Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 1

Sponsored Links

page 1⃣

garin gazban garine mai albarka da yawan mutane yana d’aya daga cikin garuruwan da ake alfahari da su.

sun kasance suna da babbar Masarautar da babu kamarta wajen girma da kyau sarkin garin ya kasance sarki mai adalci duk kud’in mutum bai isa yazalunci nak’asa da shi ba indai har yazalunta labari yazo ma sarki toh sai yad’auki mataki,

Related Articles

sarki umar yana son talakawansa sosai suma suna sonsa abun mamaki wannan sarki ya manyanta domin zai kai shekaru 76 ammah indai ba ka saniba sai kad’auka d’an shekara 50 ne, domin babu alamun tsufa a tare da shi idan dukiyarce ya tara, idan sarautarce yana d’aya daga cikin manyan sarakuna kai intabbatar muku wannan babbar Masarautar ko da me kazo anfika.

Sarki faruk matarsa d’aya dattijuwa dada, saidai abun mamakin duk mulkin nasa ammah ‘ya’yansa biyu dukansu maza ne Ahmad shine babba sai k’anensa Abbas sun taso atare sun kasance suna son junansu.

 

saidai a tsarin mulkin garin indai sarki yahaura shekaru arba’in (40) saman karagar mulki toh d’ansa ba zai ta6a gadon mulkinba saidai babban jikan gidan, saidai idan babu jika namiji shine d’an sarkin yake hawa mulkin

 

lokacin da ‘ya’yansa suka tasa yaza6a musu mata inda Ahmad ya auri d’iyar sarkin agadaz wato sultana Bilkisu, shi kuma Abbas sarki ya aura masa d’iyar d’an uwansa da yamutu yabari wato Sultana Sadiya.

A cikin babbar Masarautar kowa aka fitar masa da 6angarensa.

Suna zaune lafiya da matansu, inda sultana Bilkisu takasance macece mai hak’uri da tawakkali ga ta macece mai kyauta ta kasance mai son jama’a,

inda Sultana Sadiya takasance akasin haka domin bata son talakkawa suna ra6arta dan ma mijinta a tsaye yake sun d’auko hali irin na mahaifinsu, ammah duk da haka taci alwashin ita take da burin tafara haihuwar d’a namiji.

 

saidai kash sultana Bilkisu ita tafara samun ciki, hankalin sultana Sadiya ya tashi sosai ganin ita ko 6atan wata bata ta6a yiba,

Bayan wata goma sultana bilkisu tahaifi d’iyarta mace murna wajen iyayen ba’a magana hatta ita kanta sultana Sadiya tayi murna ganin ba namiji bane ta haifa.

ranar suna anyi shagali sosai kud’i sunyi kuka tsakanin masarautar gazban da masarautar agadaz anzuba naira sosai a inda yarinya taci sunan dada wato Asma’u ammah ana kiranta da husna.

 

Bayan shekara ukku Sultana bilkisu tak’ara haihuwa inda tasamu d’anta namiji kyakkyawa domin ita yabiyo kamar antsaga kara murna wajen su sarki ba’a magana hatta su kansu jama’a sun shaida wannan haihuwar domin sarki sadaka yadinga yi da dukiya sosai,

akasin sultana Sadiya da takasa 6oye bak’in cikinta turakar mijinta taje tasameshi a zaune yana ta kiran waya yana fad’a ma mutane, zama tayi gefensa tana kallonsa cike da takaici har yagama wayar sannan yakalleta fuskarsa d’auke da murmushi yace sultana akwai abinda kike buk’ata ne?

sultana sadiya d’auke fuskarta tayi daga kallonsa tace ranka yadad’e meyasa kake murna dan matar d’an uwanka ta haifi namiji kar fa kamance shine zai hau karagar mulki bayan ran sarki,

da mamaki sultan abbas yake kallonta yace sultana ba dai bak’in ciki kike ma d’an uwana ba dai ko?

d’aure fuska sultana tayi tace bak’in cikin me zanyi masa, naga kana ta murna ne mukuma kaduba kaga ko 6atan wata ban ta6a yiba bamu da d’a ko d’aya kuma kyau ace d’an kane zai gaji masarautanan.

sultan Abbas sakin baki yayi yana kallonta har takai aya sannan yace sultana inaso kisan wani abu wlh da zuciya d’aya nake son d’an uwana ban damu da sarautar da d’ansa zai hau ba domin nima d’ana ne sannan da kike magana akan rashin haihuwa inaso kisani Allah shi yake badawa ga Wanda yaso kuma yahana Wanda yaso ban cire rai ba idan da rabo nima zanga tsatsona, dan haka kar ink’ara jin kinyi wannan maganar, kibinneta daga nan da kika yi ta.

Mik’ewa sultana tayi cikin fushi tace daman nasan ba zaka ta6a fahimtaba ammah nan gaba dakanka zaka fahimci abinda nake nufi. wucewa tayi fuuu tafita tabar d’akin.

Sultan Abbas binta yayi da kallo har tafita sannan yagirgiza kai cike da takaicin abinda matarsa tayi yace Allah yashiryeki sadiya.

 

 

Ranar suna yaro yaci suna Umar sunan maimartaba ammah suna kiransa da suhail,

suhail yataso cikin gata domin yana samun kulawa sosai a wajen iyayensa da kakanninsa hatta shi kansa sultan Abbas yana ji da d’an nasu,

akasin sultana sadiya da ta tsanesa bata d’aukarsa sai idan gaban su Dada ne nan take nuna tana sonsa sosai, ammah a cikin zuciyarts ji take ina ma ace yamutu.

ahaka yataso cikin gata tun yana shekara ukku maimartaba yakesawa ad’aukosa akawo sa fada yazaunar da shi kusa da shi saisa suhail yataso ya shak’u da kakansa sosai.

Bayan shekara biyu sultana sadiya tasami ciki murna wajensu da wajebnsu sultan Ahmad ba a magana,

kulawa sultana sadiya take samu sosai daga wajensu maimartaba da mijinta hatta ita kanta sultana bilkisu tana bata kulawa sosai.
inda sultana sadiya take addu’a akan Allah yasa tahaifi d’a namiji.

inda itama sultana Bilkisu take d’auke da d’an k’aramin cikinta.

 

bayan wata tara sultana sadiya tahaifi d’iyarta mace ta yi bak’in ciki sosai ammah daga baya tahak’ura, murna wajen su maimartaba ba’a magana kowa ya nuna farin cikinsa,

ranar suna yarinya taci suna sumayya, anyi shagali sosai anci ansha.
inda sultana sadiya taci alwashin ta kowane hali sai d’iyarta ta auri sarki mai jiran gado .

 

bayan wata ukku sultana bilkisu tahaifi d’iyarta mace inda taci sunan mahaifiyarta wato Rahama,

tun daga lokacin babu wadda tak’ara ko da 6atan watane, sumayya da Rahma sun taso a tare komai nasu d’aya bacci kawai yake rabasu.

 

Yarima Suhail duk halin maimartaba yad’auko yatashi mutum ne mai tausayi kuma mai girmama na sama da shi saidai ya kasance bai da son hayaniya miskiline na sosai baya shiga abinda bai shafesaba baya da yawan fara’a sosai saidai ga wanda bai sansaba zai masa kallon mutum mai girman kai.

In ko kagansa a fada toh maimartabane yasa yaje ammah shi kwata-kwata baida burin yin sarauta, ko da dakagansa komai nasa irin na sarauta yakeyi.

tun da yataso abokinsa d’aya d’an waziri wato shahid tare suka taso tun suna yara sunyi makarantar arabi da boko a garinsu.

bayan sun gama secondary yarima suhail yanuna yanaso yafita waje yayo karatunsa, anyi daga sosai da maimartaba afin ya amince domin cewa yayi shi da zai gaji sarauta mezaisa yafita waje karatu, daga baya dai dakyar aka samu maimartaba ya amince inda yarima yaje india yayi karatunsa na likitanci inda yakaranci surgeon.

bayan shekara biyu akasha bikkin Gimbiya husna inda ta auri d’an chairman d’in garin anyi shagali sosai anyi bikkin da ba a ta6a irinsaba a garin, inda husna tatare a gidan mijinta
yarima suhail yaso yazo ayi bikkin da shi ammah iyayensa suka hana sukace yazauna yayi karatunsa.

 

Gimbiya Sumayya da Gimbiya Rahama sun shak’u da juna sosai saidai suna da banbancin halayya sumayya tana da wulak’anci sosai kuma ta tsani talaka yara6eta bata abota da kowa sai wanda yakasance jinin sarauta ko d’an wani attajiri.

akasin Gimbiya Rahama da takasance mai son jama’a kuma bata da wulak’anci kowa natane abinda yake had’ata fad’a da sumayya kenan ko a school.

 

 

 

Bayan shekara hud’u yarima suhail yakammala karatunsa yadawo k’asarsa ta haihu ya k’ara girma da kyau miskilancinsa ya k’aru da kagansa ka ga jinin sarauta,
murna wajen maimartaba da iyayensa ba a magana hatta kansu jama’ar gari sunyi murnar dawowarsa.
ba kamar abokinsa shahid da yayi missing d’insa sosai.

gidan sarautar hidima akayi sosai inda dukkan ma’aikatan gidan suka had’u adafa wancan asafke ad’aura wancan,

walima akayi ta azo agani hatta kansu talakawa sun ci sun sha,

Sumayya tun da tad’aura idonta akansa tace ai tayi miji ba zata auri kowaba sai shi ko da taje ma mahaifiyarta da maganar itama tayi murna sosai domin itama burin da take da shi kenan a rayuwarta inda tabata shawara akan taje tasanarwa dada.

sumayya ta d’auki shawarar da mahaifiyarta tabata dan haka tawuce tanufi 6angaren su maimartaba lokacin da tashiga d’akin dada zaune take saman kujera gefenta dama da haggu duk kuyangine suna ta mata hidima,

sumayya bisa kujerar da kaka take zaune taje tazauna tace ranki yadad’e ‘yar tsohuwarmu Allah yak’ara miki tsawon kwana,

dariya dada tayi tace Ameen gimbiya ganinki da nayi haka nasan bakinki yana d’auke da magana,
sumayya murmushi tayi tace tabbas hakane ranki yadad’e akwai abinda yake tafe da ni.

kaka sallamar kuyanginta tayi duk suka fita sannan tatattara kallonta ga jikartata cike da kulawa tace ya ke sumayya inaso kifad’a min abinda yake tafe da ke nikuma indai baifi k’arfina zan taimaka miki.

sumayya duk’ar da kanta tayi cike da kunya tace dada daman akan yaya suhail ne,
murmushi kaka tayi jin an ambaci nagaban goshinta tace ina jinki me suhail d’in yayi?

sumayya tace babu abinda yayi saidai nice wlh dada tun tuni nakeson yaya suhail kuma ina tsoron intaresa da maganar dan nasan zai iya min wulak’anci saisa nace bari infara samunki da maganar wlh dada ina sonsa har cikin raina.

dada tunda sumayya tafara maganar kasa rufe baki tayi saboda jin dad’i, saida sumayya takai aya sannan dada tace masha Allah gaskiya naji dad’in labarin nan da kikazo dashi domin daman nima ina da burin hakan a raina ammah tunda har kikafurta da kanki toh ai shikenan.

sumayya kallon dada take cike da jin dad’i tace toh dada shikuma yaya suhail fa idan yace baya sona?

dada tace kikwantar da hankalinki zai ma soki domin babu yadda za’ayi nagida bai k’oshiba aba na waje ke dolene mane yasoki dan haka kikwantar da hankalinki shalele kamar kin zama matarsane kibari zamuyi maganar da shi da maimartaba.

 

sumayya cike da jin dad’i taduk’a takwashi gaisuwa tare da yin godia sannan tayi ma dada sallama tafito tanufi 6angarensu duk inda ta gifta tun kan ta ida isowa inda bayi da ma’aikata suke ake zubewa kwasar gaisuwa kowa tsoronsa kar tace yayi badaidaiba domin sunsan halin gimbiya sumayya da mahaifiyarta yi musu laifi abune maisauk’i, kowa yau yana mamakin yadda fuskarta take a sake sa6anin da dakullum take a d’aure.

dada ko da tasamu maimartaba da labarin shima yayi murna sosai inda yace zai gana da su gobe.

 

 

yarima suhail ne kwance saman makeken gadonsa inda shahid yake gefensa yana ta zuba masa surutu shi dai yarima daga uhm sai uhm-uhm bai cewa komai sai ma dannar wayarsa da yakeyi.

shahid ya k’ule sosai tsaki yaja yace kai fa matsalata da kai kenan sai ana yi maka magana kadinga share mutum kamar ba dakai akeba.

shuru yarima yayi yacigaba da dannar wayarsa takaici yakama shahid dan haka yafizge wayar, ganin haka yasa yarima yamaida idanunsa yalumshe.

shahid baiyi mamaki ba domin yasan halin abokin nasa tun suna yara.

knocking d’in k’ofar da akayine yasa shahid yabada izini da ashigo, wani dogarine yashigo tare da zubewa k’asa yana k’wasar gaisuwa shahid ne kawai ya amsa masa,

dogarin kansa yana k’asa yace Allah yaja da ran yarima mai jiran gado daman Maimartaba ne yake kiranka ya ce kasamesa a turaka,

yarima batare da yabud’e idonsaba yad’aga ma dogarin hannu alamun yatafi.

tashi dogarin yayi yace nabarku lafiya sannan yaficce daga d’akin.

shahid kallonsa yayi yana murmushi yace yau sarautar ta motsa kenan…..

 

 

_Comment_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

 

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_Sak’on gaisuwata agareku intelligent writer’s Allah yabar k’auna_

 

_My k’anwa janaf Allah yabar min ke_

 

_*Wannan page d’in nakine Asma’u Yusuf Beji kiyi yadda kikeso da shi ina godia da kulawarki agareni*_

Back to top button