Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 99

Sponsored Links

99……
A hankali Ikram ta sake sa daga rikon da tayi masa ta nutsu, hawaye na ci gaba da gangaro mata tace “wacece Rukayya? Me ya sameta” Khaleel ya kasa dagowa bare ya bata amsa har lkcin yana rike da kansa, wani kukan ta sakar masa tace “ka min mgna mana ya Khaleel ban santa ba” ya dago da kyar idonsa ya kada ssae ya sauko da kafafuwansa daga kan gadon a hankali yace “matar Aliyu” Ikram ta dawo kusa da shi da sauri tace “me ya sameta ya Khaleel” sau uku tana tambayarsa a rude snn a hankali yace “she’s late” tsayawa tayi tana kallonsa helplessly ta kasa cewa komai, ssae ta fashe da kuka ta fada kansa tace “ban gane ba ya Khaleel” bae kuma cewa komai ba ya rungumeta yana lallashinta a hankali, daren ranar basu yi bacci ba gaba daya gidan, har Maryam da bata wani san Rukayyar ba taji mutuwar ta, washegari da asuba suna sllh duka suka ba gidan suka tafi can gida, sun tar da frndx din Mami da dama a falo har da Hajiyar Aliyu, suka gaisa sama sama snn suka nufi stairs a sanyaye, Ikram har ta fara wani sabon kukan har da shessheka, dakin Mami Khaleel ya bude a hankali yyi sallama a sanyaye ya shiga, bbu kowa dakin sae Aliyu dake kwance yana bacci ga roban drip da aka cire yyi rabi sama kusa da shi, kuka ssae Ikram ta saki ta toshe bakinta, Khaleel ya ja ta suka fita daga dakin ya kullo kofar, daya dakin Mami suka shiga suka tarar da ita xaune kan darduma tana jan carbi, momy ma na xaune gefenta da wata aminiyarta, Sudais na kwance kan gado yana bacci an lullubesa, Ikram ta karasa gun Mami da gudu ta fada kanta tana kuka ssae, kasa cewa komai Mami tayi, Momy ta jawo ta jikinta ta shiga lallashinta tana cewa “ba kuka xaki yi ba Ikram Addu’a xaki mata, wnn kukan bae da amfani” juyawa Khaleel yyi ya bar dakin a sanyaye, Maryam ta durkushe inda take ita ma tana hawayen, kan gari ya waye gidan ya cika ssae da Jama’a don har lkcn ba a kai Rukayya ba kuma gawar na nn gidan Mami, Ammi da yayarta da Shatu ma duk sun iso da safen, ynda Ikram ta dinga kuka sae ka rantse kace ta taba shiri da Rukayyar ne. Karfe takwas aka kai Rukayya gidanta na gskya bbu wanda bae yi hawaye ba, duk ynda Abba ya so Mami ta bari a tado Aliyu yyi mata Addua ko ma baxae iya binsu ba amma taki bari a tada shi wae daga baya xae je sbda ynda taga condition dinsa, bbu ynda ya iya da Mami hka suka tafi, bbu wanda bae yaba da halin Rukayya ba don mace ce ta gari mai hkuri da kirki, sae kusan karfe sha biyu Khaleel ya sami damar xaunawa da Maminsa yake tambayarta ko rashin lfya Rukayyar tayi, Mami tace “hatsari suka yi jiya da daddare a hanyarsu ta dawowa daga kaduna wae” da kyar bayan yan mintoci Khaleel ya iya cewa “ita kadae ta tafi kadunan” Mami tace “A’a har da Aliyun amma ita ke tukin, shima ya bugu a kai ina ga ta ynda na naga yanayinsa, but anjima idan mutane suka ragu xan dubasa, shiyasa ma ban bari an tada sa daxu ba” Khaleel yace “amma sudais bae ji ciwo ba ko” Mami tace “shima sae na dubasa don yana ta koke koke tun jiyan” hawaye ya cika idon Khaleel ya dafe kai yace “to Allah yaji kanta yasa ta huta, idan namu ya xo muma yasa mu cika da imani” Mami tace “Ameen Ameen” karfe biyu saura Mami ta tada Ikram dake bacci jikinta ta koma kan gado, Ikram ta mike tana mitsike ido ta koma kan gado Mami ta tashi tace ma su Momy tana xuwa snn nufi dakinta gun Aliyu, har lkcn bae tashi ba, ta xauna gefensa kan gado tana kallonsa, ta daura hannunta kan goshinsa ya bude ido a hankali yana kallonta, ta dan sakar masa murmushi tace “ka tashi ne dama son” bakin kofa taga yana kallo, ta juya da sauri ta ga Ikram tsaye bakin kofar tana hawaye, ya dauke idonsa wajen ya shiga kkrin mikewa xaune, ta rikesa da sauri tace “aa kayi kwanciyarka son, ko kana son wani abu ne” juyawa Ikram tayi da sauri ta bar dakin, Aliyu ya daura kansa kan kafar Mami a hankali yana hawaye, Mami ta dago sa da sauri tace “haba, ni fa ban son hka Aliyu, kai baxa ka dauki faith ba baxa kayi tawakali da Allah ba, Rukayya ba wnn take bukata daga gare ka ba pray 4 her my son, ka gaya min ina ke maka ciwo ynxu” kansa kawae ya nuna mata, ta mike tace “to koma ka kwanta” ya koma da kyar ya kwanta, ta dauki waya ta kira jummai tace ta kawo mata cup din tea, snn ta nufi show glass din allurori da magungunanta ta bude.
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikhram~ By Khaleesat Haiydar

Back to top button