Ikraam 44
By Khaleesat Haiydar 44…. Da daddare Ikram na xaune daki tana assignment dinta, momy kuma na wanka, seeyama ta shigo dakin daukar text buk dinta, Ikram tace “ni xan bi ki inda xa ki” Seeyama tayi murmushi tace “ae bbu inda xanje Ikram kallo muke a falo” Ikram ta mike da sauri tace “nima kallon xanyi” bata jira me Seeyama xata ce ba ta fice da sauri, seeyama ta bi bayanta ita ma da sauri tana dariya. Duk yan matan na xaune falo suna kallon Indian film, duk suka bi Ikram da kallo har ta karaso cikin falon seeyama na biye da ita a baya suka xauna, farida ta tabe baki ta ci gaba da kallonta, Ikram tayi shiru tana kallon film din da suke kallo can ta mike ta dauki remote din dake kan centre table ta canxa tashar xuwa Mbc3 tace “ni cartoon xan kalla” cikin tsawa Farida tace “keee kina da hankali kuwa” Murguda mata baki Ikram tayi tace “ehh” Saiham tace “wae wacce yarinya ce wnn 4 Godsake” seeyama ta karbe remote din tace “bari su gama kallonsu Ikram sae in sa maki cartoon din” Ikram ta murguda masu baki ta koma ta xauna kmr xata yi kuka, karfe takwas da rabi aka bude kofar gidan, duk suka juya suna kallon wanda xae shigo, Khaleel ne ya shigo gidan da sallamarsa, Ikram ta mike da sauri tayi gunsa da gudu ta rungumesa kmr xata yi kuka tace “yaya Khaleel ka xo ka tafi dani ne” durkusawa yyi yana kallonta ya gyara mata hannun rigarta yace “in kai ki ina?” ta bata fuska tace “gida mana” yyi murmushi yace “ae Mami bata dawo ba, ga banana nn na kawo maki da yawa ae” ta juya masa baya kmr xata yi kuka tace “ni bana so” mikewa yyi ya kamo hannunta yace “to naji xan tafi da ke. ina momy?” ta nuna masa sama, sae a snn ya lura da su seeyama dake xaune a falon, yyi murmushi ya daga masu hannu yace “Hi” duk suka yi dariya banda Farida. Cikin falon ya shiga suka gaisa da fara’arsa snn ya kama hannun ikram suka haura sama xuwa dakin Momy, kuka ssae Ikram ta shiga rerawa da Khaleel xae tafi, ya galla mata harara yace “to ni na kawo ki da xan mayar dake” cikin kuka tace “ni wllh sae na bika din” da kyar ya samu ya bar gidan tana ta rusa kuka, Momy tayi lallashin duniyar nn amma taki yin shiru kuma taki bin ta sama, kyaleta tayi ta koma sama abunta, Hajiya ta sakko cikin tsawa tace “ke dalla rufe ma mutane baki shegiya kawae, maxa wuce gun warce kika xo kar in kifa maki mari, ance maki nn gidan ubanki ne xaki dame mutane da ihu” Shiru Ikram tayi tana kallonta. Farida ta sauko ta dungureta a ka tace “maxa bar falon nn kar in maki duka, mayya kawae” seeyama ta haura sama da gudu taje ta kira mumy, Aliyu ne ya shigo falon da sallamarsa, Ikram tayi gunsa da gudu ta fasa ihu tana nuna masa Hajiya da farida tace “yayana kaga wa en can suna min ihu ko, shine wnn har ta turani na kusa faduwa” cikin tsawa yana kallon farida yace “uban me tayi maki don uwarki” Hajiya ta yo waje da ido tace “a ina ka santa Aliyu”
[2/25