Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 29-30

Sponsored Links

2️⃣9️⃣➡️3️⃣0️⃣

Yadda Imran ya fito a firgice cikin kiɗemewa ko lura bai yi ba da Inna da ke tsaye, ƙaran dariyar da ta saki ne ya sanya ya dakata daga ƙoƙarin gudun da yake wanda shi kansa bai san ina ya nufa ba. Ganin Inna tana dariya har da nuna shi da yatsa sai ya dakata tare da haɗe rai kamar ba shi ne ya iyo gudun ceton rai ba daga cikin tukunya, sanadin zafin da ya ziyarceshi.

Kallon murhun ya yi ya ga yadda wuta ta kama take ci kamar wanda aka sanya fetur, ga sauran buhun nan wanda Inna ta saka bai gama ƙonewa ba.

“Lallai tsohuwar nan ta ga makwancina da yawa, yanzu ni ta balbalawa wuta? Dan na san dai ai ba za ta ce bata san ina cikin tukunyar ba, ” Ya faɗa a zuciyarsa sai muzurai yake kamar zai hau Inna da duka.

“Imirana wai dama kai ne a cikin tukunyar wankan jegon matarka, soyayya ce ta sanya kakeso a dafa ka ta yi wankan da kai a memekon a dafa mata ruwa?” Cewar Inna tana ƙoƙarin danne dariyarta har da ƙwalla. Gefen leɓensa na ƙasa ya danne da haƙori ji yake kamar ya saki kuka dan takaici. Juyowa ya yi yana ƙoƙarin barin wurin dan dama wurin da murhun yake a ɗan lungu ne ba a sararin tsakar gidan yake ba.Sai da ya fito idanunsa suka sauka a kan Shek da ke ƙoƙarin raɓewa a bayan Sadiya ita kuma tana gocewa tana matsawa yana ƙara bin ta. A take maganar Inna da take cewa kwarto zai yi fyaɗe ta faɗo masa, ai ganin Shek kusa da matarsa ba ƙaramin fusata shi ya yi ba, in ba iskanci ba ya za a yi yake ɓuya a bayan matar aure, shin uban me ma zai shigo da shi cikin gidansa. Cikin jin haushi da fusata ya nufo wurin su dan gabaɗaya kishi ya rufe masa idanu har wani diri-diri yake gani, hakan ya mantar da shi ƙalubalen da yasa ya shiga cikin tukunya, dan gabaɗaya ya manta da batun miciji bare har ya yi tunanin shi ne dalilin da yasa Shek ɗin ɓuya a bayan matarsa. Idanunsa sun rufe ko lura da micijin da ke gaban su Sadiyar bai yi ba,a fusace ya nufo su, dan nufinsa yana zuwa wajen zai manta da mutunci da abokantakar da ke tsakaninsa da Shek ya shaƙe masa wuya sai an ƙwaceshi dakyar a hannunsa tun da shi ma bai ga mutunci da haƙƙin makotaka ba son zuciya ya rufe masa ido har ya zo yake neman yiwa matar aure fyaɗe.
Yadda ya taho a fusace kamar kumurcin miciji za ka ɗauka yana zuwa zai ɗauki hukuncin da ba zai yiwa kowa daɗi ba, amma me sai da ya zo dab da su idanunsa suka sauka a kan Hassan da ya yi wata alkafira, kansa ya cake a ƙasa sai jelar ta zama a sama sai wani wulwula ta yake kamar fanka. Wani uban birki Imran ya ja, tare da haɗiye wani yawu muƙuuut, ajiyar zuciyar ya fara saki a jere- a jere kamar wanda ya ƙwaci kansa daga hannun ƴan fashi. Cikin sauri ya fara kalle-kalle yana so ya ga ta inda zai tsere, yana waiwayawa bayansa sai suka haɗa ido da Inna da ke dariya marar sauti, ganin abin da ke faruwa dan dama ta gama karantar cewa Imran kishi ne ya rufe masa ido ya tafi ba tare da ya lura da micijin da ke juya jekarsa kamar an ƙurewa fanka gudu ba. Ita ma Inna a tsoracen take dan abubuwan da Hassan ke yi yau sun girmi tunaninsu, amma kuma ganin Imran ya taka birki ƙiiii kamar wanda ya kusa faɗawa kwalbati ya lura da ramin gabansa, hakan ya yi lolacin da ya yi ido huɗu da micijin.

“Dole ka nemi mafaka Shek ba lefinka bane, tabbas na daina ganin lefinka ko ni na na shiga gidan matar aure tuni zan manta da igiyar aurenta, in har a irin wannan bala’in ne ko a cikin ɗan kamfai (Pant) Ɗinta sai mutum ya totsu ya yi mafaka” Cewar Imran a ransa, fuskarsa kamar ya saki kuka, ga ruwan tukunyar da ya jiƙa masa jiki sai tsiyaya yake daga jikinsa, kallon Shek ya yi da gabaɗaya gumi ya gama wanke masa fuska sai tsiyayowa gumin ke yi ta jikin gemunsa yana ɗisa a ƙasa, ga yadda ya jiƙe da fitsari da alama ya yi fitsarin sama da kifi uku.

“Wayyo maƙocina, ashe kana cikin gidan nan, wallahi Sadiya ta ce min baka nan da tuni kai zan nema amma ganin baka nan ya sa nake nema ya rungumi wuta da hannu na, yo wuta mana duk inda na rafki matar aure da hannu na ai na san na kama wutar jahannama” Shek ya faɗa yana kallon Imran da ke kalle-kalle dan shi gabaɗaya ya kasa tantance a raye yake ko a mace ko mafarki yake da yake ta haɗuwa da wannan iftila’in.

“Imirana wai ya ka toge abokinka yana maka magana, amma ka ƙeƙashe ƙasa ka tsaya kamar wani gini, kar fa Allah ya kama ka a kan haƙƙin maƙotaka maƙocinka na cikin wani hali amma ka kasa kai masa taimakon gaggawa” Cewar Inna tana kallon Imran tare da danne dariyarta dan wata uwar harara ya aika mata kamar dai ta ce ya damƙi wuta.

“Allah dai ya miki albarka tsohuwa, nagode ƙwarai da gaske da kika ƙara fahimtar da shi” Cewar Shek yana kallon Inna da ke tsaye can hanyar murhu, so yake ya gudu bayan Imran amma yana tsoron abin da zai je ya zo domun kuwa ya ga micijin zai iya wartoshi lokaci guda , a gefe ɗaya kuma ga Imran ɗin ma kamar a tsorace yake, duk da kasancewarsa uba ga micijin.

A hankali Shek ya fara lallaɓawa sai da ya tsugunna daga tsayen da yake, cikin sanɗa ya fara rarrafawa ya nufi wajen da Imran yake, sai dai a matuƙar tsorace yake dan kar micijin ya biyo shi. Imran kuwa kafe Shek ya yi da ido ganin ya tunkaroshi zai je ya goga masa kashin kaji, dan idan da micijin zai masa kara saboda kasancewarsa uab a gareshi amma yanzu ganin Shek zai sa ya canja shawara, wani kallo ya yiwa Shek ɗin, yana kallon wannan hiramin da ya ci tumuri da shi a tsantsarsa. Shek kuwa ya raba hankalinsa biyu, ɗaya yana ƙoƙarin ya kai wajen Imran ɗayan kuma a kan micijin da ya ga duk wulwula jelar da yake amma kuma idanunsa a kan Shek ɗin suke. Har ya yi kamar zai dakata sai dai ya cigaba da rarrafen, sai da ya je daf da Imran micijin ya sauke jelarsa ƙasa, cikin kiɗima Shek ya dakata da rarrafe, bai san lokacin da ya tashi ba sai ganin kansa ya yi a tsaye cankarkar sai dai ya kasa tsayuwa dai dai sakamakon karkarwar da ƙafafunsa ke yi.
Inna kallonsu kawai take tana so ta ga ta yadda wasan zai fara dan ta san babu yadda za a yi a kwashe lafiya. Tun da Hassan ya ajiye jelarsa a ƙasa sai ya juyo ya maida hankalinsa ka su ya fasa kansa yana kallonsu, Shek ganin ya ƙura musu idanu sai ya sha jinin jikinsa cikin sauri ya buɗe baki ya ce.

“Ka masa magana mana Imran kai da ɗanka, ka yi saurin bashi umarni ya koma ɗaki ni in samu in bar gidan ma dan na rasa wane tsautsayi ne ya kawo ni” Ya faɗa yana kallon Imran da ke jifansa da wata muguwar harara.

“Da yana jin umarnin ai da baka zo ka tarar da abin da ka tarar ba hatta uwata tana cikin gidan nan ban san ma a ina ta ɓoye ba, kuma da ya san cewa ni ubansa ne ai ba sai na bashi umarni ba zai yi abu, ɗazu a gabana ya tsaya yana kai sara” Ya faɗa kamar zai saki kuka.

“Ka manta baka faɗa masa cewa har ƙwaƙumar Rakiya ka yi ba cikin rashin sani” Cewar Inna tana dariya tare da tuno lokacin da ta hangi Imran da Mama sun rungume juna kamar za su koma cikin juna saboda tsoro. Banza Imran ya mata dan shi yanzu kawai so yake ya fice daga gidan dan ya gaji da wannan wasan kwaikwayon. Yana tunanin mafita sai ganin micijin suka yi ya fara zulalowa a hankali kamar baya so, sai da ya zo tsakaninsu inda suke tsaye Imran da Shek ya ja ya tsaya, Shek na ƙoƙarin matsawa ya ɓuya a bayan Imran sai Imran ya ce.

“Kar ka kuskura ka motsa dan wallahi idan ya sareka ba ruwana”

Wani yawu Shek ya haɗiye yana kallon micijin kamar ya fasa ihu saboda yadda ya ganshi dab dashi abin ya matuƙar ƙara firgita shi amma ba yadda ya iya haka ya daure ya tsaya a inda yake. Zagayesu ya fara yi amma bai yi yinƙurin yin komai ba, ganin hakan ba ƙaramin ruɗewa Shek ya yi ba, amma kuma Imran ya hanashi motsi kamar yadda shi ma Imran ɗin bai motsa ba.

Wani tsalle da micijin ya yi shi yasa Shek da Imran rungume juna, yana komawa can gefe sai suka saki juna suna maida numfashi, kowa neman hanyar gudu yake, fara zagaya su ya fara yi cikin kuskure sai Imran ya ɗan motsa aikuwa Shek ma ya matsa wurinsa, miciji kwa ya ce da wa Allah ya haɗa shi in ba da su ba, haka suka shiga tsere, Imran a gaba Shek a bayansa, sai miciji a bayan Shek suna cikin zagaye Shek da ya ga micijin a bayansa yake kuma yana neman kai masa cafka sai kawai ya yi tsalle sai gashi ya ɗane bayan Imran, da yake jallabiyar ce a cikinsa kuma da zai haye bayan Imran be tattare ta ba sai ya zamana ya kasa ware ƙafafunsa ya zamana kamar goyo ya yi, sai ya zama kamar ƙadangare a jikin bango. Ƙafafunsa a sake amma kuma sai ya maƙalƙalo wuyan Imran, Imran kuwa tsabar ruɗewa ma bai san Shek ya ɗane bayansa ba shi dai kawai ya ji wuyansa a maƙalƙale sai ya yi tunanin micijin ne, aikuwa ƙafa me na ci ban baki ba, a haka yake ta sheƙa uban gudu a tsakar gidan.

Inna da ke can jikin bango tana hango su dariya kuwa cikinta kamar ya yi ciwo. Suna cikin gudun Imran ya kalli bayansa da wutsiyar ido, aikuwa ya hango Hassan na binsu hakan ne ya ankarar da shi cewar ba Hassan bane a wuyansa hannu ya kai bayansa aikuwa ya taɓo Shek da ke manne da shi kamar cingam haushi ne ya turnuƙe shi, yana mamakin ya aka yi ma bai ji nauyi ba sai ya danganta hakan da ruɗanin da yake ciki.

Wata mugunta ya yiwa Shek wani uban wujijjiga Shek Imran ɗin ya yi sai kuwa ga Shek yashe a ƙasa ya je da reran, miciji da je binsu da gudu yana zuwa sai ya bi ta kan ruwan cikin Shek, gabaɗaya Shek numfashinsa ya ɗauke lokacin da micijin ya bi ta kansa, bai ankara ba ya ji saukar wani fitsarin daga jikinsa. Imran kuwa wani tsalle ya yi ya koma gefe, micijin kamar an ce bi Inna kawai sai ya yi hanyar lungun murhu a mugun guje yana haɗawa da tsalle.

“Inna ce a nan lungun me maka ZAMAN WANKA” Cewar Inna cikin ruɗewa dan bata taɓa zaton zai zo inda take ba, ganin ya kusa ƙarasowa sai kawai ya saddaƙar ta yi wani uban tsalle ta faɗa cikin tukunyar da Imran ya fito.

Azaba da raɗaɗin ruwan ne da ya ɗau zafi ya ziyarce ta, kuka ta saki a zuciyarta tana cewa.

“Gwara na silsilge in yaso daga nan a kai ni maƙera su bani maganin wuta in ke shafawa a kan in bari ka sareni in mutu in barwa Tasalla Malam” Tana daga cikin tukunyar ta hangi micijin ya bar wajen, a sukwane ta fito ta ɗauki wani ruwa da ke cikin bukiti ta sheƙa tun daga kanta ta jiƙe jargaf.

“Kai Allah ka rabamu da wuta, ka haramtawa wuta cin naman mu duniya da lahira, yo ni da nake cewa sai na yiwa jikina ruwan zafi, saboda sanyin da na shaƙa a firinji ai yanzu na huta duk da sai cewa ruwan zafinsa ya wuce misali, oh duniya shi yasa ake cewa idan za ka gina ramin mugunta ginashi gajere gudun kar ka afka wata rana, gashi dai Imirana bai dahu ba ni na kusa dafewa lugugu ma ba luguf ba” Ta faɗa idanunta kafe a tsakar gisdan tana leƙawa dan ganin ƙwaƙwaf.

Shek da ganin miciji ya nufi lungun nan bai san lokacin da wani ƙarfi ya zo masa ba, da mugun gudu ya nufi bishi wani tsalle ya yi sai gashi ya ɗane bishiyar lokaci guda kamar wani biri, wani reshe ya samu ya hau ya zauna ya kama ya riƙe ƙam. Yana a saman nan, Sadiya da zuwa lokacin kawai ta daina kuka tana daga inda take tana ganin iko da ƙudurar da ta sauka a gidanta, micijin kuma yana dawo wa daga lungun sai ya daina gudu yake tafiya a hankali a hankali yana zuwa tsakiyar gidan sai kawai ya yi lifet kamar ya mutu, idanunsa ma a rufe ruf. A hankali Sadiya ta nufi wurinsa cikin sanyin jiki ta sanya hannu ta ɗan taɓa shi amma ko motsi bai yi ba.

“Shikenan ke ma Allah ya yanke miki wahala ɗiyar nan Hassan ya mutu kowa ya huta Husainin kaɗai ma ya isheki” Cewar Inna cikin sanyin murya tana tahowa wajen.

“Inna da ransa fa bai mutu ba da alama gajiya ya yi ko kuma bacci ne ya ɗauke shi.
” Cewar Sadiya tana kallon micijin da tausayawa a gefe ɗaya kuma tana haushi da zafin maganar da Inna ta faɗa na cewar Hassan ya mutu.Taɓe baki Inna ta yi tana wani kallon Hassan ɗin da ke kwance kamar babu rai a tare da shi.

Shek da ke maƙale saman bishiya ya musu ƙuri da ido, duk abin da suje a kan idonsa, ganin dai micijin kwance magashiyan sai ya fara tunanin durƙowa daga sama domin ya gudu. Ƙasa ya kalla daga saman bishiyar wani uban zurfi ya gani daga saman zuwa ƙasa.

“Allah da iko ashe dai wurin haka yake da zurfi amma lokaci guda na haye saman nan ko dan a tsorace nake” Ya faɗa yana jinjina irin namijin ƙoƙarin da ya yi wajen hawa bishiyar.

“Duk da haka dai sai na durƙo na gudu ya faɗa yana seta inda zai faɗo, aikuwa wara Bismillah da ya yi sai ji kake tik ya faɗo, a tsugunne ya faɗo, dan haka ko kallon su Inna da ke wajen micijin bai yi ba da Imran da shi ma yake tsaye ya kama tsantsa a wajen. A 360 Shek ya busawa rigarsa iska.

“Yaka liman zo karɓi yajin gayyata ka kaiwa matarka” Cewar Inna tana dariyar ganin yadda ya sanya gabansa hanyar ƙofar gida a guje ko waiwaye ba ya yi.

“La shakka laisal mushkila ku riƙe abinku” Cewar Shek lokacin da ya je ga ganshi ya buɗe ƙofar gida, shi ne ya ɓuga amsar da ya baiwa Inna.

Ƙo ƙofar bai rufe musu ba yana fita ya rinƙa zabga gudu kamar an biyo shi, mutane a hanya wanda basu san shi ba sai kallon mahaukaci suke masa waɗanda suka san shi kuwa sai kallon ba lafiya ba suke masa, a haka dai ya ƙaraso ƙofar gidansa yana haki. Wani uban bugu ya yiwa ƙofar gidan sai da ƙofar ta bugu da jikin bango, Barira da ke zaune tana tankaɗe garin tuwo jin buga ƙofar da aka yi a bango sai ta tsorata, bata tantance ba sai ganin Shek ta yi ya shigo jallabiya tattare a hannunsa ga hiraminsa ɗaure a ƙugunsa ko takalmi babu a ƙafarsa.

Ta san ba abu bane ƙarami kuma ba wani abu ne me sauƙi zai sa Shek wannan gudun famfalaƙin, tunaninta sai ya bata ko dai wani aka harba ko kuma bomb aka saka a wani wurin, ai tana ganin ya nufi ɗaki da gudu ita ma ta suri robar da take tankaɗe da kuma rariya a ciki dan ta san garin nan shi kaɗai garesu idan ya salwanta sai dai su kwana da yunwa. Tana shigowa falon nasu ta garƙame ƙofa ganin Shek ba ya falon sai ta bishi bedroom ɗin, a can ma sai sa ta sanya mukulli ta kulle ƙofar sannan ta ajiye garin da ke cikin roba ta kalli Shek da ya yi zaman ƴan bori a tsakar ɗaki, wata dariya ce ta ƙwace mata gani yadda farar jallabiyarsa ta jiƙe ga kuma ƙasa a jiki sannan kuma ga tumurin hirami a ƙugunsa sannan bakinsa sai mismis yake. Sai da ta yi dariyarta son ranta sannan ta kalleshi ganin ko kulata bai yi ba ta ce.

“Ya Shak wai duk wannan gudun bomb ɗin ne kamar wanda ke gudu ranar ƙiyama, ashe dai ku ma Malamai kuna tsoron mutuwa?”

Saurin wayancewa ya yi tare da ƙoƙarin seta kansa ya ce.

“Ba haka bane Barira, wato ainihin komai muƙaddari ne amma mutuwa ai dole ce in kin ga ana irin wannan wahala ake gudu bi ma’ana ceton rai kena” Ya faɗa cikin maganar Ustazai.

“Allahu akbar Kabiran, ni wallahi na ɗauka ma wani ne ya ɗora maka bakin bindiga a kan ka” Ta faɗa tana kallonsa.

“To kusan hakan ne, ko ma fiye da haka, wallahi arangama muka yi da zulƙululu”

“Me ye kuma zulƙululu?” Ta tambaya cikin rashin fahimta.

“Miciji” Ya faɗa yana kwashe komai ya faɗa mata. Dariya take tun ƙarfinta har da hawaye.

“Yo Ya Shek ai dama na faɗa maka amma ka ca wai zancenmu ne na mata wai mu mata mun saba gutsuri tsoma da yaɗa jita-jita, yanzu kuma ai idanunka sun gani”

“Ki bari kawai Barira ai yau na yi mugun gamon da zai daɗe yana zaune daram a ƙwalƙwalwata, ni dai ko hanyar gidan Imran na daina bi”

“Kai da abokin ka”

“An bar abotar, ko fitsarin da na yiwa jallabiyar nan ya fi a ƙirga, ita kanta na san sai ta ce Shek da fitsari a jikina kuma, carbina ma a can na barshi, ko dan wa ma yake ta carbi ana ta kai wa yake ta kaya” Ya faɗa yana since ƙullin hiramin ya fitar da takalmansa na dai suka sha dariyarsu, ya yi wanka ya canja kayansa.

A can gidan Imran kuwa Imran yana ganin Sadiya ta ɗauki micijin da sauri ya yi ɗaki dan shi abin ya wuce tunaninsa. Yana shiga bedroom ua nufi wardrobe ɗinsa zai canja kaya, yana buɗewa Mama da ke can ciki ta tsorata tare da maƙurewa a can ciki, Imran da bai lura da ita ba ya miƙa hannu zai ɗakko riga sai ya ɗora hannunsa a kan ƙafar Mama da sauri ta janye ƙafar tana zazzare ido, jin ya taɓa mutum ya miƙa kansa ya leƙo ciki aikuwa suka yi ido biyu da Mama, tuna abin da ya faru tsakaninsu ɗazunya sanya ya ji kunya, Mama ma kunyar ce ta rufe ta, cikin ƴar murya ta ce .

“Ashe Imran ne” Ta faɗa tana jin kunyarsa bayan abin da ya faru ɗazu yanzu kuma ya kamata a cikin lokarsa.

“Mama micijin nan fa ya yi bacci” Ya faɗa, jin hakan sai Mama ta ce.

“To, to, to” Ta faɗa tana zuro ƙafarta ta fito daga drower wata muguwar kunyar Imran na kama ta.

Hajiya da ke ƙasan gado jin Imran ya ce miciji ya yi bacci sai ta ɗan yunƙura za ta tashi amma ta ji ba hali.

“Imran, Imran, Imran” Ta shiga kiran ɗan nata.
Imran jin muryar Hajiya a ƙasan gado cikin sauri ya durƙusa ya kamo hannunta, jin ta maƙale a take ya, ya ɗage katifar ya fito da ita yana mata sannu.

“Kai yau mun ga ta kan mu, ko ma in ce na ga ta kaina, wallahi cinnaku ne a ƙasan gadon nan haka suka rinƙa safa da marwa a jikina babu yadda na iya, cizo kamar wani ƙudan cizo haka nake ji idan suka manne a jikin fatata” Ta faɗa kamar za ta yi kuka, sannun dai Imran ya cigaba da mata, ana haka sai ga Inna ta shigo, ganin Hajiya na karkaɗe jiki tana faɗar zaman uƙubar da ta yi a ƙasan gado sai ta shiga dariya, kowa kallonta yake da mamaki ta ce.

“Yo ni dama kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha kuma sata a gidan ɓarawo wallahi rance ce, ba ni ka yi ta yiwa dariya ba ranar da na ƙarasa kwana a ƙasan gado ba yau na rama a kan uwaka dama ai ɗan kuka shi ke jawa uwarsa jifa” Cewar Inna tana dariya.

“Yau dai an yi kwaɗo, sirika a lokar siriki, hallaw sirika a ƙasan gadon sirika kuma duk jika ne ya haddasa hakan, sannu Amina, sannu Rakiya” Inna ta faɗa tana dariya. Babu wanda ya tanka ta dan su burinsu ma su bar gidan kawai.Haka suka fito suka bar Imran da ke shirin canja kaya, sai da ya canja ya fito daga ɗakin, sannan me ƙunshi ta buɗe kayan wankin da ke jibge a kanta ta fito. Tana fitowa ta zo za ta fita daga ɗakin kamar an ce ta duba mudubi ta hango wani baƙin aljani baƙiƙƙirin da shi ƙirji ta dafe tana ambaton Allah sai da ta yi gaba za ta fice daga ɗakin sai ta gane ashe ita ce, kawai baƙin lallan ya mayar da ita haka. Fuskarta ta tsaya ta ƙarewa kallo sai kawai ta rushe da kuka, a haka ta fito lokacin ƴan matan nan har sun fito daga maɓoyarsu sun tafi, sai Ashrof kaɗai, da kuka ta fito falon kowa yana kallonta Imran takaici ne yasa ya ɗauke kai Inna kuwa dariya kawai take tana cewa.

“Gobe ma ki ƙara yiwa tsoffi haka, ita ma yarinyar nan me ƙananun nono ta tafi wai ita nan mace ce ƙirji babu komai yo irinsu ne idan suka tarki saka rigar nono za ki ga rigar nonon da ban ƙirjin da ban”
Ba abin da ta ce a haka ta sanya mayafinta ta naɗe kamar niƙaf duk da haka ana iya ganinta amma hakan ya ɗan suturta ta dan idan bata rufe ba ta san duk inda ta fita gudunta za a ke.

Imran ɗaki ya koma ya ɗakko kayansa cikin jaka, ya fito. Mama da Ashrof sun tafi dan yau babu damar yin girki ko wani abu da gabaɗaya Ashrof a ruɗe take har lokacin tana zabura. Hajiya da ke yiwa Sadiya sallama ta kalli Imran da ya fito riƙi-riƙi da jaka. Kowa da mamaki yake kallonsa Hajiya ce ta yi ƙarfin halin cewa.

“Ina zaka da kaya haka Imran?”

“Tare za mu tafi”

“Tare za ku tafi da wa?”

“Da ke”

“Ina?”

“Gida mana , kawai tafiya zan yi can in zauna a tsohon ɗakina tun da ga Inna nan ta zo ZAMAN WANKA in ya so ta zauna ma har Sadiya ta yaye yaran” Ya faɗa yana sunkuyar da kai, dan kunyar Sadiya yake ji sun haifi ɗan amma yana so ya gudu, shi kuma har ga Allah so yake ya tafi dan ya gaji da darun gidan kuma dai ya ga alama Hassan ya ƙi dawo wa mutum.

” Ikon Allah wai na kwance ya faɗi, Taɓɗiiii, ashe kuwa za a yita a gidan nan, wane shegen ne zai zauna bayan kai ma uban micijin gudunsa kake, wato ga Inna kuka me daɗin hawa, wacce take so ta bar duniya a kwana kusa sai in zauna in maka ZAMAN WANKA, yo ai abin ma ya wuce ZAMAN WANKA ya koma reno wai har a yaye su in ya so idan micijin ma ya sareni baka da asara iyakarta idan na mutu a ZAMAN MAKOKI ka ce Allah jiƙan Inna, ana karɓar sadaka kana afa shinkafa kana kora lemo, haɗe da kunun zaƙi, to wallahi baka isa ba ko tsinke naka ba zai fita daga gidan nan ba” Cewar Inna da ta tashi ta kama tsantsa ta wani haƙiƙice ta rufe ido tana sababi..

09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*

*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400

Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375

 

Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

 

Check Also
Close
Back to top button