Hausa NovelsNi da Patient Dina Book 2

Ni da Patient Dina Book 2 Page 41

Sponsored Links

Fa ra bata labarin tun daga lokacin da take ciki har zuwa haihuwarta da kuma abinda take dauke dashi a jikinta da yakar kungiyoyin kaff seda ya fada mata sannan yakara da ” labari mara dadinji shine! gaskiya sarauniya a ko wani irin lokaci za ki iya tafiya domin yawan rashin adalcin da akeyi yana kusantoki! Jaaazana nakara bayyana a jikinki , duk inda aka samu irin wannan bar nan ya afku sau uku nan take zaki koma masarautar ki , ko da kuwa kin shirya ko baki shirya ba yanzu de anyi biyu ina tunanin saura daya”.
Takasa cewa komai se hawaye da kuma murmushin datakeyi atare lokaci daya ,
Tabbas masarautar take gani yana mata flash dakuma sarki abdud daar ashe itadin shugaba ce dazata kawo gyara .

Se yanzu take jinta cikakkiya amma dà se ta dinga jinta kamar akwai abinda ta rasa ,kamar ta rasa wani bàri a tare da ita amma yanzu da tasan ita wacece se taji duk wani gurbi yacike,

Duk suna jira suka reaction dinta ya zataji intaji wannan labarin, abinda basu taba zata ba tayi sujjada tayi ta daga hannunta sama tana yiwa Allah godiya ” Allah nagode maka dakasa nazama zabàbbiya ! tabbas zanyi aiki da duk wani wani karfi danake dauke dashi domin kare rayukan al’umma daga jinsin bil adama harzuwa jinni koda kuwa zezama sanadiyar rai ne , Allah kasa ta dalilin haka in zama me rabo a aljanna ”
amma data tuna za tabar iyayenta da duk wayanda ta sani se taji gaba daya duniya bata mata dadi. Kallon Abdud Shakur tayi dake jikin areef tace ” inson magana da kai sirri” dago kai kawai yayi ya wuro iska a bakinshi yace ” sarauniya za ki iya maganarki ayanzu babu wanda zeji me muka tattauna ” kallon yan falon takeyi dan ta tabbatar yasa tace ” zeenat kinaji ?” Shuru zeenat bata mata reply ba sede ta bita da ido .
Su kuwa su abba kallonsu kawai suke suna magana amma basajin abinda suke fada azaad de ya kafe bakinta da ido dansan gane abinda zata fada, gam yarike yanda bakinta yake motsi amma yagagara seta kalmomin.
Suna gama maganar abdud Shakur ya fita daga jikin areef, tashi areef yayi dan besan meyafaru yace ” antynmu yanaga kamar hawaye kikeyi wani abu yafaru ne?” Girgiza mishi kai tayi tace ” babu abinda yafaru ya areef” “okay” yace tare da wucewa part dinsu . murmushi kawai takeyi da gaba dayansu sun rasa gane na miye , tabbas samun irinsu fanan acikin al’umma abune dazeyi matukar wahala awannan duniyar koda kuwa akwaisu zasuyi wahalan samu sannan basuda yawa , ta yarda zata sadaukar da rayuwarta akan yakar azzalumai bata damu ta mutu ko ta rayu ba farin ciki ma takeyi da hakan akan shahadar da zatayi .
Jikinsu ya mutu sosai nan take tun kafin lokacin tafiyar ta yayi harsun fara kewarta , shikanshi Mr azaad seda yaji ba dadi part dinshi yatafi yabarsu afalon, lura fanan tayi baya falon yasa itama tabi bayanshi, zama sukayi duk basa cikin dadin yanayi kiran baba abba yayi ya sanar mai da fatima tariga da tasan ita wacece , murmushin takaici kawai baba yayi ranshi na kuna yace ” alh nariga da nasan wannar ranar na nan zuwa na sawa zuciyata dangana kullum kokarina in kwantar wa mahaifiyarta hankali ! Nasan yau inde taji labarin abinda yafaru hana kanta sukuni zatayi” haka sukata jinjina lamarin cikin rashin jin dadi amma babu yanda zasuyi sede sumata adduah Allah yabata saa a abinda zatayi yakareta daga sharrin wayan nan mugayen azzaluman. bedroom dinta tashiga takwanta tana tunanin tafiyarta nan take ta tuna wani abu tasa zuruf ta mike.
Toilet tashiga tayi wanka ta wanke gashinta da shampoo’s masu dadin kamshi, koda tafito she didn’t bother to dry it gogeshi kawai da towel tayi , tunawa da shawarwarin da anty amina tabata tayi , killer smile ta sake daya fito mata da kyaunta ta bude tankamemen wardrobe dinta , one by one take bin kayan dake lode aciki da kallo ,sauka idonta yayi akan bangaren wasu tsinannun kana nan kaya, tun kafin ta dagosu kunya yakamata taya zatasa wayan nan kayan taje gabanshi , dubawa takeyi hartazo kan wani yar iskar riga da ita da babu duk daya daukoshi tayi ta dagashi sama tana kare mai kallo daga sama har kasa , gallawa kayan harara tayi sekace shi yace ta dauko shi . tafi minti 5 tana tsaye tana juyashi rigar kalanshi sak da wayanda karuwai suke sawa, wurgashi kan bed tayi tadau wayarta tayi dialing number anty amina dagawa tayi tana ” assalamualaikum my feena kina lafiya?” Zama tayi a gefen mirror ta amsa sallaman tana tambayarta yasuke da junior kafin tadaura da ” am! am anty amina dama maganar da mukayi kwanaki ne to yanzu kuma…..uhmmm ” kasa karasawa tayi jin kunya yakamata, anty amina ta rigada tasan inda maganar ta dosa ,kunya ya hanata fada , yar dariya tayi jin yanda fanan take in da in da takasa fadar taka memen abinda yasa takirata ” calm down my feena kidena jin kunyata kifadamin duk abinda kikeson fada se munsan yazaayi ko?” Sosa wuyanta tayi tarufe idonta kamar anty aminar na gabanta tace ” dama zanje wajan Mr azaad ne tom kamar yanda kikace inde inaso muja hankalinshi da wuri dole se inasa kana nan kaya dakuma sauran abinda kikace” sosai anty amina taka sa kunne tana sauraranta cike da jindadin yanda fanan ta shirya karban shawaranta sannan tace ” ci gaba ina jin ki ” sake runtse ido tayi ta daura da ” tom nayi wanka na dauko wata riga wallahi anty amina baki gantaba kamar irin wayanda karuwai sukewa rigar fah yar iska ce sosai” ta karishe maganar tana dan fito da dara_daran idonta .
Dariya anty amina ta keyi sosai jin abinda fanan ta fada wai rigar fa yar iska ce sosai hhhhhh, tsaqaitawa tayi da dariyar tukun tace ” wallahi my feena za ki kashe mutum da dariya ! duk yanda rigar take karki damu kisata ahaka sannan kuma……………..” tasake fada mata wasu abubuwan da nikaina banji ba . bayan sungama wayan ne taje gaban mirror tazauna ta shafa lotion masu tsada da dadi , tayi usual make up dinta, daukar rigar tayi tsaban yanda yake da yanka_yankan tsagu ajikinshi ta rasa ma ta ina zata sashi haka tafara gwadawa dakyar tasamo kan rigar . Kallon kanta tayi a mirror zaro ido waje tayi ganin yanda rigar tamata , guntuwar rigace roba yana yalki red color du ka tsayin rigar da kadan yawuce Santala_santalan cinyoyinta da suke glowing gefen hagu na rigar tundaga hannu har inda rigar ta tsaya tsagu_tsagu ne manya ana kallon fatarta awaje yana da dogon hannu se wuyan rigar daya kasance me fadi sosai open shoulder kenan dukiyar fulaninta duk suna waje rabi ne aciki ya matseta sosai duk wani structure dinta seda yafito fili , ga lallausan chocolate fatarta awaje , inde tayi kwakwaran motsi jikinta seya motsa , seyanzu nikaina na sake mata kallo sune ainihin matan da ake kira masu shape din coca-cola, juyawa tayi tasake kallon kanta a mirror slice smile tayi tace ” Allah yashiryeni” hills black color tasa tafeshe jikinta da wasu irin daddadar tururuka masu sanyin kamshi , gashin kanta be gama bushewa ba sunyi wara_wara nan ne takara fitowa very sexy, tsayawa fadar kyaun datayi bata bakine , wani taku takeyi step by step cike da nutsuwa take tafiyarta , yanda body ta ke juyawa dakanshi wani zeyi tunanin da gangan ne amma ita kanta batasan sunayi ba .
_

Back to top button