Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 38

Sponsored Links

38
Benazir data kasa yadda da sumayyah ta tafi barsu rawa dukkanin jikinta rawa yakeyi ahankali tana kasa Jin hawaye ko Daya cikin idanuwanta,
Bakinta da makoshinta Wani irin bushewa sukai tana kasa samun yawu ko kadan cikin bakin da moqoshinta.

Babyn dake jikinta ce ta motsa ahankali
Hannuwanta dake rawa ahankali tasaka ta sake rungume ‘yar tana sake Jin zuciyarsa, idanuwanta da bakinta na bushewa sbd su ‘yar uwarsu,Rabin jikinsu suka rasa ita Kuma babyn uwa da ubanta ta rasa a lokaci Daya.

Ababa Da ake kokarin kwasa zuwa Asibiti Anne ta kalla da idanuwanta dasukai jajir Amma babu Wanda ya samu Kuka a cikinsu sbd basuda sauran Abinda suke ji a zuciyoyinsu dasuka sanqare,

Hande Kuka takeyi tana qarawa akan kada ta rasa ‘danta,
Mutane ta samo aka shigo aka dauki Ababan zuwa Asibiti cikin tashin hankalin kada a rasa shi.

A wannan lokacin ne Wani irin kukan da Bata San dashiba ya zuwar mata dukkanin jikinta na rawa da jijjjiga ganin ita tata ‘yar kusan mutuwa tayi cikin tsananin wahala baa damu da akaisu asibiti ba har aka rasata gashi yanzu gawar ma sun rasa a lokacinda suke sakaran Bata mutu ba Kuma labarin hadarin ta da mutuwarta da Bilal yasake tsinka fatansu,

To su kuwa a yanzu meye suke da Wani buqata ko fata bayan mutuwar Suma su huta,
Ga sabuwar Alhaki Allah ya sake jefo musu a cikin wannan lokacin da Suka gama sarewa gabaki Daya da duniyar da rayuwarma.

Benazir na Jin kukan Anne na shiga zuciyarta yana yankan Amma Bata iya matsawa saima sake rungume babynsu datayi tana Jin a yanzu da babu shigowa wannan babyn rayuwarsu da babu Abinda zai hanasu samun bugawar zuciya a ayau din su mutu su huta Amma duk motsin da babyn keyi jikinta Jin sumayyahnta takeyi a jikinta da zuciyarta Dan haka take sake qanqame babyn.

Kukan da Anne tayi Mai tsananin gaske Bai rage mata komai na nauyin da takejin zuciyarta tayi mata ba Dan haka ta share hawayenta ta miqe tsaye ta kama benazir din itama ta tayar da ita suka koma dakinsu.

Suna shiga Annen ta hau tattara dakin ta kwashe kayan da sumayyah ta haihu Akai ta fito dasu ta debo ruwa tahau aikin wankewa batareda ta furta kalma ko Daya ba.

Tana gamawa ta dawo dakin ta gyaran musu shi tas
Har lokacin benazir na zaune rungume da ‘yar Bata motsaba idanuwanta a bushe.

Anne ma da aikin fitan hayyaci takeyi tana gama gyara dakin ta fito ta share tsakar gidan ta gama ta Dora ruwan zafi suna tafasa ta juye tayo dakin dasu ta ajiye ta Kalli benazir tana miqa hannu zata karbi babyn tace

“Kawota a sake mata wanka”

Sai alokacin benazir ta dago da busashin idanuwanta ta Kalli Annen tsawon mintina
Take a lokacin siraran hawayen tausayin mahaifiyarta suka gangaro mata sbd tasan baa cikakken hayyacinta take ba.

Hannu Daya ta saka ta share hawayen tareda daurewa ta dawo hayyacinta ta Kalli Annen ta girgiza mata Kai ahankali tana Ciro babyn daga jikinta ahankali tace

“Zan Yi mata Anne ki zauna ki huta”

Hakan data fada ya saka jikin Annen sanyi sbd tasan tsoron Bata yar takeyi sbd tinanin Bata hayyacinta kada ta jefata cikin ruwan zafi.

Dan haka Bata Musa ba ta juya ahankali ta koma gefe ta zauna tana kallan benazir zubawa benazir da babyn Ido.

Hannuwa na rawa da tsoron rashin iyawa Benazir tayi qarfin halin yiwa babyn wanka hannuwanta na tsananta rawa.

Bayan ta gama mata duk ta jiqa jikinta da gurin.

Ta miqawa Anne babyn Dan ta samu miqewa ta kwashe kayan wankan
Anne ta girgiza mata Kai tareda cewa ta riqeta kawai bari ita ta kwashe kayan.

Kayan ta kwasa ta fitar ta dawo ta goge gurin tana gamawa ta karbi yar benazir ta sauya kayanta sbd kada sanyinsu ya damu babyn dake jikin nata
Tana gama saka kayan ta fice tayo alwala sbd lokacin sallar azahar da yayi tini.

Tareda Anne sukai sallah babyn na tsakiyarsu shimfide.

Suna idar da sallah suka fara jerowa sumayyah addua zuciyoyin kowannensu na dakewa da qarfafa tawakkalinsu,
Gawarta ma Basu saka ran Gani ba sbd zuwa lokacin sun sani an hadata da Bilal anrufe tinda danginsa sun San ita zai aura,
Basuda masaniyar komai sai Ababa ya dawo yajiyo idan gawar zaa Basu kokuma an rufeta tini.

Babyn suka zubawa Ido dukkaninsu suna qarewa fuskarta Kallo zuciyar benazir na karban duk Wani feeling akan babyn.

Sai alokacin takejin ‘yar cikin ranta sbd dama da sumayyahn na Raye da Bata Nan ‘yar sumayyah ‘yarta ce,
Cikin ne kawai Bata dauka ba da haihuwarsa Amma kusan duk Wani wahala,Reno,farin cikinsa da baqin cikinsa Dede sukaisa da sumayyahn a yanzu Kuma ta tafi tabar mata ‘yar bayan tazo duniya.

Anne kuwa miqewa tayi ta fito ta Dora musu abinci duk da tasan ba cinsa zasu iya ba Amma dole zasu rayu suci gaba da rayuwa sbd ‘yar sumayyah data barmusu Dan haka komai a yanzu ba Dan kansu zasuyi ba sbd babyn zasuyi.

Tana gamawa ta tilasta benazir suka zauna suna cusa abincin a dole
Suna gamawa sukai sallar laasar
Lokacin babyn tafara Kuka sosai tana Neman Nono.

Kukanta ya saka radadinsu dasuke dannewa Neman tsinkewa Amma Anne ta daure ta shiga dakin Ababa cikin kayan haihuwar Daya Tara ta samo ruwan zamzam suka taho suna cikin bawa yarinyar Aka dawo da Ababa a jeme ya zabge cikin wuni Daya.

Hande ma har lokacin kukan takeyi Akai Akai.

Gidan tsit ya dauka kowa na jimamin mutuwa da rashin da sukai gashi kaman yan kankan Kai baa ma San anyi mutuwa ba gidan bare a shigo musu gaisuwa tinda baa ga ana janaiza ba bare karban gaisuwa.

Ababa Dayake fama da Kansa Jin kukan babyn yayi yawa yasa jamilu yaronsa siyo madarar jarirai gwangwani uku da ruwan roba Katan Daya.

Ana kawowa aka bawa benazir batareda an sanar da ita yanda ake bayarwar ba.

Dayake babyn tafara galabaita Bata tsaya Bata lokaci ba itada Anne suka dafa ruwan zafi suka hada mata a fidar dake cikin kayan haihuwar da hande ta watso musu daki bayan dawowar tasu.

Ana sakawa jaririyar fidar farko kasa kamawa tayi dai daga baya Anne ta karba ta ringa diga mata madarar cikin baki tukuna ta Dan fara motsa bakinta madaran na shigewa.

Hawaye masu zafi ne suka gangarowa benazir lokacin da babyn ke Shan madaran tana motsawa ahankali batareda tasan Tayaya zasuyi rayuwa da babyn a haka ba.

A haka suka kwana zaune gidan babu Wanda ya iya kwantawa bare ya iya rintsawa sai hande kawai Amma Ababan ma a zaune ya kwana cikin ciwon zuciya Dayake Neman Kaisa lahira a kwana daya da wuni biyu.

Har safe zuciyarsa cikin mummunan hali take ciki Yana saka da warwara Dan kuwa yasan ya tabbatarda sumayyah akwai Abinda dai yake qasan bacewarta bat,
Gawar da aka samu cikin motar Bilal kaante guda Daya ce bayan biyu ya kamata a gani idan Kuma drivernsa ne ya tuqosa gawa uku yakamata a gani Amma Daya aka samu wadda Suma jamian tsaron kaman wainda aka Basu San aikinsu ba baida tabbacin anduba gawar an tabbatarda ya waye.

Zafin da Kansa ya dauka ya sakasa kasa tantance komai bayan tabbatarda koma meyake qasan wannan lamarin Bai lalata komai nasa ba ya janyo masa lukutar masifar dazata Kaisa qasa.

Dan haka da safe bayana ya sake samun saukin dawowa hayyacinsa Ya Yanke Wani mummunan kudirinsa akan Abinda yayi Niya Dan haka Yana fitowa Abinda yafara shine sanar da benazir da Anne dake jiransa akan maganar sumayyahn cewa anriga anyi janaizarta tareda Bilal tin jiyan addua da fatan samun rahamar ubangiji kawai zaa ringa mata harma da Bilal din.

Daga Anne har benazir ga mamakinsa babu Wanda ya some masa kaman yanda ya tsammata,. Abinda Bai saniba sun riqa sun Riga zuciyoyinsu sun bushe sun saddakar sun karbi kaddarar mutuwar sumayyahn tin jiyan dan haka suna samun tabbacin daga bakinsa suka sake daukan taurin zuciya suka sawa kansu.

Ababa kuwa Daman Hakan yakeso Dan haka shiryawa yayi ya nufi KAANTES gurin gaisuwa da sanar dasu an haihu lafiya kalau.

*******A Kaantes ana cikin tsananin hali da qunci da baqin cikin rasuwar ta Bilal wadda kusan duka ta taba iyayensa da kakan nasa da basusan suna kaunarsa ba sai a yanzu da bayanan yabar musu duniyar Dan haka dukkaninsu babu Wanda yake zaune da qafafunsa a kwance suke ba lafiya hakanan ake daurewa ana karban gaisuwar daga manyan mutane da baqin dake zuwa na kusa Dana nesa.

DD kaante ma rashin lafiya ce a jikinsa sosai sbd Bilal Wani bangare ne na jikinsa da bayan iyayensa shine halittar dayafi tsananin so a duniya,
Rashin Bilal lokaci Daya ya girgiza duniyarsa da Bata taba girgizuwa ba,
Dan haka tin ranar da Bilal din Ya rasu Yana bangarensa Nan kaantes Yana fama da Kansa Shima
Sai likitan dake zuwa dubasa kullum ko gurin karban gaisuwar baya iya fitowa.

Ababa Koda ya iso baisha wahalan shigowaba sbd Abbakar dake gate Dan haka Kai tsaye Akai masa iso ciki.

A palon dd babba ya zauna cikin jimami yafara yiwa dd babban gaisuwa kafin yayiwa dad kaante da sauran uncle din Bilal din dake gurin.

Amsa gaisuwar sukai kafin Shima ya zauna cikin yan karban gaisuwar Yana bayyanarda jimaminsa harda Kuka sosai Wanda yasaka dad kaante Ganewa da shine Mahaifin yarinyar da Bilal din su ke tsananin so harya rasa ransa akanta.

Ganin suna cikin jamaa ya Hana dd babba da dad kaante tambayan idan ‘yar Ababan ta sauka lafiya ita.

Ababa da Kansa ya bayyanarda Yana son yiwa ummen Bilal gaisuwa babu musawa Abbakar yayi masa jagora zuwan babban palon dad kaante aka shiga aka kirawo ta.

Zata fito DD na shigawa palonta sanye cikin black Balmain jumpsuits kyakyawan fuskarsa fresh a kame kaman baa tabawa da hannu
Duka masu masa gaisuwan Bilal din Daya shigo amsawa yayi a takaice cikin nutsuwa batareda ya tantance su waye da waye ba duk da harda mummyn Sbb amaryasa aciki.

Ganinsa yasaka Umme hadiye hawayenta tana kama hannunsa Daya miqa mata Dan kuwa yanzu shine sanyin idaniyarta.

Tare suka juya zuwa palon dad kaante suna shiga qamshinsa yafara ankarar da Ababa ba haj fatman bace kadai ta shigo Dan haka ya dago idanuwansa daidai tsayuwar DD a palon ya zubawa Ababa idanuwansa a Karo na farko Daya zubawa Wani idanuwansa Yana kallan tsaf.

Kwarjininsa yasa Ababa miqewa tsaye daga zaunen Dayake bakinsa na Tara masa yawun dazai hadiywa maqoshinsa Daya bushe sbd tabbatarda wannan shine DAWOOD KAANTE din da duniya tafi sani akan duka sauran ‘yaya da jikokin gidan,Kuma qanin Alh Bilal.

Rawa hannuwansa suka dauka take baisan lokacinda yace

“Nine Mahaifin Benazir,
Yarinyar da Alh Bilal zai aura kafin afkuwan wannan kaddarar ta rashinsa”……

Daga Umme har DD a tare suka sake sauke masa idanuwansu bakin Umme na rawa tace

“Ta haihu?
Me ta….. Bata qarasa ba Ababan ya katseta da cewa

“Ta haihu lafiya ta samu ‘ya mace Kuma duk suna lafiya uwar da ‘yar.”

Daidai Nan dd babba da dad kaante dakeson magana dashi din suka shigo Kuma a kunnesu zancen an haihun ya sauka.

Wani kukan da Umme batasan ko na menene ba ya kunce mata tana Jin bayan babyn a yanzu baby Abinda take buqatan a kawo mata tagani.

Ababa kuwa take ya Yanke shawarar benazir ce uwar yar Kuma babu Mai sanin ba ita din bace matiqar Yana Raye.

*Masu buqatan pages da Akai Nisa sosai suyi following Dina arewabooks at mamuhgee kokuma suyi joining VIP*
09033181070
09032345899
#MAMUH#
#MARRIAGE
#DD
#BENA
#AMNAH

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

 

Back to top button