Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 102

Sponsored Links

Ikhram~ By Khaleesat Haiydar 102….. Khaleel ya
juya yana kallon Maminsa da ta kasa daina kallon
Ikram, juyawa yyi ya fita daga dakin, Mami tace
“sbda me baxa ki bi su” Ikram ta bata fuska tace
“Mami ni bana son komawa gidan sbda abubuwan
da suke min” Mami ta kafa mata ido snn tace “me
suke maki?” kmr xata yi kuka tace “ba ynxu xan
gaya maki ba Mami, amma ni baxan bi su ba”
Mami tayi shiru tana kallnta snn tace “to tashi ki
shirya ku tafi idan baxa ki fada min ba” Ikram ta
marairaice tace “don Allah Mami ki bar su su tafiya
xan gaya maki” Mami xata yi magana Khaleel ya
shigo dakin yace “sae da safe Mami lkci na
wucewa” Mami ta juya tana kallon Ikram ta daure
fuska tace “ba magana ake maki ba Ikram, waye
sa’an ki a nn” mikewa Ikram tayi hawaye ya cika
idonta ta dauki xani ta daura kan kayan baccin
jikinta snn ta sa Hijab hawaye na bin kuncinta tace
“sae da safe Mami” ta fice daga dakin Khaleel ya bi
ta da kallo, Mami ta hade rae tana masa mugun
kallo tace “ka gaya min me kuke ma Ikram tun kan
ta fada min da kanta khaleel” yyi shiru yana kallon
Mami don ya ma rasa amsan da xae ba ta, can
dae yace “tace ina mata abu ne Mami” Mami tace
“ban sani ba, ka bani amsan tambayata” ya girgixa
kai yace “wllh Mami ni a iya sanina lfya muke
xaune, sae dae in cikin rashin sani nake bata mata
ban sani ba” Mami na ci gaba da harararsa tace
“matarka fa” nn ma rasa abun cewa yyi sae
kallonta yake, a hnkli yace “in tace muna mata
wani abu ne ki gaya min Mami sae mu gyara
amma ni dae duk lfya muke xaune wllh” Mami tace
“sae da safe” kasa amsawa yyi ya juya xae bar
dakin, tace “Aliyu yyi bacci ne” ya girgixa mata kai
yace “A’a” snn ya fita xuwa falo, yyi ma Jummae
sae da safe don Maryam na jiransa tun daxu cikin
mota bayan ta sallami Mami, tsaye yaga Ikram a
balcony ta wani hade rae ba kyan gani, har tsoro
take basa in ya ganta a hka, bae ce mata kmai ba
ya nufi motarsa, ta bi bayansa hannunta rungume a
kirjinta, Maryam na xaune bayan mota tana danna
wayarta, Ikram ta bude gaba ta shiga, ya xaga ya
shiga driver seat ya tada motar suka bar gidan,
goma ya wuce suka isa gida yana gama parkn
Ikram ta bude motar ta fice ta nufi balcony, daga
shi har Maryam suka bi ta da kallo, tana nn tsaye
suka iso balconyn Maryam ta bude gidan don
Makulli na gunta tana budewa Ikram ta bi ta
gefenta ta shige ta nufi sama abunta, Maryam tayi
murmushi tace “halan fada kuka yi da mutuniyar”
Khaleel ya kirkiro murmushi bae dae ce komai ba
suka shiga gidan. Daki ya shiga ya sameta har ta
kwanta ya xauna gefen gadon yana kallonta yace
“Ikram nayi maki laifi ne ki gaya min don Allah”
juya masa baya tayi, ya fi minti goma xaune bata
ce komai ba kuma idonta biyu, mikewa yyi ya fita
daga dakin ya rufo mata kofar a hnkli. Washegari
da safe Khaleel ya shigo dakin ya tarar har tayi sllh
ta koma ta kwanta, ya tada ta yace “baxa ki sch
bne yau Ikram tun monday fa ku ka yi resume” ta
mike xaune da sauri tace “to nace ban sani bne,
banyi niyyar xuwa bne” tana gama fadin hka ta
koma ta kwanta, ya xauna kan gadon ya dagota
yace “haba My Ikram ki gaya min me nayi maki
plss” kuka ta saki tana kkrin kwace kanta ya
rungumeta tsam yace “plss tok 2 me kanwata”
cikin kuka tace “ni gidan Mami nake son in koma”
yyi shiru yana kallonta, jin shirun yasa ta daga kai
ta kallesa, ya saketa ya mike ya fice daga dakin
tayi tsaki ta koma ta kwanta, can karfe tara saura
Maryam ta shigo dakin tace “ki xo muyi breakfst
Ikram, kin tashi lfya” Ikram ta dauke kai tace
“anjima xan yi ba ynxu ba” Maryam tace “to” snn
ta fita daga dakin, har rana Ikram bata fito ba, hkn
yasa Maryam ta kuma komawa dakinta taga ko
lfya, tana jin shigowarta ta rufe ido da sauri kmr
me bacci, ganin hka yasa Maryam ta fita ta rufo
mata kofar. Cikin yan kwanakin nn gaba daya suka
rasa gane kan Ikram kwata kwata ta bar xama falo,
girkin ma ta daina sae dae Maryam tayi, kullum
cikin daure fuska xaka ganta, da farko Maryam kan
shiga dakinta taya ta hira ganin bata wani kulata
yasa ta daina shiga, khaleel kam har fargaban
shiga dakinta yake sbda masifa in ran girkinta ne
ma sae ya bari tayi bacci xae shiga ya kwanta, ran
sunday da daddare karfe takwas ya shigo dakinta
yi mata mgnr makaranta don gobe sati daya da
komawarsu knn, tana xaune gaban Madubi ta fito
daga wanka, ya nemi kujera ya xauna yace “Ikram”
tayi kmr bata ji sa ba, ya kuma kiranta ta juya tana
kallonsa ba yabo bare fallasa tace “ina jin ka” ya
shafa kansa yana kallonta yace “ki fadi min laifin
da nayi maki, in nemi gafara” ta dauke kai tana ci
gaba da shafa lotion din da take tace “ni kawae
bana sonka ne wanda nke so daban shi yasa kaga
nke maka hka, kila idan ka gaji dani xaka sakeni in
huta kai ma ka huta tunda dae kana da matarka” a
fusace ya mike ya fincikota daga kan kujerar da
take xaune yana huci yace “kika ce me?” duk da
irin tsoratar da tayi don har rawa jikinta ya fara hkn
bae hanata mgna ba, don cikin tsawa ita ma tace
“bana sonka ka sakeni” wani wawan mari ya kai
mata tayi kasa a gigice yyi wani irin ball da ita
yana huci.
Like · Reply · Report · Just now

Back to top button