Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 38

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*38*

Sultan ne yake jikin motarsa Yana jiran fitowar hajjo saboda sunyi waya ta fada masa lokacin da zata gama class din, dai dai wannan lokacin Ayman ya hangosa Yana mamakin meyake Yi a nan da can baisan shi ba amma lokacin aurensa sunje daurin aure Kuma da yazo yanzu Ammi ta fada masa cewa ya Bude kamfani a nan Abuja Yana yawan zama a Nigeria. Hajjo sun fito hannunta na cikin hannun Ummeey d’ayan hannun Kuma tana rike da waya da bag nata , ganin sultan yasa ta ja ta tsaya murmushi suke sakarwa juna Ummeey ta zare hannunta bayan sun gaisa da ya sultan ta Kara gaba. Hajjo ta tsaya nesa dashi tana masa murmushi suka gaisa tana tambayarsa ya dawo lafiya , suna tsaye suna hira harda dariya Ayman ya zuba musu ido Yana Jin zuciyarsa na suya ya Sultan Kuma? daga Aman ta koma sultan why? Meyasa Yan uwan nasa ke masa hakane, kirjinsa na masa zafi ya Kalli Fauzan yace su koma gida.
Ayman Bai Kara zuwa gidan inna ba ya tura Fauzan ya Kai sakon hajjo washegari ya nemi flight ticket suka wuce Sudan yayi kwana 3 sannan suka koma Jeddah, a nan ya samu kyakkyawar albishir cewa Failuzaa na dauke da cikin wata biyu yayi murna ba kadan ba duk da cewa Bai fito fili ya nuna mata ba sai hanyar kyautatawa saboda ya Siya mata sabuwar mota.

*1 year later*

Abubuwa dayawa sun faru ciki kuwa harda haihuwan matar Ayman wacce ta haifi mace har tayi watanni 5 sunanta Amina suna kiranta meenal , Ayman ya dauki son duniya ya dora mata a nan Failuzaa ta gane lagonsa tana amfani da soyayyar da yakewa y’arsa tana juyasa ga kudi sun zauna har anfara saninsa a fadin Nigeria da Sudan, Hajjo suna jarabawar gama 200 level har ynxu Bata da tsayayyen saurayi Wanda suke soyayya Mahfouz da sultan dai kullum sai sunyi waya, akwai shakuwa tsakaninsu amma Babu Wanda ya Kara furta mata Kalmar so. Yanzu Hajjo na Neman 20 years ta Kara hankali da wayo ga ilimin addini saboda yanzu inna ta Kara tashi tsaye akan tarbiyarta don ganin tana Neman canza sheka , yanzu dole tana saka hijab ba don son ra’ayinta ba haka inna ke tilasta mata. Yau Ummeey Bata zo skul ba Bata da lafiya Hajjo tana son biyawa ta gidansu ta dubata donhaka Bata kira driver ba don tasan zata dade a gidan, ta fito school nasu tana dan trekking har ta iso wajen FMC Jabi Bata samu abin Hawa ba Kuma Bata kira bolt ba. ta iso wajen junction din EFCC da Open university tana tsaye tana kallon hanya, ya fito daga office nasu zai wuce gida yazo wajen junction din zaiyi kwana kamar daga sama ya kalleta tana tsaye , birki yaja don tabbatar da cewa ba mafarki yake ba Amma kamannin yayi yawa dole ya tsaya ya tabbatar. Parking yayi kusa da ita ya leka ta window yace ” besty Hajjo ” kamar a mafarki ta juya tana kallonsa saboda andaina kiranta da wannan suna, kallon juna suke Hajjo ta Bude Baki tace ” Am..Aman are you the one” ya Bude mota ya fito tamkar zai rungumeta ya tsaya saitin fuskata Yana murmushi” dama kece? Yaushe kika dawo Abuja, Kinga yadda kika koma kuwa , u totally change ” murmushi take masa ta kasa magana” muje na saukeki ” ya Bude mata front sit ta shige ya rufe ya zagaya ya shiga ya tada motar. driving yake cikin kwarewa ya Kara kyau da girma ” it’s been long besty ya kike ” alhmdllh ya bayan rabuwa” “lafiya kalau kawai na nemeki na rasa, nayi ta zuwa nemanki ance kina yola ”
“Really.. yaushe?”
“C’mon nasan inna ta fada Miki don’t pretend” murmushi tayi daga Jin ya ambaci inna amma tayi mamaki meyasa inna Bata taba fada mata ba ko sau d’aya, “tell me daga Ina kika fito Kuma ki bani labarin meya faru bayan rabuwarmu ” daga skul nake Baze university” “really..da gaske kina Baze wow…I see that kinzama big girl” kaima ka girma ai besty nah ” ba dole ba na ajiye iyali, aure ba wasa bane dear ” u min..kana nufin kayi aure ?” ta tambaya a bukace ” yeah nayi aure da boy dina Fahad he is 2 years+ ” jikinta yayi sanyi a hankali ta furta”congrats Allah Sanya alheri” Ameen thanks”. Yana ta zuba Bai kula cewa mood nata ya canza ba, “Ina muka dosa ” ya tambaya” maitama lake Chad street ” wow a nan kike zama yanzu?” Umm.. no Muna Apo ne yanzu ”
“Owk..” haka ya cigaba da Bata labari Wanda yawanci batasan meyake fada ba tunda hankalinta baya wajen tayi zurfi cikin tunani. Sun iso lake Chad street ta nuna masa gidansu Ummeey da mamaki yake kallonta saboda da safe ya Sauke zee kafin ya wuce wajen aiki so Yana tunani kar dai a ce Hajjo tasan zee , da mamaki yake kallonta yace ” waye kika sani a gidan ?” kamar Batason magana tace ” nazo wajen friend dita Ummeey” “oh..ok Daz good so give me your digits” ” no need” Kai tsaye ta bashi amsa ” but why? Saboda nace Miki Ina da aure , c’mon bani number ki I’ll call you best ” hararinsa tayi ba tare da ta sake magana ba ta Bude kofa tayi wucewarta , murmushi yayi wato tana kishinsa ko me? Har yanzu tana kaunarsa kamar yadda yakejin sonta cikin zuciyarsa. Cikin gida kuwa hajjo ta samu kyakkyawar tarba dama can mum tasan hajjo saboda shakuwarsu da Ummeey Amma mum din tana office Bata dawo ba , masu aiki ne ke ta hidima da ita Ummeey ta zauna suna hira can aka shigo da Fahad kyakkyawan yaro fali ta dashi yayi kama da Aman da Kuma zee din . Hajjo tasa hannu ta karbesa tace ” Masha Allah wat a fine boy yaron waye ?” Yaron anty zee ne tun safe suka zo ta wuce gidan suna tabaro shi a nan, hira sukayi sosai sai bayan magariba hajjo tayi booking bolt ta koma gida. The next day still Ummeey bataje skul ba hajjo ta fito lectures kenan ta duba time 1 Kuma tana da class by 2 , tsaki take fama ja ta sake duba wrist watch nata a karo na biyu tana son zuwa masjid sallah tana Kuma Jin yunwa. Wata mota kirar Camry SE ce blue black tayi parking dai dai inda take tsaye a hankali ake sauke glass din motar , ko kallon inda motar yake batayi ba ta Kara tamke fuska ta dauka ko irin samarin skul nasu dake yawan nuna interest akanta ne, ” hey besty nah” ta juya Ido a hankali ta saukesu akansa Aman ne yayi matukar kyau cikin fararen suits nasa da brown inner shirt Wanda ya matukar karban farin fatarsa, kallo d’aya ta masa ta kauda fuska tana kallon Wani bangaren hurn ya danna mata taki juyowa sai ma fara tafiya da tayi tana takawa tamkar me tsoron kasa. Fitowa yayi ya fara bin bayanta ” haba Yan mata Jan ajin ya Isa haka a barni na huta ” yazo kusa da ita qamshin turarensa ne ya fara shiga brain nata batasan lokacin da ta lumshe idanu ba tana shakar dadadan qamshin ” Hajjo ! ya furta a hankali nan taja ta tsaya” point of correction Mr, sunana Aysha ” oh.. really my bestie angirma an zama big girl harda canza suna ” hararinsa tayi tace ” me kake Wani Bina tamkar akwai bashin da naci ban biya ba ” ” of course yes! Kinci bashin abota saboda haka kizo ki sauke nauyin ” nidai ka tafi ka kyaleni ”
“I can’t n I’ll never do that again, wancan lokacin ma tsautsayi ne yanzu bazan sake bari kiyi Nisa dani ba har abada ” kallonsa tayi suka kurawa juna Ido” yes.. I mean wat I said, please we need to talk please ” shiru tayi ta kasa cigaba da tafiya tana Jin bugun zuciyarta na fitowa da sauri da sauri, ” please best even if you want me to kneel n beg you don Allah ki bani lokacin ki even 15 minutes ” juya idanu tayi cikin Wani salon Sace zuciya tace” ok fine..na baka 10 minutes ” thank you, if you don’t mind let’s have a lunch” shiru tayi kamar bazata je ba sai kawai ta gyada Kai, ya Sauke Wani numfashin samun nasara haka suka koma mota yayi driving suka fita daga harabar school din ta kallesa tace ” where are we heading to?” “Eatery of course” cikin Jabi ya shiga da ita zuwa Wani hadaden eatery me suna tasty food, suka jera zuwa cikin wajen waitress ta kawo musu menu sukayi ordering. Bata Wani sake dashi sosai ba tana dan juya spoon ta kasa ci ya kalleta yace ” do you want me to feed you” ya d’aga mata gira ta hararesa Yana murmushi yace ” u look more good idan kika bata rai ” abincin take ci a hankali tamkar Bata so kadan taci ta ajiye spoon din , ya gama cinye nasa yasha orange juice ita ko ruwa kadai tasha ta goge baki da tissue ta dauki phone nata tana pressing. ” So Besty all these while baki taba missing dina ba n Baki taba tempting din nemana ba ” ta Ina zan fara nemanka best n u know I missed you alot ” murmushin jindadi yai tare da cewa” toh meyasa kika kasa Sakin jiki dani ” ” bcos u married, bana son zama problem a gidanka ” awn…I understand, don’t worry matsayin ku daban daban” meaning?” ta tambaya a hasale ” ohh..calm down ki fahimci me nake nufi please ” duba agogo tayi tace” I have class by 2 Kuma I need to pray before then ” alright let’s go ni nayi sallah ne na fito lunch but please u wait for me idan kika fito class” Bata tanka masa ba suka fara tafiya yace ” please mana Jan ajin ana sassautawa bawan Allah a tausaya mishi ” guntun murmushi tayi batayi magana ba suka shige mota yadau hanyar school nasu.

Wasa wasa shakuwar hajjo da Aman ya dawo har ya zarce tunanin me tunani kullum suna makale da juna a waya dare da rana, Basu cika haduwa a school ba yanzu saboda exams da take Bata da lokaci Amma a Rana zasuyi waya sau 7 at least. Wani irin soyayya suke Wanda su kansu basusan sunayi ba.sun gama exams suna Hutu yanzu kullum Hajjo tana gida Bata zuwa ko’ina sai dai aikan inna Wanda ba kullum ba. Yau Hajjo zata raka Ummeey gidan anty zee zasuje duba Fahad ba lafiya ta gama shirinta ta fito cikin wata doguwar Riga y’ar turkey me Karen kyau da tsada pitch color tayi light makeup tayi kyau sosai, ta fito falo inna na tare da sabuwar aminiyarta Hajiya luba wacce suke cikin estate din nasu matar abokin Abba ne. Sadeeq na ganinta ya tashi tsaye ya girma Yana yawo ko’ina cikin gidan ” ayawo toh Babu inda zakaje ” ta fada tana dariya inna tace ” ku kuka b’ata shi sai ki daukesa ku tafi tare ” hajiya luba wacce suke kira da momy tace ” kaji min mata Ina kika taba ganin budurwa na yawo da yara, so kike ya kashe mata kasuwa , jeki abinki dota Allah ya Bada sa’a wannan kyau haka Allah yasa a dawo mana da suruki” murmushi hajjo take ta gaisheta ta amsa cike da fara’a, ta shaidawa inna zataje ta mata a dawo lafiya ta kama hanyar fita Sadeeq yasa kuka inna ta faman rarrashi.
Gidan su Ummeey ta fara zuwa daga nan driver ya daukesu zuwa wuse gidan anty zee bayan sun tsaya sun masa shopping din chocolates da ice cream da biscuits, a katafaren gidan driver yayi parking gidan duplex ne da bq a waje sai d’akin maigadi, motoci 3 ne a harabar gidan Ummeey da hajjo suka fito driver na jiransu. door bell ta danna bayan few minutes aka Bude wata mata ce da alama Mai aikinsu ce ta musu sannu da zuwa tace ” hajiya na sama tare da megidan ” ok bara mu sameta a can ” Ummeey ta amsa mata hajjo dai kanta na kallon kasa suka haura staircase volume din TV kake ji har suka karasa

Back to top button