Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 67

Sponsored Links

PAGE* 6⃣7⃣

Su sultan ahamad suna a tsaye nan wasu doctors guda ukku sukazo zasu shiga room d’in da memartaba yake a ciki,,Dr muhammad Bashir ne yace ku kuma ina zakuje?

‘Daya daga cikinsune yace ranka yadad’e Dr S ne yabamu umurni akan muje muyi ma patient d’in injection sannan musanya masa drip, ya ce sai zuwa gobe by 10am zai shigo.

Gabad’ayansu murmushin jin dad’i sukayi tare da furta Alhmdllh.

Haka suka shiga sukayi abinda aka umurcesu sannan suka fito, su dada nan aka basu izini sushiga suzauna ammah kar sudinga yin hayaniya saboda patient d’in ba a so atashesa daga baccin da yake.

Haka suka dawo bayan drip d’in ya k’are suka cire sukace kar asaki abashi wani abu yaci, nan ma da dare suka dawo sukayi masa wata injection d’in tare da k’ara gargad’insu kar abashi komai.

 

Yarima ko a ranar kasa samun sukuni yayi dan tun baiga yanayin da memartaba yake cikiba ammah hankalinsa ya tashi sosai musamman ma da yaga case d’in da yake tare da shi, dafe kansa yayi yana jin k’unci a ransa nan hawaye yashiga kwarara cike da tausayin memartaba da baida kamarsa bayan iyayensa.

Zarah da take gefensa ganin halin da yake ciki yasa tafashe da kuka dan tun d’azu yarima bai kalli ko inda takeba bare tasa ran zaiyi mata magana.

Kukanta yasa yadawo cikin hayyacinsa ahankali yabud’e idanunsa tare da share hawayen fuskarsa sannan yakalleta yace Zarah meyake faruwa ne? Bakida lafiya ne?

Cigaba tayi da kukanta tare da juya masa baya, murmushin k’arfin hali yayi sannan yajanyota a jikinsa yarungume d’ago mata kanta yayi yakalli cikin idanunta yace kifad’amin abinda yake damunki.

Rage sautin kukanta tayi tace ba kai bane kake ta shareni inma wani abu nayi maka ai sai kafad’amin inbaka hak’uri, kuma tun d’azun kake cikin damuwa har fa kuka kayi yanzu.

Jan hancinta yayi yace injiwa yace miki kuka nayi? Kidaina damuwa kidinga yi min addu’a kinji ko baby?

Turo bakinta tayi tace toh, murmushi yayi yace fushin ya isa haka.
Murgud’a masa baki tayi tace ank’i d’in.
Kwantar da ita yayi a k’irjinsa yace baby please muyi bacci.
Nan Zarah talumshe idanunta saboda daman baccin takeji ganin yarima ne a wannan yanayin yahanata bacci,
Shafa bayanta yashiga yi ahankali ahaka bacci yai awon gaba da ita, nan yazameta daga jikinsa tare da tashi zaune yadafe kansa,,,,,ya dad’e a zaune sannan daga baya yakoma yakwanta yana ta juyi ahaka bacci yai awon gaba da shi.

 

Wajen 8am yagama shirinsa kallon zarah yayi da take baccinta hankali kwance, zuwa yayi yai mata peck a kumata tare da shafar cikinta sannan yaficce batare da yayi ko breakfast ba.

 

Koda ya isa direct office d’in MD yaje lokacin MD yana zaune yana cike wasu files, ganin yarima yasa saida gabansa yafad’i dan fuskarsa ba alamun fara’a kujera yarima yajanyo yazauna muryar MD tana rawa yace am Dr S sannu da shigowa.

Wani irin kallo yarima yawurga masa yace Dr muhammad kar kayi tunani na shigo hospital d’innan ko zanyi theater d’innan saboda kai ne, murmushi yarima yayi sannan lokaci guda yahad’e fuska yace na amince zanyine saboda amfanina da na dangina, jiya ka fad’a min magana son ranka ammah na yi maka uzuri saboda bakasan wanene ni ba, ammah inaso kasani ya zama dole kakiyaye kalamanka akaina inbahaka zansanyaka kayi nadamar da batada amfani.

K’ut dr muhammad yahad’e yawu sannan yace shikenan dr s nagode sosai da ka fahimtar da ni.

Ta6e baki yarima yayi tare da mik’ewa yace wannan ya rage ruwanka, har ya fara tafiya sai kuma yajuyo yace am ban yarda akar6i ko naira d’ayaba daga garesu domin duk abinda ake buk’ata na bada ansiyo min sannan kuma nasaka kud’i a account d’inku na hospital zaka iya zuwa wajen accountant for confirmation, ammah idan nasaki naji kun kar6i kud’insu, girgiza kai yayi tare da murmushin mugunta sannan yace a lokacin zani nuna muku kalata zakusan wanene ni,,,,yana fad’in haka yajuya yafita yabar office d’in.

Cike da takaici MD yabuga hannunsa a table d’in da yake gabansa yace suhail ka 6atamin duk wani budget nawa,, dan dama abu guda yasa yashige gaba a lamarin dan yasan ba k’aramar riba zai samuba cikin jin haushi yamik’e yashiga zagaye d’akin cikin ransa yashiga tunanin maganar yarima yace anya mutanen chan ba wajen Dr s suka zagaye sukaje ba suka bashi kud’i? toh inma ba hakaba taya zai iya biya musu mak’udan kud’i,, chan kuma yace kokuma ai yana da taimako,,,cikin d’aga murya yace inaaa hakan ba zai ta6a yuwuwaba akwai dai wata a k’asa, fuuu yawuce yafita daga office d’insa rai a 6ace.

Yarima koda yakoma office d’insa system d’insan yazuba ma ido yana wani nazari a cikinta, dr mu’az ne yaturo k’ofan yashigo tare da yin sallama bai jira aka amsa masaba yashigo tsaye yayi wajen kan yarima yace haba suhail ammah baka kyautaba ashe memartaba ne su daddy suka kawo bayada lafiya shine baka fad’aminba har kana ik’irarin cewa bazakayi masa operation ba, toh na je na gansu.

‘Dago kai yarima yayi cikin sauri yace mu’az bakadai fad’a musu ina nan ba dai ko?

Cike da mamaki mu’az yake kallonsa yace toh menene dan sun sani? Kawai dai kaci sa’a basu ganeniba ammah da sai nai musu bayaninka.

Ajiyar zuciya yarima yasafke sannan yace ka taimaki kanka ammah please kar kasaki kafad’a musu cewa ina nan kuma kar kabari sugane cewa nine wanda zaiyi theater d’in.

Mamaki k’arara yabayyana a fuskar Dr mu’az yace saboda me Dr?

Saboda wani dalili nawa,,,yarima yafad’a a tak’aice.
Dr mu’az har ya bud’e baki zaiyi magana nan yarima yai sauri yatari numfashinsa yace saura 30minutes inshiga theatre room please kaje kakar6o min constant foam kawakilce ni kaje kuyi agreement da relatives d’insa inkuka gama sai kakawo min inyi sing.

Toh kai saboda me bazakaje da kankaba?

Yarima duba agogon hannunsa yayi sannan yace kana 6ata min lokaci kasan dai na yi maka duk wani bayani.

Murmushi Dr mu’az yayi sannan yajuya yafita yabar office d’in.

Zuwa yayi sukayi komai da su sultan ahmad sannan yazo yakawo ma yarima foam d’in yayi singing.

Bayan yarima ya gama singing d’in kallonsa yayi yace saura abu d’aya yanzu dai kaje kasasu subar wajen sannan kasa nurse sutura min shi a theater room ganinan zuwa.

Haushi ne yakama Dr mu’az yace wai kai prince ni zaka maida kamar wani yaronka.

Shuru yarima yayi yakyalesa, ganin haka yasa Dr mu’az yawuce yafita yana ‘yan maganganu.

Sa nurses yayi suka tura memartaba zuwa theater room sannan yakalli su sultan abbas da sukayi jugudum yace ranku yadad’e zaku iya shiga daga cikin room kuzauna kujira yanzu doctor d’in zai shiga.

Dada ce tace a’a d’annan kabarmu Kawai a nan dan inmukaje wani wajen hankalinmu bazai ta6a kwanciyaba.

Murmushi Dr mu’az yayi yace ranki yadad’e hak’uri zakuyi kucigaba da yin addu’a akan Allah yasa adace, saidai doctor d’inne idan yafito yaganku a nan bazaiji dad’iba domin bayaso yaga ana tsayawa a nan ransa yake 6aci.

Cike da gamsuwa da maganarsa sultan abbas yace toh shikenan doctor bari mubar wajen fatanmu dai Allah yasa adace, Ameen sukace sannan suka wuce sukashige room.

Yana ganin sun shiga nan yajanyo wayarsa yakira Dr suhail yashaida masa, mik’ewa yarima yayi yacanza kayansa zuwa na theater sannan yafito yanufi room d’in, a bakin theater room d’in yatarar da doctors biyu da nurse d’aya suna jiransa, har ya wuce zai shiga doctor mu’az yakira sunansa.
tsayawa yayi batare da ya juyoba, cikin sanyin jiki Dr mu’az yace ina maka fatan sa’a.
‘Daga masa hannu kawai yayi sannan yawuce yashige theater room d’in.

Tsaye yayi yana kallon memartaba da gabad’aya baisan inda hankalinsa yakeba saboda allurar da akayi masa, tausayinsane yakamasa,,,dafasa da akayine ta baya yasa yadawo cikin hayyacinsa nan yamatsa domin sufara aikin.

Su dada alwallah sukayi suka fara sallah tare da rok’on Allah sa’a acikin aikin nan da za’ayi wayoyinsu ko saidai suka kashesu saboda kiran da akeyi musu tun daga iyalansu zuwa mutanen garin gazban dan har gajiya sukayi da amsa wayoyi daga jiya zuwa yau.
dan su sultana bilkisu, sultana sadiya, rahama, sumayya, Aunty husna dukkansu suma sallah suka shigayi, hatta wasu daga cikin mutanen gari, fada ko liman yashige gaba aka dinga suburbud’a addu’o’i da karatun alk’ur’ani, gabad’aya garin wani irin shuru yayi mutane d’aid’ayane zaka gani suna raharsu sai kuma k’ananun yara da basusan abinda ake cikiba, hatta gidansu zarah.

Tun wajen k’arfe goma suka shiga theater room d’in ammah basu suka fitoba sai wajen 12 suka gama komai dan daga k’arshe baya sukaja sukayi cirko-cirko sukabar Dr suhail da aikin kasancewar shi yayi komai dama su kayan aikin ne kawai suke mik’a masa har yagama yamaida yad’inke, bayan ya gamane yajuyo yakallesu yai musu nuni da sunyi nasara ai nan sai suka shiga murna.

Zamewa yayi yaficce daga theater room d’in yakoma office d’insa yacire kayan yasaka nashi.

Nan nurses suka tura memartaba zuwa room d’in da aka admitting d’insa, su dada akayi ma albishir da anyi a sa’a nan suka hau godia ga ubangiji harda duk’awa yin sujjada, dasauri suka fito sukanufi room d’in zasu shiga nan nurses sukace a’a babu damar sushiga a yanzu saboda bacci yake, daganan suka bud’e wayoyinsu kamar jira ake suna kirawa kira na shigowa nan suka shiga yi ma mutane albishir da anyi a sa’a kowa yayi murna sosai.

Yarima kife kansa yayi a table d’in da yake gabansa shi kansa ya rasa shin murna yake ko me, dan ji yake hankalinsa ya d’an kwanta a yanzu ba kamar kafin ayi aikin ba, nan Dr mu’az yashigo yataya murna akan nasarar da aka samu.

Wajen k’arfe ukku badda kama yayi yaje yashiga room d’in yak’ara duba memartaba da har lokacin yake bacci nan daga gafe ya aje wata injection sannan yafito, bai d’ago yakalli su dada ba lokacin da zai wuce ta gabansu ammah saida gabansa yafad’i su kansu saida fad’uwar gaba ta ziyarcesu, haka yafito yawuce yashiga motarsa yanufi gida.

Koda aka kirasa akafad’a masa farkawar memartaba umurni yabada akayi masa injection d’in da ya aje sannan yace za’a iya barin iyalansa sushiga sugansa ammah kar a bari suyi hayaniya.

 

Zarah da take zaune gefensa ta kafesa da ido tana sauraren wayar da yake, bayan ya gama juyowa yayi yakalleta yace baby ya dai?
Murmushi tayi sannan tace ai tunda naga ka fita da wuri nasan theater ce zakayi.

Murmushi suhail yayi,,,kwantar da kanta tayi saman kafad’ansa nan ta marairaice kamar zatayi kuka tace please kadaina fita bakayi breakfast ba, indai ka san zaka fita da wuri toh tun dare kadinga fad’amin kaga sai intashi dawuri inhad’a maka breakfast.

Murmushi yayi yace toh ranki yadad’e angama.

‘Dago kai tayi takallesa saida tad’aure fuska sannan tace duk ranar da kak’ara fita batare da kayi breakfast ba zamu had’e.

Dariya ce taci Yarima ammah yadanneta yace toh Aunty angama.

au nima ce Aunty?
Eh man tun kan inji safkar bulala,,,dariya sukasaka gabad’ayansu nan yad’age mata riga yana kallon cikinta da yake motsawa, d’ago kai yayi yakalleta, murmushi tasakar masa tare da lumshe idanunta,
shafa cikin yashiga yi yace kinga babyna shima ya k’agara yafito yaga daddynsa.

Uhm nima ai na k’agara yafito inhuta da wahalar nan, har ma rasa rigimar wa zanji da ita nake tsakanin babyn ko daddynsa.

Ido yazuba mata yace au nima rigimar nake?
Fari tayi masa da ido sannan tace wata ran ma k’ara na babyn dan taka rigimar har rasa yadda zanyi nake.

Haka kika ce?
Eh,
Tallabo fuskarta yayi tare da kallon cikin idanunta yayi ahankali kamar me rad’a yak’ara cewa haka kikace?
Gira tad’aga masa alamun eh, bata ankaraba sai jin bakinsa tayi cikin nata nan tabiye masa suka shiga nuna ma juna salon so, gabad’aya suka fita hayyacinsu a nan parlour suka baje, saida taga yana shirin wuce tunaninta sannan tasamu tazame jikinta tamik’e dak’yar tanufi bedroom dan gabad’aya ya kashe mata jiki.

Nan yarima yai pillow da hannunsa tare da maida idanuwansa yalumshe, ahankali yayi k’ayataccen murmushinsa cike da k’asaita.

 

Bayan kwana d’aya sultana bilkisu da sultana sadiya visarsu tafito nan suma suka kama hanyar garin Abuja sosai sukaji dad’i da sukaga memartaba dan a yanzu har ‘yar magana yana d’anyi.

 

Yarima ko tun ranar da yayi masa aiki rabon da yak’ara sakasa a idonsa, saidai yatura wasu doctors domin sugano masa lafiyarsa ammah duk da haka duk wani abu da za’ayi masa shi yake bada umurni ahaka har memartaba yacika sati guda yawarke garas kamar bashiba dan har takawa yakeyi dakansa batare da anrik’esaba, dressing ko kusan kullum akeyi masa dan a yanzu d’inkin ma ya had’e har an warwaresa.

A ranar da yacika sati guda saida yarima yatabbatar da ba abinda yake damunsa sannan yasallami doctors d’in da suka taimaka masa wajen kula da memartaba dan burinsa ya cika nan shi kuma yafito yanufi gida.

A ranar bayan wani doctor yashigo yai masa injection nan dr muhammad bashir da Dr mu’az suka shigo, bayan sun gaisa da su memartaba, Dr muhammad Bashir kallon memartaba yayi yana murmushi yace ranka yadad’e ya kake jin jikin naka?

Shima memartaba murmushin yayi yace Alhmdllh discharge kawai nake jira dan najini daidai nake, ance min ma har yanzu baku fad’i kud’in da za’a biyaba ai yakamata ace zuwa yanzu kun fad’a anbiyaku.

Murmushi sukayi tare da kallon juna sannan Dr mu’az yace kar kudamu ai angama komai ranka yadad’e.

Memartaba kallon sultan ahmad yayi yace karubuta musu cheque kabasu tunda bazasu fad’i kud’inba hakama mungode da karamcin da akayi mana Allah yabiya.

Dada ce tace ai naso inga wannan d’an albarkan da yayi aikin inmasa godia ammah har yau doctor baku gwada mana shi ba.

Dr muhammad Bashir yaga samu yaga rashi haka aka basu cheque d’in ammah yak’i kar6a.

Sultan abbas ne yace kukar6a mana ai duk abinda zamuyi muku bamu biyakuba saidai addu’a,,,
girgiza kai Dr mu’az yayi yace ai doctor d’in da yayi theater d’in ya riga yabiya komai babu abinda baiyiba dan ya ma ce kar a kar6i komai naku.

Gabad’ayansu da mamaki suke binsa da kallo,,,sultan ahmad ne yayi k’arfin halin cewa ya biya komai fa kace? Saboda me zai biya?

Dr muhammad Bashir murmushi yayi yace wannan kad’anne daga cikin halin Dr S, mutum ne mai kyauta da karamci.

Girgiza kai sultan ahmad yayi yace duk da haka baidace yataimaki irin mu ba, taimakon da yayi mana na theater ma kawai ya isa mungode dan bamuda abinda zamu biyasa, yanzu kukar6i wannan kukaimasa.

Memartaba ne yace wai wanene wannan Dr S d’in? Miye full name d’insa? Dan Allah kuyi masa magana yazo mugaisa insaka masa da abinda yayi mani.

Shuru Dr mu’az yayi dan shi ya ma rasa abinda zaice musu,,,muryar Dr muhammad Bashir ce yajiyo yana cewa Dr suhail shine full name d’insa.

Gabad’ayansu saida gabansu yafad’i kusan a tare suka maimaita Dr suhail? Ummi da dada fashewa sukayi da kuka dan antuna musu da suhail d’insu.

Memartaba ne yace dan Allah wanene wannan Dr suhail d’in? daman d’an nan garin ne ko zuwa yayi? Kutaimaka kukaini ingansa ko jikanane.

Shuru sukayi sukarasa amsar da zasu bashi sai chan Dr muhammad yakalli Dr mu’az Girgiza masa kai Dr mu’az yayi alamun kar yafad’a.

Memartaba mik’ewa yayi ya isa inda suke yace dan Allah Kutaimaka min ingansa inaji a raina suhail d’ina ne da nake nema kusan wata ukku kenan yatafi yabarni.

Sultan abbas ne yazo yarik’osa yace ranka yadad’e anya suhail d’inmu ne? Kayi hak’uri kaga bakada lafiya, bana tunanin shine me zaizo yi a garin abuja alhali baida kowa a nan, kuma taya zai ganmu batare da yayi mana magana ba.

Girgiza kai memartaba yayi yace bazan ta6a gamsuwa da maganarkaba har sai nagane ma idona, nidai kukaini ingansa dan Allah.

Dr mu’az cike da jin tausayinsu yace tabbas suhail d’inku ne ranka yadad’e.

Arazane gabad’ayansu suke kallonsa ummi dasauri tamatso inda yake tsaye dada da sultana sadiya suka take mata baya, memartaba ko rik’o masa hannu yayi yace k’ara maimaita min abinda kace kamar kunnena bai jiye min daidaiba kasan inba sunan yarima ba babu abinda yake son ji.

Murmushi Dr mu’az yayi yace tabbas ranka yadad’e abinda kaji gaskiya ne, yarima ne yai maka komai shi yabuk’aci da kar abayyana muku kansa.

Alhmdllh, sultan abbas da sultan ahmad sukashiga furtawa.

Hawayene suka shiga zuba daga idanun memartaba yace dan Allah kataimaika kakaini inga suhail d’ina.

sultana bilkisu ma cikin kuka tace na rok’ek’a kataimaika kakaini inga d’ana.

Dada ma cikin kuka tace kakaini inga jikana ko nasamu sanyi a raina.

cike da tausayin family d’in Dr mu”az yace na amince zan kaiku kugansa a duk lokacin da kuka shirya.

Sultan abbas ne yayi karaf yace yanzu mukeso kataimaka kakaimu.

jinjina kai Dr mu’az yayi yace toh shikenan ranka yadad’e zamu iya tafiya.

 

Yarima yana komawa gida a bedroom yatarar da zarah tsaye tana shiryawa da alamu wanka tafito, kallonta yayi yace yisauri kishirya yanzu zamubar gidannan.

da mamaki zarah take kallonsa tace barin gida? Ina kuma zamuje daga nan?
Wata uwar harara yarima yawurga mata yace ba shawara nake nemaba umurni nabaki,,,,yana fad’in haka yawuce yaje yabud’e wardrobe yafara tsintar musu kayansu.

Zarah kasa ida sanya kayan tayi nan tai tsaye tana kallonsa cike da mamakin dalilin da zaisa subar gidan alhali mutanen suna da kirki, chan kuma sai tace ko dai gida zamu koma, har yagama shirya kayan tana tsaye ,,,juyowar da zaiyi ganinta tsaye yasa cikin fad’a yace bazakisa kayanba?

Nan cikin sauri Zarah tacigaba da saka kayan dan gabad’aya ya koma mata yarima suhail sak.

 

 

_Comment_
*Nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_[5/1, 7:01 PM] Sis Naj Atu:

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

Back to top button