Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 55-56

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*55&56*

 

 

……..yana cikin wannan tunanin yaji sanyayyan k’amshin turaren ta da sautin siririyar muryarta tana masa sallama “be Amsa ba sai cewa yayi inye salfad d’ita ta zama Amarya….kai hamma Abinda ko bikin ba’a yiba”dukda haka ke Amarya ce ko?”nidai Allah ah ah”kinsan wani abu?”ah ah”kiran gaggawa yasameni A office ,shine saina sanar musu baby nah ta hanani zuwa sbd bata san yin nesa dani”sai suka buk’aci kuyi mgn ta waya kokin yadda na tafi….. Ayya hamma niba zan hanaka zuwa ba”kaje kawai Allah yabaku sa’a”tayi maganar kanta sunkuye”yanata kallonta yana nazarinta kafin ya koma mgn ta rigashi da cewa bara nakawo maka sakon Ammin”shifa d’an Aiken banda shine?”eh mana “idan kanaso sai kadawo next week”ni Allah ban yardaba yanzun nakeso”tayi murmushi kawai ta juya ta tafi ranta gaba d’aya babu dad’i sbd zai tafi”shi kansa beson yatafi ya barta”zai dai tafi ne sbd yana yin Aikinsa”bata jumaba tadawo rik’e da kwalaye guda biyu manya da aka shirya meat pie da donut had’e da samosa, cake, dambun kaji….ko baki fad’a ba nike da na k’asan Ammi nada na saman”gyad’a masa kanta tayi ya Amsa yana kallon ta yace”muje mota”babu musu suka jera suka nufi wajen get”idanuwanta sun ciko da k’wallah “bataso tasaka shi Adamuwa shiyasa ta daure dai”mus’ab dake zaune yana kallonsu ta glass”bayan shariff yasaka sak’on a boot ya kalleta yana murmushi murya can k’asa yace”karkiyi kuka salfad kinjiko?”idan kuma kikayi raina zai bani hakan”idan mun shiga jirgi zan kiraki”to hamma Allah yatsare kuma nidai karka dinga mgn da wasu matan ko?”kishi ko?”turo baki tayi ta matsa ta bud’e masa k’ofar motar”Aba zata taji yashafi gefen fuskarta da karan hancinta sannan yashiga cikin motar “ta kallesa da sauri”yad’aga mata gira yana kasheta da tsadaddan murmushinsa”ta kawar da kanta tana fad’in ka gaishemun dasu Ammin sosai”yaya mus’ab ina gaida Ahmed da ummansa”to shikenan Amaan zasuji”shariff ya kalleta yana d’an d’aure fuska yace”wannan shashashan nasaka sun sakesa na kuma bashi Abinda ya bukata”bance bayan gaisuwar zumunci ba wata mgn ta had’aki dashi “dato ta Amsa tana rufe musu k’ofar ta wuce”mus’ab ya jinjina kai yana fad’in sai kace Aurenta kakeyi?bakada labarin ta zama matata ne?”dariyar rainin hankali mus’ab ya shek’e da ita….sai yamma gab da sallar magrib shariff yashigo cikin gidan”fuskarsa d’auke da k’ayataccen murmushi”kallo d’aya zaka masa kasan yana cikin farin ciki”yaransa biyu na biye dashi da kaya nik’i nik’i”Abdallah da Ammi na zaune a parlourn tana masa mgn yatafi masjeed Ankusan kiran sallar magrib”murmushi Ammin tayi ta Amsa sallamar tasa”ya zauna kan kujerah”Abdallah na murna yace”yaya ka kusan zama mijin Anty Amaan”Allah yasa Alkhairi “ko Ajikin shariff yace”Ameen Autan mu”Ammi na sameku lafiya?”Alhamdulillah! kagama b’oyemun inda kaje ko?”yayi y’ar dariya yana fad’in duk suna gaisheku”gashi tabayar Akawo miki”Allah sarki y’ata me kuma nasamu?da kansa yatashi ya d’akko kwalayen ya ajiye gabanta”tana dubawa k’amshin spices da curry yadaki hancinta”komai na nad’e cikin leda me k’yalk’yali Anyi rafin…. Abdallah ya mik’e tsaye yana fad’in bara nakawo plate Azuba mun kasona Ammi”nasan yaya sadeeq daya gani k’ilan kasona yarage yawa”yak’are maganar yana nufar dining area”Ammi tace”bazan zuba ba kaje kayi sallah tukum”shagwab’a yakamayi wai Azuba masa idan yadawo zaici”sharesa Ammi tayi tana duba komai”masha Allah! gaskiya naji dad’i sosai kaga na Ajiye wasu da bazasu lalace da sauri ba sbd bak’i”dama mommyta ta sanar mun kasuwancin datakeyi kenan?eh hakane”bara na wuce nayi Alwallah “Ad’ibarmin nawa pls”babu kasonka tunda kaci Acan”bece komai ba yayi dai murmushi yana k’ok’arin tashi kiran Amaan yashigo cikin wayarsa”ya d’auka yana fad’in my salfad! uhmm” har ka iso gidan?”eh inama gaban Ammi….batayi mgn ba d’it ta kashe wayar “yabi wayar da kallo yana sakin murmushi yace”yanzun Ammi y’arki kunyarki takeji”zata dena insha Allah”su Alh lawal sunmun bayanin komai ta waya”hak’ik’a na yaba da karamcin iyayenta”Allah yasa Alkhairi yakaimu lokacin lafiya”muma nan sati me zuwa zamuyi namu taron saka ranar”shariff na kok’arin mgn sadeeq yashigo”da Alama daga Asibiti yake”Ango Ango!!harararsa sharif yayi yatab’e baki”pls yaya kaga madeenah?”tunda naje ni ban gantaba”to Ammi nidai da Anyi bikinsu yaya sai Adawo maganarmu da madeenah ko?”dakk’uwa Ammi ta masa”yayi k’asa da kai yana murmushi “Abdallah dake duk’e gaban Ammi Ana zuba masa snacks d’in yadinga b’abbaka dariya”kai da waye kake ne?”kaga dan Allah rabu dashi kaje kayi Alwallah kutafi masallaci”cewar Ammi”shiru sadeeq yayi yana hararar Abdallah “shariff ya mik’e tsaye yana kallon sadeeq yace”ina fatan wannan k’azamar yarinyar tabar Asibintin ka? yak’are maganar yana yatsina fuska “kayi hak’uri yaya kasan Anan Aka mata Aiki kaga dole saita d’an yi ko 2 days haka sannan Abata sallama”naga kuma Alamar nadama Atare da ita”dukda tasamu matsala A mahaifarta”bazata iya d’aukar ciki ba yarayu”saidai data samu ciki zai iya zubewa”subahanallahi! Allah ya kyauta”cewar Ammi”shariff yatab’e baki yana d’age kafad’a yace”damuwarta ce taje taci gaba mana”kowa ya tuba dan wuya tubansa beyiba”daga haka ya wuce upstairs……
*bayan wata ukku*
kwanci tashi Asaran me rai “da safiya tayi sai gari ya waye cikin ikon Allah”tunda Aka saka ranar shariff da Amaan suka bud’e sabon shafin tsabtatacciyar soyayya”duk week end yana k’ok’arin zuwa yaganta susha fira”baya gajiya dayimata hidima da dukiyarsa kamar besan zafin nema ba”gefe guda kuma madeenah da sadeeq soyayyar su kowa yasan da ita”ayanzun haka dai nasir da mahaifiyarsa iya karsu da family d’in Amaan sai gaisuwa”dan nasir yatsorata da shariff matuk’a “ya yadda ba k’aramin mutum bane shi, yanada izzah da k’arfin iko sbd dukiyarsa da Aikinsa”yayinda gefen Anty zabba’u tuni ta warke tabaro Asibiti Ana cigaba da yimata maganin gargajiya”kuma daddy yabata gida da sanarwa yaranta idan zasu bita babu damuwa idan gidanshi zasu zauna shima babu laifi”sai dangin zabba’u suka hanata Amsar gidan ta koma wajen iyayenta da zama”kowa nata na cewa sbd yaganta da Lalura shine yasaketa”su shamsiya kuma suka zauna gidan ubansu Adak’in mahaifiyarsu”Abin mamaki har waje Anty zabba’u ke fita yawo sbd kamar k’aramar yarinya ta koma”wata rana aka sami wasu matasa su biyu sukayi mata fyad’e”daga ranar ba’a koma barinta fitaba”danginta nata Aibata daddy da mommy”Amma su harkan gabansu sukeyi”Ahaka har lokacin gagarumin bikin su Amaan yafara zuwa”tun saura sati ukku invitition card nasu da free weeding pics nasu ke yawo a social media “wanda shariff yayi mamaki hakan yasa yace”to babu wata bid’ar da za’a yi”da an d’aura Aure zaizo ya d’auki matarsa sutafi ta jirgi gidan Ammi”idan danginta daya saka A d’akkosu ta mota sun iso saisu ka masa ita, washe gari su koma gida…tun saura 2weeks mus’ab da uban gayyar suka kawo lefen daya girgiza jama’ar dake adamawa state da gewayenta”sbd tsananin dukiyar da shariff yazuba Acikin lefen dozin 3 ,harda mota da sark’an gold”kuma Abin murna ba mata suka kawo lefenba balle Ayi zancen tukwici”Aranar Amaan har kukan farin ciki tayi domin ta fahimci mak’iya sunso su tozarta rayuwarta Amma Allah ya had’a ta da wanda zai zama Alkhairi ga rayuwarta”lokacin datake kukan itama mommy shi takeyi”yayinda y’an b’akin ciki ke cewa sbd daddy yaga kud’i yak’i Auramawa nasir salma”su kansu su shamsiya jikinsu yayi sanyi sunadai gefe basu saka kansu cikin hidimar komai ba”mommy bata kyaransu ko tsangwamarsu”ko girki tasanarwa daddy yabasu su dingayin Abinsu da kansu…..wa’azi kawai da lalle Amaan tayi itada k’awayenta”wanda kuma Agobe Asabar Ake d’aura Aure”Ango tun wajen k’arfe 12 pm ya iso shida zugar Abokansa ta jirgi suka kama masauki na musammun”bayan Antaso sallar juma’a yayiwa gidansu Amaan tsinke shi kad’ai….tsananin gyaran da Amaan tasha idan kaganta zaka d’auka baturiyace”tun safe da Aka gama mata dilka ta tafi wajen lalle”wanda lallen yamata masifar kyau Abinka da farar mace”An mata ja da bak’i Abin sai wanda ya gani”tun tana wajen lallen shariff ya sanar mata suna cikin jirki”hakan yasa wajen k’arfe 12:30 pm tadawo gidan ta nema masa Abinda zaici sannan tayi wanka da sallar Azahar “gidan nasu cike yake da bak’i na nesa da sukazo su kwana Ayi biki dasu “madeenah na gefenta tana kallonta tana shiryawa gashin nata bak’i yasha gyara tana d’aure sa yazubo har tsakkiyar bayanta”masha Allah Amaryar hamma shariff”cewar madeenah daketa kallonta”hmm! toya san ranki?”shiru bema kirani ba”to kiran meye zai miki bayan gobe da an d’aura zaku tafi?” ke kiran meye sadeeq ke miki?”deenah na kok’arin mgn wayar Amaan tayi ringing “ta duba wayar tana sakin murmushi tace”Allah sarki my baby shine yakira”shewa deenah tayi”Amaan ta harareta ta d’auki wayar tana masa sallama”sai kuma tace okay gani nan zuwa”daga haka ta yanke wayar tana kallon madeenah tace”pls kije store komai dana Ajiye masa yana cikin tray ki d’auka ki kaimasa zan wuto masa da drinks”kinga ga keys d’in store d’in saiki d’auka”to shikenan Antynmu”Amaan na dariya tace”da karma kice Antyn mana”deena na dariya ta d’auki key d’in ta fita”Amaan ta shafa kwalli da lips stick”ta shafa turarukan da aka had’a mata”sannan ta d’akko sabon d’inkin doguwar rigar shadda da Akayiwa Aiki da pink d’in zare tasaka”ta d’auki mayafi pink ta Aza saman kanta”saida ta kalli kanta ta cikin mirror d’in sannan ta saki murmushi “wasu k’annan mommy ta suka dinga wasa irin kyawun datayi”tana dariya ta wuce ta zuba drinks a tray zata fita suka had’u da deenah zata shigo cikin parlourn”kin kai?”Eh mana” Amma yace ke yafi buk’atar gani ba wani Abuba”gaskiya yaya shariff beda kunya da wuya wannan gobe yasarara miki wlh”gaban Amaan yafad’i, ta bita da kallon ukku saura kwata tana yin gaba”madeenah kuwa ta dinga yimata dariya……tunda Amaan ta murd’a handle d’in k’ofar k’irjinta ke bugawa”tun kafin ta shigo ta shak’i daddad’an k’amshin turarensa da yau tajishi yafi kullum dad’in k’amshi”saidai gaba d’aya yau ta tsintsi kanta da k’in son had’a Ido dashi”kuma yau sai taji fargaban Auren Aranta”da k’yar ta rintse Ido ta daure tayi masa sallama….tunda yaji motsin turo k’ofar ya kafe bakin k’ofar da kyawawan idanuwansa” yana binta da irin mayen kallon tamkar yaune yafara ganinta”fuskarsa shimfid’e da tattausan murmushi”wanda yayi masifar haska fuskar tasa”kasancewar Ammasa Aski da gyaran fuska”b’akin sajen nan nasa har d’aukar Ido yakeyi”Anutse ya Amsa sallamar ta lokacin data k’araso gabansa ta Ajiye tray d’in hannunta ta duk’a murya can k’asa tace”hamma sannu da zuwa ya hanya?”saida ya d’auki kusan second 5 kafin yace”lpy qlau Alhmdllh! batace komai ba tazuba ruwa a cup ta mik’a masa “daya tashi karb’an ruwan saiya had’e da hannunta ya rik’e….da sauri ta d’ago kanta idanuwanta na shigewa cikin k’wayar idonsa”yad’age gira yana kashe mata Ido”cikin k’asa da murya yace”sbd dama kawai ki kalleni yasaka na rik’e hannun”ya fad’a yana cika hannun da sauri sbd wani taushi da yaji hannun nadashi”Amaan kuwa mik’ewa tsaye tayi zata wuce”ya dakatar da ita gun cewa dawo nan mu zauna ki fad’amun yadda kikayi kewata”gaba d’aya yau na fahimci bakison mgn da kallonah ko?”kuma ko d’okin zuwanama baki yiba”saima naga kamar kina jin tsoron zama inda nake”bafa haka bane hamma”uhmm kima dena mun hakan sbd bana so”batace komai ba ta zauna gefensa”ya sauke Ajiyar zuciya yanata kallonta yace”kinyi kyau Amaryata”irin wannan canzawa haka kodai nima naje nayi gyaran jikinne?”yafad’a cikin wata iriyar muryar data haddasa mata jin kasala lokaci guda…waye yamiki lallan nan?”watace “yayi kyau sosai gobe idan an d’aura na dubasa sosai tunda sbd ni Akayishi ko? nidai Allah babu ruwana”kuma shine ka hana Ayi dinner ko?”ta fad’a cikin shagwab’a “salfad bakyajin rarrashi ko?”banaso pictures naki suyita yawo a social media “nasan da Anyi dinner pics za’a yita mana”Ina kishin ko wane kara biti ya kallemun ke”shikenan na fahimta”to wai meyasa tunda nazo bakiyi murmushi ba?”turo baki tayi murmushi na sub’uce mata”shima d’an murmushin yayi yace”kinga gobe kamar haka And’aura ko?”nidai bara na zuba maka Abinci “no fira zamuyi irinta masu Aure…..tasaki kukan shagwab’a tana juya masa baya”kinga ya Isa haka na dena tunda bakyaso”my shagwab’ab’biya”nasan dai gobe zansha shagwab’a ko?”k’in mgn tayi ta sakko k’asa ta zuba masa Abincin”yana ci yana kallon ta yana shak’ar k’amshin turarukan jikinta”saida aka kira sallar la’asar sannan yatafi da nufin da dare yadawo”saidai bedawo ba da daren sbd busy da yayi”Adaren ranar mommy da umman madeenah da k’awar mommy suka zauna suna k’ara yiwa Amaan lactures d’in zaman Aure….
washe gari….✍️

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button