Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 9

Sponsored Links

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of experts & perfect Writers)_

 

*GARIN DAƊI…..!*

Free Book

*_NA_*

_*UMMI A’ISHA*_

 

*Wattpad:ummishatu*

 

*9*

 

~~~Yau da wuri na tashi daga office ban zame ko ina ba sai makarantar makafi, can na iskesu suna yin wasanni abun gwanin burgewa, an ɗaure zakara ansakeshi a tsakiyar fili sun bazu kowa yana yunƙurin kamawa, wuri na samu na zauna ina murmushi ni ɗaya duk da babu hashim acikinsu amma hakan ya sanyaya raina ganin suna rayuwa cikin farin ciki, suma kenan da halittarsu ta samu tawaya sun fawwalawa Allah komai suna rayuwa cikin godiyar ubangiji da farin ciki ina ga mu da Allah bai tauye mana komai na halitta ba ya zama dole mu kasance cikin hali na godiya da kuma takatsantsan akan duk wani abu da ya haramta,

Neman hashim na shiga yi ina yi ina tambayar ma’aikatan wurin da haka har aka kai ni wani wuri mai kama da office inda yake zaune kan kujera da wata na’ura gabansa yana yin typing sai dai tasu na’urar ba irin tamu bace masu idanu akwai bambance bambance masu tarin yawa, jin motsin shigowa ta yasa shi saurarawa daga abin da yake yi yayin da ni kuma nayi shiru ina takowa a hankali har na zo dab dashi ɗan karkato da kanshi yayi kafin naga yayi murmushi ya cigaba da aikin sa, zuwa can yace,

“munatu na ya aka yi kika san cewa ina nan? waye ya kawo ki?”

Murmushi nayi na nemi wuri na zauna kan wata kujerar roba koriya,

“kayi mamakin ganina ne a wannan lokaci?”

“a’a banyi mamaki ba, kawai dai na tambaya ne”

“Rakoni aka yi”

“to barka da zuwa, bari yanzu zan ƙarasa sai mu tafi”

“to shikenan”

Wayata na ciro daga cikin handbag ɗina ina yi masa hotona shi kuma yana cigaba da aikin sa har ya kammala. Gidansu muka wuce direct dan ina so inji ko iya ta samu zuwa gidan ɗan bahago, ita kaɗai muka tarar a gidan tana zaune ta kunna radio tana saurara maganin zaman kaɗaici, shigowarmu ya sanya ta kashe radion tana yi mana sannu da zuwa, nidai a tsattsaye muka gaisa na soma tambayarta ya maganar zuwanta wurin iyalan ɗan bahago?

“insha Allah dama gobe nake son zuwa, sammako ma zanyi da yardar Allah kan azahar na dawo”

“to shikenan iya ubangiji Allah ya kiyaye hanya sai kin dawo ɗin”

Sallama muka yi dasu na tashi na tafi kuma tun ina cikin napep naga manager na kirana amma ban ɗauka ba har sai da na sauka sannan na kira shi nan yake faɗa min komai ya zama daidai insha Allah zasu bani loan ɗin da na buƙata godiya nayi masa muka yi sallama na shiga gida.

Kamar yadda na tsara hakance ta kasance ba tare da wani kuskure ba domin na samu duk kuɗaɗen da nake buƙata, sannan cikin Ikon Allah lokacin da Iya taje gidan Malam Ɗan bahago ta iskeshi ya dawo daga doguwar tafiyar da yayi shekara da shekara a ƙasar Mali nan suka shirya maganar yadda zasu tafi Chadi domin shine zai yi musu jagora har zuwa gidan mutumin da yace shine zai baiwa Hashim maganin lalurarsa da izinin ubangiji,a ranar da na ɗauki adashena na haɗa da kuɗin wurina wanda na karɓi loan na kai musu domin cikin satin nan zasu yi tafiyar, ban tsaya iya nan ba har sai da na siyo musu wayar hannu mai sauƙin kuɗi wacce zasu iya sarrafawa domin jin halin da suke ciki domin tafiya ce zasu yi ta mota ba wai jirgi ba sannan hanyar cike take da ƙalubale kala kala kamar yadda Malam Ɗan bahago ya faɗa.

Tamkar zanyi kuka lokacin da naje yi musu sallama saboda da asuba zasu kama hanya gobe, duk nabi na shiga damuwa jikina yayi sanyi, tafiyar nan da Hashim zai yi ina ji ajikina kamar zan rasa wani ɓangare ajikina mai muhimmanci sai yanzu ne na gane irin ƙarfin girman shaƙuwar da muka yi dan na kasa ɓoye damuwata ji nake kamar inbisu mu tafi tare ayi komai akan idona in gani, shi da kansa sai da ya fahimci ina cikin matsananciyar damuwa daga ƙarshe yace to ko dai a fasa tafiyar tunda hakan na neman sakani cikin damuwa?,

Hawayen dake tsere akan kumatuna na goge sannan cikin raunin zuciya nace,

“A’a dan Allah karku fasa Hashim, lafiyarka itace gaba da komai awurina, kuje Allah ya kiyaye hanya ya dawo daku lafiya”

Shima ɗin dai cikin damuwar yake sai dai yafini dauriya, na gane hakanne ta dalilin yanda muryarsa tayi sanyi kana ji kasan akwai wani raɗaɗi dake nuƙurƙursar can ƙasan ransa, haka dai muka rabu zuciyoyinmu duk babu daɗi kowa yana jin zafi da raɗaɗin rabuwar da za muyi na tsawon lokaci domin Allah kaɗai yasan ranar dawowarsu,nidai har naje gida ina kukan zuci, hawayen ne dai nayi ta maza wurin dakatar dasu da hanasu zubowa sai dai suna nan suna kwaranya cikin zuciya ta wanda hakan shi yafi komai illa ga zuciyar tawa,hatta bacci daren ranar gagarata yayi sai dab da asuba sannan na samu ya saceni.

Misalin ƙarfe 10 na safe na tashi daga nannauyan baccin da na jima inayi mai cike da mafarkai kala kala wanda duk basa rasa nasaba da tafiyar Hashim wanda na san dan dai na saka abun a raina ne shiyasa nake ta yin mafarkai iri iri, wanka nayi na fito na shirya cikin doguwar riga milk colour, wayata na ɗauka ina duba miss calls ɗin da aka yi min lokacin da ina bacci, Bishra ce da Manager sai su Hashim, su Hashim ɗin na fara kira amma wayar bata shiga har na gaji na daina ma kiran na haƙura na ajiye wayar na fita, haka dai yau na wuni nidai gani nan gani nan ne dai gashi wannan Manager ɗin ya takura min da kira daga ƙarshe da na gaji na ɗaga,

“Ranki ya daɗe na dameki ko? Kiyi haƙuri na kasa jurewa ne wallahi, tun ranar da na ganki naji kin shiga raina lokaci guda, to ina ta so in sanar dake amma baki bani lokaci ba, kamar dai yadda kika sani sunana Ahmad Idris, ni haifaffen garin Kano ne amma asalinmu ƴan Albasu local Government ne, mu biyu ne a wurin iyayen mu daga ni sai ƙanwata zarah, nidai yanzu babu abin da nake buƙata wanda ya wuce in samu matar aure, mahaifiyata itama kullum maganarta in samo matar aure….. To kin san ba wai matan ne babu ba a’a nagari masu mutunci da halin ƙwarai sune ba afiya samu ba amma ke dai insha Allah ina kyautata miki zato kuma na san insha Allah ba zanyi dana sani ba…… Maimuna ki bani dama in aure ki… ”

Ajiyar zuciya na sauke bayan gama jin duk waɗannan uban bayanan da ya rattaɓo min, cikin sanyin muryata wadda ta haɗu da damuwar da nake ciki nace,

” Nagode sosai da soyayyarka, sai dai zan baka haƙuri saboda akwai wanda muka yi alƙawarin aure tare dashi kuma duk mun yi amanna muna son junanmu,da ace babu alƙawarin wani a kaina da babu abin da zai hanani baka damar neman aure na”

Shiru naji yayi irin shirun da yaya Faisal yayi lokacin da na sanar dashi na fasa aurensa, bayan wasu mintuna naji yace,

“Shi wanda kuka yi alƙawarin auren dashi ya tura gidanku ne an amince anbashi ke?”

“Ehh..” na faɗa aƙule domin na fara ƙosawa da waɗannan maganganun nasa masu kama da ƴaƴan barkono tsabar zafin su a cikin raina,

“To shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi ya sanya albarka, ina yi miki fatan alkhairi”

“Amin, nagode”

Ajiye wayar yayi daidai da shigowar ƙanwata Bishra wacce take bina,

“Yaya Widat inata kiran wayarki baki ɗauka ba”

“Ban tashi daga bacci ba lokacin, ya aka yi?”

“Lafiya Lau…. Ashe wai bikin Yaya Faisal next 2 months ko”

“Allah yasanya alkhairi” na faɗa adaƙile dan yau ɗinnan sai a hankali sam bana son hayaniya.
***
Yau kimanin watanni uku kenan da tafiyar su Hashim kullum muna waya dasu kuma muna gaisawa suna sanar dani irin cigaban da ake samu wurin maganin da ake yi masa wanda insha Allah ana sa ran samun nasara. A ɓangaren Hashim yafi kowa farin ciki domin ya jima yana burin tozali da kyakkyawar fuskar masoyiyarsa kuma abar ƙaunarsa wadda bashi da kamarta duk duniya kuma ko gaba baya jin zai samu kamarta balle wacce ta fita, shi kansa yanzu yasan yana samun sauƙi domin duhun da yake gani yana yayewa sannu sannu amma har yau dai bai fara gani ba sai dai yana ganin wannan duhun yana raguwa lokaci zuwa lokaci wanda insha Allah da haka da haka zai gushe gaba ɗaya kamar yadda mai maganin ya faɗa musu.

Yau dai itace rana ta ƙarshe da Hashim zai gama amfani da maganin da aka bashi wanda yake wanke fuskar shi dashi, tunda ya faɗa min daren jiya banyi bacci ba kwana nayi ina sallar nafila da karatun Alqur’ani inata yi masa addu’a akan Allah yasa adace kuma ya bashi cikakkiyar lafiya mai ɗorewa,

Tun asussuba nake ta kiran su amma ban samesu ba haka na haƙura na shirya na tafi wurin aiki, har na taso daga aiki ban samesu ba su kuma basu kirani ba, haƙura nayi na yada zuciya ta kuma na kwantar da hankali na,daga ƙarshe gidan su ƙawalli ma na shiga dan kawar wa da kaina tunani muka kuwa sha hirarmu zuwa magariba na dawo gida,

Ina zaune kan abin salla bayan na idar da salla kamar yadda ƙa’idata take duk bayan sallar magariba na kan zauna in yi tasbihi da karatun Alqur’ani har zuwa lokacin sallar ishah, wayata ce ta katseni daga karatun da nake yi inda nake karanta suratul Ibrahim, ganin su Hashim ne sai da naji gabana ya faɗi da wani irin matsanancin ƙarfi,nan nayi sallama duk a duburce,

“Amincin Allah ya tabbata ga ma’abociyar kyau da cikar halitta, Sarauniya wacce babu kamarta, ma’abociyar kwarjini da kuma kyautatawa….. Tabbas kece bugun numfashi na, idan har babu ke rayuwa ta bata da sauran amfani domin idanuwa na ke kaɗai suka cancanci suyita kallo har ranar da zan koma ga Mahalicci na wanda ya buɗe min idanuwa na ta silarki tare da taimakonki da kuma jajurcewarki….. Dan Allah ki bani dukkan umarnin da kike so zana bi, ki buƙaci dukkan abin da kike buƙata daga gareni nayi miki alƙawarin zanyi…. Wai dama haka duniyar nan tamu take? Ashe haka duniya ke cike da abubuwan kyawu gami da ban mamaki…. ”

Kasa motsi nayi sai hawayen farin ciki dake kaiwa da komowa daga idanuwa jin wai idanuwan Hashim sun buɗe, ban san lokacin da nakai goshina ƙasa ba dan yin sujjadar godiya ga ubangiji na……… ✍

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*

Back to top button