Hausa NovelsNamijin Zuma Hausa Novel

Namijin Zuma 18

Sponsored Links

💖🐝NAMIJIN ZUMA PAID PAGE 18💖🐝 THIS BOOKS IS ONLY 1K 0810162684

Tinda nabeelah taga maganganun manya na shiga tsakaninta da Aeezad har an kaiga ya bude baki yace ze zuqa bakinta kuma ya taba nono, Dan haka tadena sakar masa Fuska, tsakaninta dashi ya jiki kawai ke rabasu . Sam hakan be hana Aeezad Dena abinda yakeyi ba sbda bayin kansa bane, yadda kasan me Aljanu haka ya rikice, ko gaban big hajiyata be iya daurewa se yayita mata kalamai kasa kasa, kullum cikin shafar mata hannu yakeyi kamar tsohon maye , data ajiye hannunta a gefen gadon da yake se ya hau shafar mata hannu, sede tayi sauri ta dauke hannunta, gabaki daya ya haukace duk inda nabeelah tayi idansa na kanta kamar mahaukaci, ya zamar ma nabeelah matsifa. Yau da Hauwa’u tazo garin kadunan duba jikin Aeezad domin bata samu zuwa ba da suna garin katsina, seda hafsat ta Kira Aeezad ta sanar dashi hauwa’u zatazo kana aka barta tashigo. (Tini an kawo masa duka wayoyinsa da aka gani a cikin motarsa , ba abinda ya samu motarsa da komi nasa na ciki , komi an kawo masashi yadda yake)

Tinda hauwa’u aminiyar nabeelah tazo ta fahimci Tabbas akwai wani abu a tsakanin Aeezad da nabeelah ne tsanani, daman tin kafin abun yayi zurfi jikin hauwa’u ke bata abubuwa da dama a kan Aeezad, Tasha zuwa ta gansa zaune kan cinyar nabeelah a gidan Aunty hafsat, tin a nan ta fahimci tabbas wani abu na iya faruwa nan gaba, Tasha gayawa nabeelah amma seta nuna mata ba komai kawai.

Da yammaci , Bayan sun fito harabar asibitin nabeelah sanye da hijjabi har kasa ta rako hauwa’u wadda ke sanye da babban mayafi har Kai, zata tafi gidan wata yayarta dake aure a kadunan hayin d’an mani, daman tayi niyar intazo taje gidan yar uwarta tayi 2days sbda a mota dreva ya kawota. Suna tafe suna yar hira hauwa’u ta chanza hirar dacewa, bayan sun tsaya gefe gindin wata bishiya. “ kawata yanzu de kin tabbatar Aeezad na sanki kou?” Nabeelah ta kalli hauwa’u dake mgnr kawai ba tare datace komi ba. Hauwa’u bata damu da shirun datayi ba sbda tasanta da zurfin ciki se ajiyar zuciya kawai nabeelah ke saukewa. “Kawata ya kamata ki rage zurfin ciki nan naki, ki dinga fadin cikinki, duk kinbi kin rame kmr bake ba, ki dena barin abu a ranki, ba komi ake bari a rai ba, me shawara aikinsa baya baci sede bashi da sirri …” kmr nabeelah na jira ta amshe da “wallahi kawata na rasa ya zanyi, tunanin Aeezad ne kawai ke ramar dani,..” nabeelah ta fadi sbda ta gaji da Ajiyar abun a ranta, ko yayane tanaso tayi sharing problems dinta ko zata samu sasssaucin abinda ke ranta. “Kamar ya? Gaki a kusa dashi tunaninsa name kkyi?” Hauwa’u ta tambayeta fuska cike da mamaki , a zuciyarta Tana hango tashin hankalin dake tinkaro kawarta sbda tas hajiya rafi’ah. “No ba wannan ba,, bakiga abinda yakeyi ba, se yadinga kmr wani sabon kamun hauka, se yadinga wannan abu haka bakai ba gindi, ni tsorona Allah da Annabi kada big hajiya ta gane, ko kuma wasu daga family dinsa su gane, wlhi a tsorace nake kullum cikin tunani-tunani nake, kaf dina a tsorace nake kar abun ya kai har na’eema matarsa ko hajiya mommy su gani, wlhi tsoro nakeji kmr na gudu na bar gidan na koma kasata nagaji…” nabeelah ta fadi muryar cikin tashin hankali, gabaki daya bata da kwanciyar hankali. “Sone Aunty naneelah, tin tini na fahimci akwai sanki a kwayoyin idanuwan Aeezad,, yanzu na fahimci abin yayi yawa, kin gansa kmr zeyi hauka, wlhi duk baya hayyacinsa, kamar ba Aeezad ba dan mulki…” “hmmm kadan kika gani, wallahi gabaki daya yaron ya rainani, nifa na rainasa tin yana jariri , naci kashinshi naci fitsarinsa Hauwa’u , amma yanzu ya rasa wazece yanaso wai seni,, gabaki daya ya fita a raina, rainin da yakemin yasa har gidansu naji ya fitarmin a raina wlhi…” Cewar nabeelah. “Wani irin raini?” Hauwa’u ta tambayeta cikin rashin fahimta . “Kinji abinda yake gayamin ne ,,,waishi yana sona , shi kaza-kaza, wallahi wata maganar ma bazata fadu ba, hauwa’u yadda kksan bani na reni yaronnan ba, a banza fa na bashi 10yrs, wlhi in yana gayamin kalmar so kazanta kalmar kemin se inji kamar in kashe kaina in huta,,,,yaronnan yasa gabaki daya duniya ta batamin dadih, so yakeyi kawai indena Jin dadin duniya kuma nadena ji kwata-kwata, duk na kosa da zaman jinyar nan tasa, dabadan daddy ba wlhi tafiyata zanyi , ni barin kasar yafimin Alheri se in bar masa kawa…”hauwa’u dake kallon nabeelah harta Kai ayar zancenta, kana hauwa’u ta dauke dacewa “kawai danyace yana sanki seya zama mgnr rashin kunya, So halitta ne kuma ba karya bane, duniyar ma a kan SO aka ginata, shiyasa Ubangiji ya halicci namiji da mace yayinda yasanya soyayya a tsakaninsu, gabaki daya in zaki kula shi kansa bayin kansa bane, duk me hankali inya kallesa seya tabbatar be cikin hankalinsa, gabaki daya bashi da nutsuwa se kallonki yakeyi kmr ze hauka, bakiga da kika fito falo ba Dazu yadda yadinga lekar kofar daki, har cemin yayi dan Allah inzo in dubaki , zan fito dubakinne kika dawo, bakiga ba kmr zararree shi kansa nasan ko matarsa ta Aure be mata san da yake miki, domin da yana mata da baze taba yarda ya zauna asibitin bata nan ba…” nabeelah daketa kallon hauwa’u yayinda kalamanta ke bata mata rai ji takeyi kamar ta rufeta da duka saboda zallar takaici da bakin cikin yadda taketa goyawa Aeezad baya, ita ta kilama Sam bata ganin lefin Aeezad a kan wannan lamarin . “Hmmmmm…. Wai shin kin manta ni na renesa da hannayena, na Goyasa a bayana, yanzu yazo min da mgnr SO harda mgnr Aure,..Haba Hauwa’u wlhi ana barin halal dan kunya, ko SOna ne Ajalinsa bazan SOshi ba gaskiya, ni bazan iya abun kunya ba,bada niba!”
“Inke kika renesa ai bake kk haifesa ba, kuma Addini be Hana Aurenki dashi ba, aunty nabeelah karki bari kiqi sharar masallaci kiyi ta kasuwa, ki duba kiga yadda yakeyi, har taba miki hannu yayi fa Dazu ina gani, gabaki daya a rikice yake a sanki tin zuwana na fahimci hakan, nabeelah dan Allah ki Amince masa kuyi Aurennan da hanzari, kar gudun abun kunya, yasa kisema kanki abun kunya da kudinki…” Cewar hauwa’u ita mutum ce me saurin fahimta data zauna dakai a yan seconni take fahimtarka. “Allah ya kyauta, karamin yaro kmr wannan, ubangiji ya tsareni… dan Allah kima bar mgnr nan, wlhi babu sanshi a raina, bazan taba San Aeezad ba, San Da Uwa takewa d’a nake masa bawai san soyayya ba…” nabeelah ta fadi yayinda data chanza face, maganar Aeezad dince a gabaki daya ta ginsheta. Nan take hauwa’u ta fahimci hakan dan haka tace “To shikenan Aunty nabeelah, amma ki sani masoyinka yafi makiyinka ako wani irin hali, wani yanacan ko numfashinka beso inya ganka ma bakin ciki yakeji kmr ya kasheka, amma shi kinga in be ganki ba kmr za a zare masa rai wlhi bakiga yadda ya dinga yiba dazu, kmr wanda zeyi hauka tuburan, Ina kula dake da abinda kk masa, koda baki sanshi be kamata ki dinga wulakantasa ba, ko ya-ya ne masoyi yafi makiyi, kuma bashi yasawa kansa ba, wlhi wanda yace yana sanka koda a fatar baki ne ya gama maka komi duniya da lahira, Balle shi wannan dayake kmr zararre, ki duba lamarin nan dannAllah’’ saurarenta kawai nabeelah keyi amma babu kalmar datai tasiri a ranta, tama hauwa’u uzuri sbda batasan mezeje ya dawo bane ita, ita kuma nabeelah tasani. “Kawata koda ace bani na raini Aeezad ba ai kinsan ni ba sa’arh soyayya dashi bace Balle Aure, ya fini gata, yafi kaf dangina kudi, yafi kowa nawa mukami, ga ilmi Kinganshi me ilmi ne ni kuma bani dashi, ban taba zuwa makarantar boko ba, kece kika koyamin saving suna da iya karantun hausa da rubutawa,,, ki gayamin ta yadda za ayi ace anyi kwad’on tuwo da Toka? Ai kinga hkn bame yuwwa bane, sannan koda ban girmesa ba jama’ah zasu zageni ace dan kudi zan Auresa a misali kenan” “ke kika damu da wad’annan, shi SO ina ruwansa da Kudi ko nasana ko ilmi, So ba ruwansa da wannan, Kinga SO ba ruwansa da kunyar duniyar, meyin SO idanuwansa kullewa sukeyi, baya bukatar a kara masa zafi biyu, ga Zafin SO ga wani zafi can da ban,,,,” Cewar hauwa’U gabaki daya tinda taga yadda Aeezad keyi na yau kawai data gani tausansa ya cika mata zuwa. Kauda Kai kawai nabeelah tayi danta kula hauwa’u bazata fahimci me take nufi ba. “A bar mgnr kawai kawata bazaki gane ba…. Na hadu da wani tin a kano Sadi, ya kwantamin a rai dukda ba wani fara sanshi nayi ba, amma kawai ya burgeni ne ya hada abinda nakeso a jikin d’ana miji, inaga time yayi da zanyi Aure, naji a raina zan iya Aure ynzu a kan wannan bawan Allahn…” nabeelah ta kare da bawa hauwa’u labarin haduwarsu da Alhaji Sadi da yadda akayi suka hadu, ta bata labarin komi bata boye mata ba. Jinjina zancen hauwa’u tashiga yi a ranta,. “ Allah ya zaba abinda yafi Alkhairi…” shine kawai abinda hauwa’u ta fadi yayinda a ranta tunannika tashigayi. Aunty nabeelah ta amshe da Amin amma a ranta tasan Alhaji Sadi nema Alkhairi gareta. “Har waje fa zaki rakani napep zan hau zuwa gidan Aunty nafisa, kinsan da dreva ya ajiyeni kawai wucewarsa yayi gurin gyara, motar daman da kyar ta karaso Damu garinnan…” nabeelah tace “Subhanallahi,,, Danma Allah ya rufa asiri duk kin bar yaran gida…” hauwa’u tace .”Eh wallahi, inda Allah ya temakeni kenan, da Bansanma yazanyi ba, Kinsan har mutuwa tadinga mana a daji motar nan Kai karfen nasara ba tabbatas…” “gaskiya Allah ya kara tsarewa…” Cewar nabeelah . Hauwa’u ta amshe da Amin yayinda sunaci gaba da tafiya zuwa bakin get. Suna tafe sunaci gaba da hirarrakinsu. nabeelah nata kara bawa hauwa’u labarin Alhaji sadi, nan hauwa’u ta kara tabbatar da tabbas Alhaji Sadi ya samu matsunni a zuciyar kawarta, domin tinda nabeelah take bata taba bawa hauwa’u labari ba a kan wani saurayi. Daga haka suka iso bakin ti-ti, nabeelah na shirin tarewa hauwa’u me napep, wata dankareriyar mota tayi packing daf dasu, motar bakace kirin , kirar Mercedes new model ta shekarar, dagani ko ba a gaya maka ba, Zakasan mamallakin motar ba karamin mutum bane , tako ina motar ta tara kyau se wal-wal takeyi Sam karamin me kudi be isa ya hau irin wannan motar ba. Ba bata lokaci ya bude motar ya ziraro kafafuwansa na zallar yan hutu wadanda launin kalar fatarsu daban take data kowa sbda Hutu. tin kafin ya karasa fitowa kamshin danyar shaddar gezner dake jikinsa ta doki kaf hancinayensu. Ya fito sanye da shadda launin C-green se walkiya shaddar keyi kmr bayan maciji, ya kafa hular sakar hannu ta kasar waje, hannunsa sanye da danyen diamond, se murmushi yake sakarwa nabeelah yayinda nabeelah tuni ta ganesa Alhaji sadi ne, tabbas ya kara shiga ransa, dukda bashi da kyau amma komi nasa ya mata. “Ina wuni ranki ya dade…” ya gaishe da nabeelah cikin ladabin da SO kesaka ka koyeshi dole komin girmanka, ko ince komin mukami da isarka, Inkaga mutum na rawar Kai ka kyalesa kawai be afka so bane, SO ne kadai ya isa ya koyar da mutum ladabi da biyayya. Kafin nabeelah tayi magama hauwa’u ta amshe da . “Bawan Allah lafiya zaka tare mutane a ti-ti bamu sanka ba baka sanmu ba…” Alhaji Sadi ya kara fadada murmushinsa yace “Allah sarki yar uwa kece baki sanni ba ita ta sanni kou?” Nabeelah ta daga Kai hadi da Tabawa hauwa’u hannu kasa kasa tace “Shine wanda nake baki labari…” “okay..yi hkri dan Allah nasha bata sanka bane… Ina wuni…” hauwa’u ta karashe da gaidasa cikin girmamawa sbda ko a ido tasan ba sa’anta bane. Alhaji sadi daketa washe baki kmr yaga lafiyayyen gindi a bude yace “Aaahh bakomai yayarmu…” ya amsa gaisuwar hauwa’u danshi a zatonsa ko itace yayar nabeelah sbda ya ganta wata shirgigiya da ita tanada kyau sosai, amma jikinta da Fuskarta sun nuna masa alamar ta girmi nabeelah nesa ba kusa ba, a zahiri kuwa nabeelah ce ta girmi hauwa’u,. “Ba yayata bace kawata ce …” Cewar nabeelah. Alhaji Sadi dake tsaye yace. “Af yi hkri kawarmu, kice itace a high table a dinner party dinmu…” wani murmushi ya subucewa nabeelah, bata taba tsayawa da namiji ba a lokaci kankani ta sakar masa wannan murmushin me tsada ba se yau,. Aiko nan take murmushin yayi tasiri a zuciyar Alhaji Sadi ya kuma narke wa a soyayyarta, nan suka shiga sakarwa juna murmushin Soyayya, ganin sun tafi a juna yasa aunty hauwa’u matsawa gefe ta zubo musu idanuwa kawai. “Kusan kullum senazo amma sojojin dake bakin get basa barina shiga , na rasa ya zanyi da sanki a raina, wlhi Ina sanki, so nakeyi se kun bar asibitinnan se inje gidanku na turo maganata na, a wacce anguwa kike a katsinar?…” Cewar Alhaji Sadi. Nabeelah da kanta ke kasa sbda kunyar da take dashi in Tana gaban namiji Sam bata kallansa, musammanma Alhaji Sadi Tana jin kunyarsa sosai, a kunyace tace “ni ba yar katsina bace…” Alhaji Sadi seda ya lumshe ido sbda dadin muryarta daya ratsa shi. “Kaji mace, ynzu zanyi Auren macee me aji wadda ko magana tayi se naji gabana ya tashi, ba mace me muryar maza ba….” Alhaji Sadi ya fadi a ransa, domin shi mutum ne me lafiya, yana bukatar mace, bashi da ciwo ko daya a jikinsa balle yasa al’aurarsa rauni, mabukaci neshi sosai. “Okay a wani gari kke? Niko yakai nan da birnin sin zanje garin masoyi ai baya nisa….” Alhaji Sadi ya iya kalamai Kai kace matashi ne dan shekara ashirin da biyar, dan haka nan da nan ya kuma narka zuciyatar nabeelah ya kara burgeta sbda tanaso ta Auri namiji d’an soyayya sannan me jaraba, sbda itama tasan jarababbiya ce ta karshe tana tsaka da bukatuwa da d’ana miji, kawai kawaici ne da juriya datake dashi, amma dataci ta koshi abu na biyu da take bukata d’ana miji, tanada cikakkiyar lafiya itama datakeda tabbacin iya mata se ainifin jarababben namiji. “A Niger 🇳🇪 nake cikin garin agadex…” cikin mamaki Alhaji Sadi yace “haba ni ai nasan da mamaki wannan halittar ace a nigeria kike, ni ai nasha ko balarabiya ce ke ma iyayenki suka kawoki nigeria, ashe buzuwa ce, na kara sanki sosai, wani mataki kk a karatu?” Nabeelah da kanta ke kasa tayi shiru bata basa amsarsa ba amma a fuskarta Alhaji Sadi ya fahimci amsarta. “Karki damu ina sanki a haka, in mukayi Aure se muje Kasashen dasuka fimu ci gaba kiyi karatu a can, nide Ina sanki so me tsanani, dafatan kema haka ?” Rufe fuska nabeelah tayi cikin kunya Alhaji Sadi ya bude baki zeci gaba da magana hauwa’u dake gefe ta gaji da tsayuwa tace “kawata inaga napep dinnan zan tara, sena dawo zuwa goben kawai naga yammaci na karayi har biyar na neman wucewa …” Alhaji Sadi ya amshe da “Ina zakije?” Hauwa’u tace “nan gidan yayata zanje dake nan hayin d’an mani…” Alhaji sadi yace “Toh nagane d’an mani, inba damuwa ki shiga se in kaiki kawai …” hauwa’u tace “Aah ka barshi kawai zan hau abun hawa kar in katse muku zancenku…” nabeelah ta amshe da “kawai ki hau a kaiki hauwa’u inde ba damuwa…” hauwa’u tace “ba damuwa wallahi…” Alhaji Sadi yace “To shikenan bari in kaikin,, minti biyu mu karasa mgnr mu…” hauwa’u tace “bakomai….” Ta d’an kara matsawa daga inda suke. Alhaji Sadi ya koma Cikin motar ya dakko wata yar leda me azabar kyau pink, ya bude ledar kwalin waya ne a ciki , ya fito da kwalin wayar ya bude, nan iPhone 12prp ta bayyana, ya mikowa nabeelah wayar hadi dacewa “Ga wayar danase miki tin rannan bansamu an barni na shiga ba aka cemin sir Ahamad ne ya hana a bar kowa zuwa inda yake… nasa miki sim a ciki , kiyi using kafin ki koma gida seki cire sim dinki na dayar wayarki kisa a ciki, in kika shiga ciki seki fara da bude ICloud dinki first kafin ki fara dauko Apps…” nabeelah ta dago ta kalli wayar dayake miko mata, nan take ta girgiza Kai Alamar “Aah…” “meyasa? Ki temakeni ki amsa, sbda innazo se in dinga kiranki ko fitowa ne se kiyi muyi zancenmu in koma base na shiga ba, inaga ma nan da 4days zan koma daman sbda ke nake zaune a garin nan..” nabeelah ta kara cewa Aah ya barshi ita tanada waya. Nan Alhaji Sadi yashiga rokonta Allah Annabi ta Amsa, da kyar ta amsa Sam badan taso ba, ta amsa tashiga jero masa godiya hadi da sakawa dukiya albarka, Alhaji Sadi ya kureta da ido yaji dadin adduarhta garesa, aduniya ba a taba masa adduah data dinga masa ba, ko matarsa da yake aure duk abinda ze bata bata taba masa irin wannan godiya da Adduarh ba, nan take Alhaji sadi ya tabbatar nabeelah tasamu karatun addini me zurfi. “Nine da godiya fatanade Allah ya nunamin ranar Aurenmu…” nabeelah tayi murmushi kawai, daman tini alhaji sadi ya fahimci yarinyar nada kunya me tsanani. “Shikenan se munyi waya bari inje in kai kawarmu, zuwa anjima zan kiraki …” Cewar Alhaji sadi. Nabeelah tace Toh hadi da kara masa godiya har seda yace ta isa hakanan godiyar, kana nabeelah tayi shiru, ta Kira hauwa’u dake kallon komi dasukeyi jinsu ne kawai batayi, ta nuna mata wayar da Alhaji yase mata nan hauwa’u ta masa godiya itama, Alhaji yace bakomai. Hauwa’u tashiga motar Alhaji Sadi gidan gaba, sadin yashiga dreva side, ya sauke glashinsa ya kure nabeelah da ido se murmushin SO da kauna yake sakar mata “ki kula da kanki,,,,” nabeelah ta daga masa Kai alamar toh, kana Alhaji ya juya motar yabar gurin idansa na kanta har seda ya kule ya dena ganinta kana ya rufe glass dinsa, nan ya farawa hauwa hirar irin San da yakewa nabeelah hauwa’u najinsa ne kawai, amma a ranta tasan San da Alhajin sadi kema nabeelah ba komai bane ,akan San da Alhaji Aeezad ke mata a duniyar nan hauwa’u ta tabbatar nabeelah bazata taba samun me mata San hauka kmr yadda Aeezad ke mata.

Seda nabeelah tadena hango motar Alhaji sadi kana ta koma cikin asibitin wayarta rike da ledar dake dauke da kwalin wayar. A harabar asibitin packing space nabeelah taga motar Zaks, tin tsayuwarta ba jimawa taga motar zaks din tashigo asibitin amma bata lura da motar ta Zaks bace se yanzu dataga lambar motar domin kusan lamba daya suke using , lambobin mota daya suke using Aeezad da Zaks. ba tare da nabeelah tayi wani tunani ba, ta nufa ciki. Tana sako Kai ta gansa tsaye a falo, yayinda zaks ke tsaye kusa dashi yanata basa hkrin da nabeelah batasan ko hakurin meye ba, batasan tin shigowar Zaks daya ganta tsaye da Alhaji Sadi, yazo cikin raha ya sanar da Aeezad “naga mamanka me kayan Alayu tsaye jikin wata mota tana zance da wani Alhaji me tumbin kudi….” Ai nan Aeezad yaji kamar an tsikaresa ya tashi a gigice, daman yaga ta juma sosai, big hajiya dake kusa bataji me Zaks ya sanar da Aeezad ba, kawai sede taga ya mike tsaye a gigice. “Meya faru me suna me daraja?” Big hajiya ta tambayi Aeezad wanda keta huci. “Bakomai big hajiya.,.” Kawai shine abinda Aeezad ya fadi besanma ya fadi ba sbda baya hayyacinsa ya fice a dakin gabaki daya kishi ya rufe masa ido da kyar yake tafiya, tinda ya fara ciwo be taka kafarsa ba se yau, ko ranar dasukaxo asibitin har kofar dakinsa mota ta kawosa ya fita taku kadan ya isa cikin dakinsa dake kasa downstairs. Hajiya se tambayarsa takeyi ina zeje amma Sam bejita ba ko ganin hnya beyi sosai ya kosa yaje wajen ya tabbatar da Abinda Zaks ya gaya masa. “Hajiya zamuje ne ya d’an zagaya…” Cewar Zaks. Big hajiya tace “Toh ze iya tafiyar kou? Kode inzo in rikesa ne? Naga har yanzu nabeelah bata dawo daga rakiyar hauwa’u ba balle ta rakasa ita ,,,” Zaks yace “Karki damu big hajiya ni bari in bishi,….” Big hajiya tace “To d’annan ka kulamin da jikana kagade hannun nasa ba wani warkewa yayi ba… ni bari in shiga wanka…” Zaks yace “To hajiya’’ kana ya fice a dakin ya biyo Aeezad, nan bakin get ya gansa ya zubowa nabeelah da Alhaji Sadi dasuke tsaye ido , zuciyarsa ta cunkushe kmr zata tarwatse idanuwan nasa sukayi red, da badan nabeelah da Alhaji Sadi sun afka a kogin soyayya ba Tabbas dase sun hango Aeezad sbda basu da wata tazara sosai. “Kaga renin hankali kou ? Ashe tad’i zatazo yi, ta tsaya da wani shege se murmushi take masa, bari in karasa in kasheshi kowa ya huta….” Aeezad ya fadi a zafafe sbda bacin rai da kyar muryarsa ke fita. Zaks ne ya rikosa da kyar yashiga basa hkri, Ada yaso ya isa inda suke, Zaks yayi nadamar fada masa da yayi, tini Zaks ya fahimci Aeezad nasan nabeelah amma daya tambayesa yace masa kawai San uwa yake mata last zuwansa sukayi wannan maganar. Aiko zaks yaga hauka da kyar yasamu ya jawo aeezad zuwa cikin falon dakinsa, yashiga dannar masa zuciya yadda ya rikice wa Zaks din ba karamin tsoro ya
Bashi ba, Tabbas Zaks ya kuma tabbatarwa da bakaramin SO Aeezad kema nabeelah ba, San da duk wanda ya rabasu dole se ubangiji ya kamasa. Nan ya kara rikicewa Zaks da kyar Zaks ya dinga basa hkri har yasamu ya tsaya a falon amma da dakinsa ze nufa ya dakko bindiga yaje ya kashe Alhaji sadi, ran maza ya baci nan take allurar sojojinsa ta motsa ya gigice ya zama kmr bashi ba, a haka nabeelah tashigo tasamesa tsaye ya zubo mata red eyes dinsa jikinsa se rawa yakeyi bata taba ganinsa a yanayin data gansa yanzu ba, dan haka nan take ta tsorata. “Daga gun dan gidan uban wa kike? Aeezad ya tambayeta cikin kunar zuciya muryarsa ta kuma disashewa sbda zallar bakin ciki da azababben kishinta da yakeyi. Yadda yayi mgnr yasa jikin nabeelah rawa, nan take taji wani irin tsoronsa ya rufeta ledar dake hannunta ta fadi, itama ta gigice sbda bata taba ganinsa a yanayin da yake ba yanzu, yadda ya mata tambayar ya tabbatar mata da kila yaganta ne da sadin, sbda ta kula da kishin dake kwance Cikin fuskarsa. “Ni zakiwa iskanci da wulakanci da cin mutumci, Ina tambayaki kinyi shiru munafuka!. nace daga gidan uban wa kke?”” Ya kara tambayarta Cikin tsawa Tabbas da muryarsa na fita dole se big hajiya dake ciki taji. Zaks dake tsaye yace “pls sir ka sassauta dan Allah…” shi kansa Zaks din hankalinsa a tashe yake. Nabeelah kam Tana tsaye jiki se rawa yakeyi. “Bazan sassauta ba ….!!” Aeezad ya fadi cikin matsifa yana kallon Zaks, Zaks be kuma mgna ba ganin bala’i na neman dawowa kansa. “Ke bada ke nake ba?” Aeezad ya fadi yayin da yake nufo kan nabeelah gadan gadan tsoro ya kara kamata ganin yana tinkarora, tayi hanzarin cewa murya na rawa “daga…daga….daga,….rakiyar,,,,hauwa,,,,u….” “Hauwa’un ubanwa? Ni zakima karya? Kina wasa dani kou? Ni zakima karya dan wulakancin banza da hofi zaks kaji me take cemin kou? Kaji Tana min renin hankali bayan na ganta tsaye da Tsinanen nan tanata masa murmushi kmr kanin ubanta, ashe ke mayyar maza ce bansa ba, ni zaki mayar dan iska, toh yau zan tabbatar miki ni waye a duniyar nan …” yana mgnr ne bayan ya karaso daf da ita duk yabi ya rud’e ya rikice hankalin nabeelah kam in yafi dubu seda ya tashi . “Easy mana pls sir,,, kayi hkri…” Cewar Zaks daya fadi a tsorace dan shima tsoronsa yakeji sbda kar yadawo Kansa dan yanzu in ya rufe nabeelah da duka shi ba iya kwantaeta zeyi ba dukda hannunsa daya ne me lafiya. “Durun uwar hakuri zanyi,,, ni wannan yarinyar zata renawa hankali wlhi bazan hakura ba!” Aeeezad ya fadi yana kallon Zaks, nabeelah jiki se rawa yakeyi yayinda kalmar daya fadi ta yarinya ta tsaya mata a rai a zuciyarta tace “Lallai raininsa ya shahara wai yau itace Aeezad kecewa yarinya…” a zahiri de babu bakin mgna sbda tsoro. dukawa Aeezad yayi ya dauki ledar da nabeelah tashigo da ita ta wurgar a kasa, ya fito da waya da makudan kudi rafa daya na dollars , Sam nabeelah batasanma Alhaji Sadi yasa mata kudi a ciki ba Tasha waya ce kawai a ciki. “Ni zakima karya? Kince daga gun hauwa’u kk? Waya baki wannan wayar da kudinnan?” Nabeelah tayi shiru yayinda kmr muryarsa zata fasa mata dodon kunne sbda daf take dashi. “Bada ke nake mgna ba… ni zakiwa wulakanci,, wlhi wlhi senayi maganinki, wani dan Tsinanniyar ne ya kawo miki wayarnan da kudinnan!?” Ya karashe hadi da buga wayar da kasa cikin zafin zuciyar dashi kansa besan yanadashi ba se yau, nan wayar ta tarwatse a kasan tiles ta fashe ta gaba ta baya, ya wurgar da ledar kudin dake hannunsa ya dago hannunsa me lafiya, ya watsawa nabeelah wani irin mari me tsananin zafi ji kake tasssssssssss! Wani irin zafi ya ratsa fuskar nabeelah zuwa kaf jikinta nan take ta farajin kukan tsintsaye na mata shawagi a cikin brain dinta sbda azabar zafin dataji na marin, nan take ta dafe kuncinta wasu zafafan hawaye suka wanke mata kunci, ga zafin Marin daya mata ga zafin wai yau itace karamin yaron data raina ya mareta, a haihuwar kaji tini zata haifesa . Zaks dake gefe yaji tamkar a fuskarsa Aeezad yayi marin. “ dan Allah kayi hkri mana…” Zaks ya fadi hadi da karasowa inda Aeezad da nabeelah ke tsaye. Sam ma Aeezad bejisa ba. “Aikin banza aikin hofi,,,ni zakima haka, ni zaki ma wannan iskancin kinje gun namiji kina min karya saboda reni,,,wannan yarinyar har ta isa ta renani wlhi baki isa ba kedin banza da hofi, Wulakancinki na banza, wlhi baki isa ba, yau zan maganinki, yau zaki gane waye ni , gabaki daya karyar iskanci kkyi…” Aeezad ya fadi a zafafe yayin dayakeji Sam be huce ba dukda Marin daya mata,. A matukar wani zafin Aeezad ya fito hannunta da hannunsa me lafiya ya fisgota suka fice a falon zuwa farfajiyar Asibitin Zaks ya biyosu yana tambayar “Ina zakaje da ita?” Ina Sam Aeezad bebi ta kan zaks ba, nabeelah ta kasa katafus se janta yakeyi kikiki kmr tsohuwar mota, yayinda har yanzu hannunta ke dafe da kuncinta. Tinda Aeezad yajata basu tsaya ako ina ba se a bakin motar zaks, tinda zaks yaga ya tinkari motarsa tini ya bude motar kafin ya kara sa, Aeezad ya bude gidan baya ya wurga nabeelah ciki, ya bude gidan gaba fannin me zaman banza ya shiga ya kulle motar da karfi Kai kace motar ce ta masa lefin. Ba tare da zaks yajira Karin bayani ba domin shima a tsorace yake da Aeezad duk ya chanza kamanni, cikin hanzari kawai Zaks yashiga dreva side yayi reverse ya fice da motar a asibitin ya jefata titin yamma, ba tare dayasan ina zasuje ba , kuma yana tsoron tambaya, nabeelah se kuka takeyi me tsuma zuciya, shi kan gogan se girgiza kawai yakeyi shi kadai ya kumbura yayi suntum a wannan lokacin babu abinda baze iya Aikatawa ba.

 

Saadatubintuabdullahi 💖

Ingantattun magunguna ina kuke manyan mata masu fada aji ku *marmatso kusa-kusa 😄🤤 kuzo ku gyara gindinku mazajenku su shiga suji dadih su Dinka ihu suna makalkaleku a gado🤤 kayan dadih se mata masu daraja💃🏼*

Akwai gumbar madara
Akwai gumbar ridi
Akwai gumbar zuma
Akwai gumbar bata gaban matan duniya
Akwai gumbar farar saka
Akwai gumbar rubutu
Akwai gumbar cikakkiyar mace
Akwai gumbar dake ciko da farjin mace ba ruwanki da ciccibi
Akwai gumbar goron tulah😂hajiya ba a magana in beyi ihu ba yana cikin gindinki kimin magana in biyaki kudinki 💃🏼
Akwai gumbar nonon rakumi
Akwai gumbar kin fita zakka

Akwai gumba iri daban daban shaaaa yanzu magani yanzu dakinsha dakin jike sharkar tana karawa mace dadin farji sede kiji ziiirrrrr gabanki na motsin ddh oga na kara motso mikishi da Abun dadinsa 🤤 akwai Ingantattun garirrikan magani na niimah, akwai maganin maza, akwai sahihin maganin sanyi dana basir, manyan mata ku kula da jikinku.

Chart me up hajjaju 08101626484

Back to top button