙyar wani dr ya iya buɗe baki yace”Danish Fatan Ka tashi Lafiya, tsawon lokaci muna jiran ranar da zaka buɗe idanuwanka, Sai yau muka samu damar ganin ka, Mun ji daɗi sosai” yai maganar tare da miƙa mashi hannu don su gaisa, Man ɗin fa bai yarda da su ba, dama yana da wuyar sha’ani ga ƙiwuya kamar ƙaramin Yaro.

“Danish Ka miƙa mashi hannu ku gaisa” Angel ce tayi mashi magana, goya hannayenshi yai saman broad chest dinsa, Alamar ba zai miƙa mashi hannun ba”

murmusi yaƙe ta ɗan saki”ku yi haƙuri, Danish baisan ku ba, Har yanzu baccin bai sake shi ba, nasan kafin zuwa gobe zai Warware’

Nurse rebecca tace “badamuwa, Dama mu fatan mu Ya farka da ranshi da lafiyarshi, Hakan ma ya wadatar”

Dr. Anthony Yace”Calm down, Danish. No one will bother you. We are doctors, and we have the right to check your health until you feel better.” still bai tanka masu ba.

Dr harry yace”ni dama tun kafin Ya farfaɗo raina Ya bani zai yi wuyar sha’ani, sai gashi maganata ta tabbata, mutane masu irin Kyanshi bakowa suke kulawa ba” da zolaya yai maganar, Ya ƙara da cewa “mu dai yakamata asaki jiki damu tunda malaman lafiya ne, muna so ka bamu dama mu ƙara bincika Lafiyarka” tun da suka fara Magana bai tanka masu ba sai kallo da yake binsu dashi kamar yaga wasu halittu daba na mutane ba.

“Ko akwai Inda ke yi maka ciwo yanzu”? Dr anthony ne yai mashi maganar, Angel sai ƙoƙarin ingiza hannunshi take Yi don yayi masu magana amma Yaƙiya, Nurse jessica tace”ga dukkam alamu rowar muryarsa yake yi mana, Ni inaga Mu ƙyale shi zuwa gobe nasan zai warware kuma zai saki jiki da mu”

Kamar za su yi hauka wurin yi mashi magiya don yayi masu magana yayi shiru abunshi, har so sukayi su bincika lafiyarshi amma Ya hana, duk wanda yai gigin matsowa kusa dashi, zazzare masu ido yake yi alamar zaiyi fighting dinsu, lamarin ya ɗaure masu kai, ganin sun sanya naci akan sai sun duba shi, Angel ta roƙe su akan su ƙyale shi zuwa gobe, fargabanta kada su hayaƙa shi azo asamu matsala, tunda harya fara zare masu ido yana ɗaure masu fuska. Ba don sun so ba, su ka yi masu sallama da niyar gobe zasu dawo, kusan atare suka fuce waje, aransu suna Ayyana irin kyawun fuskarshi da surarshi, sai santin shi suke Yi musamman nurses din cikin su.

Su Uku Suka rage a ɗakin, Nurse Jessica ta dubi Angel”na lura brother ɗin nan naki, ke kaɗai yake jin maganarki, Inaso ki tambayar min shi ko akwai abunda yake buƙatar ci”? Kallon shi Angel Tayi, idonshi na akan plasma tv ta ɗakin, sai ƴan kalle kalle yake yi.

“My man kana jin Yunwa”? Da budar bakinsa sai cewa yai”Ina haris da su Batul? Inason ganinsu”

Kallon Nurse din Tayi”yace yana son ganin ƴan uwanmu” gyaɗa kai tayi”badamuwa Zamu Iya zuwa”

Ruƙo Hannunshi tayi acikin nata”muje in nuna maka su” nurse jessica tana agaba suna abayanta, tun da suka fito daga ɗakin Yake ƙarewa ko’ina kallo, agogo kaɗai mutun zai kalla ya gane cewa dare ne amma donta hasken light bulbs na asibitin ba za ka ta6a gane dare bane.

Nurses ɗin dake yin zarya da doctors sai satar kallon shi suke yi, hada masu yin tuntu6e.

Ɗakin Haris suka Shiga, tun bayan fitar Angel bacci ya ɗauke shi.

Rabin jikinshi lullu6e da bargo, da sauri Danish ya ƙarasa daga gefen gadonshi Ya zauna Yana kallon shi, nurse da Angel suna a tsaye suna dubanshi.

“Bacci ya ke yi Danish, ko zamu bari sai gobe idan Ya farka mu dawo” ɗaga mata kai Yai alamar eh, dama burinshi ya gansu hankalinshi sai yafi kwanciya, ɗaura hannunshi yai saman sumar kan Haris ya shafata a hankali, tsantsar farin Cikine akan face dinsa’ mintuna Biyar kafin Ya miƙe, suka nufi ɗakin Batul, ko da suka shiga, basu sameta a saman gadonta ba, nan fa hankalin Angel Ya tashi, “ina batul taje” nurse jessica harta buɗe baki zata bata amsa, suka ji motsin fitowarta daga toilet, Kamar a mafarki take kallonsu kafin ta tsayar da idonta kan Danish, da ƙarfi ta ambaci sunanshi, da gudun gaske fa ƙarasa ta faɗa saman faffaɗan ƙirjinshi, ɗaura Hannayenshi yai saman bayanta sosai ya yi tighting ɗinta, daɗi kamar zai kasheta, annurin fuskarshi sai ƙara nunkuwa yake yi, da alama yaji daɗin canjin rayuwar da suka samu.

Ɗagowa tayi da kanta daga saman chest dinsa, ido cikin ido suke kallon juna, tuni hawaye sun cika idonta muryarta na rawa ta soma yin magana

“Ɗan uwana rabin raina, kaga canjin rayuwar da muka samu ko? Nasan Angel ta faɗa maka komai, Danish ba zamu Iya misalta kewarka da mu ka yi ba, wlh naji daɗin farkawarka nayi farin cikin ganinka” a tsanake ya furta mata”nima nayi farin ciki Batul, Ina taya mu murna, ina yi mana fatan wannan ya kasance ƙarshen wahalarmu” Angel da nurse jessica sai murmushi suke saki yayin da suke kallonsu.

“Danish nasan za ka ji wani iri, nan ba kamar prison ba, inda aka ƙuntata rayuwarmu, tun muna Yara wannan ne karo na farko da muka fara tsintar kanmu awajen prison cikin mutanan duniya, Iskar da muke shaƙa a yanzu ta ƴanci ce bata kurkukun ƙaddara ba” kalamai masu daɗi take faɗa mashi

“Muna samun kyakkyawar kulawa awurin mutanan nan” tayi maganar tana nuna mashi nurse jessica”sun bincika Lafiyarmu, kuma sun taimaka mana wurin samun sauƙi, sannan muna samun Cin abinci har sau uku arana, komai muke so sunayi mana, Ina fata kaima zaka saki jikinka da su sannan ka ba su haɗin kai donsu duba lafiyarka, idan akwai wani abu dake damunka zasu taimaka maka wurin samun sauƙi in sha Allah, sannan idan kana Jin yunwa ka yi masu magana zasu baka abinci, ba sai kasha wahalar neman abunda zaka Ci ba…” muryarta na rawa ta ƙarasa maganar, hawaye tuni sun cigaba da wanke face dinta

Ɗaura tafin hannunsa yai saman face nata, share mata hawayen fuskarta ya soma Yi Calmly ya furta”its ok, stop shedding ur tears, ngde da shawararki, zan basu haɗin kai,”

“Danish babu wasu kalmomi da zan Iya yin amfani da su wurin yi maku godiya kai da Angel, Allah ne kaɗai zai Iya biyan ku, haƙiƙa kun taimaki Rayuwarmu kun gatanta mu, kun yi mana silar barin mu kurkukun ƙaddara, duk wani cigaba da zamu samu a duniyar nan kune sila, ba zamu ta6a mantawa da halaccin ku agare mu ba, kun fiye mana iyayenmu sau dubu, matsayin da suka rasa awurinmu kune kuke ruƙe da shi….” sosai ta fashe masu da kuka, Janyota yai zuwa saman chest dinsa ya ƙara yin hugging dinta yana lallashinta.

Daƙyar ya samu Batul ta dakata da yin kukan, bayan ya raba ta da jikinsa, ta rungume Angel sosai suka ƙanƙame juna, tsawon mintuna kafin suka raba jikinsu.

“Allah yabar Mana ke, Our Super star, Allah ya cika maki burikanki dake da Danishi ɗinmu” murmushi kowan nan su ya saki, sun ɗan jima a ɗakin Batul kafin suka Yi mata sallama, Sauran ɗaku nan su Azeeza suka shiga kowan nan su bacci ya ke yi, Ya haƙura sai zuwa gobe zai gaisa da su.

Komawa ɗakinshi su ka Yi, nurse jessica tace da Angel, zata kawo mashi Abinci, kafin ta dawo ta taimaka mashi Ya shiga toilet ya gyara jikin shi, amsa mata tayi da toh, Bayan fitar nurse ɗin, Taja hannun Danish suka shiga toilet, tun da suka shiga yake bin ko’ina da kallo, Karaf Ya ɗaura Idonshi Kan madubin toilet din A firgice taga Ya Juya mashi Baya.

“Danish meya faru”? Hankali atashe tayi mashi Tambayar

“Bana son ganin shi,” ba ta yi mamakin jin abunda yace mata ba, tunawa da ranar da tsohuwa tamira ta basu kyautar madubi, kowa ya duba fuskarshi, amma shi Yaƙi Yarda ya kalle shi.

Dubara tayi wurin Cire Hijabin jikinta, taje gaban mirror ɗin ta lullu6e shi.

“Nayi maganin matsalar Juyo ka gani” a hankali Ya juya yana kallon mirror din nan take ya sauke ajiyar zuciya, ganin ta rufe madubin.

“My Man, Ka fara Yin wankan, almost one week jikin ka bai ga ruwa ba, I’ll wait for you outside.” Akan idon shi ta fuce, a bakin ƙofar toilet din ta jingina Bayanta tana jiran fitowarshi, ta kasa kunne tana sauraron motsinshi, daɗi take ji kamar wadda akayiwa albishiri da gidan Aljanna, a ƙalla ta sauke ajiyar zuciya yafi a ƙirga fatanta Allah yasa subar america batare da sun samu wata matsala ba.

Gaba ɗaya hankalinta baya atare da ita, gangar jikin ce kaɗai, ruhin Yana atare da Danish dake acikin toilet, har Nurse jessica ta shigo ɗakin hannunta ruƙe da food trolley, ta gunguro shi zuwa gaban table, murmushi tasaki tana kallon Angel dake maƙale jikin toilet door, aranta ta ayyana ko dai soyayya ce a tsakaninsu, don wannan shaƙuwar tasu tafi ƙarfin a kirata da abokantaka.

Bayan ta ƙaraso gaban table din, ta soma jera kayan abincin saman shi, har ta gama jera su, ta juya da food trolley din duk Angel bata lura da ita ba, Har ta fuce daga ɗakin.

Jin motsin buɗe ƙofarshi, Yasa tayi saurin komawa gefen gado ta zauna tana faman sakin murmushi kamar wata zautacciya.

Zuro ƙafarshi yai saman carpet dake gaban ƙofar shiga toilet ɗin, Kafin ya ƙarasa fitowa, jikinsa da danshin ruwan wanka da yai, Ya maida uniform dinsa da aka sanya mashi.

Tun ya fito idonshi na akanta, ya lura da tsantsar farin cikin dake akan fuskarta, Hakan ba ƙaramin daɗi yayi masa ba.

Gefenta Ya zauna yana ƙare mata kallo

“Na fito” sai da ya ambaci hakan tukunna ta ɗago suka haɗa ido wani irin asirtaccen kallo suke jefa ma junansu kamar zasu haɗiye kawunansu tsabar ƙauna.

Lokaci ɗaya ta samu kanta da jin kunyar shi, Muryarta adabarbarce ta furta”am..um.. Ga abincinka da nurse ta kawo nasan kana jin yunwa” ta yi maganar haɗi da nuna mashi table din, ɗaura idonshi yai akan kayan abincin kafin ya dawo da dubanshi gareta”baki jin bacci? Naga sauran ƴan uwanmu suna yin bacci, ta hakan na fahimci dare ya nutsa”

Maƙe mashi kafaɗa tayi”bana jin bacci, inaso na zauna a kusa dakai, don na taimaka maka da wasu abubuwan, tun da yau ka farka ba ka san komai dangane da wurin nan ba, bana so in tafi in barka kai kaɗai a room” natsuwa yai yana kallonta, har ta ƙare maganar tukunna ya furta mata”nagode da kulawarki agareni, kuma nagode da nuna damurki akaina” still murmushin fuskarta bai washe ba
“Zamu ci abincin atare? Ko kin ci naki”? Yai tambayar yana duban fuskarta, Yafi son tana kallon Cikin idonshi idan suna magana.

“Bana jin yunwa, amma Zan Iya taimaka maka ka ci naka” amsa mata yai da”okey, ” miƙa hannu tayi tana buɗe plates din, lafiyayyan abinci aka haɗa mashi Grilled chicken with roasted vegetables, and black bean burger with sweet potatoes fries, hada Green tea a mug.

“My Man, komi da ka gani a saman table ɗin nan duka sai ka cinye shi, yadda kasha baccin nan na tsawon kwanaki nasan cikin ka babu komai ko ruwa ma babu, yanzu faɗamin me ka ke son fara ci? Cikin kulawa take yi mashi magana.

“Ki za6a min” murmushi ta sakar mashi, Mug din ta miƙa mashi, Yasa hannu biyu ya kar6a, a tsanake yake kur6anshi da zafi zafinshi, idonshi na akan face dinta, ta ƙurawa adam’s apple dinsa ido.

Batasan Ya janye cup din ba sai dai taji muryarshi acikin kunnanta”me kike kallo”? Yamutsa fuska ta ɗanyi”bakomai, tun da ka gama shan tea din, zaka Sha ruwa? Ko lemu”? Girgiza mata kai yai”a’a, tea din ya ishe ni, sai dai wani abun”

Kamar wani ƙaramin yaro haka take tarairayarshi, da hannu ta dinga bashi grilled chicken din yana ci, Idan ka kallesu a yadda suke zaune sai ka sha mamaki saboda girman da yai ma Angel, Bata wuci Ya lullu6eta da faffaɗan kirjinshi ba, amma saboda sabo da juna, da kuma shaƙuwa da ƙaunar dake a tsakaninsu bata ganin girman shi.

Ɗaya daga cikin abunda ke burgeta, idan ta tura mashi abincin abaki yadda yake motsa tattausan full lips nasa da kuma motsin Adam’s apple dinsa, komai nashi ƙayatar da ita yake yi kamar yarda itama ta ke burge shi, a ƙarshe sai suka koma suna feeding din junansu tana bashi abaki, Shima yana bata abaki.

Abunda basu sani ba, Har safiya tayi gari ya ware babu wanda Ya lura a cikinsu, tuni sun kammala cin abincin, sun shagala suna kallon juna.

*ABUJA NIGERIA A GIDAN ƊAN IYA*

A round ƙarfe 10 na safe agogon Nigeria, tun bayan kammala sallar Asubahi da ta koma bacci bata farkaba ba saboda Jiya sun sha fira da Aneelerh sun kusa raba dare kamar ƴa’ƴan Aljanu, shiyasa yau take ta sharar baccinta kamar matatta, ta wawware ƙafafuwanta saman mattress, ta saki baki da hanci, sai jan minshari ta ke yi kamar ragon sallah, daɗin bacci hada yawu a gefen bakinta, Gajeran wandone a jikinta sai ƴar farar half vest data zura, sumar kanta babu kitso zallar gashinta a hargitse ba gyara.

Tayi zurfi acikin baccinta, Wayarta dake ajiye saman side drawer ta buga uban ringing, Babu alamun zata farka har kiran ya katse, wani ya kuma shigowa, sautin ya cika ko’ina banda kunnan zahra dake yin bacci.

Shigowa cikin ɗakin Aneelerh Tayi, jikinta asanye da doguwar riga, ta yi rolling mayafi akanta, kaitsaye ta nufi drawer din ta miƙa hannu ta ɗauki wayar tana faɗin”Allah ya shirya zahra, wannan bacci haka kamar matatta, ana ta kiran mutun awaya wama ya sani ko arziƙi ne ke kiranta…” Waro ido waje aneeleeh tayi ganin sunan mutumin dake kiran Aneelerh, Ya fito 6aro 6aro saman screen din, bakowa bace face Hajiya Saratu Obinna, Jiki na rawa ta haye saman gadon takai hannu tana bubbuga ƙafar zahra”banza, ki tashi arziƙine ke kiran ki, zahra ki tashi kada muyi asara” yamutsa fuska zahra tayi muryarta kamar ta mashayin giya ta furta”dallah wanene ke takuramin, ni a ƙyaleni inyi bacci na, ba dama mutun ya ɗan kwanta ya runtsa sai an samu wani uban anacin ya tada shi’

cikin magagin bacci take yin sambatun. kiran har yayi rejecting, zuƙunnawa Aneeleeh tayi saitin kunnan ta da karfi ta furta”Shashasha Hajiya saratu obinna ce ke Kira” A haukace Zahra ta zabura Ta miƙe tana faman mutsustsuke ido, A fujajen take fadin”Wai dagaske? Ina wayar? Gaba ɗaya tabi ta ruɗe jin an ambaci sunan Hajiya saratu obinna, sai faman zazzare ido take yi.

Miƙa mata wayar Aneelerh ta yi “yo har yayi rejecting, Tun ɗazu nake ta ƙoƙarin tada ki, Kinƙi ki farka gashi yanzu kin ja mana asara….” bubbuga katifa zahra tayi da hannu tsabar takaici hada hawaye akan fuskarta”Aunty aneelerh, kin karyamin jari, meyasa da kika tada ni naƙi tashi baki shiga toilet kin ciko bokiti da ruwa kin watsa mun ba”?

Babu wasa akan face dinta ta yi maganar, Sakin Baki aneeleeh tayi tana kallonta

Zahra ta ci gaba da yin kuka tana faɗin “Nashiga uku, wayyo Allahna, ni wlh bakiyi min adalci ba, wama ya sani ko kujerar Hajji za’a raba mana,” sosai ta fashe ma Aneelerh da kuka. Lamarin ya ɗaure mata kai, ta rasa ina zahra da mahboob suka gado shegen son kuɗi, sai dai tafi tunanin ta 6angaren mahaifinsu ne.

Lallashinta ta soma yi”Kiyi hakuri sister kukan Ya isa haka, wata’kil ta ƙara Kiran ki,” cikin shessheƙar kuka tace”taya za’ae ta sake kira na, bakisan halin masu kuɗin nan ba, basu ɗaukar raini, za ta yi tsammanin dagangan naƙi ɗaga kiranta, Wayyo Allahna aunty Aneelerh, nayi wa arziki ƙulli, har ƙiyamil laili nayi akan Allah ya bude mun kofofin samu, da kuma miji nagari a sabuwar shekarar da zamu shiga…” dariyace kumshe abakin Aneelerh.

Dafa kafaɗarta tayi”Sorry My lovely sis, Yanzu abunda za’ae, Ki kira Layinta mu gani ko zata ɗaga” kar6ar wayar tayi daga hannun Aneelerh, Yatsun hannunta har kerma sukeyi sam babu natsuwa, kiran layin ta soma Yi, tamkar zata fashe da kuka ta kalli Aneelerh”line busy, dama ni nasani, wlh basa ɗaga kira, idan ba su suka kira mutun ba”

Aneelerh tace”mu ɗan ƙara haƙuri, zuwa anjima sai mu ƙara jaraba kiran layinta, yanzu ki tashi ki shiga toilet ki ki gyara jikin ki, zan Jiraki anan,” cikin shessheƙar kuka ta amsa da toh, kafin ta sauko daga saman gadon ta nufi toilet ta shige.

Bayan shigarta da mintuna biyar Aneeleeh tana zaune tsakiyar gadon tana jiran fitowarta, zuciyarta acunkushe take da tunanin baby junaid ɗinta tayi kewarshi, tun shekaran Jiya Uncle abdallah da hajiya adama suka koma gidansu, anyi rabuwar mutunci sun nemi alfarma Junaid ya zauna wurinsu na tsawon 2 weeks, zai dawo gida, sannan duk weekend za’a dinga kai masu shi, yanzu haka yana acan gidan nasu, tsawon kwana uku da yayi acan kullum ne sai ya matsa masu akan su kira mashi Mommyn nasa, wani lokacin tun kafin ta farka daga bacci kiran su ke shigowa wayarta saboda jarabar junaid.

Tayi zurfi cikin tunaninta, Wayar Zahra ta soma yin ringing, Kafin ta wurga idonta kan inda zahra ta ajiye wayar saman drawer, da ƙarfi taji sautin buɗe ƙofar toilet, Ras taji gabanta Ya fadi ganin zahra ta watso aguje, jikinta duk kumfa daga ita sai gajeran towel tayi ɗaurin gaba da shi, hatta fuskarta kumfar sabulu ce, miƙa hannu tayi ta rurumi wayar, tsabar zumuɗin ganin wanene ke kiranta, fatanta Allah yasa hajiya saratu obinna ce, cikin sa’a idonta yai mata nuni da sunanta akan screen, sai ƙoƙarin ɗaga kiran takeyi kumfar hannunta ta hana touching din yin aiki, kamar zata fashe da kuka, sai da aneelerh ta taimaka mata wurin answer mata call din tukunna ta samu natsuwa, a Hands free ta sanya kiran don suji me zata je
Cikin girmamawa zahra tayi mata sallama”Assalamu alaikum” kamar tana agabanta.
On the other hand sautin muryar hajiya saratu ya karaɗe kunnuwansu
“Wa’alaikum salam”
“Ina kwana hajiya, fatan kun tashi Lafiya, wlh bana a kusa da wayar ne, kunata kira bansamu damar ɗagawa ba, da yake na ɗan shiga toilet ne”

Aneeleeh dake zaune saman gado, dariyace ta kubce mata da sauri ta cakumi pillow ta toshe fuskarta dashi don kada sautin Ya fita, bakomai ne ya sanyata yin dariya ba face yadda zahara keyin waya kamar ƴar maroƙa, ga kumfa a jikinta.

“Bawani abu ai, nayi maki uziri, dalilin dayasa na kira layin ki, last time da kukayi mana decoration aikin ku ya yi mana kyau, muna so za’a ƙara Yi mana wani next week, sannan muna so za’a fidda mana anko wanda zai dace damu”

Da sauri zahra ta kar6e da cewa”in sha Allah hajiya komai kuke so za’ayi yadda ya dace, hada ƙunshi da kitso idan akwai mai buƙata”

Hajiya saratu tace”okey, You can send me the list of your services and I’ll add what I want to the list, through text message zaki tura min”

“Toh hajiya in sha Allah, Mun gode sosai, da kiranmu da ku kayi, kuma in sha Allah zaku same mu masu biyayya ga duk abunda kuke so,” bayan sunyi sallama da Hajiya saratu, Zahra ta sauke nauyayyar Ajiyar zuciya, Ta fasa ihu Tana faɗin”Alhamdulillah! lokacin Yin arziki na Yayi, wai yau ni ce Aunty saratu ta kira awaya? nayi mamaki wlh, matar tana burgeni bata ɗaukar raini, akwai harkar arziƙi.

Ta saki baki sai sambatu take yi, Kumfar Jikinta duk ta bushe har ƙasan tiles ruwan ke zuba, sautin dariyar Aneelerh ne Ya fargar da ita, da sauri ta jefa wayar saman mattress din, ta ruga da gudu ta faɗa toilet tana dariya.

Daƙyar Aneeleeh ta samu ta tsagaita da yin dariyar. Ta ɗago da kanta daga jikin pillow ta jingina bayan jikin head board.
“Aneelerh” muryar Mamie ce ta ratsa kunnanta, zumbur ta sauko daga saman gadon ta nufi kofar ɗakin, shigowa ɗakin Mamie Ta yi suka ci karo da ita”oh dama kina anan? Inata kiranki na duba ko’ina ban ganki ba” Aneelerh na murmushi tace”mamie kema kinsan bani da wurin zuwa a gidan nan inba ɗakin Ƴar uwata zahra ba”
“Okey, ina zahran”?

“Ta shiga toilet yin wanka, amma takusa fitowa

Mamie tace”Okey, idan ta fito, muna jiran ku a dining, ku zo muci abinci”

Ta amsa mata da toh, bayan fitar mami ɗakin, komawa ta yi gefen gadon zahra ta zauna, bada jimawa ba zahra ta fito chest dinta daure da towel, da zolaya Aneelerh tace”Lashe money an fito lafiya”? Tuntsirewa zahra tayi da dariya tana fadin”aunty aneelerh kuɗi duniyane, Dole inso kuɗi, saboda sune maganin talauci, maganin ƙasƙanci da wulaƙanci, idan kina da kuɗi kin fi ƙarfin raini wlh, girmama ki za’a dinga yi kamar wata basarakiya, taya mutum bazai so kuɗi ba? Yanzu fa ko a dangi masu kuɗi sune masu faɗa aji, idan baka da kuɗi toh baka da banbanci da Allon bango”

Fashewa Aneeleeh tayi da dariya, zahra ta zaƙe sai kora mata jawabi ta ke yi dangane da kuɗi.

“Zahra wasu kuɗinfa ba alkhairi bane, suna kai mutun ga shagalar duniya har ya halaka”

“Aunty Aneelerh, nima ai bana roƙon Allah yabani kuɗi kaitsaye batare da nace Allah yabani masu albarka ba, kuma ni burina inyi arziƙi don al’umar annabi su amfana da ni, Ina kwaɗayin inga na taimaki marasa ƙarfi….”.

“Zahra Allah ya dubi kyakkyawar niyarki, inayi maki fatan Alkhairi”
“Ameen auntyna”

Shaf shaf ta kammala shiryawa, cikin riga da skirt, ta dawo gefen Aneeleerh ta zauna bayan ta ɗauki wayarta

“Ki tashi muje muci abinci, su mamie suna jiran mu a dining”
“Inaso ne in fara turama aunty saratu list na abunda mukeyi, zaki Iya zuwa kada su ji mu shiru” miƙewa Aneelerh tayi daga gefen gadon ta fuce daga ɗakin.

Through text message ta tura mata saƙon kamar haka

Here’s a list of services that “Zahra’s World of Beauty” could offer:

– Bridal makeup and hairstyling
– Event planning and decoration
– Haircuts, color, and styling
– Manicures and pedicures
– Facials and skin care treatments
– Massage and body treatments
– Waxing and other hair removal services.

Bayan ta kammala rubuta sakon a ƙalla saida ta maimaita shi yayi sau ashirin gudun kada ace tayi kuskure kafin ta tura mata, fuskarta ɗauke da murmushi ta ajiye wayar saman pillow, ta miƙe ta nufi falo domin Yin breakfast, fatanta Allah yasa Hajiya saratu ta mayar mata da martanin saƙon da wuri, taci buri sosai akan zuwa estate dinsu, ko dan ta haɗu da Owais idan Allah yasa lokacin ya dawo ƙasar.

*KURKUKUN ƘADDARA*

*AN YANKA TA TASHI☠️*

Babban ɗakin tarone mai girman gaske, wanda akeyiwa laƙabi da fadar matsafa, Mallakin shuwagabannin kurkukun ƙaddara, ta ko’ina manya manyan matsafane maƙil acikin fadar, zazzaune saman kujeru dake a jere tsakiyar fadar, kowannansu yana sanye cikin shiga ta baƙaƙen dogayen riguna masu huluna, sunyi 6adda kama ta yadda mutun bazai ta6a Iya ganin koda ziririn gashin kansu bane, Hannayensu da ƙafafuwansu baƙaƙen safunane, Yayin da fuskokinsu sun sanya masu mask me suffar ƙwarangwal gwanin ban tsoro, saƙo da lungu ta fadar, Wasu Gabza gabzan giants ne daga masu ƙaramin miƙami har izuwa manyansu masu star uku a gaban kakinsu, wata irin ƙira garesu mai matuƙar ruɗarwa, rikitarwa da razanarwa da kuma tsoratarwa, kallonsu kaɗai zai Iyasa zuciyar mutun ta buga, Ga tsawo da Allah yayi masu tun daga kan tsayuwarsu zaka tabbatar babu ɗigon imani akansu.

Daga can saman karagar fadar, wasu jigunannun arm chairs ne guda shidda ƴan ubansu, mutane shiddan dake zaune saman kujerun dogayen rigunane launin jajaye na maza a jikinsu masu huluna, baka ta6a Iya tantance suffarsu saboda sun 6oye ko’ina na jikinsu, hannyensu na ruƙe da Sanda wadda aka ƙerata da zallar zinari, daga gabansu zungureran teburi ne, samanshi maƙil Yake da kayan ciye ciye dana shaye shaye daga ciki hada Jinin mutun da farfesun naman mutun ga zungura zunguran kwalaban giya, da Kayan marmari nau’i kala kala, da gasasshen nama na dabbobi daban daban.

Komai na fadar matsafan tun daga kan ƙofofi da tagogi da fentinta da jan carpet din dake shimfiɗe ƙasanta, gaba ɗaya Launin baƙi da Ja ne, saman rufin fadar wasu haɗaɗɗun fitilune masu haskaka cikinta.

Zanunnukan dake a jikin bangon fadar, na kan ƙwarangwal ne, da yatsun hannun shaiɗanu masu akaifu zaƙo zaƙo da sauran zanunnuka masu ban tsoro.

Daga gefe ɗaya tacan 6angaren da Arm chairs din nan suke Tanƙameman madubine wanda suke Kira da Allon tsafi, gaba ɗaya Hankalin matsafan yana akan Allon tsafin nasu, fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta gifta, ga dukkan alamu wani abu suke kallo wanda yai silar ɗauke masu hankulansu……….

(Nima kuma na ɗauke alƙalamina)

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

 

First bank

 

3196407426,

 

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

Back to top button