Adandi Hausa NovelHausa Novels

Adandi 21

Sponsored Links

*21*

 

Kallonsa yayi baki sake murya na rawa ya shaqeshi yace “me…me kakeso kacemin kanada masaniya akan abinda ya faru kenan?” Janye hanunsa yayi daga wuyansa yace “ita qaddara ta riga fata wlh a gabana suka shirya plan dinnan jiya ina qoqarin zuwa na sanar dakai sai babata ta kirani a waya na koma gefe ina amsa waya bayan shigowar Nasir ya kawo maka lemon da suka zuba qwayoyin qara qarfin sha’awar me suna Signature da Vigor na gama waya na biyoshi da sauri amma kafin nazo harya fito daga dakinka yana murmushi yana cewa “kiyi hqr Samha yau zakisan namijin gaske yau zakiji abinda akeji badon komai ba saidon kankaro miki da darajarki tabbas barna ce zamu hada amma wannan barnar gyara ce wannan hanyar ce kadai zaki tsarkaka daga zargin da wannan shashashan masoyin naki yake miki”

 

 

Dafe kansa yayi yana kiran “innanillahi wa Innah ilaihirraji’un” mugun juya masa kansa yakeyi yanajin wani jiri yana daukarsa ya durqushe a gurin yace “Allah kabimin haqqina kai kadai zaka fitar dania gurin yarinyar nan” yanda zuciyarsa take tafasa yasashi tashi ya shiga motarsa ya tafi gda yaje ya kwanta shi dama ba lfy ce ta isheshi ba wani zazzabi ya rufeshi yana kuka kamar qaramin yaro yanata Istigfari yana rawar sanyi yana kuka mecin rai baisan da wanne ido zai kalli Samha ba idanunsa sunyi qananu su kalli tsabar idonta suce zasu bata hqr dole ya barta tayi masa duk hukuncin da take ganin ya dace dashi.

 

Itakuwa Samha takurawa Rahmah tayi akan dole sai sunbar asibitin a yau takeson barin garin Katsina ta tsani garin fiye da yanda ta tsani kanta a yau Allah ya isa kuwa Abdul yashata tafi cikin tifa hakanan kan dole Rahmah taje ta kira likitan tazo ta sake dubata Dr Hasina mutuniyar kirki me kishin yan’wanta mata haka ta rinqa tattalin Samha da bata hqr harda hawayenta tana fada mata jinta takeyi kamar yarta ta cikinta daqyar ta samu ta rarrasheta amma saida tayi mata alqawarin zatabar asibitin da ita ita kuma tace “tunda kunce service kukeyi anan iyayenku baanan sukeba to saidai kubini gdana ku zauna idan kinji sauqi saiku koma gdanku” badon Samha taso ba hakanan sukabi Dr Hasina gdanta anan taci gaba da kula da Samha sosai tare da bata shawarwari musamman da ta fada Mata auranta saura wata uku.

 

Satinsu biyu a gdan kullum Rahmah da Aunty Hasina cikin lallashin Samha suke saboda kullum cikin kuka take tana fadawa Allah ya saka mata abinda Abdul yayi mata tsanarsa takeji aduk wata gaba ta jikinta duk sanda ta tuna barnar da yayi mata takanyi tur dashi taji dama baa rubutoshi a cikin qaddarorinta ba a cikin sati na ukune sukaso barin gdan Dr Hasina amma ta hanasu ta zaunar da ita tana tambayarta tana cewa na hango wata matsalar yata kasalarki tayi yawa ya kamata ki shirya muje a dubaki kada muyi gyaran gangar auzinawa itadai Samha bata kawo komai ba ta shirya cikin wata blue din gown tayi rolling da dankwalin duk da ramar da tayi tayi kyau sosai amma har yanzu tafiyarta bata koma normal ba Dr Hasina tace a qalla zata iya daukan wata biyu kafin ta koma daidai hakadai take dan daddaburawa.

 

Suna zuwa asibitin Dr Hasina ta shigar da ita Lab tace taje tayo fitsari ta kawo mata taje tayo ta kawo mata ta debi jininta ta bawa ma’aikatan Lab din suka fita suka tafi office din Dr Hasina suna shiga motar Abdul tana shigowa asibitin yayi parking yaci gaba da bincikensa kamar yanda ya saba duk wani kalar hauka saida Abdul yayishi a asibitin lkcn daya dawo Dr Hasina ta sanar dashi iyayen Samha sunzo sun tafi da ita a lkcn shaqer Dr Hasina yayi yace “kika barta akanme zaki bari su tafi da ita ban nemi yafiyarta ba ban nemi afuwarta ba sannan ban fada mata sirrin zuciyata ba meyasa kika bari ta tafi tana fushi dani Dr ki taimakeni don Allah wlh sonta zai kasheni bansan inason Samha ba sai yanzu wlh bayin kaina bane magani abokaina suka zubamin kawai saboda na lalata rayuwarta na lalata tawa don Allah ki… Dr kice ta dawo muyi aure nasan tana sona…”

 

Duk da zafinsa da Dr Hasina takeji saida ya bata tausayi amma tayiwa Samha alqawarin bazata taba sanar dashi tana gurinta ba dole ta waske ta qwace daga hanunsa tace “toni mene bawa ma a ciki” zubewa yayi a gurin yana kuka me ban tausayi yace “kina cikin list kema ban yarda dake ba waima kinsan wayeni da zanke fada kina fada to ki tambayi kowa waye Mainah Abdu a masarautar Katsina” saida gaban Dr Hasina ya fadi amma dole ta dake ta zube tace “kayi hqr ranka ya dade banida wata masaniya a game da patient dinka an kirani gda akan nazo yarona babu lfy na fita da niyyar zanje na dawo nazo na tarar sun gudu….”

 

 

Daga mata hanu yayi yace “sakacinki ne koma mene” tun daga ranar kullum sai yazo asibitin yayi zagayensa sannan ya fita har tambayar Dr Hasina yayi wai bata bada saqo a bashi ba baisan inda zai nemeta ba kuma yanason ganinta ya fadawa me martaba aika² da yayi mata yace ya kawo masa ita tayi Istibra’ih a gdan sarautar sannan ta koma gdansu su nemi aurenta” jikin Dr Hasina a sanyaye tace “kayi hqr kaci gaba da addu’a idan rabonka ce zaka sameta amma ni banida wata masaniya game da patient dinka” tana fadin haka ta juya ta shiga wani daki da zata duba patience dinta saboda gudun kada ta shiga office ya biyota aikuwa tana tafe yana binta yanayi mata magiya daqyar ta bashi hqr akan zata tayashi binciken inda zai samu Samha hakanne yasashi hqr ya tafi.

 

Ajiyar zuciya tayi tace “qaraqaqa qaqa ya kamata ta bawa Samha hqr karta bari wannan damar ta wucce ta ta lura ba qaramin so Yariman masarautar tasu yakewa yarinyar ba” haka ta koma Lab ta karbi gwajin abindai da take zargin shine gabanta ya fadi sosai tace “ciki? Na shiga uku ni Hasina wai meyasa indai aka samu irin wannan cases din zaiyi wahala ciki be shiga ba?” Kallonta Dr Mabaruka tayi tace “bangane ba” ajiyar zuciya tayi saboda Dr Mabaruka batasan da case dinba kuma tasan surutunta da neman sunanta tsaf zata nemi Abdul ta fada masa, murmushin yaqe tayi ta nufi bangaren saida magani ta siyo wasu qwayoyi na zubar da ciki ta wucce tana zuwa “bata fadawa Samha qullin dake cikinta ba saida ta bare magungunan guda uku ta bata tasha sannan tace juya nayi miki allurar nan Emergency ce yanzu zata baro dashi wannan magungunan na rage zafin ciwon marar da zaki iya fuskanta ne” cikin kuka tace “Aunty Hasina kina nufin cikin Abdul ne a jikina…” Rufe mata baki tayi tace “karki wani damu cikin yan mintina zai fita daga jikinki tunda ba qwari yayi ba cikin sati uku ai ruwane nafiso ki zama normal Samha banason na barki da tabon abunnan daya faru ko kadan shiyasa kikaga na dage wajan nema maki mafita” tana kuka ta juya Dr Hasina tayi mata Allurar sannan tace “ba wani wahala zakisha ba dan ciwon marane kadan da baifi na period ba inma yafi kadanne” tashi sukayi suka tafi suka shiga mota tun kafin su isa gdan cikinta ya fara hautsinawa suna zuwa gdan ta shige ta kwanta a daki bayan tayi sallar azahar lkcn ne Dr Hasina take basu lbrn yanda sukayi da Abdul yau itadai batace komai ba amma tayi alqawarin ko ita Dr Hasina bazata bawa asalin address din gdansu ba so take suyi rabuwa ta har abada ita da Abdul ta tsaneshi tsana mara misali ko sunanshi bata qaunar taji wani ya ambata.

 

Ciwon marar be matsanta mataba sai dare cikin ikon Allah sai jini amma da dan qarfinsa hamdala Dr Hasina tayi tace “kinga kin tsarkaka bakida wani tabo na fyade a tare dake amma da ace na barku kun tafi lkcn da kika nace saikin tafi dinnan da yanzu ma baku gane da cikin ba sanda zaku gane yayi qwarin da idan aka tabashi zaa shiga hurumin ubangiji sai kuma ayi daban kwalo laifi cikin laifi amma kinga yanzu baikai lkcn da idan an zubar zaace anyi kisa ba” itadai Samha ciwon mararta bai barta tace wani Abu ba saida Aunty Hasina ta sake yi mata Allurar relief sannan ta samu dama dama ta miqe ta shiga bathroom ta sake gyara jikinta ta dawo ta kwanta Dad ne ya kirata yake fada Mata ya dawo daga Brazil din da yaje gobe zaizo ya ganta takuwa sanya masa kuka tace ita ta gama service yasan yanda zaiyi kawai Allah sarki Alh Sa’ad take yace Mata an gama indai kudi zasu iya to tagama service”

 

Washe gari kuwa da wuri ya gama yimata komai ya sanar dasu yarsa batada lfy shiyasa hakanan dai dake a 9ja ne aka yi duk me yuwuwa ya kirata yace yaje gdanta batanan ta kwatanta masa inda take yazo ya ganta ya rinqa latsata kamar rago yana magana cikin tashin hankali “Pretty na meye ya ramar dake haka ciwo kikayi baki fadawa kowa ba Mamynki tace idan ta kiraki bakya dagawa kina fushi da ita meyasa” fadawa tayi jikinsa tace “Dad yanzu nayi uwa a duniya amma Mamy bata sona ni Ina tantamar itace ta haifeni Dad duk wata kulawa da iyaye suke bawa yayansu Mamy bata bani tsayin sati biyu bata kirani taji lfyta ba bayan tasani duk safiyar duniya ina kiranku mu gaisa amma batayi tunanin meye yasa bana kiranta ba sai cikin satinnan sannan ta kirani wacce irin uwace wannan da bata damu da halin da amanar da Allah ya bata take ciki ba?”

 

Qara rungumeta ya qarayi yana bubbuga bayanta yace “kema Lovely kinsan halin Mamynki ki qara hqr kwana nawa ma ya rage ku rabu kema ki tafi naki gdan jiya mukayi waya da Mus’ab yake neman alfarmar a rage tsayin lkcn bikinku saboda tafiyarsa ta kama cikin watan da zamu shiga so naso nace masa aa saboda wani badaqala data taso a gdanmu nan Katsina akan aurenki da Mainah Abdu kamar yanda dokar gdan yake bama ba da aure a waje matsawar munada zaratan samari a cikin gdanmu so bandai san ya zamuyi dasu ba amma inasonki da Mus’ab baby naso mu wucce nakaiki kiga yan’uwanki amma wani kiran gaggawa ya sameni daga shugaban qasa saboda haka zamu wucce yanzu muje ku fara shirye² itadai batayi mgn ba saida taji yanayi mata rada a kunne yana cewa “me kikeso ayiwa likitanki na kula dake da tayi?” Ajiyar zuciya tayi dake daga ita saishi tace.

 

“mijinta ya mutu shekara bakwai bata da da saboda mijinta baya haihuwa haya takeyi a wannan gdan gashi gdan ma ya tsufa da yawa ka siya mata gda kuma kayi mata wani abu a cikin gwabnati sannan idanma zaka aureta zanyi farin ciki Dad tasan sirrin da Mamy na bata saniba a kaina kuma inada yaqinin zata riqeni amana ko babu ran Mamy na tanada sauqin kai sosai”

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/13, 2:55 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*

 

*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*

 

Back to top button