Hausa NovelsMatar So Hausa Novel

Matar So 27

Sponsored Links

 

Shiru yayi jikinshi yayi matukar sanyi, shi dai abinda yake ji akaina daban ne da sauran sai dai baya jin zai iya zuwa ga abinda zuciyarshi ke tilasa shi, dukda mallakinshine ni ɗin.

Janye jikinshi yayi  bayan ya ja hancina, yace.
“Baki da kunya kin wani makale ni sai kace wacce kika sami wani pillow common my dear zoki ci abinci.”
Karamin murmushi nayi wanda ya karawa fuskana kyau nace.
“Allah ko Mai Nasara? Ji bika kato da kaine zan makalewa kasami jinjiran yarinya sai juyata kake son ranka, ko ba haka ba.”

Ware idanunshi yayi nima na kashe mishi nawa nace.
“Iya gaskiya na faɗa maka babu karya ciknta, sai gaskya tsiraranta.”
Rike baki yayi yana wani gyaɗa kai kaman kadangare, sai ya bani dariya har ina rike cikina, nuna shi nayi da yatsar hannuna nace.
“Ɗaddy!! Kaga yanda kake kuwa hmmm.”
“Karki bari na kamaki, dan zakifu kowa wahala sai na kashe bakin rashin kunyarki nan.

Murguɗa bakina nayi na fashe da dariya har ina tafa hannuna nace.
“Yo…”
Ganinshi nayi a gabana, cak na haɗiye tsokanar ina kallonshi cikin tsoro nace.
“Daddy Am sorry, bazan kuma ba Allah yana tare da masu hakuri kaga ni har ynz am still baby.”
Sama gado yayi dani na fasa mishi ihu sai da ya toshe kunenshi, ganin haka na zille zan sauka ya kamoni, tare da jibga min nauyinshi.

A nan idanuna suka rena fata, dan ji nayi kamar ya ɗaura min aiki.
“Kayi hakuri ban kumawa.”
“Karya knn ina kyaleki zaki kara min wani.”
“Da gaske nake.”
Haka ya gama tumurmushime ni son ranshi kafin ya kyaleni dan yace shi ynx kukana baya damunshi kaman da.
****
Kwanaki goma mukayi kuma kowacce kwana sabonta kanta take da abubuwan Al’ajabi ga dai miji nasame shi amma banzar aqidar Yahudawa ta kama zuciyarshi ko nace ra’ayi rikauu.

Ranar da muka cika sha ɗaya muka bar garin bayan munyi tsaraba, sosai har dasu Umma Hajiyan zaria kowa dai, ya samu.
Mun sauka a lag daga nan muka bi jirgin kaduna, muna isowa Aman yazo ɗaukarmu sai tsiya yake mashi,  yaki magana sai murmushi kawai.

Koda isa gidan mun sami Aneesah, gaida ita nayi a mutunci tare da tambayarta ya jikinta.
Taɓe baki tayi tare da yatsina fuska tace.
“Sauki.”
“Allah ya baki lafiya.”
Amin tace min,
Sosai nake kallon ramar da tayi, shigowarshi ya kafeta da ido, cike da mamaki yanda ta rame ta zabge, a cikin kwanakin ds basu fi sati biyu ba.
Zama yayi a kusada ita tare da riko hannunta mai lafiyar Yace.
“Neesah mi yasameki haka? Ko kinyi ciwone?”
Narkewa tayi a jikinshi tare da gyara kanta a kirjinshi, satar kallona yayi yaga sam ban sauya fuska ba saima tausayinta da nake ji.
“Mai nasara cikine, na six wks amma nayi abortion ɗinshi sabida wahalar karta min yawa ga ciwo a hannu ga wahalar laulayi, ga rashin zuwa aikina.”
Shafa kanta yayi cikin tausayawa, yace.
“Sannu haka da kikayi shine dai dai, kuma ya kamata ki nemi wani abun kariy……”

“Daddy!!! Kai da kanka kake kara mata kwarin gwiwa dan ta zubda kyautar Allah, wannan wani irin rayuwa ce kuke yi a gidanka, Cikin da wasu suke nima kasa kasa, har ɗakin Allah suke zuwa suna kuka Allah ya basu haihuwa, Anya kayiwa ɗan tayin da aka cire adalci wallahi Allah bazai kyaleku ba.”

Sam ya manta ina falon ya zauna suke maganar cikin.
……Tsawa ya buga min, tare da mikewa kamar zai cinye ni, lokaci guda jikina yayi matukar sanyi yanda yake faɗa min magana har da kirana jahils shashasha, wannan kalmar tasani kuka musaman jahilar,.saukar da kai nayi.
“Kayi hakuri mantawa nayi manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi yace.
Karda kashi ga abinda babu ruwanku, sannan a gaba kuma yace Imanin ɗayanku baya cika har sai ya sayawa ɗan uwanshi abinda yasaiwa kanshi kuyi hakuri dan mu rabauta tare ne yasa nayi magana amma Insha Allah bazan kuma ba. Kayi hakuri Daddy.”
“Wucce ki bamu guri, sai kinyi abu ki koma kamar na Allah nan kuwa kinfi kowa salon munafucin da kinibibi, Don Allah kace  tabar min nan kaina ciwo yake ”
D’ago kanshi yayi ya kalleni tun bai karasa abinda zai fito bakinshi ba, na bar falon har nakai step yace.
“Waye zai kwashe miki kayan? Ko baki ga halin da nasami Aneesah bane,oya sauko ki kwashe.?
Kamar zan fasa ihu haka na sauko nazo na kwashi kayan, na wucce da nashi ɗakinshi, nawa kuma nakai sama. Cire kayana nayi na shiga gyara ɗakina, ina gamawa nayi wnka da sllah, sannan nazo niman abinda zanci.
Duk sun halarra a falon, har da balkisu sai hira suke dukda akwai rashin sabo amma na fahimci anyi haka ne dan a nisantani dashi, kuma hakan ce ta faru.
Shinkafa da miya nayi sai salad, da zoɓo. Ina gamawa na zuba mishi nashi a warm na ajiye akan dinner na kwashi nawa zuwa sama, babban kuskurana shine rashin faɗa mishi na gama amma ai nasan dukda haka yasan na gama girkin tunda, sau biyu yana ɗaga kanshi ya duba ni daga falon sai ayi dace mun haɗa ido.
Ina zaune a falona nasaka abincin a gaba, sai ga Mufeeda ta shigo ko sallama batayi min ba, ɗago kaina nayi tare da murmushi nace.
“Lafiya mufeeda?”
Tsaki tayi min, sannan tace.
“Ki sauka da abincinki kasa daddynmu nakiranki, yaran talakawa kawai.”
Lumshe idanuna nayi sabida kaifin maganarta tafi ta reza ko wuka.
Tana gama faɗar haka tafita, shiru nayi ina nazarin kiyayyar da suke min, wanda nidai Allah ya gani bana nufin cutar dasu amma a hakan suke kokarin ganin sun kuntattamin.

D’an zaman da nayi a gurin ba tare da tashi naje naji sakonshi ba, ya sake ja min fitina.
Daukar abincin nayi na sauka kasa, yana zaune akan table ɗin sai juya abincin yake da cokali, duk sun yanyame shi, kallona yayi dan dama idanunshi nakan step ɗine, yayinda suke ta zuga shi ya cika fam fuskarshi har wani ja tayi, tunda na kalli cikin idanunshi na hango wutar bala’i sai na shiga nanata kalmar Innalillah…da wasu addu’o’i har na isa gurin. Lumshe idanushi yayi bayan ya shaki kamshin turarena, mutum ne mai masifar son turare dan matukar zai shaki kamshin turare yakan tsinci kanshi da samun nutsuwa.
Buɗe rinanun idanunshi yayi, ya sauke a kaina. Shiru yayi ya cigaba da juya cokalin, araina nace.
*Hali zanen dutse, yau kuma miskilancine ya motsa*

Duk suka shiga hankalinsu dan basu san irin hukuncin da zai min ba, amma in so samune basu ki yayi min shegen duka ba, tunda mugun laifi nayi.
Can da nagaji da tsayuwa nace.
“Daddy ka kirani, kuma kayi shiru. ”
Yanda nayi maganar in low voice ya sashi ɗago kanshi ya kalleni, sannan ya mai da idanunshi kujeran dake kusadashi.
Nufinshi na zauna ajiye abincin nayi wnd na sauko da shi akan table, zama nayi ina kallonshi. Tura min filet ɗinshi yayi ya janyo kular shimkafar da ta miyar, ya zuba a wani filet ina kallonshi a nutse ya fara cin abincin, sai da yayi spoon uku sannan yace.
“Kici nagabanki.”
Jikina ne ya ɗauki rawa, duk suka zuba min ido. D’ibar abincin nayi a cokali nakai bakina, wani masifaffen yaji da gishiri suka kama min, kan harshena da bakina baki ɗaya rike bakina nayi zan mike ya maidani ta hanyar take min kafana cikin fushi yace.
“Sai kincinye kuma kika kuskura kika dawo min dashi zan miki dukar da sai kin kwanta a gadon asibiti.”

Dakyar na haɗiya tare da jan kofin ruwa nakafa kaina, aikuwa na fara amai. Wnda yasashi dole barina na mike, gashi na kware numfashi na ya ɗauke cak, zuba gwiwa na nayi kasa ina fincikar numfashi, dukda hankalinshi a tashe yake ganin halin da nake ciki, maganar da Fareeda tayi yasashi kauda tausayina da yake ji ya faɗi abinda yake ranshi.
“Laaaa cikine ashe da ita.”
Aikuwa ya juya ya dalla mata harara, yace.
“Ke kika mata cikin, wannan Yar yarinyarce zata iya ɗaukar ciki ko ta ɗauka zubda shi za’ayi dan bata da hankali da nutsuwar renon wani yaro itama yaushe ta reni kanta, kar na kuma jin wannan maganar, dan ni ban ɗauketa a mata ba ina kallonta a matsayin Y’ar cikina ne.”

“Indai haka ne. Toh kar takuma shiga d’akinka ko kuma tayi maka girki, dama bason girkin Johson kake ba sai ta karɓi aikinshi, da kuma kula dani tunda kaga bani da hannun da zan iyayin komi.” Inji Aneesah.

D’aga kai nayi ina kallon yanayinshi, kuma ina jiran abinda zai ce sai kawai naji yace.
“Ok haka yayi ma”

“Wallahi baxanyi ba.”
Na faɗa kai tsaye,
“Mi kika ce?” ya tambaye ni.
Shiru nayi ban kula shi ba, riko hannuna yayi ya haura dani sama, nomber mama kilishi ya kira ya faɗa mata, abinda nayi mishi mika min wayar yayi, ya fice a ɗakin.
“Maryam ya muna yabanki sallah zaki kasa alola, ko kina son Malama taji abinda kikewa mijinki ne, yau kuka dawo amma zaki haɗa mishi rigima da matanshi, ai balkisu ta faɗa min komi don Allah ku xauna lafiya kece karama kece kuma za’a sami matsala dake, toh ki nutsu kar ya kuma kawo min karanki.”
Cikin kuka nace.
“Insha Allah…” ban iya magana ba sai kuka.
Kashe wayar tayi, na rasa mike min daɗi. Ummana nakira a wayata, na cigaba da kuka tanq jina bata kashe ba, nima ban kashe ba sai kuka kawai nake mata sai na buɗe baki nace Umma sai kuma kuka ya kwace min, munfi awa guda kuma batayi min magana ba, saida taji ina ajiyar zuciya sannan tace.
“Yau ɗaya danaji muryanki cikin kuka, toh ki maida kukanki nafili zuwa kukan zuci karki kuma bari kukanki yafito. Kiyi hakuri dan ko kin faɗa min damuwarki toh ba makawa, hakuri zan baki da kuma nasiha, maryam kowani mutum da irin nashi kaddaran kowa hakuri yake da zaki tambayi Rahilah ko Rahimah miye matsalarsu zasu faɗa miki, dikda kulawar da suke samu bai hanasu shiga damuwa ba, Maryam kasancewarki mace matar aure bazai hanaki fuskantar kalubale ba, ina ga ko iya haka nabarki kin fahimci abinda xance miki shine hakuri idan shi kikawa laifi ko yayi miki kije ki bashi hakuri, idan kuma abokan zamankine ki basu hakuri yau kaine gobe bakai bane kiyi hakuri wata rana sai labari.”

Tana gama faɗar haka ta kashe wayar, kifa hannuna nayi saman goshina da yayi min nauyi, tunda muke wayar naji kamshinsa amma ban damu da na katse wayar ba,

Duk yana jin abinda umma tace min, dan haka ya shigo ya ɗauki wayar zai fita a hankali nace.
“Kayi hakuri ban sakewa.”

Murmushin gefen baki yayi sannan yafita.

***
Akala wata biyu kenan zaman gidan Yunus na shirin fin karfina, ana cikin haka hidimar sallah laya tazo, ana sallar saura kwana biyu Huda tazo da farin cikina nake ganin karewar wasu matsalar, ashe wutar matsalace zata kuno min, dan tsakanin ɗa da Mahaifi sai Allah tunda Uwarta ta kitsan mata magana a ɗaki shi knn ta daina shiga damuwata, ga Aneesah da kullum sai taci min mutunci. Karshe ta haɗa ni dashi ya ci min mutunci sosai.

Abubuwa sun min yawa, dakyar wata labara ya barni zuwa gida, cike da farin ciki na haɗa kayana tsaf na bar gidan, sai gidan Aunty Shema’u.

Tun da ta ga yanda nazo tasan ba lafiya, dake anyi salla ganin yanda nake zare ido yasa ta tirkeni da tambaya mi ya kawo ni.
Sunkuyar da kaina nayi kwalla na zuba daga idanuna nace.
“Aunty nagaji da zaman aurene.”
Sallamar matar abokin mijinta yasata amsawa tare da juyawa ta kalli kofar falon da bakuwar zata shigo.
Da fara a matar tashigo ta nime guri ta xauna, gaisawa sukayi sannan nima na gaisheta,

Dawo da hankalinta kaina Aunty Shema’u tayi tace.
“Auta mikika ce.”
Ta zuba min ido, rike bakina nayi nasake mai maita mata, abinda nace.
“Bata bincike ni ba, ta shiga min faɗa min faɗa, ainu ita da bakuwarta. Ka basu ji ta bakina ba suka min tass, da yamma tayi suka sauke ni a gidan. Ji nake kamar na gudu nabar gidan duk na kare nafita hayacina. Haka kwanaki suke tafiya cike da abubuwan al’ajabi.

Tunda suka ga sun kasara tsakaninmu sai kowacce ta fecce ta cigaba da uzurin gabanta, dama da suka nemi shiga tsakaninmu haɗe kansu sukayi inda suka amshi dutyn su gurin kulawa dashi, bashi duk wani hakkinshi da duk wani abinda zan mishi, suka ɗauka.
Girki kuwa nice keyi duk gidan a kullum zanyi sau biyar a safiya, wai takaitawa nayi, dan kowcce da abinda take so. Gana yaransu daga falon sama zan fara shara har falon kasa, ɗakinshi kuwa shida kanshi ya haramta min shiga cikinta.

……Ada nake kallon matsalar gidan labcecciyar amma a yanzun bana damuwa da kowa, na tara kowa na zuba a gefe, har shima na tarashi a wani gefe guda.
Kimanin wata huɗu kenan ina cikin damuwa, Allah cikin ikonshi ya sauki rahilah lafiya, inda ta haifi ɗan namiji.
Anyi haihuwar kwana huɗu, sannan nasami labarin haihuwar dan yasani sai da yakai duk matanshi suka ga baby,
Ina zaune a gurin cin abinci suka shigo, suna raha.
“Ai Maman Huda nayi mamakin yanda matar Aman ɗin nan ta haifi katon yaro haka, koda yake bazanyi mamaki ba, tunda ai mace ce zata iya ko muma ta gidan nan da tasami Mai nasara ai itama haihuwar zatayi.”

Shiru nayi ina shan fruit, nan suka juya suna kallona tare da fashewa da dariya. Toh ya zanyi tunda ya kwace wayar, haka sukayita hiransu,

…..
A can kuwa kowa mamakin rashin zuwa na yayi tun Umma na kawaici har ta kalli Ahmad tace.
“Ahmad wai Maryam bazata zo bane, yau kwana huɗu muna asibiti dan ma Haihuwar tazo da matsala, da lafiya ta haihu ai sai dai kowa yaje ya dubasu a gidansu.”

“Kiyi hakuri Umma zan duba shi, tunda naga ya kawo sauran tayu ita ya kawota daga baya.” ya faɗa mata,

Koda yasami Mai nasara da maganar biris yayi bai kaini ba, har ana gobe suna sai ga Mamie.
Sun sani a gaba shida matanshi suna tsigeni,dan nayi musu abinci gishiri yayi yawa, ina durkushe sai kuka nake.
Ta danno kai da sallamah, basuji ba dan zuciyarsu ya raja’a da mugun nufi,
Yana zaune matan sun zageye ni kowacce da abinda take faɗa, Mamie tashigo gidan, tsayawa tayi a bakin kofa tace.
“Sannunku da kokari”
D’ago kai nayi na kalleta bansan lokacinda kukana ya kwace ba, mikewa nayi tace.
“Koma ki zauna.”
Komawa nayi muryana na tashi a falon, cikin ko in kula ta kalleshi da ya sauka akan kujeran yana gaida ita, dakatar dashi tayi sannan tace.
“Ai nasan haka kawai Maryam bazataki zuwa duba Rahilah da ɗanta ba,sai sa dalili da Ahmad yayi maka magana kayi shiru ashe kana azbtarmu da Y’a ce,,ba zan faɗawa Iyayenta abinda kayi mata ba, dan nasan bazasu iya hukuntaka ba, sai dai ka kiyayyi ranar da zata kwaɓe maka, da iyayenka da iyayenra zaka nemi damar sulhu bazaka samu ba, domin duk wanda aka gina mishi zuciya da kuntatawa toh tabbas yafi kowa fusata, Sajida jeki ɗsuko kayanki da zakiyi amfani dashi gobe suna.”

Kallonshi nayi a hankali, na girgiza kai nace.
“Mamie bani da lafiya, ki bata hakuri zanzo bayan suna.” Wani irin kallo tayi mishi me cike da tsantsar ɓacin rai tace.
“Allah ya kara miki hakuri.”

Tana faɗar haka tafita, mikewa nayi na koma ɗakina, na zauna ina kuka, ga koshi ga kwanar yunwa.

Shigowa yayi ya buɗe wardrob ɗina ya shiga ciro min kayan da zansaka. Duk sun min yawa, ina kawa zasu nemi faɗuwa. Dalilin ramar da nayi yasa shi kin kaini, kallona yayi bayan ya ciro wani doguwar riga ya mika min yace.
“Idan muka je kowa ya tambayeki mi yasameki kice baki da lafiya ne idan naji wata magana bayan haka zaki gamu da ɓacin raina”

Shiru nayi bance komi ba, ya ajiye min kayan kallonshi nayi cikin sanyin murya nace.
“Wallahi babu inda zani, kawai kaje bana son magana, ai na faɗawa Mamie bazanzo ba.”

“Kina hauka ne ina magana kina cewa bazaki ba tashi.” ya daka min tsawa, sam banji komi ba nace.
“Na rantse da Allah wanda rayuwata da mutuwata take hannunshi baxan je ba, kawai karabu dani, idan kuma ka matsa na fita toh bazan dawo ba na tafi kenan, dan zan faɗawa Iyayena bazan dawo gidanka ba.”

 

Back to top button