Dalibina Hausa NovelHausa Novels

Dalibina 13-14

Sponsored Links

*_D’alibina_*
By maman nurul hudah

Aslamu Alaikum fans da fatan mun kwana lafiya,Ina me bakin cikin sanar daku cewa watsaap sun kulle min account so ga sabuwar number da zaku iya samuna yanzu 08130884200/08148088368 ta Nan za a sameni IAM very sorry for the inconveniences…and ga me son complete book Dina yayi min magana ta wanan layin thank you for sopporting me

Ga Wanda suke telegram zaku iya following wanan links din Dan nafi posting acan
https://t.me/+4ykt7Q-BjSswMDU0

1️⃣3️⃣⏏️1️⃣4️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Wanan maganar ya karawa Abba haushi yace”aikuwa Fatima wata biyu na Baki ki fito da miji in ba Haka Zan hadaki da duk Wanda na samu as in zanyi sadaka dake a massalaci ”

Anty amarya tace”toh Allah yasa a dace Wanda beda ko mashishini za a bawa wata biyu da dai akwai Wanda ya kyasa ne sai a ce toh gashi Amma ai Babu kawai sai a yanke wa’adi kaima alhaji jibeka da wata magana”

Dukar da Kai Fatima tayi Jin inda suke ta ci Mata mutunci ita da mahaifiyarta abinda ke Mata ciwo shine inda Abba ke biye musu Wanda a baya be lamunce a ci Mata mutunci ko a rainata ba

Mikewa yayi ganin magrib ya gabatoh yace”nidai na Gama magana “Yana fadin Haka ya fita

Binshi da kallo duk sukayi anty amarya ta bawa mama hanun suka tafa Fatima tayi ciki

Dariya taji sun kece dashi umma tace”ai Ina gan har abada wanan bazatayi aure ba abinda tsufa duk ya bayyana ko Ina wa zai d’ibeta ”
Anty amarya race”ko zanyi yawo tsirara saina hanata aure
Umma tayi wani murmushi tace”toh ke da Zama zamuyi ne
Tana zuwa kofar d’akinta ta bude ta Shiga gado ta fad’a ta fashe da kuka Mai ban tausayi sai ta fad’a tunanin mahaifiyarta

Ita kadai mahaifiyarta ta Haifa Kuma itace babba wajen iyayenta ,mahaifiyarta ita CE matar Abba ta faru Wanda da ita sukayi auren kuruciya

Kasancewar mahaifiyarta Yar maigidan abbanta ne dan a wanan lokacin Yana Mata tsaron shago ne abbanta na karkashin kakanta attajirine saboda gaskiya da rikon amanar abbanta yasa abbu ya yarda dashi har ya bashi yar’sa Maryam
Saidai mahaifiyar Abba Bata so ba Dan a ganinta tunda iyayen ummi nada kudi juya Mata d’an za ayi tayi bama Haka ba ta so ya auri yar’uwarsa ce Jamila Yar wan’ta uwa d’aya uba d’aya har akayi auren Bata so ba gudun ta toshe Masa hanya cin abinci yasa Bata tada daru ba Kuma tasan in har ta nimi yin fitina mijinta bazai Bata goyon ba

Bata tab’a nunawa Maryam kauna ba kullum cikin hantarata take da niman laifinta da ko tayi shekara biyu Bata haihu ba ta tada daru sai ya Kara aure haka ko akayi aka sa auren Abba da Jamila auren nasu da wata biyu ciki ya bayyana jikin Maryam wata uku itako Jamila tana shiga Allah ya Bata

Cikinta na shiga watan haihuwa ta haifi yar’ta bàyan wata biyu Jamila ta haifi na miji,Inna dama tana nuna musu bambamci kullum cikin kushe Maryam take ko a ya’yan Bata tab’a kaunar Fatima ba

Shiko Abba Yana son Maryam Dan dukda Inna Bata nuna Mata kaunar Kuma tana hantararta Bata tab’a Kai Kara gida ba ko ta sanar da wani nata shi kansa yasan rayuwar kunci take da rashin gata a Haka har Suka share shekaru ashirin a lokacin ya Kara ta uku salame itama Inna ce tasa shi a cewarta Jamila ta Mata rashin kunya lokacin ko shekaran7 beyi da auo jamila ba tunda ya Karo salame gida ya koma filin daga

 

 

Maman Nur

Back to top button