Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 7

Sponsored Links

AM] ‪+234 706 205 5793‬: Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 7…… Hudu saura Mami ta iso gun mai Fruits, har lkcn ikram na kasuwar amma gun wata mata mai saida cherry ta tafi tana ta mata xuba duk don ta bata cherryn matar dae sae dariya tke, malam sani ne ya shiga kwada mata kira don ba nisa daga shagonsa ta taho da gudu ba tare da ta lura da Mami dake tsaye tana kallonta dauke da murmushi a fuskarta ba, ikram tace “matar nn muguwa ce bata ban agwaliman ba,” mami tace “Ikram,” ikram ta juyo da sauri tana kallonta da gudu taje ta rungumeta tace “lah Anty yaushe kika xo,” Mami tayi murmushi tace “ynxu na xo Ikram, ynxu ki fada min ina ne gidanku mu tafi” Ikram tayo waje da ido tace “me xa kiyi a gidanmu Anty,” Mami tace “iyayenki nake son gani” ikram ta dauke kai tace “ba kowa a gidanmu ni dae,” Mami ta dafa kafadarta tace “haba Ikram xan siya maki Ayaba da yawa fa,” ikram ta washe hakori da sauri tace “to xan nuna maki, amma ni sae kin fara kai ni yawo a motarki” Mami tayi murmushi tana kallon kyakkyawar fuskarta tace “to naji ikram” Banana bunch daya ta karba gun malam sani, ya sa mata a leda snn ta karba ta mika ma Ikram, da sauri ikram ta karba, Mami tace “to muje,” bata yi musu ba ta shiga gaba Mami na biye da ita a baya har suka iso bakin titi gun motarta, Driver ya fito da sauri yace “sannu Hajiya,” Mami tace “yauwa Habu, snnu da jira,” mami ta bude motar tace “shiga Ikram,” ikram ta shiga motar tana cewa “wnn ma yaronki ne Anty,” Mami tayi yar dariya tace “A’a driver ne,” driver yace “ina muka nufa hajiya?” mami tace “mu tafi gida kawae” hka Ikram ta dinga mata surutu barkatae cikin motar har suka shigo cikin garin Abuja, nan fa ta manna goshinta da glass din mota tana kallon manya manyan Buildings din Abuja da tituna, kauyanci ta dinga yi ma Mami, ko me ta gani sai tayi magana, driver dae sae murmushi yake, ikram duk ta rude ita a barta ta fita tayi tafiya da kafarta wani gun ma idan an wuce sae tace ita bata gani ssae ba, sae Mami tasa driver ya koma snn su ci gaba da tafiyar, wani lafiyayyan Anguwa suka shigo driver yyi horn a wani makeken gida mai kyan gske, mai gadi ya wangale gate, ya ja motar suka shiga, idanuwan ikraam kmr su yi magana tana kikkifta su tace “nan ne gidan mamarki Anty,” mami tayi murmushi ta gyada mata kai kawae, snn ta bude motar ta fito da ikraam suka yi balcony din shiga gidan, sae waige waige Ikram take, har suka shiga wani kantamemen falo, ikram ta yo waje da ido tace “ina ne nn Anty, ni dae ki maida ni gidanmu,” murmushi Mami tayi ta ja ta suka haura sama, snn ta bude dakinta tana rike da hannunta suka shiga, ikram ta dan marairaice kmr xata yi kuka Mami ta xaunar da ita gefen gado tace “kar ki damu dota, nn ma gidanku ne kin ji,” kai kawae Ikram ta gyada mata, Mami ta bude fridge ta ciro lemon five alive ta ajiye gabanta tace “bari na dauko maki kofi dota,” nan ma kai kawae ta gyada mata, mami ta fita xuwa kitchen, a hankali ikram ta xamo daga kan gadon ta dawo kasa ta xauna ta cire hijabinta da hula snn ta jawo lemon gabanta ta bude da kyar da hakorinta ta kafa kai, mami ta shigo dakin rike da cup tace “kai dota, ga cup na dauko maki,” ko kallonta ikram bata yi ba idonta lumshe sae kwankwadar five alive take, mami ta xauna tana kallonta, cike da sha’awa, Allah yasa iyayenki su yrda su bani ke ikram, abinda ta fada a xuciyarta knn, don kanta ta ajiye lemon bayan ta koshi ta lafta uban gyatsa, Mami ta dawo kusa da ita tace “kina jin yunwa ne ikram,” kai kawae ta girgixa mata, mami ta shiga kwance roban da Ammi ta nade mata gashinta da, gashin suka xubo har kusan bayanta, mami ta dauko comb dinta da man kai da ribbons, ta shiga gyara mata gashin, ita ko sae kallon cartoon din da Mami ta kunna mata take, duk inda ta ga ana fada sae ta fasa ihu, mami sae dariya take, har ta gama gyara mata gashin snn ta dauko mata gasasshiyar kaxa a fridge ta dumama mata, tana cikin ci aka bude kofar dakin, wani dogon handsome ya shigo sanye da 3qtre da polo ya fada gefen mami ya kwanta, ta juya tana kallonsa ganin bata ce komai ba yasa a hankali yace “mami ban fa ci komai ba har ynxu, am jet hungry,” mami tace “to ban san me kke so
[1/1, 6:29 PM] Aishat muhd: TSAFI TSAFI

Back to top button