Yar Zaman Wanka 49-50
4️⃣9️⃣➡️5️⃣0️⃣
*LAST PAGE*
Barkanmu da kasancewa a ckn watan rahma watan ibadah RAMADAN MUBARAK
*RANAR SUNA*
Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, Tasalla dai yau yadda ta ga rana haka ta ga dare, dan gabaɗaya bacci ya kasa zuwar mata, tsaf ta nemesa ta rasa bacci ya ƙauracewa idanunta sai zumuɗi take d murnar a kan gari ya yi ya waye su ɗauki hanyar birni, tun kiran sallar farko ta tashi ta yi alwala ta zauna tana lazimi, ita kana murmushi sai ƙwace mata yake ita kaɗai ta san irin daɗin da take ji da irin farincikin da take ciki.
“Kai Allah da ikonsa komai sai Allah ya nufa shi yasa wasu ke cewa kishiya in alkairi ce Allah tabbatar da alkairi to ni dai gashi kishiya ta wani wajen ta zame mini alkairi tun da gashi sanadin kishiya (Buk ɗina, labarin yadda sanadin kishiya ta haɗu da ƙalubale gidan aurenta tun daga ranar da ta sanya ƙafarta a gidan aure ta fara arba da bala’i kala-kala har makancewa sai da ta yi sanadin kishiya) Duk da dai ta wani wajen Azumi ba kanwar lasa bace amma dai yau ta mini rana har da yammaci ma” Cewar Tasalla da ta tashi daga kan abin sallah tana linkewa da hijabinta.
Babu ɓata lokaci ta shiga wanka ta fito ta shiga shiryawa cikin atamfarta mai kyau, tana cikin sanya kwalli sai ga Malam ya shigo ɗakin nata daga masallaci yake, ganinta zaune da ƙaramin madubi a hannu tana gwale ido yake kallonta da mamaki, washe haƙora ta yi tana kallon Malam da ke mata kallon mamaki.
“Malam har an dawo daga masallacin”
“Eh na dawo” Ya faɗa yana kallon wani jambaki sabo da ta fito dashi daga wata baƙar leda ta daddage za ta shafa.
“Tasalla menene hakan kike yi dan Allah” Cewar Malam yana kallonta.
“Wai a ina ?” Ta faɗa tana kallonsa.
“Wannan ba gazar bane da yara ke sanyawa?”
“Au wai wannan? Ba gazar bane Malam jambaki ake ce masa fa”
“Ko ma dai menene, ba dai sawa za ki yi ba”
“Shafawa zan yi mana Malam, saƙo na yi kasuwa aka siyo mini saboda na shafa, ko so kake in tafi birni suna dangin kishiya ake nuna ni da baki ana gulmata ko kwalliya ban iya ba bare kuma dama Azumi da ke min kallon ban taɓa zuwa birni ba ta faɗa musu cewa babu abin da ma iya wallahi ba zan juri baƙinciki ba gwara dai na cancaɗa adona da kwalliya yadda babu mai mini kallon raini alqur’an”
Ta faɗa tana wani shafa jambakin tare da haɗe laɓɓanta waje ɗaya ta daidaita jambakin.
“Ni na ga ikon Allah saboda zuwa birnin ne za ki shafa gazar da girmanki da komai tsofe-tsofe da ke saboda gudun magana za ki shafa, kuma ma da kike cewa Azumi za ta faɗa musu magana a kan ki bake kika ce mini ita ta gayyaceki ba, kin ga Tasalla wallahi bana son tashin hankali kar fa ku je cikin mutane kuke raba jaha ke da ita ij kin san da matsala kamar kullum kawai ki yi zamanki dan ni ba na son haɗin gurugudu”
Wani uban bugawa ƙirjin Tasalla ya yi da ƙarfi jin Malam zai shiga tsakaninta da burinta na zuwa birni, sai yanzu ta gane ɓaran ɓaramar da ta yi na cewa Azumi za ta faɗi magana a kan ta ai da sauri ta washe bakin nan na tsohuwa da ya sha jambaki ta ce.
‘Allah sarki Malam ni fa ba haka nake nufi ba ka dan san mu mata ba ma rabuwa da gutsuri tsoma dole dai idan aka haɗu a gidan suna ko biki sai an yi da mutum tun daga suturar da ya saka zuwa kwalliyar da ya yi kai hatta tafiyar mace ma sai an saka ido musamman kuma aka ce maka kishiya ce ya je dangin kishiyarta to qur’ani hatta ƙasan zanen da ta saka sai an duba an ga wace irin atamfa ce ko leshi shi yasa ka ga na faɗi hakan, kuma jambaki da na shafa ai ba haramun bane ko Malam, in kuma kana ganin na goge sai na goge, dama na siya ne dan kar a kawo maka raini”
“A kawo mini raini?”
“Eh mana wallahi idan ban gyara jikina ba na fito fes muna zuwa za a ke cewa baka adalci a tsakanin matanka banbanci kake nunawa a tsakaninmu wata tafi wata a wurinka” Ta faɗa cikin sanyin murya tana wani karkata kai kamar ƙadangaruwa ita a dole kissa.
“Kuma fa haka ne da gaskiyarki to in kwa haka ne ki gyara abinki fes ki fito ɗoɗar da ke” Cewar Malam yana washe baki dan yadda Tasalla ta yi magana da kissa sai ya ganta kamar Azumi dan ita ce mai irin wannan yanzu za ta sanya shi yin abin da bai yi niyya ba.
“Ka ce fa ai dama na ce bari in gwada yadda Azumi ke yi, dan ko ranar da za ta tafi birni ZAMAN WANKA haka ta shaƙe murya ta rinƙa karairaye murya har sai da ka barta ta tafi, shi yasa na ce ni ma yau dai bari na gwada sa’a ta” Ta faɗa a zuciyarta tana wani jin ita ma yau ita ce.
” Aikuwa zan gyara ɗin dan ba na so a yiwa Malam ɗina kallon marar adalci a tsakanin iyalansa” Ta faɗa tana rufe fuska da tafin hannunta, alamar kunya wai ta ce Malam ɗinta. Shi kuma wani irin murmushi ne da dariya suka haɗe masa lokaci guda yana jin wani kansa na neman fashewa.
“Wayyo daɗi kasheni wahala ta huta, ashe dai ni ma da saurana a fannin soyayya ashe dai matata bata ganin tsufana take ce min Malam ɗinta duk da dama masana fannin so sun ce soyayya bata tsufa sai dai masu yinta su tsofe” Cewar Malam a zuciyarsa yana jin zuciyarsa fes.
Haka dai ta cigaba da shirinta ta shirya tsaf ta shafa turare ta ajiye bokitin da ta zuba fura a ciki da galan ɗin nonon da za ta kai gidan sunan. Tana gamawa lokacin Malam ya shiga ɗakinsa ta fito ta galgala wuta ta ɗora ɗumamen tuwo, tana ɗorawa kuwa ta barshi kafin ya yi zafi ta tafi gidan Tsahare tun daga nesa ta fara hango Tsahare tana haɗa kan ita ce a murhu ko wanka bata yi ba wani takaici ne ya cikata tana ji a ranta dama da a ce ta san birnij nan da tafiyarta za ta yi in ya so ita Tsaharen ta taho daga baya, dan ta ga aminiyarta ce Azumin shi yasa take mata wani jan aji.
Da sallama ta ƙaraso a bakinta kana kallon fuskarta za ka fahimci cewa ranta a ɓace yake. Amsa mata sallamar Tsahare ta yi ta ɗago daga sunkuyen da take tana ƙarewa Tasalla kalko. Babu inda ya ɗauki hankalinta haɗe da bata mamaki irin bakin Tasalla da ya sha jambaki gashi ta zana jagira da kwalli sai ka ce wata ƙaramar yarinya.
“Haba Tsahare wai ma baki shirya ba kuma na ga kina ƙoƙarin haɗa wuta ga wani ƙullin ƙosai a gefe in ce dai wata za ki barwa ta soya miki” Tasalla ta katsewa Tsahare tunanin mamakin da take na mai ya kai jambaki bakin Tasalla har da su jagira da girmanta da komai.
“Wai kamar ya wace irin magana kike haka, kawai dan zan tafi suna sai in kasa yin sana’ata shin kin manta ba a ƙafa za mu je ba kuɗin mota za mu biya daga nan ma zuwa tasha sai mun biya kuɗin machine, a can ma in an sauke mu sai mun hau adaidaita sahu, ga kuɗin gudunmuwa mutum ba ya je baƙiƙƙirin ba” Ta faɗa tana kallon ƙafar Tasalla da ta sha wani uban vasiline sanye da takalmi ɗan madina kore.
“Haba Tsahare yanzu dan wannan ne zaki yi sana’a yau so kike sai shinkafar da za a dafa ta suna ta ƙare bamu je ba gaskiya dai baki kyauta ba”
“Dan Allah ki rabu dani da wani zancen shinkafa yunwa za mu je, da za a ke tunanin shinkafar rabo, duk wannan abin da kike fa har yanzu a ƙarfe bakwai saura ake dan Allah ki koma gida duka ƙullin ma na kwano guda ne yanxu zan gama kinsan dai na kwano uku da rabi nake yi kullum”
“To ai shikenan ya na iya da abin da ya fi ƙarfina ni da ko hanyar ban sani ba ai dole na jira ki” Cewar Tasalla tana taɓe baki ta juya ta tafi.
Da kallo kawai Tsahare ta bi bayanta tana mamakin irin kwalliyar yaran da ta yi a fuskarta, gashi har yanxu ta kasa daina mamakin wai Azumi ce ya gayyaci Tasalla suna, dan ta san dai basa ga miciji da juna.
Sai wajen ƙarfe tara suka baro ƙauyen, zuwa lokacin sawun Tasalla ya fi biyar gidan Tsahare a kan ta yi ta shirya su tafi ƙarshe dai sai da suka yi faɗa a haka dai suka samu mashinan da suka kai su Garki L.G inda suka samu motar Kano suka hau. Tun da aka fara tafiya bakin Tasalla bai rufu ba ta ce wannan ta ce wancan tun Tsahare na biya ta har ta gaji ta yi shiru dan ta ga abin nata ba na ƙare bane, kuma kamar ma duk murna da zazzaɗin zuwa birnin ne ya sanya bakinta ya ƙi rufuwa. Tun da motar ta shigo garin Kano ta dabo tunbin giwa sai kuma gabaɗaya Tasalla ta ruɗe bakinta ko rufuwa ba ya yi ta sake shi galala saboda kallon motoci da kuma gine-gine kai ba ma su kaɗai ba hatta mutanen da ta gani masu yawa kowa yana harkar gabansa suj zame mata TV saboda ita bata taɓa zuwa gari kamar Kano ba iyakacinta ƙauyukan wajejensu kawai.
Tsahare da ta ɗauke kanta ta mayar gefe daga kallon Tasalla saboda nune -nune abubuwa da ta dame ta da su, ta ji Tasalla ta saki kuka cikin sauri ta waiwayo wajenta take tambayarta dalili dan har lokacin fa basu sauka daga mota ba kawai dai sun shigo garin Kano ne, motar tana tafiya zuwa tasha ne dan ta sauke lodi.
“Dole na yi kuka Tsahare wallahi dole na yi kuka, kawai ki barni kar ma ki baiwa kan ki wahala wajen lallashina dan ba shiru ba zan yi sai na yi mai isata na ji zuciyata ta yi sanyi”
“To ikon Allah” Cewar wasu daga cikin motar da suka haɗa baki wajen faɗa.
“Haba ke kuwa baiwar Allah ana zaune ƙalaw muna murna Allah ya kawo mu lafiya saura mu sauka, kawai za ki fashe da kuka kuma ki ce wai ba za ki saurara ba sai ka ce wata ƙaramar yarinya, kuma mu babu wanda ya ga kin ɗaga waya bare a ce ko mutuwa aka faɗa miki” Cewar wani mutum da ke gefe.
“Wallahi bawan Allah ba mutuwa aka faɗa mini ba, kawai takaici ne na abin da ka mini, ni nan da kake gani ina da shanaye da dabobi da nake kiwo ina dai da abin hannuna amma a ce a duniya akwai gari ya Kano amma ban taɓa zuwa ba? Kuma ko bani da kowa a Kano wallahi da na san haka take da ko iya tasha ne na biya kuɗi na zo na ga gari na koma amma aka barni a can ƙauye a garƙame, kuma dan baƙin hali irin na kishiyata, bata taɓa gayyata ta garin nan ba wajen ƴan uwanta ai ko, dan na kashe ƙwarƙwatar idona a faɗa min Kano haka take”
Gabaɗaya motar dariya aka kwashe da ita kowa yana jin abin da Tasalla ke faɗa sai ya yi dariya, abin nasu sai ya sosa mata rai dan haka ta ɗauke kan ta gefe ta cigaba da baiwa idonta nama. Kowa ya fita daga motar Tasalla kuwa tun da ta fito sai idanunta suka kasa samun matsaya ta kalli can ta kalli nan, da yake bakin titi aka sauke su a tashar ba a shiga cikin tasha ba. Sosai Tsahare ta yi da na sanin zuwa da Tasalla saboda babu abin d take sai kalle-kalle, a haka dai ta samu dakyar ta tsayar musu da ɗan sahu suka shiga suka nufi gidan suna murna fal cikin Tasalla dan har lokacin ma a ɗan sahun kalle-kalle take.
“Taɓɗi shi yasa ashe ake cewa hankali shi ne gani wai wani ya je Kano bai ga mota ba, yo in ba haka irin motocin nan na garin Kano kwantsam kamar jamfa a jos duk da ban taɓa zuwa Jos ɗin ba, amma gaskiya yawan motocin Kano ya ɓaci yadda ka san ba mutane kaɗai ke hawa motocin ba har da aljannu” Cewar Tasalla da ke ta kalle -kalle. Daga Tsahare har ɗan sahun babu wanda ya tanka mata a haka suka cigaba da tafiya.
A daidai ƙofar gidan aka sauke su, suna sauka sai Tsahare t tsaya tana baiwa ɗan sahun kuɗinsa, Tasalla kwa dama ta biya shi, dan haka sai ta ɗan tsaya daga gefe take jiranta kusa da wasu mata guda biyu da ke ƙusƙus.
“Wallahi fa nake faɗa miki miciji sak Hassan ɗin ke zama ya yi ta firgita mutane, in kika ji irin uƙubar da mutanen gidan ke fuskanta za ki yi mamaki” Cewar ɗaya daga cikin matan da ke tsaye gefe, Tasalla da ke saurarensu cikinta ne ya bada wani ƙululuuuu ta fara zare ido a take ta ji gabaɗaya Kanon ma ta ginsheta ji take kamar ma kar ta shiga gidan.
“Ikon Allah shi kuma irin tashi baiwar kenan, to gaskiya dole mutane suke tsorata yo ina kai ina miciji”
“Himm ke dai bari kuma fa a haka suke kwana da shi ɗaki ɗaya har kakar mai jego kin jo sunanta Inna Azumi”
Ai sunan Azumi da aka ambata shi ya ƙara tabbatarwa Tasalla da jariran ƴan biyun da suka zo sunan ake.
“Mu je mana ga gidan fa kina gani mutane sai shige da fita suke ni wallahi na ƙosa na sanya amini a idanuna ” Cewar Tsahare tana kallon Tasalla da gabaɗaya jikinta ya yi sanyi ƙalaw kamar dai ba ita ce ta ishi mutane da surutu ba ɗazu.
“Kai ai ni unguwar ce duk sai na ji kaina yaba juyawa da alama mutanen ɓoye na ne ke son tashi shi yasa, idan kika sa ni a ɗan sahu za su maida ni tashar mota in koma gida” Cewar Tasalla dan duk son da take yiwa birni gabaɗaya ya fice mata a rai dan gabaɗaya hanjin cikinta ya hautsina.
“Ki koma gida kuma garin yaya wato sai da kika zo har ƙofar gida sannan tsoron mai zai je ya dawo ya zo miki, ai ni dama na san babu yadda za a yi Azumi ta ce ki zo sunan nan” Cewar Tsahare tana yiwa Tasalla wani kallo.
“Eh bata gayyace ni ba da Allah yi maza ki sama mini ɗan sahu ya maidani tasha” Cewar Tasalla dan gwara Tsahare ta ce mata komai a kan ta shiga gidan da miciji yake.
“Ai fa tun da kin riga kin zo to komai ta famjama fanjam jam” Cewar Tsahare tana kaɗa kan Tasalla suka tasarma cikin gidan.
*INNA*
Tun sanda ta fara nafilfilin nan ko hutawa bata yi haka take bari sai ta yi raka’a huɗu sannan ta sallame ta rinƙa jero addu’oi ta rinƙa kuka hawaye na zuba tana ta neman yafiyar ubangiji.
Haƙiƙa Inna tana cikin tashin hankali domin ba ƙaramin abu bane a ce ka san ranar mutuwarka duk da zai kasance za kake neman yafiya kafin lokacin amma tabbas za ka shiga tashin hankali, shi yasa yana daga cikin hikima ta ubangiji da ya ɓoyewa bayinsa sanin ranar mutuwarsu, da a ce kowa ya san ranar da wa’adinsa zai cika tabbas zai cigaba da rayuwa a cikin tashin hankali to wannan halin shi Inna ta shiga. Tana jin sanda Sadiya ta tashi tana shayar da yaranta da suka tashi amma ko ɗaga kai bata yi ta kalleta ba. Har sai da aka kira sallar asuba tana nan tana ibada amma kuma ko alamar bacci babu a idanunta dan gani take ita da ke shirin barin duniyar ma baki ɗaya to bata da wani lokacin jin daɗi a cikinta.
Haka ta tashi ta je ta tsaya a kan Imran tana kiran sunansa, ya tashi ya tafi masallaci Imran kuwa dama shi ma bai koma bacci ba dan gabaɗaya sai ya ji tausayin Inna har ma yana da na sanin mata abin da ya mata, dan tun lokacin da ya kama hannunta irin yadda ya ga ta rikice da kuma bayyanar tashin hankali a tare da ita shi yasa ma ya yi saurin cewa sai nan d sati biyu amma da niyyarsa sai ya dinga ja mata rai yadda za ta tsure sosai amma ganin ta tsorata sosai shi yasa ma ya ƙyaleta. Kuma yanzu yana tsoron ya fito ya faɗa mata gaskiya ido ya kuye da mujiya dan ya san Inna ba kanwar lasa bace dole za ta yi shirin ɗaukan fansa dan haka sai ya bar maganar a zuciyarsa yana fatan Allah sa ta saki ranta ta yi rayuwa cikin salama a kwanaki sha huɗun da yace za ta mutu duk da ya san da kamar wuya gurguwa da auren nesa amma yana fatan hakan.
Tana kiran sunansa sai alerm ɗin wayarsa ya shiga ƙara dan haka sai ya yi kamar ƙaran wayar ne ya tashe sa.
“Inna har kin tashi ke ma” Ya faɗa cikin sanyin murya dan duk da a gabansa take tana kiran sunansa amma in ta kirashi sau ɗaya sai ta ja carbin da ke hannunta bakinta ya motsa sannan za ta ƙara kiran nasa abin ya so bashi dariya sosai amma sai ya ji tausayin ya danne dariyar.
“Kayya Imirana ni dama ina nan ido biyu ai ban ko yi gyangyaɗi ba”
“Allah sarki Inna ki ce dai yau duk mun sha addu’a mun more?” Ya faɗa dan ya ɗan jata da hira ta saki ranta ko yaya ne dan ya ji daɗi dan yana ganin ya tauyeta, saboda ita duk abin da take masa na iya duniya ne ma’ana bata masa abin da zai nuna barinsa duniya ba duk da miciji ma abin halakarwa ne amma ya san daga an raba shi dashi to zai daina jin tsoro ita kuma y mat abin da a ko yaushe za ta kasance cikin tsoro mai tsanani.
“An muku kam ba laifi, fa kaina kaɗai name yiwa amma daga baya sai nake yi da sauran al’umma ma dan addu’ar da ka yi a jama’i tafi saurin karɓuwa a kan wacce ka yiwa kan ka kai kaɗai”
“Allah sarki Inna mun gode, bari na yi sallah a je a shigo da abin yanka na suna wanda tun ranar da kika zo kikr yi da bakin ki cewa ba a kawo ba” Cewar Imran lokacin da ya tashi yana ƴar dariya duk dan ya sanya Inna farinciki.
“To Imirana” Cewar Inna cikin halin ko in kula ɗin nan. Haka ta shige ɗaki ta barshi dan bata so ta yawaita magana lokacinta ya tafi a banza ba tare da ta yi istigfari ba.
Haka dai Imran ya yi shirin zuwa masallacin zuciyarsa duk ba daɗi bai taɓa jin ya yi da na sani ba a kan abin da yake yiwa Inna sai yau, duk da a da ya ɗauka cewa duk abin da ta masa sai ya rama har ma yana ikirarin ramuwar gayya ai tafi ta gayya zafi, amma kuma yau ya ji ba daɗi sosai. Yana dawo wa daga masallaci ya samu suna ɗan zantawa da Sadiya amma har lokacin carbinta yana hannunta, haka Inna ta fito dan ɗora ruwan wanka a lokacin ne kuma Imran ya ɗauki kayan nan da ya yi amfani da su ya ɓoye a drowersa kafin gari ya waye ya fice d su dga gidan.
“Wai ni Inna dama kin san bakya iya kwanciya da ƙunshi kika yi kika kwanta, kalli yadda kika ɓata ƙafarki ai dama baki yi ba da dai wannan caɓe ƙafar da kika yi, kuma gashi ya kama sosai sai dai gabaɗaya kin caɓe shi” Cewar Sadiya da za ta tafi ta shiga wanka tana kallon Inna da ke ajiye ruwan wankan za ta fara yiwa yaran wanka. Kallon ƙafar kawai Inna ta yi ta sauke wata ajiyar zuciya tana rayawa a ranta cewa ƙafar da saura kwana sha uku a binne ta a cikin ƙasa menene ma na damuwa da caɓewar kunshi. Sadiya jin Inna bata, bata amsa ba sai kawai ta kaɗa kanta ta fita dan ta lura Inna shiru ya fiye mata yau ko magana bata so ga babu walwala a tare da ita bare ma ita da ke murna aminiyarta za ta zo yau amma sai ta ga yau ko murna fa maganar Tsaharen ma bata yi kawai ko yaushe bakin motsi yake alamar tana karanta wani abu ta kasa gane dalilin yin hakan. Ta san halin Inna dai bakinta baya shiru baya rabuwa d abin faɗa amma kuma yau sai ta ga Innar ta canja mata.
Bayan Sadiya ta yi wankanta shirya abinta tsaf lokacin har Mama da Ashrof sun zo ga kuma ƴan uwan Mama duk sun fara zuwa haka zalika Hajiya ma da maƙotanta da wasu dga cikin danginta sun iso gidan dai sai san barka amma gida ya fara cika, kuma sai maganar miciji ta kwanta kamar ma babu ita dan kowa sai sabgar gabansa yake. Ashrof da Mama da Hajiya kai da duk wani wanda ya san Inna kawai mamakin ta yake yau dan akwai wasu daga cikin matan nan da suka zo ranar da aka musu ƙunshi ƴan uwan su Imran amma ganin Inna shiru yau su ma sun fahimci akwai damuwa a tare da ita kowa sai ya tambaya ko lafiya sai ta ce lafiya lau wasu dai sun danganta hakan da cewa ko wani abu ke damunta kuma bata so ta faɗa. Dan dakyar ma ta yi wanka ko shi ma sai da Sadiya ta matsa mata, ko da ta fito babu abin da ta shafa kawai atamfarta ta ɗauka ta sanya ta ɗaura ɗankwali ta ɗauki carbinta ta zauna a kan kujera take lazimi tana kallon shige da ficen mutane ana ta hada hadar yin abubuwan suna. Dan ko lokacin da aka shigo da raguna manya -manya guda biyu da tinkiyoyi su ma manya guda biyu Inna tana gani aka shigo da su, jim kaɗan aka fita da su aka dawo da su a yanke aka rataye amma ko ci kan ka inna bata ce ba. Imran ma lemuka katan uku ya siyo mata da cake irin mai biyun nan ƙanana guda hamsin dan ta yi farinciki ya ce ga kashinya ta rabawa wanda take so amma haka ta karɓa ta yi godiya da fatan alkairi ta ajiye amma ba wai dan ta ji abin ya birgeta ba sai dai kawai ita yanzu komai na duniyar ya fice a ranta tafi so kawai ta ganta a gidan mijinta hankalinta zai fi kwanciya.
Tana nan zaune kamar an ce ta ɗaga kai sai kawai ta hango aminiyarta Tsahare riƙe da kaya ta shigo, tabbas ta ji daɗi a ranta amma ba kamar yadda take zaton ji ba a baya.Kafin ta tantance sai kawai ta hango Tasalla da wani bokiti da galan da wata jakar kaya madaidaiciya a hannnunta. Ai Inna da ta wani ajiye carbi a gefe ta ji wani takaici ya turnuƙeta ai cikin hanzari ta tashi tsaye kafin ka ce kwabo ita ma bata tantance ba sai kawai ganinta ta yi a bakin ƙofa ta taho a fusace kamar kumurcin miciji.
“Yau ake yinta lallai Tasalla kin ga makwancina har ni za ki zo wa sunan jika ban gayyaceki ba? Ni saboda bana son ki raɓeni na fi so kullum hawainiyarki ta kiyayi rama ta shi yasa ko da bikin Halima ban gayyaceki ba amma shi ne yanzu saboda ƙoƙari faɗawa mijin baya tariya, kika ɗakko ƙafa kika zo, duk da cewa na san ruwa baya tsami banza, amma ki sani sara da sassaƙa bata hana gamji toho, kuma wallahi iya gani iya ƙyalewa, wannan abin da kika yi wayon a ci ne an kori kare daga gindin ɗinya, amma ki bar murna dan karenki zai kama zomo, amma duk da haka na san ba za a tambayi kalwa zaƙin miya ba sai dai a tambayi barkono a sha labari, tabbas yau allura za ta tono garma, domin kuwa ba wahalalle sai mai kwaɗayi, duk da kin cika burinki na zuwa birni dama hausawa sun ce buƙatar maje hajji sallah, amma yau zan nuna miki zafin nema baya kawo samu, kuma duk esnda ya ce wutar kara ta kwana tana ci, to tabbas bai yi bacci ba, Tasalla yau zan nuna miki wanda zai je sama ya taka leda to haƙiƙa ya ci ƙarfin tafiya!!!” Cewar Inna a zuciyarta lokacin da ta taho a fusace gadan -gadan ta iyo wajen Tasalla.Tasalla wacce dama gabaɗaya zuwa birni take da na sani duk da cewa da na sani ƙeya ce amma kuma ita babban tashin hankalinta micijin da aka ce akwai a cikin gidan wanda ta ji labari cewar ɗaya daga cikin tagwayen ne yake komawa, ga kuma hango Inna ta taso kamar wata kububuwa ya ƙara tada mata hankali wato dai bokitin furarta da galan ɗin nono da take sa rai za su kankaro mata mutunci a wajen kishiyarta ta ba haka bane dan kwata-kwata bata ga kyan wuri a kunnen jaka ba, shikenan yanzu Azumi za ta kunyata ta a cikin jama’a duk da ta wani ɓangaren tana jin ƙwara dai ta kwaɓe tsakaninta da Azumin ko ta samu damar barin gidan dan ta san dai in suka kwashi ƴan kallo to tabbas ko dan neman masalaha a ce ta koma inda ta fito, ita ma Tsaharen za ta bata goyon bayan hakan wanda ta ƙi bata a ƙofar gida dan da ta barta ma da tuni ta kai tasha ko da kuwa a ƙafa ne dan sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba, duk da ta san ba lallai ta iya zuwa ba sai dai za ta yi tambaya dan matambayi baya ɓata.
Tsahare ma ganin aminiyarta ta, ra doso su sai jikinta ya bata yau za a cancanre dan dama ta san da walakin goro a miya,dan ta san ko menene tsakanin Azumi da Tasalla to shigo-shigo ba zurfi ne, dan komai za a yi sai dai ya zamana bita da ƙulli ne dukan kabarin kishiya, dan dama ita ta san za a rina wai an saci zanen mahaukaciya. Inna kuwa da sai da ta zo dab da su sai zancen mala’ikan mutuwa ya faɗo mata na saura sati biyu ta mutu kuma dai yau ma tun da gari ya waye har ta ci kwana ɗayanta, saura sha uku, dan ita lokacin da ta hango Tasalla gabaɗaya sai ta ji wani kishi ya turnuƙeta a take ta sha’afa da halin da take ciki dan bata ma san lokacin data ajiye carbinta ba kawai dai ta ganta ta tunkaresu cikin zafin nama, amma tuno da mala’ikan mutuwa da kuma cewar in ma kishi take to wanda take kishin za ta mutu ta barshi da kishiyarta ta, ita tata ta kusa ƙarewa to ma menene na ɗaukan duniya da faɗi ita da za ta barta ma nan da kwana kaɗan.
Wani uban washe baki Inna ta yi na ƙarfin hali dan ita yanzu in ba larura ba bata ƙaunar ma a ga haƙorinta saboda ai wanda ke cikin farinciki shi ne zai yi dariya, amma kuma yanxu ya zama dole ta saki fuska da jama’a har ma da Tasalla dan an ce shimfiɗar fuska tafi ta tabarma kuma ta haka ne mutane za su yafe mata da mata addu’a in sun samu labarin mutuwarta, kuma wannan dama ce da za ta yi amfani da ita wajen gyara ma’amalarta da kishiyarta, wanda dama ya dace tun a baya hakan ya kasance dan ko da a ce mutum bai san ranar mutuwarsa ba to fa ya sani tabbas wannan ranar akwai lokacin da za ta zo ko ba daɗe ko ba jima sai kowa ya kwanta dama dan haka yana da kyau ka mu’amalanci mutane da mu’amala mai kyau, dan shaidar mutane ita ce ta ƙiyama, iya yabon da za a yiwa kyawawan halayenka iya yadda mutane suka ji daɗin mu’amalantarsu da ka yi ne, dan haka kyakkyawar mu’a mala tana da kyau.
“Gasu, gasu, sannunku da zuwa mutanen arziƙi sannunku da ɗabbaƙa zumunci ” Cewar Inna tana ƙarasowa wajensu fuska a sake take kallon Tasalla da Tsahare. Ba Tasalla ba hatta Tsahare ta yi mamakin wannan tarɓar da Inna ta yi, kuma ta kasa gane dalilin yin hakan dan ta ga a yadda ta zo amma bata san ya ka yi ido ya juye da mujiya ba, dan ta saa halin aminiyarta Azumi babu tsoro kuma ba munafurci dan ta san Azumi dai bata san cewa wai dan tana ganin mutane ta ɓoye abin da ke ranta ba ita haka take fitowa ta nuna gaskiyarta, ita dama ƴar gaskiya ce. Tasalla mutuwar tsaye ta yi ganin Azumi ta sauya daga yadda ta nufo su da farko, sai gabaɗaya ta yi fosta mamaki al’ajabi suka dirar mata lokaci guda dan ita da a ce an wulaƙanta ta a bainar jama’a gwara ta bari in ta koma gida bayan ta gama ZAMAN WANKAN ta mata duk abin da za ta mata, sannan si ta ji daɗi da kuma buri d lafahrin yadda kishiyarta ta ta tarɓeta sai kawai ta ji babu abin da ya fi zaman lafiya daɗi, da a ce haka suke zaune tun farko da tuni ta yi zuwa Kano ba adadi dan da Azumi za ta gayyaceta wurin danginta in suna zama lafiya, kuma ko da a ce bata gayyaceta sunan nan ba sa zaman lafiya suke ba za ta ji ɗar ko shayin zuwa ba. A take ita ma Tasalla ta saki murmushi tana kallon Inna Azumi ai gabaɗaya sai suka zame wa Tsahare TV ta kalli wannan ta kalli wannan.
“Ke kallon ya isa haka” Cewar Inna cikin zolaya tana kallon Tsahare da ta saki murmushin jin daɗi lokaci guda dan ita ma ta ji daɗin yadda aminiyarta ta, ta tarɓesu.
Haka Inna ta shigar da su tana murna, dan ita ta karɓi bokitin furar gannun Tasalla ma, tana zolayar Tsahare wai ba za ta karɓi kayanta ba kayan ƴar uwarta Tasalla za ta karɓa. Haka sai ta musu masauki tare da gabatar musu da abin kaiwa baka. Nan Tasalla ta gabatarwa Inna nono da fura a matsayin abin da Malam ya ce a kawo ita kuma ta fito da riguna da dubu biyu ta bai wa Inna wai a baiwa mai jego, aikuwa Inna ta yi godiya sosai amma ta ce ba za a karɓi kuɗin ba dan wahalar ta isa ita kuma ta rantse a kan ba za ta karɓa ba tun da ta yi niyya kuma ba Innar ai ta baiwa ba jikarta da ƴaƴanta ta baiwa, sosai Inna ta ji daɗin kyautar da Tasalla ta yi, dama zuciya tana son mai kyautata mata, kuma sai Inna take cewa ashe haka zaman lafiya yake da daɗi. Tsahare ma turmin atamfa da riguna biyu ta kawo haka dai aka sha godiya da fatan ƙara samun danƙon zumunci.
Sai da Tasalla ta tafi yin alwala Inna da Tsahare suka samu keɓewa.
“Wai amini mai yake damunki ne, ke da kika zo birni dan ki murmure abinki sai kuma na zo na ganki duk a wani firgice?”
“Ke dai bari wallahi ZAMAN WANKAN nawa ne ya zo da wani salo”
“Kamar ya?”
“Yo Hassan ɗin ne miciji yake zama, tun da na zo a harƙalla ake dan wataran ma ina ake zama a ci abinci ana ta gudun famfalaƙi gugun ceton rai duk fa hankali ba a kwanceka yake ba, dan ma dai ina da ƙarfin hali ma da wallahi ba lallai ki same ni yadda kika ganni ba” Nan Inna ta shiga baiwa aminiyarta labari tun daga ranar farko da ta yi arangama da aljani har kawo yadda aka sha artabu da miciji da jama’a babu abin da ta rage mata amma dai bata faɗa mata labarin mala’ikan mutuwar da ya ziyarceta a daren jiya ba wanda shi ne silar dawowarta yadda ta ganta ba ta dai faɗa mata gabaɗaya hankalinta ya yi gida so take ta tafi in son samu ne gobe idan za su tafi ta bisu.
Sosai Tsahare ta sha dariyar artabun mutane da micijin da Inna ta bata musamman zuwan Malam mai sittin wata kan wata, da zuwan su Mama ranar da Imran ya sha yiwa Nigeri’a ranar da ya shiga tukunya kai ta sha dariya a wajen da Inna ta ce an rufe ta a freezer, da yadda suka yi artabu da ajani a bayi duk cikin labaran babu na yarwa dan dariya dai ta sha ta. Sai da ta tsagaita ta ce.
“Akwai dai wani abi da zai sa ki tafi dan na san miciji ba zai sa ki tafi ba da zai sa ki tafi da tuni kin bar gidan menene wannan wanda ya sanya har kika nunawa Tasalla ƙauna da kulawa haka? Lallai wannan ba ƙaramin abu bane”
Shiru Inna ta yi tana so ta faɗawa aminiyarta tana tsoron mala’ikan ya ce kar ta faɗa Haka dai ta ce mata babu komai.
Da yamma haka su Tsahare suka sauya kaya, dan gidan suna ya cika taf, yadda ba a yi zato ba dan duk an ɗauka ba za a zo ba saboda micijin to kuma cikin ikon Allah sai ma Hassan ɗin ya zauna a mutum bai zama miciji ba ranar sunan. Haka aka sha kiɗe kiɗe har da ƴan kiɗan ƙwarya, dakyar dai su Tasalla suka ja Inna wurin kiɗan ƙwarya ta ɗan taka rawa dan har da liƙi Imran da Abid da Sadiya da Ashrof suka mata sai dariya jama’a suke da yadda Inna take rawa da kuma yadda ake zuba mata kuɗi kowa yana murna dan gabaɗaya hankalin mutane sai ya dawo wurin kaɗan ƙwarya dan sosai Inna ke ba mutane dariya.
Haka dai taro ya watse kowa da kayan rabo masu yawa sai dai fatan Allah raya yara. Haka Imran ya koma gidan Hajiya ya kwana saboda baƙin Inna dan daɗi yake ji da ya ga ta ɗan saki jikinta ma.Haka suka yi hira sosai amma suna yin bacci Inna ta tashi ta kalli gabas haka ta kwana sallah da kazimi.
Washe gari haka aka yiwa su Tsahare sha tara ta arziƙi lemo Tasalla da Tsahare kowa katan Inna ta basu cake guda ashirin ashirin. Sannan ga wanda Sadiya ma ta basu sosai Inna ta so binsu amma Imran ya hanata dan yana so ta zauna a nan ita kuma ta zauna a nan dan yana ɗauke mata kewa haka dai ta zauna ba dan ranta ya so ba. Bayan suna da kwana biyu Imran da Abid suka zo da wani Malamin sunna ya shiga yiwa Hassan addu’a ya daɗe yana yi sannan aljanin ya bayyana kansa ya yi magana, a nan ya faɗi cewa tun lokacin da aka haifi yaran ya shigi Hassan, dan ko yadda bayan Hassan yake alamarsa ce ba wai a haka aka haifeshi ba duk da ana samun a haifi tagwaye da baiwar zama micijin amma shi na Hassan aljani ne. Haka aka fitar masa da shi sosai kowa ya yi farinciki da murnar hakan.
Inna dai ta ci gaba da rayuwarta wurin ƙanƙan da kai da komawa ibada da kasancewa da mahaliccinmu ko yaushe tana bauta masa, a haka ta cika kwana sha uku ana gobe kwananta sha huɗu za su cika sosai aka kasa gane kan Inna haka ta wuni kuka da neman yafiya kuma taƙu faɗar dalili, har Malam ma sai ta kira sau ba adadi tana neman yafiyarsa.
Ranar da kwanaki kuwa suka cika Inna bata magana sai ta bebaye dan kawai a sallaya take sai dai ta tashi ta sako alwala ta cigaba da sallarta. Kai har gari ya waye Inna bata mutu ba kwanaki sha huɗu sun cika har da kwana ɗaya amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa sosai Inna ta yi mmaki tana ta tunanin shin su ma mala’iku suna mantuwa ne? Ko kums yawan ibadarta ne ya sanya aka ƙara mata kwanaki, a haka dai ta ɗan saki jikinta amma kuma yawan ibada da lazimi ya gama shige mata jiki sun zame mata jiki duk da dama kasancewarta mau yawan ibada amma dai ta ƙara fiye da sanin mutum ga zuhudu (Gudun duniya) da ya ƙara shiga zuciyarta sosai. A haka ta yi kwana arba’in ɗinta ta haɗa kayanta ta je yiwa Hajiya da su Mama da Ashrof sallama suka haɗa mata sha tara ta arziƙi haka ta baro Sadiya da jariranta cikin ƙoshin lafiya duk da tana jin ba daɗi da za ta rabuwa da su Imran da Abid ne suka kaita har gida a motar Abid sosai su ma suka ji ba daɗi lokacin da za su baro garin su Inna sabo tirken wawa.
Imran ya nemi yafiyar Inna kan abubuwan da suka faru, har dai ma sai da ya bayyana mata cewa shi ne aljaninta kuma shi ne mala’ikanta.
“Kai Imirana amma ka iya shegantaka wallahi, yo Allah na tuba ai ka tsurar danu gabaɗaya ka sanya ina jiran ranar mutuwa ta” Cewar Inna tana dariya shi ma da Abid dariyar suka yi , aikuwa Inna ta ce ta yafewa Imran shi ma ta nemi yafiyarsa, suka baro Inna suna kewarta dan har suka shiga garin Kano labarin Inna kawai suke suna dariya irin yadda ta sha yin abubuwan abin dariya da cikin mutum zai ƙulle.
Tun da Inna ta koma gidan Malam zaman lafiya ya wanzu tsakaninta da Tasalla sosai Malam yake jin daɗin zama da su yanzu. Inna kuwa kullum ta tuno Imran ne silar gyara rayuwarta sai ta ji daɗi ta rinƙa sanya masa albarka.
“Ina son ku masoyan ƳAR ZAMAN WANKA KWANA ARBA’IN, musamman ƴan paid grp wanda suka biya kuɗinsu domin cigaban labarina da na Hassan da kuma Imirana, yo Allah na tuba ai ba zan manta da ku ba” Cewar Inna tana ɗagowa masoyanta hannu
Alhamdulillahi kasiran, ina godewa Allah dabya nuna mini farko da ƙarshen littafin nan, ina godiya ga masoyana a duk inda kuke musamman wanda suka biyani kuɗi dan bibiyar labarina na gode sosai da sosai son so fisabilillahi!
Ina neman afuwar dj wanda na ɓatawa a ckn rubutun nan da ya yafe mini ko ma ba a kan rubutun bane ina neman afuwar kowa, dama ɗan adam ajizi ne
ALƘALAMIN MMN AFRAHH BA YA RUBUTA SHIRME♀️
Allah bamu ikon gabatar da ibadunmu lafiya Allah sa a sallace da mu muna raye lafiya
♀️♀️♀️