Auren Gado Hausa NovelHausa Novels

Auren Gado 43-44

Sponsored Links

 

………… A gida bayan fitar su da sauri ta fada dakin nashi, taga zani daya a kasa ga nakan gadon ma yayi kaca kaca, wani irin turnuki taji a zuciyar ta, wato khaleel da ace Asibiti ta haifeshi da tace anyi mata canje, ta manta da kana haihuwar Wanda yafika tsaurin ra’ayi, kwalawa mai aiki Kira tayi, ta nuna mata dakin cikin takaici ” clean this mess right away. Ta Fita sai zagaye takeyi tana neman mafita tarasa ta Ina zata bullowa Al amarin khaleel, Zarah ta Kira tunda farar Safiya, ” Aunty lafiya fa safen nan? Tafada cikin tsoro, ” Ina fa lafiya zarah, ni bangane aikin malamin nan ba waya rana yayi wata rana kuma lamari ya barkace. ” meyafaru Aunty? ” khaleel….. Tafada mata komai in details. “Kema Aunty ke keja ki cire idanun ki aiki ai ahankali yake farawa kuma idan kika matsa za ayi biyu don tsab khaleel zai sallami salifa. “Bazaiyi ba don yana tsoron tsinuwa ta shiyasa ko yanzu na fada mai karta dawomin gida inba hakaba banyafe mai ba. “Kash Aunty me kikayi? Kinsan dai bazai sake taba, what up ya nema mata gida daban? Dafe kirji tayi ta tuna da kalmar shi bazai taba sakin Naziya ba, kuma tasan halin Abinta, “zarah kice na bato lamari? “Gaskiya Aunty wata rana bakya shawara kike aikata Abu, bakya yin Abinda ya dace. “Zan janye tsinuwar bari inkirashi in lallaba shi don karya sauke akan salifa. ” zai aikata kinsani sarai bai barin Abu abanza.
Kashe wayar tayi ta fara neman shi jiki na rawa. Lokacin ya fito daga Asibiti domin duk hankalin shi na cikin dakin yanda yabarshi yasan momy bazata gyara ba, yaji karar wayar ta, dauka yayi kamar nothing happened, ” khaleel Ina kakai yarinyar nan? Shine tanbayar da tafara yimai, yayi shiru kadan yace ” Ina hanyar dawowa am close, ya kashe wayar.
Yana dukan sitiyarin yana fesar da numfashi, ” I will fight this battle alone Yaya Ahmed, Allah ya jikan ka ya biyaka da Aljannah. Yafada yana jin duk wani damuwar sa ta gushe da ya tuna da cikin ni’ima da farin cikin da ya Kwana, Aure dadi, Naziya karshe ce a cikin mata, tuni yafara kewar ta yaji kamar ya juya ya koma ya rungume ta, jin kanshi yakeyi a sama, koda ya shiga gidan ya parking, masu aiki na gaishe shi yana amsawa cikin fara’a da wani irin Annuri. Gefen momy ya wuce, tana tsaye tana zagaye taja doguwar Ajiyar zuciya ganin shi, ta tashi, matsowa yayi fuskar shi a sake ya zauna a gefen ta ” momy good morning, dazu na Fita ba a natse ba. Kallon fuskar shi tayi tana hango sheki da Annuri tareda kwantaccen farin ciki a fuskar shi,
“Khaleel Ina ka kai ta? Answer me? ” Momy in her condition Ina yakamata inkaita inba hospital ba? And forgive me if I did anything wrong to you, Ina so inyi miki biyayya momy nima one day kiyi min Addu’a exactly yanda kikewa Yaya na, idan nabata miki rai, forgive me bakin ki guba ne dafi ne, fushin ki damuwa ne, Ina sonki mama na, please ki tayani son Abinda nake so, Momy kin tanbaye ni why I marry Naziya without rejection? How can I reject the woman I love more than my life? Momy Ina son Naziya tun Yaya na na Auren ta batareda nasan zan mallake taba, kince karta dawo cikin gidan nan, bazan dawo da ita ba, insha Allahu I will obey you Momy. Ya zabura ya kama hanyar dakin shi takasa cewa komai, sometimes sai zuciyar ta taso tausar ta saita kasa so take ta bashi hakuri Amma tunanin Alkawarin da tayiwa kawarta da kuma ego dinta ya hanata tana kallo harya shige dakin lokacin maid din na kokarin shinfida mai wani bedsheets, wani irin tsawa ya buga mata ” ke uban waye yace ki taba min kaya? Get out.
Jikinta na rawa ta fice, ya kwashe zanin gadon masu stain ya kwabe ya shiga bathroom da kanshi ya wanke su tas Abinda bai tabayi ba wanki irin wannan,
Saida ya gama ya dawo cikin dakin ya canja bedsheets da kanshi, ya daura towel ya shiga bathroom saida ya hada ruwa mai zafi ya shiga ciki shima domin shikan shi yana bukatar su, kwanciya yayi yana wani irin murmushi mai cikeda da ma’anoni, “baby this is your work fa, kinsani gashi, all my joint are paining me, what a sugar. Yafada yana sude lips domin he can still feels her sweetness,
Imagine yake idan ta warke how he is going to spoil her, yanda bazata iya rayuwa batareda shiba, ” we are going far away from all this problems. Ya dauki dogon lokaci a cikin ruwan kafin ya fito, zama yayi gaban mirror ya fara kalkale ko Ina na jikinshi, kafin ya fito dakin, saida ya gama nazari kafin ya fito da wata farar shadda, ” am ango today. Ya zura harda hula ya ciro agogon shi ya daura tareda katon Azurfan shi,
Kamar ka sace shi ka gudu, haka ya baza kamshi, ya kwashi wayoyin shi ya fito harda nata,

Yana fitowa tana sawo kai cikin karai raya da sanabe, lokacin da tayi arba dashi saida ta kusa zubewa saboda ya tafi da imanin ta, ” wow is he really my husband? Oh my gosh. Kamar invisible haka ya ganta, ya fito da wayar shi dake Kara ya yi saurin picking, “Aunty kinzo ne? OK gani nan zuwa. Yafada yana wuce ta cikin sauri.
Kamar doluwa haka ta tsaya har ya bacewa ganin ta yabarta da fitinannen kamshin shi.
Saida Momy ta fito rikeda jaka zata tafi aiki taganta a tsaye kamar wata yar kwaya tana bin kamshi, “Salifa lafiya?
“Hmmm Momy. Tafada tana matsowa cikin salon iya shege, ” kin iya haihuwa what an Angel. Tafada tana rungume ta, ” kingan shi kuwa? He look very handsome and classy, wow I love him wallahi yafi Ahmed komai wow gwara da ya mutu na Auri wannan……… “Ke meye haka banson hauka, agaban Idona kice gwara da Dana ya mutu? Banson rashin hankalin ki da rashin iya magana. ” Allah ya baki hakuri Momy yau ba kida laifi ganin khaleel yasa ba Abinda zai batamin rai yau. Ta rungume ta, ” Momy kisa yau yazo gareni please. Cireta tayi a jikinta ” matsa min zanje aiki karinyi latti. Kawai ta iya fada domin Abun ya mata wani iri wannan idanun ta budewar su ya wuce misali,
Fita tayi tabarta tana faman tsallen shauki da son khaleel, momy da kanta ta shiga motar ta ta tayar idan ka kalleta zaka gano cewa jikinta a mace yake yau, kawai maganar da Khaleel ya fada mata ce ta dameta musamman kodai ba ita ta haifesu ba? D’an cikinta na tantaba akanta, is she that bad? Me tayi musu wrong a rayuwa da har yafada mata irin wannan maganar? A haka ta tafi jikinta yayi matukar sanyi.

Asibitin ya shiga, saida ya nemi likitar, tace ta sallameta ruwan ya kare kawai zata rika yin sit bath ne, akai akai har dinkin ya warke, nama yiwa Y’ar uwar ta bayani. Tafada tareda rubuta musu wani cream mai saurin warkar da ciwo, ya karba, ya Fita, saida ya d’an tsaya a kofar dakin da take domin kunyar Aunty Raliya yakeji sosai kafin yayi ta maza. Yana tura kofar, ta dukar da kanta kasa domin basai yace komai ba wannan fitinannen kamshin nashi ya isar mata da sakon isowar shi, sallamar shice ta biyo baya, Aunty ta mike daga kan kujerar ta amsa fuskar ta cikeda fara’a. “Harka iso khaleel? “Eh Aunty yafada yana mai kallon cup din hannun ta dake dauke da kunun gyadar da Aunty tazo mata dashi.
Juyawa tayi tafita kawai domin basu space, Wanda hakan yakeso dama, tun shigowar shi yake satar kallon ta,
Tayi mai kyau so yake ya matsa jikinta har wani irin fisgar shi gangan jikinshi keyi zuwa gareta, don haka Aunty na Fita ya daga kafa cikin sauri ya isa gefen ta ya zauna tareda karbar cup din ya Ajiye, taki yarda su hada ido dashi domin ita kam tasan kunya duk Abinda ya faru Ina taga karfin zuciyar hada ido dashi,
Ji kawai tayi ya rungume ta gam a gefen kafadar shi, “Am sorry baby nasa anyi miki stitches, ba laifina bane, lafin kine you are so sweet, so so sweet that I can’t control myself, you deserve a gift, but not here, ya dago kanta ta runtse idanun ta, ya ce ” please open your eyes kinji I want to see them. Kara runtse idanun tayi don kunya takeji, ” oh come on, meye kunya a tsakanin mu yanzu, kin zama ni nazama ke we shear the same bond same blood I can feel you all over my body and my soul,
Lafewa tayi luf a kirjin shi, bata bude idanun ta ba kuma batace komai ba,
” why are you always silent? Talk to me feel free, complained let me know what is going on in your heart even once please, Momy a kullum tana miki fada duk kalmar ta akanki batada dadi it hurt and touch me, ke kuma you don’t even react, why?
Sai lokacin ta dago tareda kallon shi cikin ido ” me kakeso inyi? In Rama? ” you have the right. Yafada yana mata wani irin kallo. ” girgiza kai tayi ba tarbiyar da aka dora mu akai ba kenan, babba kullum adai dai yake yaro ke laifi, me tayi wrong? Saboda tanaso ku Auri mata dai dai da Rayuwar ku? She is right tanada dama kuma uwace ta isa, kuma ra’ayi da burinta takeson cikawa, kayi mata biyayya please give her what she want.
Hade fuskar shi yayi, ” do you know what that means? ” yes ka sake…… Bakin shi yayi saurin dorawa akan nata ya fara tsotsa cikin zafi zafi, har tanajin yana cizon lips dinta da d’an mugunta saida ya dauki lokaci ya janye, ” don’t repeat that, it hurt to hear from your mouth, na tsani kalmar rabuwa dake ko a mafarki, don’t even imagine that again, Aure na dake mutu ka raba takalmin kaza ban rabu dake tun farko ba sai yanzu, mahaukaci ne ni, rabuwa dake yana nufin rabuwa da numfashi na, zan iya rabuwa da kowa bazan iya rayuwa babu ke ba.
Wani irin sanyaya mata zuciya da gangan jikinta kalaman shi sukeyi, duk sun warkar da wani ciwo da damuwar ta, yes da zata iya bude baki data fadamai itama bazata iya rayuwa bashi ba, tsanar da taji wasu Amare na yiwa Angwayen su just saboda sunyi musu biji biji ita ba haka bane a zuciyar ta, she love him more, yes tana son khaleel saboda shi din namiji ne tsayayye d’an ra’ayi in yace yes baya canjawa, ba kamar Ahmed ba, shine ya cika burinta shine yazamo mata mijin da ke share hawayen ta da damuwar zuciyar ta, yes she love him koda shi baya sonta, domin ita har yanzu gani take yanayi ne domin yayan shi,
Jin hannun shi a saman kirjinta yasa ta zabura ta kalle shi, kashe mata ido yayi tareda rada mata” Allow me, I missed them tunfa jiya yafada yana maria raice fuskar shi kamar wani jariri,
Ture hannun shi tayi “Aunty na jira. Dafe kai yayi ya duro, ” kinga kinja mun shanyata. Hannu yasa ya sauketa, yace “walk slowly karki karamin wasu kwanakin kisa in suma.
Shiru tayi kawai don yaci ta gano cewa shifa baisan kunya ba, hijabin ta ta gyara ta zura silifas dinta, Aunty Raliya tayi sallama, yace “ya gama kimtsawa Aunty muje. Gaba yayi cikin sauri, sukuma suka biyo shi, satar kallon shi takeyi, yana tafiya, a karon farko tana hango mazantaka da jarumtar shi komai nashi Abin burgewa ne, sai Ajiyar zuciya takeyi har suka isa wurin dalleliyar motar shi,
yanzu take lura da lamarin shi, a koda yaushe sabuwar mota take ganin shi da ita, saboda Alfahari ko rashin sanin Abinda zaiyi da kudi ne ya janyo?

Saurin zagaya wa yayi ya bude mata gaba tareda kallon ta yace “here. Zagaya wa tayi a natse take tafiya domin zafin da takeji, a hankali ta zauna, Aunty Raliya tuni ta shige baya. Saida ya fita cikin Asibiti yace “Aunty kinyi magana da doctor? ” eh tafada min komai yanzu ba damuwa muje gidan nawa da ita, Amma banson malam yasani don zai iya yin fada. ” no ba Wanda zai sani, in one week ma zanzo indauke ta. ” Allah ya kaimu. Tanajin su batace komai ba sai sauke hannun ta da tayi gefen break, Wanda kamar jira yakeyi ya dora kyakkyawan hannun shi akan nata, ya damke tareda murzawa kadan, kallon shi tayi cikin sauri tareda nuna mai Aunty da ido, yagane me take nufi ya basar tareda dauke kanshi yasa a titi, tuki yakeyi cikeda nishadi da farin ciki, Aunty Raliya kuwa batama san me sukeyi ba tana danna wayar ta tareda yiwa Aisha bayani ta wtsp don bata yin Abu batareda sanin kanwar tata ba,
Naziya kuwa hannun shi ta kalla, haka kawai ta kasa dauke idanun ta bata taba ganin namijin da Agogo ya zauna a tsintsiyar hannun shi ba kamar khaleel, ga sumar dake kwance a ko Ina har bayan hannun shi, takasa dauke idanun ta akai ga kasalar da ya sakarwa gangar jikinta saboda y’an da ya ke murza tafin hannun ta. Komawa tayi ta lafe tana kallon hannun har suka isa unguwar su Aunty Raliya, yana tsayawa Aunty Raliya ta bude tafita, itama ta juya zata bude ya riketa gam, Aunty tace ” kushigo khaleel, Naziya falo a bude yake. Tayi gaba, datse kofar motar yayi tareda matsowa yace ” kema kina son agogon mijinki? Yes mata da yawa nafadamin agogo na yimin kyau a hannu, gashi kema ya burge ki. Kwace hannun ta tayi cikin haushi tace ” su yake burgewa meye Abun burgewa a nan? Dariya yayi ya fisgota zuwa tsakiyar cinyoyin shi, tace ” meye haka a waje fa muke inwani ya ganmu fa?

” Nida matata ne Ina ruwan wani, kuma ai ba maiganin mu sai dai mu ga mutane. ” let me go? “Let go inside together bangaji da ganin kiba, kinsan yakamata by now ace muna can cikin bargo muna shan dumin juna amma kinja mana, “wait yaza ayi yau inyi bacci? Yafada yana matse fuskar shi, “akwai matsala gaskiya. Ya shafo kanshi ji yake kamar ya fasa barin ta anan Amma yasan bazai iya fadawa Aunty Raliya ba. Sauke ta yayi cikeda damuwa ya bude motar tana kallon shi, ya zagaya ya bude gefen ta, kamar wata kwai haka ya dagota, saida ta matsa saboda unguwar akwai idon jama’a gashi anga first class car kowa dole ya kalla, ita tafara yin gaba ya bi bayanta baya ko kifta ido,
Tafiyar ta yake kallo yasan akwai matsala, yayi dariya kadan, ” khaleel kazama namiji. Cikin dan madai daicin falon ta shigar dashi kafin tace Ina zuwa. Tayi gaba, Aunty Raliya har ta hado mai breakfast a tray, tace “ungo jeki bashi yaci daga gani ko karyawa baiyi ba. Ba musu ta karba takoma falon, yana ganin ta ya mike ya karba, ya Ajiye tareda cewa “bakowa ne agidan? ” eh yaran suna school megidan ya fita aiki.
“Hmmm yace ya nufi kofar da ta shigo ya kulle tareda dawowa ya kulle ta falon ya janyota kasan carpet din ya zaunar da ita a natse , hijabin jikinta ya cire mata, ya kalli tulin kirjinta yaga ba bra domin bai samu tsayawa ya saka mata ba, hannun shi ya dora tareda shafowa suka ja Ajiyar zuciya a tare, tuni lafiyar shi ta harba ya shige jikinta yana jan numfashi, ” baby zan wahala wallahi da yawa, how can I spend two weeks without…….. Ya dora bakinshi saman wuyan ta ya tsotsa har zuwa kirjinta inda yake d’an bayyane saboda wuyan nada fadi, sai dada sauke wuyan yakeyi badon badon ba ko…. Hmmm, manne kawai yakeyi yarasa Ina zai sa kanshi, ” ki lallabani in bar gidan nan kar inyi barna, yaja dogon numfashi.
Muryar ta a shake domin shidin ba namijin da zai taba mace ta ture bane don haka duk lokacin da ya kusanto ta bata iya tserewa ko me yasa? Cikin rawar murya tace ” ga breakfast kayi ka tafi. ” you are the best breakfast for me now. Yayi saurin cafkar lips dinta yanasha kamar su zasu bashi natsuwa, saida ya kwashi tsawon lokaci, yaji karawa kanshi damuwa ma yakeyi, saida taji tausayin shi badon akwai dinki jikinta ba, ba Abinda zai hanata kashe kanta a yau ta rayashi koda a zauren malam ne, domin jitake kamar su kasance tare kar yaje ko nan da can.
Da kyar tasamu yaci breakfast din kadan ya mike tareda cewa ki cewa Aunty sai nadawo Anjima. Ya ciro wayar ta ya d’an ka mata tafiya jikinshi a mace.
Yabata tausayi sosai,
Kwashe kayan tayi ta koma ciki, Aunty na zaune ta tashi ta karba ta wuce tana cewa kizo ki shiga ruwan zafi kiyi wanka. Saida ta gasa jikinta sosai ta fito Aunty tabata wata doguwar rigar da zatayi mata, tace ” kisa ya kawo miki kaya mana. ” uhm tace, saida tasha magani ta kwanta a kujera Aunty ta zauna tace ” Naziya, meke faruwa ne agidan naku? ” bakomai Aunty likita ce tace Ina bukatar hutu…. ” no mezaisa ya kawomin ke akwai matsala inada wayau fa niba yarinya bace, yanda nake ganin Abinda ke faruwa tsakanin ku yanzu nasan kuna son juna keda shi, kuma dole ki fuskanci matsala, Ina kishiyar ki take? “Ni Aunty ko ganin ta banyi ba, kuma momy ce tace idan yadawo dani cikin gidan bata yafe mai ba. “Hmm Allah ya kyauta’ to yanzu shi yacemin zai dawo ya dauke ki meye plan dinshi? ” Bansani ba don baice komai ba akai.
“Shawarata kibi mijinki duk yanda yakeso ba biyayya akan sabon Allah, koda kuwa umarnin uwar shi ce don haka Ina respecting dinshi namiji ne khaleel jajurtacce ki natsu ki saki jiki ki rungumi kayanki.
Sun dade suna hira har Aunty ta shiga kitchen ta barta domin dora lunch, wayarta ta janyo, so take ta kirashi tana tunanin me zata cemai she is Already missing him, shikuwa office dinshi ya wuce, yana zaune dafe da kanshi saboda damuwa, bayajin zai iya komawa gidan su bata ciki bazai taba jin dadi ba, yaga ringing daya na kiranta kuma ta kashe domin harta fara dialing ta kashe don batasan me zata fada mai ba,
Murmushi yayi ya ce ” just call me mana why this plashing? Ya d’an jira kadan yaga bata kiraba, kawai yayi dariya ya dauki wayar shi ya mata transfer na ten k kai tsaye, saida yaga sunje ya tura mata message “no need to plash Mrs khaleel.
Kunya taji sosai dataga kudin da ya turo mata all her life bata wuce na dari biyar tun Ahmed na nan sai gashi ya turo mata na dubu goma kai tsaye me zatayi dasu? Kuma ma ai tanada kudin kiran kawai kunya takeji.
Jin shiru bata kiraba yasa ya kirata, ba wani jan Aji tayi picking hade da sallama cikin sanyin murya. “Mrs khaleel ya akayi ne? Are you missing your husband? ” no kayana nakeso akawo min. Tayi saurin fada. “No problem koda missing dina kikeyi, ni Ina kewarki Ina office nakasa sarrafa Kaina……. 🖊

 

 

Back to top button