Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 19

Sponsored Links

By Khaleesat Haiydar 19…… Ikram ta buge hannunsa cikin tsiwa tace “meye kke wani rufe kofa” shaqeta yyi yana mata wani mugun kallo yace “me ke kawo ki gidanmu?” Ikram ta fasa wani shegen Ihu tana kwala ma Anty kira, dai dai lkcn da Aliyu da Mami suka hauro sama, Aliyu yyi kofar Khaleel da sauri don har lkcin ihun take da duk karfinta, bubbuga kofar ya shiga yi yana kiransa jin kofar a rufe, ita kanta Mami duk ta rude, khaleel ya bude kofar yana hararan Aliyu yace “lfya kke neman cire min kofa” Aliyu bae bi ta kansa ba yyi gun Ikram dake tsaye har lkcn ta dage sae kakalo ihu take, durkusawa yyi gabanta a rude yake cewa “me yyi maki Ikram” Mami ma ta karaso cikin dakin da sauri tana kallon Ikram tana jiran jin me xata ce, washe hakora Ikram tayi ganin indomie hannun Mami tace “lah Anty wnn na waye” Aliyu ya fixgota ganin gun Mami ta nufa da saurinta, cikin tsawa yace “baxa ki gaya min ihun me kike ba” ta murguda masa baki ta fixge hannunta tace “kai! Kyaleni” tana fadin hka tayi gun Mami tana kallon Indomin tace “Ammina tana dafa min irin wnn amma guda daya kuma bana koshi” Aliyu ya mike ya shake Khaleel a fusace yace “uban me yasa ka rufe kofa, kuma ihun me Ikram ke yi” Khaleel ya shaqesa shima a fusace yace “ubanka yasa na rufe kofar, ci ka ni kar nayi loosin temper na” Ikram ta yo waje da ido ta ja hannun Mami dake tsaye tana kallonsu tace “Anty mu tafi ki ban indomiena fada xa suyi” Mami ta ajiye indomien hannunta gaban Madubi tana kallon Khaleel fuskarta a daure tace “cika sa Khaleel kar in saba maka” turasa Khaleel yyi, yyi kofa yana huci Mami tace “dawo nn” dawowa yyi ya tsaya kansa a kasa yana huci, Ikram tayi sum sum ta karasa gaban Madubin ta dauki indomin a hankali ta fice. Aliyu yyi kofa xae fita Mami ta kirasa shima, ba tare da ya juya ya kalleta ba yace “gida xan wuce” yana kai wa nn yyi gaba. Mami tace “to Allah ya kiyaye” ta maida dubanta ga Khaleel tace “ihun me Yarinyar nn take Khaleel?” a fusace ya fara magana “haba mum wnn wace yarinya ce xata dinga shigo ma mutane gida tana takurasu, don Allah kice ta tafi, wllh ban son ganinta, Allah idan na sake ganinta xan ji mata ciwo” Mami tace “to don uwarka ka fitar min da ita idan har gidanka ne nn, ka fita harkarta wllh don ina iya saba maka sbda ita, kaji min mara hankali” tana kai wa nn tayi kwafa ta fice daga dakin, ya dafe kansa yana huci tare da fadawa kan gado, dakinta ta shiga bata ga Ikram ba ta sauko kasa, xaune ta ganta da Aliyu yana bata indomie sae xuba take masa ratatata kmr radio, shi kam sae Murmushi yake, Mami tace “me nace maki Ikram” Ikram tace “kika ce kar in kuma fitowa daga dakin ki, ae ynxun nn xan koma bari ya gama bani taliyar akwae xafi,” Mami ta danne bacin ranta a nutse tace “tashe ki koma dakin kar in saba maki, Allah idan baki jin maganata Ikram baxa mu shirya ba” Ikram ta bata fuska kmr xata yi kuka tana kallon Aliyu, Aliyu na kallon Mami yace “Mami ki bari ta gama cin abincin mana” Mami tana nuna masa kofa tace “tashi ka tafi gidanku kar ka bata min rae Aliyu, ba gida kace xaka ba” Murmushi yyi bae ce komai ba, ta daga Ikram ta dauki kwanon abincin gabanta ta ja ta suka haura sama, Ikram sae waigawa take tana kallon Aliyu kmr xata yi kuka, suna isa daki Mami tace “kar ki sake barin dakin nn, idan ba hka ba xan dokeki” tana kai wa nn ta fice daga dakin, dakin Khaleel ta koma yana kwance yyi rub da ciki, ta xauna gefensa ta kira sa, ya juya yana kallonta, tayi murmushi cikin lallami tace “kayi hkuri Khaleel, Ikram baxata sake shiga sabgarka ba a gidan nn i assure yhu, Aliyu kuma ka daina biye masa kaji son,” bae ce komai ba ta shafa kansa tace “ga abincin ka can na hada maka a dinnin” mikewa yyi ya xauna kmr xae mata kuka yace “to Mami me take yi a gidan nn, wllh ni bana son damuwa tana daga min hnkli dayawa bana ma son ganinta” Mami tayi murmushi tace “kar ka damu baxa ka dinga ganinta ba, ita da xata fara makaranta ma” bata jira me xae ce ba ta fita tana cewa “ka tashi kaje kaci abinci son” bin ta kawae yyi da kallo da mamaki, kai Mami ma dae, ynxu a in ta samo wnn abun tsoron, don Ikram abun tsoro ce a wajensa. Mami na komawa daki ta ga Ikram tsaye jikin kofa tana kuka a hankali har da shessheka ga indomin can taki ci, da mamaki Mami tace “Ikram me ya same ki?” tana wasa da rigarta a hnkli tace “ni gurin Ammina xan tafi” Mami ta jawo ta jikinta da mamaki tace “Ikram nan ma ae gidanku” wani ihu mai ban tsoro Ikram ta sakar mata ta fada kasa ta shiga birgima da shure shure tana cewa it gurin Amminta xa ta, Mami kasa rufe baki tayi don mmki sae kallonta take, dagota tayi ta shiga lallashinta amma kmr tana tunxurata duk ta cika gida da Ihu, hankalin Mami ya tashi, ta dauko wayarta da sauri ta shiga kiran Aliyu,Mami na xaune kusa da ita ta xuba tagumi sae kallon haukan da take takeyi Aliyu ya shigo dakin, jallabiya ce jikinsa yyi gunta da sauri ya dagota yace “me ya sameki Ikram” cikin kuka tace “gurin Ammina xan tafi dare yyi” rungumeta yyi yace to fara min shiru tukunna, ba shiri tayi tsit.
[2/25, 08:17] Zjy: ~Ikraam~

Back to top button