Nasarar Rayuwata 33
*Talented writers forum*
*33*
Ayman ango ya iso tare da tawagar Fulani da amaryarsa da Kuma Fauzan , d’aki guda aka warewa Failuzaa a yayinda Ayman kuwa ya shige cikin abokan ango duk da cewa baya son hayaniya da rubibi Amma yayi Hakan ne saboda qaucewa Failuzaa idan bahaka ba zatace lallai d’aki d’aya zasu zauna. Yanzu tana makale dashi kullum Batason yayi Nisa da ita ko kadan gashi saura mako biyu su shiga camp a Abuja zaiyi camping kafin ya wuce Lagos inda yake son ayi posting nashi already ana aiki akan hakan, baby tana ganin matar Ayman ta dauke Kai ta gaida Fulani kawai ta Kara gaba ita har ynxu Bata cire ran auren Ayman ba. An fara programs anyi kamu anyi walima washe gari ne daurin auren donhaka gidan SGF a cike yake makil da jama’a, ma’aikata kuwa sai Kaiwa da komawa suke Babu zama Ammi ana fama da jama’a irin yadda take so wato manyan mata sun cika gidan nata sai annashuwa take Babu dangin mijinta ko d’aya a gidan suna can masaukinsu. Malam Sule Yana ta mamakin wannan lamarin suna hira da maigadi yace ” wato masu kudin nan dai sun more wallahi , dubi yadda Ake almubazzarancin abinci kamar Babu gobe talaka na fama da rayuwa Wani na Neman ma sakawa bakin salati bare a wannan zamani da muke ciki komai yayi tsada ” maigadi ya gyara zama “ai kadan ka Gani Ina gayamaka bari a daura auren kaje wajen dinner kaga iKon Allah, toh ba y’ar gidan mataimakin shugaban kasa zai aura ba Kuma mace uwar yarinyar minister ce kwanaki aka Bata mukamin ” “iKon Allah…toh..kace kogi ne aka karawa ruwa, ga sakataren Gwamnatin kasa , toh Allah ya Basu zaman lafiya” hmm Amin dai Amma irin wannan auren baya qarko ” Kai dai ka musu fatan alheri” hmm malam Sule bakasan halin masu kudin nan bane..Kai ashe wancan basaraken yayi aure zuwansa gida ” wanne kenan” malam Sule ya tambaya ” wannan d’ayan matashin da nace Maka Dan sarkin kasar waje ” toh toh..wannan yaron kirkin zakace ai kwanaki…” Malam Sule zo mana don Allah ” Dad ne ya fto ya katse musu hirar ” barka da fitowa ranka ya dade ya jama’a Allah yasa a gama lafiya ” “Ameen don Allah abinci nake so a Kaiwa Yan uwana can area 8 ” toh ranka ya dade a bani address” zaku tafi da tanimu yasan gidan zai nuna Maka ” “toh shikenan Allah ya taimaka ” daga haka hirar ta katse.
Ansha biki bayan daurin aure anyi reception hadadde Wanda kasar gaba d’aya ta shaida saboda gidajen TV da radio duk hirar ake, angama taro lafiya amarya ta tare a makeken gidanta dake wuse 2 parakou street. Yau Ayman ya dauko inna zai kaita wajen fulani, inna ta shirya cikin shiga ta alfarma atamfa ce doguwar Riga me stones daga sama har kasa ta saka hijab milk color sai qamshin humra takeyi. Fauzan ke Jan motar Ayman na gidan gaba inna tana baya daga ita sai karamar wallet sai wata bakar leda dake dauke da karamar bucket din turaren wuta sai wata leda cake da fruits danginsu ayaba lemu kankana da abarba, tafiyar 40 minutes yakaisu maitama new extension horn Fauzan ya danna malam Sule ya tashi ya Bude gate a wannan lokacin hankalin inna na bisa waya. Yayi parking suka fito Ayman ya Bude mata kofa ta fito Fauzan yazo ya karbi ledojin Ayman na gaba inna na biye dashi a baya suka karasa cikin gidan.
Ammi na hakimce a falo tana waya sai dariya take suka shigo da sallama ta gyada musu Kai nan ta Kalli inna kallon sama da kasa ta cigaba da wayarta, Ayman yace ” Bismillah innata zauna bari na kira Umma tana ciki ga mom din Aman ” inna ta zauna tana Kara jinjina lamarin tun bayan Ayman ta nemi alfarma tazo ta gaisa da mahaifiyarsa sai yanzu tagane meyasa halayensu ya banbanta ashe abin daga iyaye ne, masu aiki suka shigo suka ajiye mata ruwa da kayan motsa Baki bisa umarnin Ayman . Bayan kamar minti 5 sai gashi ya fito ya zauna kusa da inna ” kiyi hakuri tana nan fitowa ” murmushi inna tayi har ynxu Ammi waya take amma rabin hankalinta na kan inna ko daga Ina take irin wannan bare baren da Ayman yake akanta. Sallamar Fulani ne ya ratsa falon mace kyakkyawa Mai natsuwa da Kamala she is so calm kamar Ayman din, inna ta amsa cikin Sakin fuska “barka da zuwa innar yarima ” ta fada a yayinda take zama bisa kujerar dake fuskantar inna ” barka hajiya kinzo lafiya ya gajiyan biki Allah ya Sanya alheri” Ameen ya rabbi nagode ya gida ya yaran ” lafiya Alhamdulillah” “Ina yawan Jin labarinki wajen yarima har Ina mamaki , shi wannan yaron Bai taba shakuwa da kowa ba idan kika cire Fauzan wallahi Koni mahaifiyarsa baya sakewa dani sosai Amma sai gashi Yana bani labarin yadda kuke Masha Allah nagode sosai” murmushi inna tayi tace ” ai da nakowa ne Kuma idan ka gane halinsa da abinda yake so ai shikenan, shi wannan asalin halittarsa ce Bai Faye hayaniya ba sai hakuri” murmushi yayi Yana kallonsu har cikin zuciyarsa Yana Jin inna ta zame masa tamkar mahaifiya saboda matar akwai ilimi ga Kuma sanin ya kamata . Inna ta katse shi da cewa ” Ina amaryar taka ko sai na roka a nunamin ita ” murmushi yayi ya snkuyar da Kai Fulani na dariya tana Jin dad’in yadda inna take masa lallai akwai shakuwa tsakaninsu, Ammi sai yanzu ta kashe wayar ta Kalli inna ” sannu da zuwa” yawwa ya gajiya ya hidiman biki Allah Sanya alheri ” Ameen amma fah banganeki ba ” kafin inna tayi magana Fulani tayi caraf tace ” uwar dakinsa ce ” uwardaki? Shi Ayman da baya magana har Yana da wata uwar d’aki?” Murmushi yayi yace” ba uwardaki kadai ba malama ta ce don har karatu tana koyamin tana da ilimin addini sosai inajin dad’in karatunta ” tabe Baki Ammi tayi tace” wace unguwa kike malama ” Ayman yayi caraf yace ” Apo take ” toh Fadi baa tambayeka ba ai naga tana da Baki sai ka bari ta amsa min ” sunkuyar da Kai yayi nan Ammin ta tashi ta bar musu falon, sauke numfashi Fulani tayi tana kallon inna tace ” kiyi hakuri baiwar Allah haka take Bata da sakewa da jama’a” lahh ai Babu komai wallahi ” waya Ayman yayi ya kira Failuzaa akan ta samesa a falo. Suna dan taba hira da Fulani yawanci hirar akan Ayman ne har Failuzaa ta fito cikin shiga ta alfarma ta risina ta gaida Fulani sannan ta nemi wajen zama , Ayman yace ” Baki ga bakuwa ba bazaki gaisheta ba ” ta juya idanu ” ohh.. sorry ban kula bane Ina wuni ” lafiya ” inna ta amsa Bata Kara komai akan hakan ba Ayman yaji Wani iri Fulani ta Kalli Failuzaa ta kada Kai batayi magana ba, inna ta tashi tace ” toh ni zan wuce Allah ya Sanya alheri ya Bada zuria dayyaba ” Ameen mungode sosai malama Allah ya Bada Lada ” Ayman ya tashi yace ” Umma bari mu sauketa gida ” my prince Nima zan bika please” “koma ciki Babu inda zaki ” kafin ta sake magana yasa Kai ya fice , inna tayi sallama da Fulani tabi bayan Ayman ta fice. Fauzan na ganin fitansu ya Bude mota Yana horn malam Sule ya wangale kofa suka fita Allah Bai bashi iKon ganin inna ba. Cikin mota Ayman Yana bawa inna hakuri tace Babu komai , har suka sauketa suka juya inda take sanar dashi zancen daurin aurenta da zaa daura a Masallaci ya tayata murna sukayi sallama suka tafi. A cikin gida inna take ba maman Nana labarin abunda ya faru tace ” gaskiya wannan mahaifiyar Aman ba mutuniyar kirki bace Kinga Wani kallon banza da takemin bayan ta karemin kallo gaba d’aya, Allah ya tsare hajjo da auren wannan yaron” “Allah ya kyauta dama masu kudi ba kowa ke son talaka ba malama , Allah ya Bata miji nagari Wanda yafisa ” “Ameen ” haka suka cigaba da hirarsu.