Ikraam 70
Ikhram~ By Khaleesat Haiydar 70…… Ikram ta galla ma Khaleel harara tace “ni ka fitan min daga dakin nn” ya xauna gefen gadon yace “baxan fita ba” da karfi ta shiga kwala ma Mami kira kmr xata yi kuka, ya mike da sauri yana hararanta ya fice daga dakin, ta murguda masa baki ta cire bargon jikinta ta mike tana kallon skirt din jikinta ta nufi bathroom da sauri, Aliyu na sakkowa downstairs ya karasa kusa da Mami a sanyaye ya durkushe gabanta yana girgixa mata kai cikin yanayi mai ban tausayi yace “mami plss ki cika min alkawarin da kika daukar min don Allah” hawaye ya cika idonsa yana kallonta, Mami ta ajiye Nail cutter din hannunta tace “wani Alkawarin son” yyi shiru ya kasa cewa komai, Mami tace “kayi shiru?” a hankali yace “Ikram” Mami bata ce komai ba ta ci gaba da yanke farcenta ba tare da ta kallesa ba. Khaleel ne xaune yana kallon Mami dake kan system tana aiki, ya dan rage volume din tv ganin ya kai minti kusan goma a xaune tun bayan da ta aika jummai ta kirasa yace “Mami baki ce komai ba kuma” Mami tayi shiru bata ce komai ba har lkcn tana ta aikinta, bayan kmr minti biyar ba tare da ta kallesa ba tace “takardar Ikram xaka bani ynxu son” ya daga kai yana kallonta snn ya mayar da dubansa ga tv yace “to Mami” yana fadin hka ya mike ya nufi kofa xae fita, ta bi sa da kallo har ya fita snn ta ci gaba da abinda take cikin rashin kuxari, yana fita Ikram ta shigo dakin, Mami ta bar abinda take ta juya tana kallonta tace “kinci abinci dota, cikin kuma ya daina ynxu ko” Ikram ta kwanta kan gadonta kmr xata yi kuka tace “kadan kadan yake min kuma ni bana so, ina son ya daina min duka” Mami tace “to ynxu Aliyu xae kawo maki wani magani, amma kinci abinci dae ko” ta gyada mata kai tace “ehh na sha tea” Mami tace “maxa ki wuce ki karbi abinci, bana son shashanci, tea abinci ne” Ikram ta mike ta fice daga dakin ba don ranta ya so ba ta nufi kitchen gun jummai, xaune ta ga Khaleel kan dinnin ga abincinsa gabansa ya tallabi chin dinsa da hannunsa biyu da ya harde idonsa a lumshe, ta karaso dinnin din a hankali da nufin basa tsoro, wani kara ta saki dai dai saitin kunnensa ya bude idonsa da sauri ta juya da gudu xata bar wajen tsantsin tiles ya kwasheta ta fasa ihu xata fadi ya mike a hanxarce ya kamota ta fado kan kirjinsa, tsit tayi idonta a kulle xuciyarta na bugawa don ta tsorata ssae, kmr xata yi kuka tace “wayyo kayi hkuri yaya Khaleel wllh wasa nake maka fa, kasan ae bani da lfya ko” yyi shiru yana kallonta har lkcn tana jikinsa, ta wara manyan idonta tana kallonsa xata yi magana aka bude kofar falon, Aliyu ne ya shigo rike da ledan Magunguna a hannunsa, tsayawa yyi yana kallonsu daga bakin kofar, Ikram ta kwace kanta daga jikin Khaleel da sauri tace “meyasa kke taba ni wae, ni ka daina taba ni” ta karashe maganr tana hararnsa, ya fixgota yana mata mugun kallo xae yi magana sae kuma ya fasa, ya turata ya nufi stairs, gun Aliyu ta tafi da sauri tace “yayana” ya dan yi murmushi bae ce komai ba, ta dan bata fuska tace “wllh xamewa nayi a tiles shine ya kama ni, da na fasa kaina ynxu, amma bae taba ni ba yayana” Aliyu ya xauna kan kujera ya jinginar da kansa jikin kujerar, ta xaune gefensa tace “ina yini yayana” ya gyada mata kai yace “lfya lau, cikin ya daina maki ciwo ynxu ko” ta rufe fuska da sauri tana yar dariya ta matso kusa da shi ta bude fuskarta tana kallon fuskarsa tace “wa yace maka bani da lfya yayana” ya dan matsa daga kusa da ita yace “Mami ce ta gaya min, kinga ma magani na kawo maki ynxu” ta yi shiru tana kallonsa.
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikhr