Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 14

Sponsored Links

A wurin Inna ta baro su ta dawo gida riƙe da ledar, tana shigowa ta ajiye ledar ta nufi kujerar da Abdallah ya zauna ta danna da hannunta, ta ƙara taɓa inda matarsa ma ta zauna ta taɓe baki ta ce.

“Halima kin ga abin da nake faɗa miki ko? Da kin ce mutanen nan su zauna a ƙasa dan wallahi baki ji yadda kujerar ta faɗa ba gabaɗaya ta lotse dan ji na yi har katako da ƙarfen ciki ina taɓowa musamman wacce Sojojo ya zauna, dai dai ma an yi ba bashi sun kawo kaya masu tsadar gaske” Ta faɗa tana taɓe baki ta zauna a ƙasa ta shiga fito da kayan jariran na cikin ledar kaya ne masu kyau da tsada har da turmin atamfa.

“Kai, kai, kai, taɓɗi ashe dai Sojojo an iya abin arziƙi, to Allah amfana” Har lokacin Sadiya bata ce mata komai ba dan ita yanzu abin Inna yana ɗaure mata kai sosai ta gaji ma da wannan ZAMAN WANKAN gabaki ɗaya.

“Yo ko ki yi magana ko ki ƙyale, duk ɗaya dan kin ga wannan kayan da suka lodo miki kamar bashi yake dan kin ga matarsa ma tsohon ciki gareta dole idan ta haihu ke ma ki ki mata” A dai dai nan Imran da ransa ke ɓace ya shigo da sallama ciki-ciki.Amsa masa Sadiya ta yi.

“Imirana ka ga abin arziƙin da Sojojo ya kawo maka, kaima dai Imirana wallahi da karambani kake, banda karambanin akuya mai sa ta leƙa ɗakin kura, ina kai ina wannan mutumin him guda dashi, yanzu a ce ka rasa aboki sai wannan rungujejen abu kamar himilin kaya ina abokin ka Abida tun ranar da ya kawo mu shiru kake ji wai malam ya ci shirwa, amma wannan Sojojon da kuka jeru sai na gan ka abu ɗul kamar ruwan aski.

Banza ya mata ya shige bedroom dan daga Inna har Sadiyar ma haushinsu yake ji.

“Aniyarka ta bika Imirana in ƴaƴan naka kake yiwa baƙinciki dan an kawo musu kaya, wato so ka yi kuɗi ya bayar ka yi wuf da su ko?, gashi ma har yau babu sadakin gado babu dalilinsa, ka murtsuke ƴar mutane ka mata ciki ta haifa maka ƴaƴa har biyu amma har yau babu ragunan suna ga lokaci na ta tafiya, sai dai ka kawo wani ɗan nama a ƴar baƙar leda wai na me jego ne, yo wane irin me jego kawai a kawo tirkakkun raguna, ah to mun gaji da gafara sa bamu ga ƙaho ba, dan ba dani ba gaɗa a kabari in ji ƴan magana”

Babu wanda ya ce komai shi ya shige ɗaki ya kwanta yana ta jiyo Inna yana kuma tunanin abin da zai mata.

“Oh ni Ashrofa sai ka ce an aiki bawa garinsu, daga cewa za ta je gidan su ƙawarta ta dawo amma har yanzu bata dawo ba”

“Me za ta miki to idan ta dawo ɗin?”

“Haba Halima har na rasa abin da za ta min yunwa nake ji”

“To ki zubo abincin mana”

“A’a ni ba shinkafa zan ci ba so nake ta dawo ta dafa mini indo momi (indomie) Taliyar yara akwai daɗi wallahi”

Kallonta kawai Sadiya ta yi bata ce komai ba.

~DARE~

Tun da ya kwanta yake juyi a katifar, ji yake kamar ya je ya iyo waje da Inna daga ɗakin nan ya kulle, dan gabaɗaya yau ba ya jin jikinsa dai dai. Zaune yake ya zabga uban tagumi mararsa sai murɗa masa take tana neman ɗauki, haka ya dafe marar yana yin salatin annabi S.A.W Ya daɗe a haka zuwa can ya tashi ya leƙa bedroom ɗin fitilar a kashe sai dai ɗakin ba duhu sosai da yake hasken farin wata ya ɗan shigo ta gefen labule. Ba ka jin komai sai ƙaran komai a ɗakin dan Inna ko munsharin ma bata yi, hakan ya sanya ya ɗan fara lalume har ya ƙarasa wajen gadon tsaye yake yana ta nazari so yake ya gano wacce ce Inna wacce ce Sadiya dan ya lura yanzu kowacce tana iya ɗaukan bargon kowacce ta rufa haka zalika suna iya canjin wurin kwanciya saɓanin da kowacce na kwanciya a gefen da take kwanciya.Kan gadon ya hau sai da ya zauna a tsakaninsu ɗare-ɗare so yake ya gane matarsa ya shiga bargonta ya kwanta a kusa da ita ko ya samarwa kansa nutsuwa, kunne ya kai ya kara a saitin bargunan dan ya tantance na Sadiya dan gabaɗaya kowacce ta rufa ne har kanta.

Kunne ya miƙa jikin bargon Sadiya dan ya tantance ita ɗince a ciki ko kuma Inna ce a ciki. Garin kara kunne sai ya ɗan zame hannunsa ya buge na cikin bargon ashe dai Inna ce a ciki, wani uban juyi da ta yi da miƙa shi ya sanya Imran tsorata dan ya ɗauka zaune za ta tashi, idan kuwa ta gan shi a kan gadon a tsakiyarsu tabbas za a kwashi daru, da sauri ya yi wata shala sai gashi a gefen gadon wurin inda akwatuna suke, durƙusawa ya yi yana kiran sunayen Allah. Jin shiru babu motsinta sai ya ɗago kai a hankali ganin ta cigaba da barcinta sai ya lallaɓa ya fito daga ɗakin da rarrafe dan ba ya so ma ya tashi tsaye ta ji motsinsa a samu matsala.

Haka ya dawo falon wani haushi da takaici na damunsa, ga mararsa da har lokacin bata daina ciwo ba, fitilar falon ya kunna ya fita domin zuwa kicin.

“Kai da matarka halalinka amma kake raɓewa in za ka wajenta kamar wani kwarto” Cewar Imran a zuciyarsa, yana nufar kicin ya ɗakko jar kanwa ya jiƙa ya sha dan ya rage sha’awar da ke damunsa haka ya dawo ya kwanta yana jin ɓacin rai fal ransa, ya so ya shiryawa Inna wani abun cikin daren nan amma rashin nutsuwa da kuzari ba za su barshi ba haka ya haƙura ya kwanta yana cewa “In kere na yawo zabo na yawo wata rana za a haɗu.

*WASHE GARI*

Kamar kullum yau ma haka Inna ta haɗa ruwa sai dai cikin ikon Allah har ta wanki Hassan ta gama amma bai sawaya ba, haka ta shirya su tsaf.

*DA YAMMA*

Suna zaune a falo Ashrof, Sadiya da kuma Inna Imran ya fita ba ya nan, sallama ake yi a Ashrof ta amsa da ta leƙa sai ta ga Abid ne.

“Ya Abid ina wuni” Lafiya ƙalaw Ashrof ya mama ina Hajiya Inna?”

“Mama tana gida Inna kuma tana ciki in nemanta kake”

“Kamar kuwa kin sani saboda ita na zo, ki ce tana nan ana shan ZAMAN WANKA”

“Eh” Cewar Ashrof tana ƴar dariya.

Tare suka shigo Inna na ganin Abid ta fara murna tana cewa

“Lale da Abida sannu da zuwa”

Shi ma dariyar ya yi ya zauna yana gaishe da Inna suka gaisa da Sadiyar.Ya tambayi kwanan yaran nan aka bashi amsa da lafiya ƙalaw.

“Wallahi abubuwa ne suka ɗan sha kaina ban samu na dawo ba, na ga yaran ba”

“To wane gani kuma kai da muka dawo da kai daga asibiti da su” Cewar Sadiya tana ɗan murmushi.

“Haba Sadiya ke me yasa kike haka ne ni wai, ai in kin ji an ce za a ga mutum ba wai gani na ido ba ake nufi. Baki ga ƴan siyasa ba ko masu kuɗi idan ƴan maula suka je wurinsu sai su ce zan ganka zuwa gobe, to ai suna nufin za su sallami mutum da wani abun shi ne hausar” Cewar Inna tana kallon Sadiya, Sadiya kwa da Ashrof kunya ce ta rufe su ai hakan kamar roƙo ne. Wani yatsina fuska Sadiya ta yi take yiwa Inna kallon irin me yasa haka.

“Kai ka ji ni da mata, yo sai ka ce wani wanda na yi saɓo, kawai dan yarinta ta sa kun kasa gane inda maganar Abida ta dosa na warware muku zare da abawa sai ki rinƙa zare min ido kamar dai ke ce uwata mai daddawa”

“Rabu da ita Inna ai gaskiya kika faɗa kuma ni ma dama irin ganin da na zo na musu kenan” Cewar Abid yana dariyar maganganun Inna sosai ya so ya dawo amm abubuwa suka masa yawa amma da tuni ya dawo ko dan ya ci dariya.Ya kuma ga irin zaman da ake tsakaninta da abokin nasa dan Imran ya ƙi bashi labarin komai kuma ya san tabbas akwai wata a ƙasa dan babu yadda za a yi a zauna lafiya tsakanin Imran da Inna.

“Ga wannan Inna naki ne wannan kuma na jarirai” Ya faɗa yana miƙa mata manyan ledoji guda biyu, ɗaya kayan jarirai ne da less mai shegen kyau na Sadiya, sai kuma ɗayar atamfa ce da goron cikin farar leda.

“Ayyiriri, taɓɗi yau ake yinta ai shi sa jiya nake tambayarka a wajen Imirana , nagode Allah saka da alkairi, ya buɗa maka, wallahi Abida ka fiye min Imirana sau dubu ka ga Imirana ko goron murtala (Ashirin) Bai taɓa siyo wa ya kawo min ba bare turmin zane” Cewar Inna tana sakin goɗa tana ɗaɗɗaga atamfar.

“La ba komai Inna in ba a kyautatawa tsofaffi ba wa za a yiwa”

“Kai dai da ka san hakan amma Imirana mai ya sani yaron nan banda ƙafafa da nuna shi mai gida ne”

“Imran ko Inna”

“Shi mana, bari ma na baka labarinsa, amma sai na fara baka daga farko ranar da na kwana ban yi bacci ba”

“Baki yi bacci ba fa Inna, garin yaya?”

“Wallahi fa Abida, haka kawai ban ji ba ban gani ba,ina ranar da ka kawo mu daga asibiti har nake baka labarin abokin Imirana wanda ke wasarere da jikinsa”

“Eh Inna na tuna”

“To wallahi a ranar nan ni na san irin kwanan da na yi a gidan nan” Ta faɗa tana share ƙwallah.

“Subhanallahi Inna ba dai a waje kika kwana ba da sanyin nan?”

“Haba Abida ana ga yaƙi kana ga ƙura yo ba gwara a saka ni a randa ba in kwana da irin kwanan da na yi ranar nan kai ni dai sai da na ji ina ma ban taho ZAMAN WANKAN nan ba, ni da na kwana a tsakanin katako sama katako ya tokare ƙasana katako ”

“Katako kuma Inna”

“Yo a ƙarƙashin gado fa na kwana, bayan nna nawa da gado ya matse yadda ka san an yiwa mota lodin shanu haka na ji, wallahi ba dan na shafa man zafi ba da Allah kaɗai ya san me zai faru.

” Ta faɗa tana ɓantarar goron da fa ɗauka daga cikin wanda aka kawo mata ta ƙulle ledar.

“Garin yaya?”

Shiru ta ɗan yi dan bata son faɗar gaskiyar dalilin da ya sa ta kwana a ƙasan gado dan har yau bata daina jin tsoron aljanin ba kuma har yau tana ganin kamar dai yana kallonta a gidan.

“Sanyin garin nan ya sa na kwana a ƙasan gado” Ta faɗa tana ƙara gutsurar goro fuskarta ɗauke da damuwa.

“Sanyi fa Inna, lallai sanyi bai kyauta ba” Ya faɗa yana dariya dan ya fuskanci bata faɗi gaskiyar abin da ya sa ta kwana a ƙasan gadon ba dan daga yadda ta faɗa ya san ta faɗa ne kawai, ga kuma
yadda take bada labarin ma kaɗai abin dariya ne.

“Sanyi mana, ai ba fa shi ne abin da na fuskanta ba kaɗai, ka san Hassan ya zo da baiwa a jikinsa wato haka kawai sai yaro ya ringa saɓaɓa-saɓa ya bar ainihin halittarsa ya koma ta miciji”

“Miciji Inna” Ya faɗa da yana son tabbatarwa dan ya san dai Imran ya xe fatar bayan yaron ta miciji ce.

“Miciji mana, ai a washe gari da haihuwarsa ya koma miciji da kan mutum amma saboda rashin imani na Imirana haka ya garƙameni da micijin nan a ɗaki tun ina neman ɗauki har na gaji, ya sanya na rinƙa karanta alif an baki waw zal, kai daga ƙarshe dai sai ga Azumi a saman drower na hau can tsililiko ina reto”

Dariya kawai yake, da jin labarin ya san dama tabbas a rina wai an saci zanin mahaukaciya dan ba za a ƙarƙe ƙalaw ba da Inna da Imran saboda basa jituwa.

.

“Lallai Inna kin yi ƙoƙari” Ya faɗa had lokacin ya kasa tsaida dariyarsa, Ashrof ma sai tayashi take duk da Sadiya ta bata labari amma sai ta ji kamar yanzu ne ake farkon jin labarin.

“Kai Abida baka cin ribar zance ne, ka tsaya ka ji yadda ta kaya mana tsakanin ni da Imirana ai bai fa ci bulus ba, mutuminka na sanya Sadiya ta ƙwala masa kira lokacin ya sha dariyarsa ya more, a raina na ce bakin dariya shi ne na kuka, ai yana shiga ɗakin na shammacesa a janyo Halima muka fito na bankeshi a ɗakin, kira yake Inna ki buɗe dan Allah, aikuwa na yi kunne uwar shegu na ce sai na rama sai da ya horu sosai a ɗakin na buɗe, ka san ya na ga Imirana” Ta faɗa tana dariya, su ma dariyar suke har Sadiya da ta kasa riƙe tata dariyar, hakan ya sanya Imran ya shigo yana ta sallama basu ji ba da yake bai wani ɓuga maganar ba dama jikinsa ya bashi ana cin namansa a gidan tun da ya ga motar Abid a waje ya san Inna tana nan tana bada labarinsa.

“Yana laɓe a jikin bango yadda ka san ƙadangare ya rakuɓe a waje ɗaya sai maƙyarƙyata yake kamar kazar da bazai ya kamata” Ai gabaɗaya suka ɗauki dariya har Inna a dai dai nan Imran ya shigo falon sai haɗe rai yake kamar zai kai musu duka.Ɗif suka daina dariyar sai Abid da ke ƙoƙarin danne dariyar taƙi tsayawa har ruwa idanunsa suka kawo saboda dariya sosai yake hango yadda abokin nasa ya yi, a rakuɓe a ɗakin ga kuma miciji a gefe, tsaf Inna ta iya bada labari yadda mai sauraro zai ji kamar a gabansa ake yi.

“Abokina ka dawo? Ka ganni kamar an jefoni daga sama ko ban maka waya ba” Cewar Abid yana goge ƙwallar idonsa da dariya ta sa ta taru. Wani mugun kallo Imran ya masa wanda ya sanya wata dariya ta ƙwacewa Abid aikuwa ya sakikayarsa dan ya kasa riƙeta.

“Ai abin akwai abin dariya Abida dan ma ba a gabanka aka yi ba” Inna ta faɗa tana dariyar dan ganin Imran ma sai ta sake ƙara ƙarfin dariyarta dan ta ƙular dashi tun da shi bai san abin arziƙi ba.

“Yo da kana siyo min ɗan goro da turmin zane, ai da na ɗan rangwanta maka ka san zuciya tana son a kyautata mata” Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma ta ce.

“Kallai abin arziƙin da abokinka ya kawo min, wancan na gaban Asharofa kuma ya ƴaƴanka ne da matarka”

“Ta faɗa tana kallon Imran da ke ƙoƙarin ajiye ledojin da ya shigo da su.

“An gode” Kawai ya ce tare da juyawa zai fita.

“Amma kuwa yau nan tabbatar ta mugun halin ka Imirana ace a kawo wannan uban kayan kuɗi amma ka yi godiya ƴar mitsitsiya, ina laifin ma ka ce an gode madalla Allah amfana Allah saka da alkairi ya bar zumunci, ka ƙara da cewa kai amma kayan sun yi kyau sosai har da Inna ma aka kawo wa to madalla, amma dan baƙinciki kake min kuma da baƙin halinka Imirana shi ne ka ce an gode a takaice” Cewar Inna tana gatsinen gefen hanci.

“Haba Inna ai tsakaninmu ba godiya” Cewar Abid a fili yana ƙara maƙe dariyarsa. A zuciyarsa kuma ya ce na tabbata Imran ya ji Inna tana bada labari amma babu yadda zai yi da ita, kuma gashi magana take faɗa masa a kan ƙin doguwar godiya kuma ba yadda zai yi da ita lallai Inna ita ce maganin Imran.

“Ka ji ɗan arziƙi irin albarka, wallahi kana birgeni Abida…

“Idan ka gama neman maganar ka same ni a waje” Imran ya katsewa Inna maganarta yana kallon Abid tare da ficewa cikin ɓacin rai.

“To ina fitowa ” Cewar Abid yana bin bayan Imran da kallo dariya na cinsa.

“Kai rabu da shi yana ta ƙuncin rai ka yi zamanka a nan mu sha hira in maka abin ban faɗa maka ba” Cewar Inna tana kallon Abid.

“To Inna”

“Ashrof miƙa masa yaran ya gan su” Sadiya ta faɗa cikin sanyin murya dan yadda ta ga Imran na harararta da ya shigo hakan ya sanya ta gane bata kyauta ba da aka zauna da ita ana bada labarinsa suna dariya.

“Lah ta barsu ma tun da bacci suke kar a tashe su, ai ni nan tunda gidan zuwa na ne na gansu wata rana”

“Kana ji ko Abida jiya kurman abokin nan naka ya kawo abokinsa Sojojo”

“Inna meye kuma Sojojo ko suna ne?”

“Ina kai ka, baka cin ribar zance”

“To ina jinki Inna”

“Nake faɗa maka Sojojo ne dan bana kirashi Soja ba saboda ragwantarsa”

“Ragwanta kuma Inna”

“I mana” Inna ta faɗa tana kwashe duk yadda aka yi da Abdallah da ya zo barka da matarsa.

“Inna haka aka yi ashe haɗe su kika yi, kai abokina ba dama” Ya faɗa yana dariya

“Kai dai bari yo shi ma Imiranan ranar nan fa suma ya yi saboda Hassan ya sawaya ya zama miciji a jikinsa” Ta faɗa tana dariya. Haka suka sha ta dariyarsu har cikin Abid yana ƙullewa dan ya ma manta Imran na jiransa a waje. Sai can ua tuna ya musu sallama ya sanya hannu a aljihu ya ɗakko dubu ɗaya ya miƙawa Inna. Hannu ta sanya ta karɓa tana washe baki.

“Haba Abid ai da ka barshi hidimar ai ta yi yawa ” Cewar Sadiya cikin jin nauyin Abid.

“Lah ba kamai ai…

“Rabu da ita kawai in banda baƙinciki meye wata dubu ɗaya dan ya bani kyauta zaki wani haƙiƙice kina cewa ya yi hidima ai dama kowa ya san ya yi hidima musamman da ya fi mijinki da bai san ya siye zuciyar mutane da kyauta ba sai baƙin hali da na zuciya fal ransa” Ta faɗa tana sanya dubun a cikin ƴar pos ɗinta.

Dariya Abid ya yi jin abin da Inna ta ce haka kawai shi ds a ce za a barshi da Inna da ya huta d shiga damuwa ko ɓacin rai, saboda ita bakinta ba ya shiru kuma bata gajiya da abin dariya duk da ita tana yin komai dan raha ne.

“To Inna sai kwana biyu”

“Kwana biyu fa Abida sai ka ce an maka baki, yanzu sai ka iya kwana biyu baka zo mun gaisa ba, ai baka ji daɗin da na ji ba da ka bani bugun Abujar nan”

” To Inna idan na samu dama da lokaci zan ke leƙowa ”

“To nagaode sosai” Ta faɗa lokacin da ta fito har ƙofar falon Abid ya sanya takalminsa ya fita.

“Oh ɗan nan da kirki yake Sa’adiyya ya fi min mijinki Imirana sau miliyan ma” Cewar Inna lokacin da ta zauna a kan kujera tana ƙara ganin atamfarta.

“Inna dan Allah kike iya bakin ki idan abokan Imran sun zo kin ga ko a fuska ya nuna ba ya so kina shiga shirginsu” Cewar Sadiya cikin lallaɓawa dan ta san Inna hukuma ce sai da lallashi.

“Ikon Allah, lallai Halima wuyanki ya fara isa yanka sauran kuma a gwada wuƙa a tabbatar, yanzu sabibi da Allah ni kike faɗawa wannan maganar to ni da banda ma gaisawa da muke a ɗan taɓa hira ina ni ina su, ni fa kawai dan na ɗaukesu ɗaya da ku ne tamakar jikokina in ba haka ba me ma zai haɗa ni da su, in kuma baƙincikin ɗan abin da zan ke samu kike yi to duk da babu wanda ya taɓa bani wani abin arziƙi in ba Abida ba”

“Abid Inna” Cewar Ashrof.

“Ke ki kiyaye ni, in ma Abu zan kirashi ina ruwanki”

“Ki yi haƙuri Inna” Cewar Sadiya.

“Da haƙurin ta mutu sadakar nawa kika bani?”

“Allah baki haƙuri”

“Haƙuri kaya ne naɗa gammo ki ɗauka”

Bayan fitar Abid Inna ta ce ta gaji da zaman cikin gidan fita za ta yi ta zagaya ƙafadunta dan ciwo suke mata, gidan Hajiya Amina za ta je. Haka ta musu sallama ta fita ta sha wata atamfarta mae kyau, ta saka ɗan madinanta ta kama hanya ta fita, har Sadiya ta bata kuɗi ta hau ɗan sahu amma ta ƙi karɓa wai ita ta fi son tafiya a ƙasa saboda kalle -kalle.

Hanyar gidan Hajiya Amina ta kama, har sai da ta je gidan bayan ta gama kalle -kalle da ratse -ratse. Haka ta je gidan Hajiya Amina suka gaisa ta ɗan jima sai kuma ta kamo hanya ta taho gida dan Hajiyar ma sai da ta yi ta yi da ita a kan ta zauna idan aka yi sallar magariba ta yi sallar sai ta tafi, amma Inna fafur taƙi zama dan ta fi so ta taho ido na ganin ido. Saboda ta fi so ta taho ido na ganin ido dan ta ga gari gari ma ya gan ta.

dan haka ta kamo hanyarta ta taho riƙe da ledar da Hajiya Amina ta zuba mata bakilawa. Tana tafe tana kalle-kallenta tana ƴar waƙarta a hankali, tana cewa.

“Carman dudu carman duduwa , carmagade, akwai wani baƙo a gidan mai gari, carmagade, ba duka ba ya lakuci, carmagade, in duka wa zai bashi ne, carmagade, aradu ta Allah ba zan bashi ba” Tana cikin yin waƙar ne ta hango wani ƙerarran gida mai shegen kyau tun daga nesa gidan ya birgeta. Dan dama ba ta hanyar ta bi ba a tafiya yanzu kuma sai ta canja hanya dan ta sake ganin wasu sabbbin abubuwa ba irin wanda ta gani a tafiya ba.

“Ikon Allah masu gidan nan kuwa sun san ana wahalar kuɗi kuwa a duniya, an ya kuww sun san sunan wani abu wai babu, ace wannan gida kamar ba a duniya ba” Ta faɗa tana tsaye tana ƙarewa gidan kallo.

“Oh ni Azumi ina can a ƙauye ina fama da ɗaki ɗaya a gidan Malam kullum ana bala’i da Tasalla to ina kuma ga na ganni a gidan nan ina ga kuma sai an mana tsakani da Tasalla dan kar take faɗawa mutane ita kaɗai ce matar gidan” Ta faɗa tana ƙarasawa ƙofar tangamemen get ɗin da ke buɗe, sai da ta tabbatar babu kowa mai gadin ma ba ya nan…

Masu son a tallata musu hajarsu MMN AFRAH 09030283375
[24/03, 5:13 AM] Mom Mashkur First class: Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

Check Also
Close
Back to top button