Hausa NovelsNi da Patient Dina Book 2

Ni da Patient Dina Book 2 Page 47

Sponsored Links

Duk abinda takeyi suna kallonta a madubin tsafi sun san yanzu zasu samu abinda sukeso tunda yar family sunsamu sun jawota cikin kungiyarsu bako wani kungiya bane wannan da yawuce vampires union, kungiya ce da suke shan jini da kuma cin naman mutane da dabbobi sunada matukar hadari Kuma sun bawa zeenat maita ne dan su rama abinda mommy ta aikata musu.

Taya akayi zeenat tazama daya daga cikin kungiyar vampires union, yau fitansu da safe ita da ya fawwaz and areef zasuje gidan anty amina daga nesa ta hango wata yarinya na tallan guiva setaji ya shiga ranta magana tayiwa fawwaz yatsayar da motar tasiya tafara sha acikine tasha maitar batare data sani ba .

Bayan sunzo gidan anty amina ne tafara jin wani irin sauyi ajikinta setaji kamar abu na mata tafiya hade da magana akunne. dakin su aslam da islam tashiga tadan kwanta ciwon Kai ne yafara damunta shisa dasu fawwaz sukace zasu tafi tace suje kawai ita se gobe zata dawo aikuwa tafiyar sukayi abinsu, anty amina data lura da yanayinta kamar bata da lafiya yasa ta tambayeta amma se kawai tace mata bakomai.

Around 10 duk sun kwanta ita kam takasa bacci wani azabebben yunwa ne yafara ciyota ,kitchen tashiga har lokacin ciwon Kai din besauka ba bude food flask din tayi dan ta dibi abinci toshe hanci tayi jin abincin namata wari kamshin danyen nama ne yadaki hancinta bin direction din da takejin kamshin tayi har izuwa fridge dauko namar tayi duka tana kallon shi , tunani” tafara taya zanci danyen nama ” jitayi andaka mata tsawa akunne cike da umarni taji murya nafadi ” ki tabbatar da kincinye naman nan ” tun kafin yagama magana tahau cin naman haka tacinye namar da yafi kilo goma , wani sabon yunwa tafaraji jitayi naman dataci yatayar mata da kwadayi kamar wata mahaukaciya haka ta birkita kitchen din tana neman nama amma babu daki takoma kamshin su aslam da islam ne yacika mata hanci shinshinasu tayi tana ajiyar zuciya tasamu nama hankali kwance bude baki tayi nan take dogayen hakwara suka fito , jitayi namar aslam yayi tauri sosai kamar dutse haka ma Islam duk yanda takai da son cinyesu to abin yagagara badan komai ba sedan adduah da mamansu da babansu sukeyi musu afusace ta tashi tabar dakin jikin bango ta shige fitowa tayi abakin titi kwance taga mutum da sauri ta karasa wajan ta farka cikinshi tafara cin naman dama su suka ajiye mata ganin abin yafara aiki ajikinta yasa sukayi murna sunada ya kinin se ta cinye yan gidansu kaff.

Washe gari.

“Mr azaad ! bansan meke faruwa ba amma yau natashi da faduwar gaba Allah shine masanin dede” cewar fanan dago Kai Mr azaad yayi yadan kalleta shikanshi inya tuna zata tafi seyaji wani irin aranshi amma babu yanda suka iya, kwantar da kanta yayi a cinyarshi sannan yace ” inkin ji faduwar gaba kidinga karanta innalillahi wainna ilaijiraji unnn in sha Allah ze dena, ” murmushi tayi ta sakeyin lamo ajikinshi , tunda sukayi breakfast suke zaune afalo yana duba wasu files, yaseer ne ya kirashi awaya ya sanar mai yana falon ummi okay kawai yace mishi kallon fanan yayi yace ” dauko hijab dinki muje falon ummi” tashi tayi dan ta dauko hijab din jikinta na sanye da Riga da skirt na kanti ,fitowa tayi tasamu ita yake jira rike hannunta yayi suka nufa falon ummi, duk suna zaune afalon banda abba da ya fita meetings ummi, yaseer, fawwaz,areef tsungunawa tayi ta gaidasu sannan ta zauna , yaseer ne kasa_kasa kamar wani munafiki yace ” dude two days kayi wuyan gani ina kashiga ” hararanshi Mr azaad yayi shida yadena nemanshi tun zuwan dayayi last harsuka so yin fada akan fanan amma yanzu yana ce mai ya buya , dariya yayi da yaga hararanshi kawai Mr azaad yayi bece mai komai ba , sallamar zeenat ne yasasu kallon bakin kofar tun kafin ta iso cike da tsokana yaseer yace ” yanzu haka ake bakunta zeenat daga zuwa kin kwana shine za ki dawo da sassafe kamar wacce aka koro ” turo baki tayi tace” ya yaseer kaiko ni nayi missing din ummina ne shisa na dawo ” itade ummi batace musu komai ba suna yar hira da fanan da gudu zeenat tafada jikin fanan tana rungumeta, ummi ne tace ” nikam zee kina da hankali kuwa karyata zakiyi” kafin takarasa maganar sukaga fanan tasa iya karfinta ta ture zeenat ajikinta seda ta kusa faduwa yaseer yariko ta dukkansu kallon mamaki suke binta dashi meye dalilin dazesa tayiwa zeenat haka ganin yanda suke shiri sosai kuma ko fada sukayi fanan bazata mata haka ba.
Tashi fanan tayi taje har gaban zeenat dake wur_wurga ido irin namasu rashin gaskiya bata taba tunanin fanan zata ganota ba .
Kamar wata tsohuwar mayya haka fanan take shinshina zeenat, Mr azaad dasu ummi sunzuba ido suna kallon ikon Allah,kallon cikin idon zeenat fanan tayi kafin tafara fadin ” zeenat meyasa kike Karnin jini?” Inda_inda zeenat tafarayi tarasa karyan dazata mata daka mata tsawa fanan tayi tana ” nace aina kika samo jini meye hadinki dashi karki bari in kara tambayarki zeenat” kansu yadaure sun rasa ina maganar fanan yadosa me take nufi da zeenat na karnin jini. Zazzare ido kawai zeenat takeyi can kuma tace ” ayyah anty fanan dazun ne dazan dawo daga gidan anty amina se naga motar ya bige wata yarinya karama shine naje na dauketa jikinta duk jini to kuma dole jikina nima yabaci da jini, nakaita asibiti to kinji dalili” ajiyar zuciya duka sukayi harta Mr azaad danshi kanshi yafara zargin wani abu saboda yasan haka kurum fanan bazatayi irin wannan maganar ba,domin ita ba kamar sauran mutane bace shisa ita kadai taji karnin jinin su basu ji ba , ko kadan fanan bawai ta yarda da abinda zeenat tafada bane kawai ta kalleta ne dan tasan tabbas akwai wani bakon lamari adangane da ita , wucewa part dinsu tayi tabarsu agun dan har tsakiyar kanta takejin karnin jinin na damunta kallon zeenat ummi tayi tace ” sekije kiyi wanka kinde ji abinda antyn ki tace ” okay ummi itama tashige bedroom dinta wata nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tasamu tasha da kyar da asirinta yatonu magana ta fara hawaye nabin fuskanta ” nashiga uku ni zeenat wannan wani irin mugun rayuwa na tsinci kaina bazeyu ba dole in fadawa anty fanan gaskiyar abinda ke faruwa nasan dole zata taimakamin” murya mara dadinji taji yana fadin ” karki kuskura ki aikata aikin da nasani domin yin hakan dede yake da salwantar da rayuwar ahalinki in kunne yaji jiki ya tsira sannan adaren yau ki tabbatar da kin cinye yaron hafsat ” cike da umarni ake mata magana babu abinda takeyi inbanda aikin girgiza kai.

 

Zaune suke a garden Mr azaad da yaseer , yaseer ne yake magana ” mutumina naga kamar yanzu kadan fara saukowa ” ajiye wayar da yake dannawa yayi sannan yace ” dude bansan meyake faruwa dani ba yanzu kwata_ kwata bana iya mata abinda nake mata da and the worst thing shine komai tayi burgeni yakeyi haka kawai nakeson kasancewa da ita I don’t know why” yaseer saboda farin ciki kamar yazuba ruwa akasa yasha haka yakeji yasan abokinshi yafada tarkon soyayya amma besani ba saboda be tabayin soyayya ba arayuwarshi yanzu bema san yana son fanan ba,” dude inna fada maka wani abu zaka yarda?” Ya tambayeshi yana kallonshi gyada masa kai Mr azaad yayi cigaba da magana yaseer yayi ” ka fara son fanan ne shisa ka kakejin wayan nan ba qin yanayin ” sosai Mr azaad yake kallonshi dan san gasgata abinda yafada gaskiya ne ko karya tayama shi yafada soyayya batare da yasani ba. sassauta murya yayi yace ” dude ba santa nakeyi ba kawai maybe kewanta nafara amma ka ajiye maganar soyayya agefe hakan baze faru ba” yar dariya yaseer yayi daya tuna wata magana da Mr azaad yataba gaya mishi ” ina ruwana da tafiyanta” kafin yace ” dude ba maganar kana kewanta da fa kafin kabara sonta ka tuna abinda kafadamin cewa fa kayi babu ruwanka da tafiyanta ko kamanta ” shuru Mr azaad yayi. daurawa yaseer yayi da ” kanason kasancewa da ita ko ?” gyada mishi kai Mr azaad yayi kamar karamin yaro yana son jin abinda yaseer ze fada. ” dude wallahi kana sonta it will be better kayarda da hakan tun kafin time ya kure maka kafada mata kana sonta kaji dude” shikanshi yanzu ya yarda da tabbas yana sonta shafa lallausan sumar kanshi yayi yace” dude bazan iya fada mata ba saboda zata iya raina ni nikuma banason raini yashigo tsakanina da ita kasan mata haka suke ” fashewa da dariya yaseer yayi Jin abinda Mr azaad yafada ” haba dude wallahi fanan bahaka take ba duk wanda ya santa yasan bata da wannan rashin kunyar da kake magana akai mutumina kawai just go and confess to her shine kawai ” murmushi ne ya subuce akan fuskar Mr azaad se yanzu ne yakejin sonta na kara shigewa zuciyarshi amma yana tsoron wani abu, yasan dole very soon zata tafi tabarshi karyazo yasabar wa kanshi da ita tazo tabarshi haka sukaci gaba da hira kafin suka bar gidan zuwa gidansu yaseer din afalo suka samu hajiyarsu yaseer tanawa kaninshi fada akan yawan yawon da yakeyi tunda suka shigo anwar yasha jinin jikinshi yasake nutsuwa ganin yaseer tare da Mr azaad dan yasan halinshi sarai hakuri yake bawa hajiyar gudun karta fada musu abinda ke faruwa watsa mishi harara Mr azaad yayi kafin yace ” hajiyarmu meyayi ” aikuwa kamar jira takeyi ya tambayeta tafara fada mishi, daura hannu akai anwar yayi aranshi yana fadin ” nashiga uku hajiya ta kasheni wallahi yau nashiga hannun ya azaad nawa ta takare” pointing dinshi da hannu Mr azaad yayi akan yazo jikinshi duk yayi la’asar haka yazo wajanshi hannu Mr azaad yasa ya damki kunnen anwar da karfi ,kara anwar yasa yana yarfa hannu dan bakaramin damke kunnen yayi ba, magana Mr azaad yafara ” wato ku yanzu kunyi girman da zaku dinga gantali ko ? Last time ya mukayi dakai ?” Kamar anwar zeyi kuka yace ” alkawari namaka bazan kara ba ! dan Allah ya azaad kayi hakuri in sha Allah daga yau natuba wallahi bazan sake ba”
frog jump Mr azaad yasashi haka yafarayi yana zagaye falon, juyawa yayi yakalli hajiya ya gaisheta fuska asake ta amsa tana fadin ” wato son se yau kayi niyar zuwa ko ? nadauka ma da matarka zakazo min ” murmushin gefen baki yayi yace ” kiyi hakuri hajiya in sha Allah zan kawo miki ita very soon” dariya tayi dan tasan halin Mr azaad yanzu setafi watanni ma bazata kara sashi a ido ba , part din yaseer suka shiga anwar de yana nan yana famanyin frog jump.

 

Haka yau fanan ta wuni wata sukuku da ita saboda lamarin zeenat ya tsaya mata arai dan tasan karya kawai zeenat tayi mata dan ta kaucewa zarginta , har tara Mr azaad be dawo daga gidansu yaseer ba abincinta taci tayi wanka tasa sleeping dress dinta ta kwanta.

Packing din motarshi yayi a packing lot tafiya yakeyi kawai yaga kamar gilmawar mutum wul ta gabanshi dakatawa yayi da tafiyar yana kallon the whole house, masu gadine kawai suke zaune suna jin radio sekuma securities da suma hiransu sukeyi , cigaba yayi da tafiyar harya shigo part dinshi har ze shiga bedroom dinshi se yajuya zuwa nata bedroom din wutan dakin a kashe flashlight din wayarshi ya kunna ya haskata akwance take tana bacci takawa yayi har izuwa bed dinta shafa cutie face dinta yayi daga bisani kuma ya manna mata kiss a forehead (goshi) komawa bedroom dinshi yayi shima wanka yayi ya kwanta. Sanyayyar murmushi fanan tasake lokacin da ya manna mata kiss tun shigowarshi ta tashi adduah takeyi aranta Allah yasa Mr azaad yafara sonta kamar yanda itama take sonshi.

To fa wato akace in zaka tona ramin mugunta ka tona dede kai yanzu de tsakanin mommy da zeenat nide narasa wazan kira mugu acikinsu.

Mommy tasamu lafiya sumul da ita tashirya fita dan taje itama tasamo yara 8 da suka rage zaayi sacrifice dinsu, itakuma zeenat tashiga part mommy har bedroom din Mansoor domin aiwatar da abinda a kasata ga shi dan banzan yunwa takeji tana bukatar jini ko nama kwance tasamu Mansoor yayi dai dai akan gado yana bacci bayan yagama shaye shayenshi dalewa kan gadon tayi tasa dogayen yatsunta tafara tsaga cikinshi , shuri daya Mansoor yayi rai yayi halinsa tass zeenat ta cinye namanshi da jininshi
Tana gamawa kuwa ta bace ta tafi dakinta tayi kwanciyarta cikinta a cike.

Karfe 3 mommy ta dawo gidan ta kashe yara biyar 5 takai kungiya, tana shigowa part dinta tafara jin karnin jini mamaki ne yakamata bin direction din inda karnin jinin ke tashi tayi tafiya takeyi har dakin Mansoor dake kwance babu rai ajikinshi babu koda tsokan nama sede kashi uwar ihu da kururuwa tayi wanda yacika gidan yayi sanadiyar tashin kowa daga bacci har rige_rige sukeyi suka fito kaff dinsu afalon ummi suka hadu suna tambayar junansu meyafaru tsaban rudewa dukkansu da kayan bacci suka fito buga kofar falon akeyi kamar zaa ballata babu ko tsoro Mr azaad yaje ya bude bangaje shi mommy tayi ta nufi abba ta rikeshi kam tana kuka kamar ranta zefita, duk ta daburtar dasu sun rasa gane abinda yake faruwa jijigata abba yayi saboda ta dawo cikin nutsuwarta cikin tashin hankali tace ” muhammad sun kasheshi sun kashe Mansoor sun kashemin dana Mansoor” innalillahi wainna ilaijiraji unnn zufa ne yafara yanko musu jin kalamanta saketa abba yayi yawuce part dinta yau ne rana ta farko da yasanya kafa a part dinta tun bayan shekara 12 saboda ya dade da sanin wacece mommy har dakin mansoor din yashiga runtse ido yayi lokacin da yayi arba da gawar mansoor ko kuma in ce gwarangwal din mansoor bakyaun gani, shigowa su ummi sukayi suma duk kallo daya sukawa gawar suka kauda kai, yau kam sun shiga matsanancinyar tashin hankali , babu abinda kirjin fanan yakeyi fa ce bugawa da karfi_karfi tsoronta daya shine kar zargin da takeyi yazama gaskiya akan zeenat saboda yanzu tasake samun hujja ganin dan kunnenta yashe akasan gadon sa kafa tayi ta bigeshi yashige can kasan gadon batare da kowa ya gani ba. bedsheet Mr azaad yasa ya rufe mansoor dashi duk karfin zuciyarshi da taurin zuciya seda yaji tsigan jikinshi yatashi barinma da yaga fuskan mansoor kaf an kwakule komai harta ido an cire , fita sukayi daga dakin zuciyarsu a karye sosai tausayin mommy yakamasu .
haka suka kwana a part din mommy batare da sun runtsu ba yanda sukaga dare haka suka ga rana .
Sallah suka tafi a masallaci Abba yafadawa liman akwai jana’iza agidanshi dan shi ya rasu , liman yayi sanarwa a masallaci mutane suka tayi musu taaziya.
haka akayi jana’izar mansoor aka kaishi gidanshi na gaskiya kowa na binshi da adduah Allah yaji kanshi , mommy kam yar karamar hauka ne kawai batayi saboda duk duniyar nan babu dan adam din da takeso sama da danta mansoor saboda halinsu yazo daya duk wani mugun nufinta bata taba tunkarar shi ba , ko magana bata iya yi balle ta karbi gaisuwar , su anty shayida da anty zainab da anty amina duk sunzo , me martaba da duk jamaar masarauta sunzo, haka su mama suma sunzo sun musu taaziya sun koma sosai mutuwar mansoor ya taba su fawwaz dukda bawani shiga harkanshi sukeyi ba saboda rashin kunyar dayake musu baya ganin kowa da mutunci kuma ko sun dakeshi hakan baze hana yakara musu wani rashin kunyar ba , haka zeje yafadawa mommy ita kuma tashigo part dinsu ta musu rashin mutunci tayi gaba .
duk wannan gaisuwan da akeyi da zaman makoki ko idon zeenat baa gani ba ko lekasu batayi ba tana can ta kulle kanta adaki tana kukan nadaman halin dataga kanta aciki abin na mugun damunta gashi kuma bata isa tafadawa kowa ba kugin yunwa cikinta yafara nan take halittar jikinta yafara sauyawa dogayen hakwara da yatsunta sun fito idonta yarine yayi jaa kuka takeyi da dan karfi dan yau kam tayi niyya sede in mutuwa zatayi sede tayi amma bazata karacin naman kowa ba tun tana iya jurewa harta kasa , fanan tana zaune a main falo dan batason yawan hayaniya sosai tabar wajan zaman makokin ita daya a falo , tana nan tana tunanin yanda zata shawo kan lamarin zeenat kenan taganta ta diro daga can upstairs ta dira a gabanta kamar wata yar biri tashi fanan tayi tana ja da baya zeenat na binta harsuka kai dungun gini yanzu kam fanan tagama tabbatarwa kanta zeenat mayyace , kafa mata hakwara tayi awuya zata fara shan jininta yaseer ya cafketa ta baya gam yariketa yaki sakinta .
kokarin fin karfinshi takeyi dan girgizan da takeyi yawuce iya karfin zeenat da akasani , fashe musu da kuka zeenat tayi tana ” wallahi mutuwa zanyi in bansha jini ba dan Allah ku taimakeni kubani in kuma ba haka ba zan iya mutu ” hawayene yakebin fuskan fanan dan jitayi duniyar ta dena mata dadi tama kasa karasa wajan yaseer da yake kokuwa da zeenat, son da yake mata ne yasa lokaci daya tausayinta yayi tasiri aranshi hannunshi yamika mata aikuwa karaff ta damki hannun yaseer din tasa abaki ta fara tsotsan jinin shi cike da tausayi suke kallonta shigowar Mr azaad kenan yayi karo da mugun gani da wani irin speed ya isa inda suke ya fincike zeenat dake shan jinin yaseer da takeyi cikin daka tsawa yace musu ” dama dukkan ku biyu baku da hankali bansani ba yaseer taya zaka bata hannunka tasha jininka ” gam yarike wuyan zeenat yasa idonta cikin nashi aikuwa nan take ta sume bin Mr azaad sukeyi da kallon tuhuma meye abinda ya aikata yanzun nan meye dalilin dazesa daga kallon idonshi zeenat zata suma, bebi ta kansu ba yadauketa cakk yanufi part din ummi da ita yakwantar da ita afalo .
Su ukun duk suna zaune a falon ummin babu wanda yacema dan uwansa kala, fanan tana yiwa yaseer dressing din hannunshi da zeenat tasha jini, daga waya Mr azaad yayi ya kira layin ummi yace mata tazo ita da abba it’s urgent, shigowa sukayi su biyar Abba,ummi, fawwaz,areef se anty amina ganin zeenat akwance bakinta da jini_jini Abba da ummi har suna hada baki wajan tambayar Mr azaad meya sameta , fada musu abinda ya gani yayi ,juyawa ummi tayi ta kalli fanan hawaye na fita a idonta jin halin da yarta ke ciki tace mata ” my feena meya sameta ” girgiza kai fanan tayi murya asanyaye tace ” ummi tun dawuwarta jiya nace naji tana karnin jini seta min karya dawani abun daban amma dukda haka ban yarda da itaba seyau na kara tabbatarwa” dama suma tunda sukaga fanan tayi hakan sunsan da walakin goro a miya amma se basu wani bawa abin mahimmanci ba.
tashi fanan tayi taje ta durkusa agaban zeenat tasa hannunta akan goshinta sannan ta rufe ido nan take tafara ganin tun lokacin da vampires union suka fara shirin bawa daya daga cikin ahalin mainasara maita harzuwa time din da daya daga cikinsu yazama karamar yarinya me tallan guiva da siyan da zeenat tayi takoma maiya da cin naman da tayi da komai da komai seda fanan tagani kamar wacce ta kunna film tana kallo . dasauri ta bude idonta ta kalli yan falon da suma ita suke kallo musamman ma Mr azaad duk abinda tagani seda ta fada musu salati kawai sukeyi zufa na keto musu ta ko ta ina duk da sun rasa abinda yahada su da vampires union,
ana haka zeenat ta tashi daga suman da tayi sauka idonta yayi akan areef dake tsayi akusa da ita , hannu takai zata rarumeshi ta ciza yayi baya , damkar gashin kanta fanan tayi suna facing din juna kafin tasa mata hannunta abaki aikuwa nan da nan tafara shan jinin fanan dakatar da ita suke kokarinyi ta daga musu hannu haka sunaji suna gani zeenat tadinga zukan jinin fanan seda suka kai almost 30mint a haka kafin dukkansu biyu suka zube a sume.

Se mun hadu gobe inme duka yakaim.
Masu comment na gode Sosai Allah yamuku albarka.

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

Story & written by ✍️
MRS ISHAM

 

JARUMAI WRITERS ASSOCIATION

Back to top button