Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 92

Sponsored Links

92
ZINNIEE’s SECRET
(One stop shop for a new sensation)

Kina Neman kamshi mai sanyaya zuciya❓
Shin kina Neman kamshi da dada❓
Ko kuwa kamshi mai ratsa zuciya kikeso❓ko Kayan gyaran jiki kike nema dry skin ne dake ko hard skin tabbas kinzo inda za’a share maki kukan ki

Tabbas Zinniee’s secret ya gama da damuwarku Ina mata masu aji mace mai aji ai Sai da gyara .tabbas Zinniee’s secret sun gama da damuwarki Hajiya ta.

Zinniee’s secret sun tanadar muku Kaya kamar……
Room freshener
Toilet spray
Bed spray
Dish wash
Mopping mist
Kai har ma da
Feminine wash
Akwai
Glowing soup dinmu mai kyau da inganci.
Glowing cream
Face cream da kuma body scrub

domin samun dadadan Kayan kamshi.da Kayan gyaran jiki maza garzayo Zinniee’s secret
Zinniee’s secret DUNIYA ne !!

Zaku iya yi mata magana a wadannan kafafan sadarwar kamar su—IG-@Zinniee’s secret
TIKTOK@ Zinniee’s secret
Ko ku tuntube su a wannan number 08080840567 za kuma ku iya mata magana ta hanyar Watsapp da wannan number.
Zinniee’s secret suna nan a kano Hadeaja road Kano state.

Zinniee’s secret one stop shop for a new sensation.

Zinniee’s secret got u covered,a trial will convince you.

 

********
Yanda yayi mata kyakyawan rungumar da yanda ya hade fuskansu da yanda yake kissing nata hawayensa na gangarowa daga cikin kyawawan idanuwansa tini ta kasa hanata Kansa ko kwacewa daga garesa sbd ita kanta ganinsa ya zo mata ne kaman a mafarkin da Bata taba kawowa a kusa ba,
Ta Riga ta cire Rai daga ganinsa har abada sbd tinanin ya haramta gareta,
Ganinsa da jinsa a jikinta yanzu ya tabbatarwa da zuciyarta bazata taba iya rayuwa babusa ba a ynzu shi din wani tsoka ce a kirjinta da bazata taba iya fitaba.

Ita kanta hawayen ne masu sanyi suka gangaro mata idanuwanta na rufewa ahankali hakama jikinta na sakewa gaba Daya a jikinsa sbd kasa yarda da ganinsa ya taho gareta.

Sake rungumeta jikinsa yayi dakyau Yana qanqameta tareda zare bakinsa daga nata Yana sake qanqameta dakyau Yana jero ajiyoyin zuciya hawayensa na kasa tsayuwa sbd sai alokacin ykejin kaman zai tsaga kirjinsa ya mayar da ita cikinsa gaba Daya ya boye ya Hana kowa da komai ko taba ta bare a sake rabasa da ita.

Shiru palon ya dauka babu Wanda ya iya magana babu Wanda ya iya motsawa Anne dake gefenta tsaya tini ta saki hannun Bena din dayake riqe a hannunta tareda matsawa gefe kadan sbd kaman bema lura da kowa a palon ba bare ita Datake riqe da Bena din,

Sumayyah da momyn Abdul Kallo dai sukai masa tin Sako Kansa palon suka fahimci shine DD qanin Bilal sbd kamarsu datai yawa.

Naseer daga kofar ya tsaya bayan shigewarsu Yana tura kofar palon ya rufe ya tsaya Yana Dan dauke Kansa daga kansu Bena din sbd Daman yasan zaayi Hakan sbd DD shi Sam baisan Yaya akeyi ko control na Kai akan lamarin da duk ya shafi Bena.

Ita kanta Bena din sai da suka jima a Hakan tsaye kafin ta Tina da akwai mutane palon ta Dan bude idanuwanta da sukai jajir tana zamewa daga jikinsa ta dago ta kallesa gabaki Daya idanuwansa dasukai laushin rashinta ya zuba mata tareda sake Kai bakinsa yayi kissing idanuwanta ahankali kafin ya dawo yayi kissing hancinta da kumatunta duk a hankali daga qarshe ya sake mayar da ita jikinsa ya rungume Yana Bude baki cikin Wani raunannan sauti yace

“Karki sake barina ko me Wani zai fada Miki,zan baki kariya ke da Annen ki, please karki sake barina,I love you,I love you”

Kasa motsawa tayi sbd kalmominsa dasuka shigeta jikinta ya sake mutuwa ta dago hannuwanta ta zagayesa dasu tareda qanqamesa tana sake shigewa jikinsa.

Kaman daga sama Bilal ya fito daga hanyar bedroom dinsa sanye cikin jallabiya fara da wayarsa a hannunsa Yana qarasowa cikin palon Abinda ya fara girgiza zuciyarsa shine qamshin da babu Wanda ya sani dashi sai mutum Daya a rayuwarsa shine DD kaante,shine ya fara shiga hancinsa shigowansa palon tareda girgiza masa zuciya a tsanake ya qarasa cikin palon ya tsaya cak daga inda yake Yana zubawa DD idanuwansa da tini suka sauya zuciyarsa na mummunan harbawa da bugawa.

Naseer Daya fara lura da Bilal din Shima kusan wutace ta daukewa jikinsa sbd jiya ya kasa yarda da cewan da gasken Bilal ne ya Gani,
Ya dauka idanuwansa ne,kenan tabbas shine,
Bilal kaante na Raye kenan?

Da sauri cikin tashin hankali ya Maida kallansa kan DD Wanda yasan zai iya samun bugawan zuciya ya sume idan yaga Dan uwansa Bilal a gabansa a Raye Dan haka ya Dan Tako kadan ya matso kusa da DD din Dan Incase kafin ya Dan Bude murya dake rawa ya danyi gyaran muryar daqyar tana yankewa ya Bude baki cikin yayyankewan kalamai ya ambaci sunan D din ya nuna nuna masa bayansa.

Budewa idanuwa DD yayi tareda dagowa batareda ya saki Bena ba hannunta na cikin nasa qanqame ya juya ya Kalli inda Naseer yake nuna masa idanuwansa suka dauka cikin na Bilal kaante dake tsaye bayansa Yana kallansa cikin firgici da tsananin so da kaunar Dan uwansa me tsananin gaske tareda Kuma tsananin mamaki da tsoron ya Akai yasan Nan din har yazo.

DD kuwa da farko dakatawa yayi dakyau Yana kallan mutumin dayake tsayen a gabansa idan Bilal ne kokuwa shine yake ganin Hakan,

Hannunsa dake riqe Dana Bena sakewa yayi ya rasa kuzarin kama komai bare iya riqewa Nan take,

Lumshe idanuwansa yayi ya sake budesu akan Bilal Wanda hawaye suka cika idanuwansa dakyau sbd yasan yanzu DD zai iya somewa idan ya tabbatarda shine sbd Kansa baya daukan shock masu girma be sababa da tashin hankali.

Motsawan Bilal ahankali tareda yowan taku daya Yana kokarin nufo DD tareda Bude baki zai kira sunan D din take DD ya fahimci tabbas Bilal ne a gabansa,
Daqyar ya iya waiwayowa ya Kalli Naseer dake gefensa Yana kokarin ganin DD din Bai shiga shock da yawa ba,
Gyada masa Kai Naseer yayi da alaman “yes Bilal dinne a gabansa Shima yana ganinsa.

Kasa riqe Kansa DD yayi Kansa yayi Wani irin sarawa qafafuwansa suka sare lokaci Daya Naseer da Bilal dasukasan zaayi Hakan dama suka taresa batareda ya Kai qasa ba
Bilal ne Kai tsaye da kansa ya cirasa da qarfi yayi kan kujera dashi Naseer na gyara masa pillows na doguwar 3 seater Turkish sofa set din aka Kwantar dashi.

Momyn Abdul kuwa na ganin Hakan tayi kitchen da sauri ta dauko ruwa me sanyi ta kawowa Bilal ta miqa masa karba yayi tareda ajiyewa gefe sbd sunyi sanyi ko babu sanyi ana saka masa su yanzu sai ya tashi da shiga Wani ciwon kan kokuma Wani abin Kuma Dan haka Naseer ne ya kalleta yace ruwan dumi zata kawo.

Bena datasan itama Daman zai iya shiga firgicin ya shiga wannan halin hawayen dake idanuwanta ne suka gangaro kan fuskarta ahankali taji qafafunta na qasa daukanta
da sauri sumayyah da Anne dasuke kallan iKon Allah sukai saurin riqota a tare suma sumayyah na rungumeta jikinta Anne Kuma na riqe da hannunta Daya tana Dan shafa bayanta da hannun Daya.

Daki sukai da ita suka zaunar bakin gado Anne ta Kalli sumayyahn tace taje ta kawowa Bena din ruwan dumi na tea itama Tasha da sauri Dan zata iya Amai da wanna firgicin sbd babu komai a cikinta.

Sumayyah kan Bena ta shafa cikeda kulawa kafin ta miqe ta fito daga bedroom din ta nufi dining ta fara kokarin hada mata tea sukuwa su Bilal na kan Dan Umme har lokacin.

Tana gama hadawa Bena din tea ta nufi dakin da sauri itama sbd Suma kokarin taimakawa tasu sukeyi.

Tana Kaiwa Anne ta karba tafara bawa Bena din wadda ta girgiza Kai tana cewa bazata iya saka komai acikintaba batajin buqatan Hakan.

Tilastata Anne tayi tareda sumayyahn suna rarrashin Tasha tea din sai alokacin sumayyah da Anne suka Kalli juna sumayyah ta zauna kan kyakyawan kujeran Dayake dakin ta Kalli Bena cikin kulawa sosai da tausasa murya tace

“Shine DD kaante din???

Anne ma shiru tayi tana jiran amsar da Bena din zata bayar sbd kansu na duhu da ganin wannan Dan madarar mara qarfin jini.

Numfashi ta fara saukewa kafin ta Dan dago ta Kalli Anne da itama ita take Kallo Dayake sun Saba ahaka suka taso basuda Wani abokai ko qawaye bayan Annensu da junansu.

Gyada Kai tayi a kasalance tareda bude baki ta furta “eh shine” ahankali tareda rufe idanuwanta hankalinta baya kanta Yana palo kan Wanda zuciyarta ke tsakanin bugawa a lokacin akansa.

Numfashi Anne da sumayyah suka sake lokaci Daya sai alokacin Anne taji kanta yayi Wani irin qato da sanyin jiki sbd kunyar kasancewarta a Palo lokacinda wannan abin ya faru,
Data sani Tim farko Hakan ze faru da yau bazata fita daga Dakinta ba zata zauna ta kame kanta acikinsa, Daman Bilal ne keta ganin Basu takura ba ko kame Kai sun saki jiki sun Saba dashi sosai yakeso sbd su zama ahali me kusanci da shaquwa da jina sosai.

Sumayyah kuwa shiru tayi sbd itama kunyar abin ne ya rufeta lokacin sbd da farkon lamarin duka shock ya hanasu Gane komai bare tinanin komai sai yanzu ne kunya da takaicin suna gurin ya shigo ke dabaibaiyesu.

Ita kanta Bena Jin yanda sukai tsit kowannensu Kansa a qasa yasata Jin kunyar komai Daya faru sbd harga Allah Bata tsammaci ganinsa ko a mafarkinta ba yanzu,hakama tasani kome zatayi a daidai wannan lokacin ko waye a gurin zai iya aikata Abinda ya aikata batareda yaji komaiba sbd Bai dauka baayin hakan ba a gaban mutanen.

A Palo Naseer ne yayi dubarunsa da ruwan dumi Yana saka qaramin sabon towel da yanzu aka fasashi Dan bazai yiyu a saka masa Wanda ba sabon ba zai iya Basa matsa a skin ya ringa sakawa a cikin ruwan zafin Yana matsewa kadan da sauran ruwan yan goga masa a tafin qafarsa da tafin hannuwansa.

Cikin zafin jikin Daya kamasa take ya Bude idanuwansa ahankali Yana kallan fuskar Bilal dake gabansa Yana shafe masa yan qananun zufan dasuka firfito daga lafiyayyar farar fatar fuskarsa.

Qurawa Bilal din idanuwansa yayi ya kasa ko qyaftawa tsawon lokaci Yana shiga tinani da abubuwa kala kala na yanda rasuwar Bilal din ta kasance da yanda daga baya yake sanin akwai yiyuwar ba gawar Bilal bace Daman aka samu a mota Ashe.

A yanzu Neman hawayensa yayi ya rasa idanuwansa sukai jajir Yana kallan bilal har lokacin ya kasa tashi daga kwancen Dayake Saida Bilal yaga shock da nauyin zuciyan na Neman yiwa DD din yawa ya ajiye tissue din hannunsa tareda Kai hannunsa biyu ya dago DD din zaune ya rungumesa jikinsa atake suka qanqame juna da qarfi kaman mata wannan Karan Bilal ne ya fara hawayen kewan Dan uwansa da yayi fiyeda yanda yayi tsammanin zuciyarsa zata riqe.

Shi DD kuwa Wani nauyi da radadin rashin Bilal da yayi tsawon shekarun ne suka danne kirjinsa idanuwansa sukai jajir baya iya ko hawayen farin cikin ganinsa sbd Wani abin busar da hawaye yakeyi.

Naseer ajiye towel din hannunsa yayi ya miqawa momyn Abdul robar yace takai kitchen tabasu guri.

Tana barin gurin Shima wayarsa ya fidda daga aljihunsa Yana nufar kofa sbd yakamata yayi magana da Zeenah Dan babu Wanda yasan sun Abuja gashi yasan tayita kiransa jiyan Bata samu sbd kashe wayarsa da yayi.

Yana fitowa daga palon tana daga Kiran nasa cikin sanyin murya da mutuwar jiki sallama kawai tayi masa tayi shiru sbd fushin datakeyi akan kashe wayarsa da yayi batareda ya nemeta ba.

Yanajin muryanta sauke ajiyan zuciya ya fara Yi sbd nutsuwar Daya samu tareda Jin kaman zazzabin kewanta zai kamasa saidai yasan Kuma muryan nata akwai fushi aciki dan haka tausasa muryarsa yayi tareda Bude mota ya zauna ciki ahankali yafara rarrashinta cikin tasa kalan soyayyar da kusan irin ta ubangidansa ce Dan kuwa tinda ya fara soyayya da Zeenah daga zaman jinyar da sukai ya mace gaba Daya akanta kallanta kawai kashe masa dukkanin jiki yakeyi.
##MAMUH#
#TOO HOT
#ROMANCE
#LOVE
#CRAZY IN LOVE
#DD LOVE
#BILAL/SUMAYYAH

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

Back to top button