Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 6

Sponsored Links

©️ *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*GARIN DAƊI……..!*

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

*Wattpad:ummishatu*

 

*6*

 

~~~Tagumi kawai ta rafka tana kallona batare da ta furta ko kalma ɗaya ba har sai da na gama bata labarin komai sannan ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ta janye tagumin da tayi ta kalleni fuskarta babu fara’a tace,

“maganar gaskiya widat banji daɗin wannan labarin naki ba sam….. Ta yaya za ki bari sheɗan yayi wasa da tunaninki, kinfa sani sarai cewar an yi miki miji sannan an bada ke, kin manta da maganar aurenku da yaya faisal ne? Wannan abun da kike yi kuskure ne kuma ya kamata ki farga, ko a shari’a babu kyau neman aure akan nema, tun wuri kiyi gaggawar fatattakar wannan mummunan lamarin tun kafin gida su sani nidai shine kawai shawararar da zan iya baki….. ”

” ƙawalli da alama har yanzu baki fahimce ni ba…. Wallahi Allah shine shaida dama ban taɓa jin son yaya faisal acikin raina ba kuma kema kin sani saboda nasha faɗa miki, to yanzu Allah ya haɗani da irin wanda nake so saboda ni dama na fi son na auri mutumin da ya kwanta min har cikin raina ba wai irin yaya faisal ba wanda daidai da rana ɗaya ban taɓa jin sonsa ba…. ”

Jin abin da na faɗa ya sanya Maryam zuba min idanuwanta gaba ɗaya tana kallona dan tama rasa abin da zata ce sai zuwa can tace dani,

” kiyi ta addu’a ƙawalli…. Dama idan aure yazo sometimes irin haka na faruwa, shaiɗan sai yayita ƙoƙarin shiga cikin lamarin dan ta wargaza komai yaga ba ayiba amma idan aka dage da addu’a sai kiga Allah ya daidaita komai….. Allah ya kyauta”

“amin ƙawalli na gode, bari naje gida dan kofa wanka banyiba na fito dan na zo na sanar dake…”

Tare muka rankaya zuwa gidan mu har wurin 8 muna tare sai lokacin na rakata ta tafi bayan ta yi min gargaɗin wai kar na kuskura na bari yaya faisal ko gida su fahimci maganar nan, da to kawai na bita domin maganar gaskiya yaya faisal ya jima da fara fahimtar akwai abin da ke faruwa ina jin wannan dalilinne ma yasa ya ɗan ja baya da kirana kuma da alama kamar fushi yayi dan yau kusan kwana shida kenan bai kirani a waya ba.

Zaune nake ina nazarin wani manual na na’ura mai ƙwaƙwalwa bayan nayi shirin bacci cikin riga da wando masu santsi light blue, jin ƙarar wayata ya sanya ni kallon agogon jikin wayar ƙarfe 11:30 na dare abin da yayi mutuƙar bani mamaki kenan saboda ganin kiran yaya faisal mutumin da ya shafe kusan wata bai nemeni ba nima ban nemeshi ba har yau ɗinnan da ya kirani, ɗagawa nayi ina son jin da wacce yazo, cikin taushin murya naji sallamarsa nan na amsa bayan na kishingiɗa na kuma rufe jibgegen littafin dake gabana,

“widat a haƙiƙanin gaskiya na kasa gane abin da yake faruwa… Gaba ɗaya kin sauya kuma kin canja daga yanda kike…. Dama da biyu kuma ina sane naƙi nemanki tsawon wannan lokacin saboda ina son gane gaskiyar abinda yake faruwa….. Widat meyasa kika daina so na? Nayi miki wani laifi ne ko kuma kinji wani mugun abu atare dani? ”

Shiru na ɗanyi har sai da ya kira sunana dan tabbatar da cewa shin har yanzu ina kan layinne ko ta yanke, ajiyar zuciya nayi sannan cikin sanyin murya nace,

” yaya faisal duk abubuwan nan da ka faɗa babu ko ɗaya aciki wanda ya faru, ni banji wani abu marar daɗi a kanka ba…. Kawai dai….” shiru nayi na kasa ƙarasawa hakan yasa shi faɗin,

“ina jinki, ki faɗi duk abin da ke ranki widat kar kiji shakka….. Kawai dai me?”

Nauyin kalmar naji shiyasa na kasa faɗa, tayaya zance masa bana sonsa tun asali?

“yaya faisal a gaskiya dama tun can baya ni akwai wanda nake so kuma har yanzu muna tare dashi”

Shiru naji shima yayi na tsawon wasu mintuna kafin ya saki ajiyar zuciya,

“idan na fahimceki dai dama bakya so na har na turo gidanku? Anyway shikenan zan yi musu bayani yanda zasu fahimta, amma ki sani ni ina son ki kuma naso na rayu dake, da kin san irin girman sonki acikin zuciya ta da irin tanadin da nayi miki na kyakkyawar kulawa da ƙauna wallahi widat da kin zaɓeni a matsayin miji amma babu matsala Allah ya cigaba da tabbatar mana da duk abin da yafi zama alkhairi, nagode saida safe…. ”

Ji nayi jikina yayi sanyi, sam banji daɗin yanayin da naji yaya faisal aciki ba wato yanayi na damuwa da ɓacin rai amma babu yadda na iya saboda nima zuciya ta na can wani wuri daban, daren ranar sai da na jima banyi bacci ba kafin bacci ɓarawo yayi nasarar ɗaukata.

Washe gari ina tsaka da bacci naji muryar Annie tana tashina, da mamaki fal cikin zuciya ta na tashi saboda a iya sanina dai yau weekend ne bare ko ince saboda fita aiki take tashina dan kar in makara,

“zo abbanku yana kiran ki….” daga haka ta juya ta fita daga cikin ɗakin, dogon hijabi na saka har ƙasa akan kayan baccina na fita idanuwa cike fal da bacci sakamakon rashin isasshen baccin da ban samu ba jiya,

Ina shiga falon Abba na hangi mama zaune da yaya Abdul hakim kusa da ita sai Annie itama zaune ɗan nesa da abba kaɗan, ganin irin yanda naga fuskokinsu ya tabbatar min da cewa ba ƙalau ba musamman ma yaya Abdul hakim dake ta faman aikin watso min harara kamar zai tashi ya bugeni,

“abba ina kwana, mama ina kwana….”

“lafiya lau maimunatu…..” abba ya amsa yana zare farin gilashin dake idanuwansa, sunkuyar da kaina ƙasa nayi saboda na fahimci ni mai laifi ce saboda yadda babu wanda ya amsa gaisuwa ta sai iya abba kaɗai, tunani na ya katse sakamakon maganar abba da naji,

” maimunatu yaya kuka yi da faisal….?” tambayar da tayi mutuƙar gigita tunani na da hankali na gaba ɗaya dan ban san irin amsar da ya dace in bawa abba ba a wannan lokaci,

“maimunatu…..” abba ya sake kiran sunana, “na’am abba”

“nace yaya kuka yi da faisal? Ina son ji”

Shirun dai na sake yi saboda ban san abin da zance ba,

“abba ai bata da gaskiya dan haka babu abin da zata iya cewa, wulaƙanci ne da ƙasƙanci ta gama yi wa faisal….. Ai ba zai yi mata ƙarya ba, duk abin da ya faɗa hakane….” yaya Abdul hakim yafaɗa cikin fushi da ɓacin rai,

“a’a ai akwai buƙatar muji daga bakin ta, gara ta faɗi koma menene da bakin ta”

“Mai shari’a babu batun aji daga bakin ta, mu muka haife ta ba ita ta haife mu ba, mu ne muke da iko da ita ba itace take da iko damu ba dan haka ya zama dole tayiwa dukkan dokar da muka shimfida biyayya, maganar auren ta da faisal ko tana so ko bata so sai an yi ta faƙat, idan kuwa bata amince ba to ta nemi wata uwar amma ba ni ba…. Nima ba ita kaɗai na haifa ba bare baƙin cikin ta yayi ajali na ” Annie ta faɗa cikin fushi ta tashi ta fita, hawaye ne suka shiga wanke min kumatu babu ƙaƙƙautawa take naji tsanar yaya faisal tsana mai tsanani domin ta dalilinsa gashi zan samu matsala da gidan mu a karo na farko cikin tarihin rayuwa ta, Karon farko da mahaifiyata tayi fushi dani tare da alwashin mummunan sakamako a gare ni, kifewa nayi awurin ina gunjin kuka wiwi.

Tsawar da yaya Abdul hakim ya daka min itace tayi sanadiyyar haɗiye kuka na,

“ke…. Idan baki yi wa mutane shiru ba sai na zo nayi ball dake, marar kunya, ana ganin ki kamar me hankali ashe ba haka bane…….”

Jin an ɗagoni yasanya ni ɗagowa ina kallon mama wadda ta riƙoni ta sani cikin jikin ta tana rarrashi, sai lokacin naji abba yayi gyaran murya alamar zai yi magana kuma maganar mai muhimmanci,

” maimunatu……. Kiyi haƙuri zan aura miki faisal wannan shine hukuncin da na yanke…..”

Jin abinda kunnuwa suka jiye min take na nemi jina da ganina na rasa na zama nidai gani nan ne dai kawai nakasa gane a wanne irin yanayi nake……….. ✍

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*

Back to top button